Showing 36001 words to 39000 words out of 92772 words
Chapter 13 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
dame ni da waya?."
Asad ya zauna yana sauke numfashi yayi masa banza ya kalle shi ganin hakan sai ya tab'e baki ya cigaba da aikin danna laptop d'in sa.
K'aramar yarinya ce ta shigo doguwa mara jiki mai kyau wacce zata kai kimanin shekaru takwas ta shigk ya kalle ta yace, "Amani kawowa masa drinks." Ba musu ta k'arasa kitchen ta kawo ruwa da lemo har da cake ta ajjiye sannan tace, "morning uncle." Jin hakan sai Asad ya bud'e ido ya kalle ta yayi murmushi amma baice komai ba ita kuma ta wuce ciki.
"U no Zaid i can't believe that beautiful girl is your own daughter" Asad ya furta a hankali yana kallon Zaid. Idanu ya d'ago ya kalle shi ya tab'e bakin sa ya shiga ba da aikin laptop kafin yace, "ka fad'a min meke tafe dakai ina da aikin yi. Ka ishe ni da waya kamar wanda yake bina bashi, kuma wallahi kar ka saka min larabci a maganar ka."
Nan ma banza Asad yayi masa sai ruwan da ya sha sai kuma Zaid ya kalle shi ya d'auki wayar gefen sa ya kira aka d'auka yace, "Precious Asad is here, please make him some breakfast" yana fad'a ya kashe wayar ya ajjiye a gefe.
Ba jimawa sai ga ta ta fito da k'aton tray a hannun ta sanye da hijjab har k'asa ta k'araso ta ajjiye a kan center table zatayi magana ya d'aga mata hannu ya mata alamun da ta koma kar tayi masa magana, murmushi tayi ta girgiza ta wuce shi ta koma ciki. Asad da yake kallon sa shima murmushin yayi kafin yace, " is that really you Zaid." Murmushi shima yayi ya kalle shi yace, "Ai naga sarautar kake ji dashi kar tayi magana kayi mata banza like yadda ka yiwa Amani bazan d'auka ba" ya fad'a yana kallon sa.
Tea d'in yasha hankali kwance babu tunanin an zuba masa wani abun sai da ya gama ya kalle shi yace, "friend Hameed fa?." Wara hannayen sa yayi alamun oho Asad ya runtse idanu yace,"Daddy fa?."
"Kano" ya bashi amsa a tak'aice.
"You know what friend? i need your help." Kunne ya nuna masa alamun yana jin sa basai ya kalle shi ba. Allah ya sani Asad bazai iya bashi labari ba hakan ya saka shi danna wayar sa yana rubuta masa text dan shima d'in ba mai son magana bane ba.
K'arar shigar message yayi ya kalle shi kafin ya d'auka yana karantawa Zaid ya tab'e baki ya kalle shi yace, "prince Asad, na fad'a maka akwai abinda ya maqale a throat d'in ka, kana buk'atar ayi maka surgery wannan rashin maganar is too much."
Asad yace, "please."
"Can you explain?."
"I can."
Tsam Zaid ya tashi ya yi masa alama da shima ya tashi ya kuwa mik'e suka shiga wani babban d'aki dake cikin falon sai gasu a baban d'akin zane da manyan boards da k'ananu da yawa ga pencils da paints na zane babu adadi a wajan. Zama yayi a kujera d'aya ya kalli Asad alamun ya fara masa bayanin ta.
Asad ya runtse ido yana tuno ta a hankali ya fara fad'a masa yanayin face d'in, Zaid ya zana ya kuma kallon sa Asad kafin ya jawo wata drawer ya d'auko samples na idanun mutane alamun ya nuna masa irin nata, Asad yayi lucky kawai ya zab'a ya saka nuna masa hanci da baki nan ma ya zab'a shi kuma yana zanawa.
Juyo masa da zanen yayi Asad yana kalla yana wara idanun sa ganin sakk irin yadda yake ganin ta a mafarki yadda yake ganin rabin face d'in ta haka ya zana rabin ya kuma k'arasa hanci da baki da kansa. Asad ya kalle shi alamun ya akayi Zaid yace, "Yeah indai har a yadda kayi min bayani fuskanta yake then definitely that's how her face should be seen."
K'arewa face d'in kallo yake amma Asad shi sam bai amince da k'arasawar da Zaid yayi ba kawai babu yadda zaiyi dashi ne amma tabbas saman fuskar nata ne k'asan ne bai amince dashi ba dan haka bai yarda face d'in ta ya fita tasss ba. "Thanks friend" ya furta yana kallon Zaid ya d'age kafad'a yana tashi daga wajan. Tare suka fito hannun Asad rik'e da board d'in.
Zaman kurame suke yi a falon har akayi azahar wata maganar kirki bata had'a su ba sai da Asad yayi azahar har abinci yaci sannan ya kalli Zaid yace, "Yaran ka nawa yanzu?."
