Showing 42001 words to 45000 words out of 92772 words
Chapter 15 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
gani in akwai abinda za'a yi" Umma ta fad'a tana kallon Baba. Baba da ya gama saka takalmi yace, "in aka d'auko sarki d'ori ke zaki biya shi?."
Umma ta buɗe baki tana kallon sa shima yana kallon ta yace, "Nidai bazan biya ba in zaki biya yanzu za'a tawo dashi."
Umma tace, "Shikenan azo dashi sai na biya d'in."
"Zab'i mai kyau, kuma kin san dai biyan da tsada tunda gida zai zo sai ki tanadi kud'i."
"Zan bayar ko nawa ne."
Ya k'are mata kallo yace, "Da uwar kud'in ki a k'ugu amma asahana in ta kare sai a turo min yaro" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo kawai.
Ba jimawa ya shigo yace, "ku gyara gashi mun zo dashi" ya fad'a yana komawa suka shigo tare aka shiga d'akin Umma ya fara duba k'afar Rauda da take zaune.
Mai gyaran k'afar da yake kusa da Rauda yana duba k'afar ta ya kalli Umma da Baba da kuma Inna yace, "Akwai sauran gyara a k'afar nan tata dole sai dai ayi mata aiki." Baba yace, "Aiki kuma?."
"Eh aiki Baba, amma kuje asibiti ayi hoton k'afar a kaiwa likita shi kuma zaiga inda za'a gyara sai ya fad'i kud'in ku biya." Umma ta girgiza kai tace, "to kuma zata iya tafiya?."
"Eh zata iya amma sai dai a bata sandina guda biyu, inda dama yanzu kuje asibitin ayi gaggawar duba k'afar tata in ba haka ba zai zama silar da za'a ce zata nakasa gabad'aya."
Baba yace, "to mun gode." Fita yayi Baba ya kalli Umma yace, "ke kina da kud'in zuwa asibitin ne?." Umma ta girgiza kai a raunane tace, "bani dashi. Suke nan na hannuna kuma na bayar yanzu." D'an k'aramin tsaki yaja ya kawar da fuska gefe yna jin haushin ciwon nata kawai za'a saka shi kashe kud'i kafin ya fita. Inna tace, "abu kad'an zai zama sanadi." Umma tace, "Allah ya yaye." Rauda dai tana jin su jikin ta yayi sanyi ta tabbatar ta rasa k'afar ta kenan sabida tasan kud'in aikin da za'a fad'a babu mai kud'in da zai iya biya.
Baba ya dawo yace, "ta tashi ta d'auki sandinan muje yanzun." Ba musu Umma da Inna suka kama ta ta tashi aka bata sandinan nata tana tafiya dasu a hankali har suka fita suka ga taxi Baba ya taro aka kwantar da ita a baya Umma ta rab'a ta zauna Baba ya shiga gaba suka tafi. Wajan hoton k'afar suka fara zuwa suka hau layi abin mamakin Baba baiyi k'yashi ba ya bada kud'in akayi hoton suka shiga asibiti wajan likita. Tun safe suke zaune har azahar layi bai zo kansu ba duk sun gaji da zama gata ita kuma a kwance tunda k'afar ba kwari tayi ba.
Bayan azahar layi yazo kan su suka shiga duka su ukun aka bawa likitan hoton yana kalli hoton sosai ya gama Nazarin duk abinda yake jiki ya juyo ya kalle su bayan ya gama dubawa yace, "Akwai wani k'ashi da ya tsage a k'afar ta yanzu kuma nama ya shiga tsakiya jini ya shiga sosai dole sai anyi aiki zan cire an had'e wannan k'ashin." Baba yace, "to kuma aikin yana kaiwa nawa?." Likitan yace, da yake bani zanyi aikin ba amma dai gaskiya yana kaiwa miliyan d'aya da dubu d'ari biyu koma yaje miliyan biyu. Aikin babba ne gaskiya dan ba'a jima da fara yin sa Nigeria ba Egypt ne da Germany da India kawai suke yin sa." A tare gaban su ya fad'i suka kalli juna Rauda idanun ta tuni sun wanke da hawaye Umma tace, "Tabd'ijam."
Likitan yace, "kuma gaskiya in ba'a yi wannan aikin ba tafiyar ta baza ta dawo ba sai dai ta cigaba da tafiya da sanda ko kuma kujerar marasa lafiya wheelchair kenan kamar yadda take yi yanzu, aikin ya zama dole." Baba yayi shiru kawai baice komai ba kafin likitan ya kuma cewa, "Wannan magungunan dana gani a katin ta da take sha tun a baya ta cigaba da shan su suna da kyau sosai zasu taimaka wajan rage mata rad'ad'i." Su dai babu wanda ya tanka jiki a sab'ule suka fito har suka koma gida babu wanda yayi magana.
Umma ta kalli Rauda da ta jingina da bango tayi shiru tace, "kiyi Hak'uri Rauda taki k'addarar kenan rasa k'afar ki, kiyi hak'uri dan wannan kud'in bamu da hanyar sa kinfi kowa sani." Rauda ta goge ido tace, "babu komai Umma a hakan ma na gode Allah wani fa ko k'afar bashi da ita ni na samu ina takawa, nafi wasu da dama a duniya." Umma ta share idanun ta bata ce komai ba Baba ya shigo yace, "to kunji dai yadda mukayi kun sani bani da wannan halin koda ina dashi ma gwara nayi jari da dai na bawa wani banzan likita gwara mu kafa jari a gidan, Rauda sai kiyi hak'uri taki jarabawar kenan." Kai kawai ta d'aga kawai bata ce komai ba zai fita tace,
"Baba magungunan sun k'are wancan lokacin ma kud'in rabi aka bashi Khairi ta karb'o wajan Bala mai pharmacy." Ya juyo ya kalle ta yace, "Wannan lokacin ma kije ya baki bashin in bazai bayar ba a hak'ura bazan iya siyan maganin dubu hamsin ba wallahi."
"Yanzu haka za'a zauna babu maganin kenan? Ina kud'in da aka bata a asibiti?" Umma ta fad'a tana kallon sa.
Ya juyo ya kalli Umma yace, "ki danne ni ki kwata in ta k'arfi ce" yana fad'a ya fita Umma ta bishi da kallo ta girgiza kanta tace, "Sam mahaifin ku yafi damuwa da kud'i akan lafiyar ku, bai damu da lafiyar mu ba gabad'aya kud'i kawai. Zan iya rantsewa yana da fin dubu d'ari kawai bazai iya bayarwa bane gani yake asara ce."
Rauda batace komai ba dan bata ga laifin Baba ba hakkin siya mata magani akan wanda ya kad'e ta yake gashi ya nakasa ta tana zaune babu ruwan sa babu abinda aka isa ayi masa kuma.
Tuna hakan sai ta fara kuka Umma tace, "kiyi hak'uri Rauda." Tace, "Umma yanzu kenan wandaya kad'e ni ya yiwa banza kenan? Gashi ya nakasa ni na rasa k'afata amma shi yana can gidan su hankalin sa a kwance bai sake waiwayo na ba, meye ribar masu kud'i da suke irin wannan banzayen halayen...? shin sun manta da lahira ne?."
Umma tace, "Akwai Allah Rauda, kiyi hak'uri hakika an cutar dake amma ki daure k'addarar kice a haka." Hawayen idanun ta ta share ta mayar da kanta ta jingina da bango bak'in ciki da takaici yana shiga zuciyar da jinin ta.
Yamma tayi Ummulkhairi da Khalil dasu Rahma suka dawo Ummulkhairi ta dawo da ciwon ciki Allah ya Umma bata rasa maganin ciwon ciki ta bata tasha Khalil ya fice Ball Rahma ma ta kwaso gajiyar siyar da abinci. Tsiko k'afar ta take mata tunda babu magani ta kwana biyu bata sha ba ta kalli Umma tace, "Umma zanje wajan mai pharmacy d'in nan da kaina ko zai bani maganin." Umma tace, "A'a Rauda keda ba k'afa ba ki zauna ni naje na bashi baki ko zai bamu."
"Zan iya Umma gwara ni naje ki zauna" ta fad'a tana tashi tsaye ta d'auki sandinan ta guda biyu ta tsaya ta saka dogon hijjabi har k'asa ta saka face mask bak'i a fuskar ta.
Umma da take kallon ta cikin tausayi tace, "Ki zauna naje da kaina Rauda ko muje taree." Rauda ta murmusa tace, "Umma babu abinda zai faru zan dawo in sha Allah."
"To kije Rahma ta raka ki ko ki nemi Khalil a waje ku tafi."
"Rahma a gajiye take kinga yanzu ta dawo daga kasuwa in naga Khalil d'in daman dashi zamu tafi."
"Allah ya kiyaye, ki kula sosai Rauda." Ta amsa da amin ta fita tana tafiya a hankali har ta bar gidan.
A waje kuwa taga Khalil ta saka shi a gaba suka tafi a hankali suke takawa har suka zo pharmacy da yake a tsallaken titi suka tsallaka suka shiga, da sallama suka shiga ta zauna akan benci tana haki mai pharmacy ya amsa a dakile yana kawar da kansa gefe. Sai da ta huta sannan ta kalle shi tace, "Ina wuni Bala."
Fuska babu walwala yace, "Lafiya, kud'ina kika kawo nin dai ko?."
Kai ta girgiza kana tace, "A'a Bala maganin nazo a kuma bani."
"Da yake jarin na baban kine ai ko? Dan baki ma da kunya baki da mutunci ina binku kud'i har naira dubu ashirin da biyar kizo kice min wai na kuma baki bashin magani, ga asararre wanda bai san abinda yake yi ba ko?." Ranta ya b'aci sosai amma da yake nema take sai ta tausasa murya ta d'ago ta kalle shi tace, "inda ina da kud'in da zan baka kuma wallahi zan biya ka kud'in ka gabad'aya nan gaba in sha Allah."
"To bazan bayar ba, kuma wallahi ko ki biyani kud'ina ko na kai k'arar ku police station."
Rauda ta kasa jurewa tace, "Dan nazo neman alfarma a wajan ka ba hakan yana nufin ka fad'a min maganar da kaga dama ba."
"Wannan kuma ke ta shafa wallahi sai an biya ni kud'i na, darajar babar ki ya saka nake bada maganin ban gano waye mahaifin ki akan kud'i ba sai bayan na baki magani dan da nasan haka yake wallahi bazan bayar ba. sai an biya ni in ba haka ba nakai k'ara wajan y'an sanda suzo su karb'ar min ta dole." Mik'ewa tsaye tayi Khalil ya bata sandar ta ta kalle shi tace, "Za'a biya ka kud'in ka in Allah ya yarda, kar ka sake kuma ka sake zagin iyaye na in ba haka ba zan nuna maka bani da mutunci nima."
"Ai nasan ki waye bai san sanfurin rashin mutuncin ki ba?, duk zafin kan ki na fiki wallahi dan na dame ki na shanye tuni. Kud'i ne dole a biya; ki daina in Allah ya yarda ai dole ne ma ki biya ni in ba haka ba kuka ga hauka keda iyayen naki." Banza tayi masa ta kalli Khalil zuciyar ta nayi mata ciwo tace, "muje Khalil."
Ba musu yayi gaba tana jin sa yana ta yi mata ihu bata juya ba tana tafiya bata kallon gaban ta bata san tazo kan titi ba sai horn d'in mota taji mai k'arfi hakan ya saka ta tsayawa cak ta runtse idsnun ta. Motar ta tab'a ta hakan ya saka ta fad'uwa sandinan suka zube katin maganin da yake hannun ta shima ya fad'i. Da sauri Khalil yazo wajan ta yana k'ok'arin d'aga ta yace, "Sannu Anty baki ji ciwo ba?."
K'ok'arin mik'ewa take taji kwarjini ya mamaye wajan lokaci guda, sanyin khamshi da zazzafan izza da k'asaita ta bayyana a wanan mai d'auke tsantsar nutsuwa da kamewa. Tsayuwar mutum da inuwar sa take ji a kanta hakan ya saka ta d'ago kai ta kalle shi idanun su suka had'u dana juya ta wara idanu tana k'are masa kallo shima kallon idanun ta yake dan iya shi kawai yake gani ta rufe sauran da face mask.
Saurin janye idanun ta taji jin wani abu kamr shocking da kwarjini yana ratsa cikin jijiyoyin idanun ta, jikin ta yayi sanyi lokaci guda taji baza ta tab'a iya jure cigaba da kallon sa ba ta dole ta janye idanun ta. A b'angaren sa shima hakan take zagayayyun idanun ta da ya kalla na wasu mintina sun masa kama da wanda ya sani amma kansa ya kasa tuna a inda ya san su hakan ya sama shi zuba mata ido yana so ya tuna.
"Kai dan Allah shine ka buge min Antyna bayan wani ya kad'e ta ta karye ya daina zuwa ya duba ta ta koma wayo da sanda, yanzu ma fa wajan mai magani muka je dan bamu dankud'i shine har da zagin Baban mu yace bazai bada maganin ba" Khalil ya fad'a kamar zaiyi kuka yana kallon Asad da yake tsaye a kanta har lokacin.
K'okarin mik'ewa take yi Khalil yana so ya rik'e ta amma ta kasa Asad da ya gama sauraron abinda Khalil yace ya dawo da kallon sa gare ta yaga tana kiciniyar tashi amma ta kasa, a hankali ya tsuguna a gaban ta khamshin turaren sa ya sake kawo mata ziyara cikin hancin ta ta runtse idanu gaban ta na fad'uwa ya kama kafad'un ta duka biyun ya mik'ar da ita tsaye, Khalil ya bata sandinan ta ta tsaya cak har lokacin kala baice ba.
"Na d'auka iya mugunta da rashin sanin darajar d'an adam ka sani ashe ka iya taimako....?. A waccan ranar ka mare ni na k'yale ban tanka ba sabida akwai abinda nake jin tsoro a gidan bawai dan ina jin tsoron ka ba. Kana da kud'i ko mulki duka basa gabana indai mutum ya tab'a ni nima sai na tab'a shi dan bai fini daraja ba, mutum shi nima mutum ce. Sa'ar ka guda ni nasan darajar d'an adam da babu abinda zai hana na wanke maka taka fuskar da mari kamar yadda ka mari tawa, banbanci na dakai kenan na fika tarbiyya da sanin ya kamata, amma koda nan gaba kasan irin matan da zaka dinga wulak'antawa domin ni da kake gani na nafi k'arfi suya sai dai babbaka" ta k'arasa fad'a tana kallon gefe domin bazata iya jure kallon saba shima yana kallon ta cike da mamakin kalaman ta.
Baki yake so ya bud'e yayi magana amma ya kasa cewa komai sai kallon ta kawai da yake yi tana zazzaga masa rashin kunya yana jin ta yana kuma kallon ta, sai da ta kai aya sannan ya kalli Khalil yace, "a ina kuke?" Ya fad'a cikin muryar sa mai taushi da ratsa zuciya. Gabanta taji ya fad'i jin kamar ba waccan muryar bace.
Muryar Khalil taji yace, "A unguwar Katsalle muke." Kallon ta yayi sai ya kalli Khalil yace, "Muje."
"Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni Rauda na shiga motar wanda bai san darajar d'an adam ba sai kansa kawai ya sani Allah ya kiyaye ni. kaje can ka k'arata kai kad'ai tunda ku y'ay'an manya da y'ay'an masu mulki baku san kowa ba sai y'an uwan ku masu mulki. Dan kana d'an sarkin garin nan baka isa ka saka ni nayi abinda banyi niya ba, bada hak'uri ya gagare ka akan buge ni d'in da kayi a yanzu me zai kaini shiga motar ka?" Rauda ta fad'a cikin masifa lokacin hijjabin ta yake ja baya har tabon sallar dake goshin ta ya bayyana.
A wannan lokacin suka tsallaka bai juya ya kalle ta ba bai kuma bar wajan ba amma kalaman ta sun tabbatar masa ta tab'a had'uwa da Aliyu ne yadda ta zayyano abinda ya faru yasan tabbas Aliyu ta gani take tunanin shine, katin maganin ya gani a k'asa ya d'auka yana kalla kafin ya juya sai yaga har sun b'ace masa, numfashi ya sauke ya shiga mota zuciyar sa na bugawa, kallo inda suka bi yake yi zuciyar sa na fizgar sa zuwa wani tunani daban ya runtse ido ya kunna motar ya buɗe idon sa ya ja ya bar wajan.
*tofa fan's an gamu fa.*🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*013.*
Rai a b'ace Rauda ta shiga gida Khalil ya taimaka mata ta ajjiye sandar hannun ta ta zauna a kan farar kujerar da take tsakar gida shi kuma ya zauna a k'asa. Yanayin ta Umma ta kalla tasan an tab'o ta kuma tasan bazai wuce akan maganin ba hakan ya saka tace, "ko baki ce ba nasan ya hana ki maganin ne shiyasa kike kunbura fuska, sai kiyi hak'uri." Rauda tace, "daga neman taimako Umma sai ya zage ni? Har yana cewa da yasan halin Baba tun farko bazai bada bashi ba."
Umma ta murmusa tace, "ban ga laifin sa ba Rauda; yanzu kafin wannan kud'ad'e masu tarin yawa su fito daga hannun baban ki a shekara goma a fama. Yayi k'ok'ari fa da ya baki ma dan ba kowa ne zai bada magani mai tsada kamar naki ba, Allah yasa baki masa rashin kunya ba dan ya taimaka miki." Shiru tayi bata amsa ba Baba da yaji komai ya shigo yana fad'in,
"In ma tayi masa rashin kunyar ita ta jiyo ai ita k'afar zata damu da ciwo sabida rashin magani bani ba." Shiru sukayi dukkan su kafin Khalil yace, "Umma wani kyakykyawa kamar balarabe ya kusa kad'e Anty yanzu har sai da ta fad'i k'asa." Umma tace, "Kuma dai?."
"Amma ai bata ji ciwo ba ai. Umma ta yi masa rashin kunya yace muzo ya kawo mu gida tak'i kuma baki ga motar ba babba" ya fad'a yana fad'ad'a hannayen sa alamun girma.
Baba da yake alwala a durk'ushe furzar da ruwan bakin sa yace, "A koda yaushe ke ai bak'in halin ki yake ja miki alkhairi yake tsallake ki ya koma kan wanin ki. inda kin shiga motar da bai siya miki maganin ba." Umma tace, "Rauda akan me zaki masa rashin kunya? Meyasa ke baka jin kunyar yiwa babba rashin kunya ne?." Rauda tace, "Umma nifa ba rashin kunya nayi masa ba na fad'a masa abinda yake raina ne. shine wanda nace miki ya mare ni lokacin da na raka su Habiba gidan sarki shine na amayar masa da abinda yake zuciya ta a lokacin ban samu dama ba ina jin tsoron doki ya hana ni mayar masa."
Umma ta wara idanu tace, "D'an sarkin Katagum guda masu ji da kud'i da mulki kika yiwa rashin kunya Rauda?, Yaron da an masa shaida bashi da kirki ina ke ina shi?, in ya saka aka yi miki wani abun fa?." Rauda ta turo baki gaba tace, "To Umma dan yana d'an sarki sai yayi min abinda yaga