"Four, maza biyu mata biyu, sun ishe ni" ya fad'a yana kallon sa Asad yayi murmushi baice komai ba Zaid yace, "Asad soon kai ma zaka tara naka yaran dakai da dream girl d'in ka dan nasan kana son tane. You're in trouble tunda ka bari ka fara soyayya it's not easy and sometimes it's painful."
Asad ya murmusa zuciyar sa na harbawa Zaid yace, "Nan gaba wannan murmushin u can't do it, forget about kai prince ne zata mayar dakai like crazy sai kaji ina ma baka san teste na love ba." Murmushi sosai Asad yayi dan ya bashi dariya shima ya sake yin dariya yace, "Dariya na baka right..? In akace soyayya ina dariya ne nima a baya i thought babu wata soyayya a duniya but daga baya fa...? ina fad'a maka hakan ne saboda ya faru dani kayi addu'a akan yarinyar taso ka idan ba haka ba you're doom wallahi" ya fad'a yana clapping hannun sa yana girgiza kai.
Asad da yake dariya kad'an ya daure cikin muryar sa da take da dad'in ji yace, “Did you think I'm also that type of guys...? actually u are mistaking don't forget who am I."
Zaid yace," well, we shall see.. soyayya dai ba ruwanta da mulki ko sarauta... taqamar ka kai din dan sarki ne u think you're sufficiently akwai ranar da zata zo wanda sarautar da kake taqama da ita da duk abin daka mallaka basu isa su baka wannan soyayyar da kake yi mata ba zaka ce na fad'a maka."
Asad ya mik'e tsaye ya ajjiye kud'i a kan table kana yace, "beside let me remind you one thing, I'm not in love with d girl. A bawa baby ta siyi chocolate."
Shima ya mik'e yace, "fad'ar gaskiyar ka shine abin da saka muka zama friends few years back, and now you're trying to deny the fact. I'm telling u, you go wipe your own tears my friend." Asad ya gaji da magana sosai yana daurewa ne kawai ya lura Zaid ya koyo surutu baice komai ba murmushi zaid ya rako shi har gate driver Zaid ya d'auke shi a mota sukayi sallama ya koma.
Da board d'in da aka zana fuskar yarinyar har cikin motar sa bayan ya sauka daga jirgi yana k'arewa hoton kallon sam bai amince da zanen ba gabad'aya sabida sanin halin Zaid d'in shiyasa bai nuna masa ba, kuma mutum yayi maka abu babu ko sisin ka bai kamata kace masa baiyi daidai ba. Window ya sauke ya cilla board d'in ya bi ta kansa ya wuce zuciyar sa na sake hararo masa kammanin yarinyar dake cikin mafarkin sa.
Yaro dake wasa a harabar wajan ya tsallako da gudu ya d'auki zanen fuskar Rauda sa aka cillar a wajan ya d'auka yana kallon face d'in yana murna ya tsinci hoto kafin ya k'arasa a guje ya shiga mota su bar wajan.
Asad baiyi nisa ba ya ja ya tsaya ya wara idanun sa tuno da yarinyar da suka had'u jiya kamar fuskar tace complete a cikin zanen ya juya kan motar ya koma amma yana zuwa wajan babu board d'in da ya cillar ya daki sitiyarin motar yace, "Ya salam!." Sai kuma ya lumshe idanun sa komai ya tuna kuma ya sake juya kan motar ya nufi Katagum kai tsaye.
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*011.*
Maimakon ya wuce gida samun kansa yayi da nufar gusset house d'in mai martaba da yake hannun sa ya shiga ya faka motar ya shiga cikin gidan, a kan kujera ya zauna yana sauke numfashi a wannan lokacin kiran Zaid ya shigo wayar sa, d'auka yayi dan yasan maganar guda d'aya ce ya ya sauka kuma daman abinda ya tambaya d'in kenan. Ajjiye wayar yayi yana kallon wani waje daban kafin ya kulle idanun sa hoton ta yana gifta masa a idanun sa.
Tuno fuskar da aka zana masa yayi ya tuno fuskar yarinyar da ya taimakawa a bayyane yace, "Akwai kama sosai, kenan suna da relation?." Sai kuma ya dafe kansa a zuciyar sa yace, _Why Asad meyasa wannan zai dame ka?, kawai dream ne fa ba gaskiya bane, ka manta da wannan tunanin ko zaka samu peace of mind._ numfashi ya sake saukewa a bayyane yace, "but why nake ganin ta a mafarki always tana taimako na?."
Sai kuma ya mik'e tsaye yana fad'in, "ya kamata na nemo wannan yarinyar" Sai kuma yaja ya tsaya ya kama k'ugu ya fad'a kan kujera ya zauna yana furta, "Oh Asad!" Ya dafe kansa yayi shiru yana sauke numfashi a hankali tunanin yake barin ransa ya runtse idanun sa yana goge fuskar ta mafarki da wacce aka zana masa a hankali suke barin idanun sa yana ajiyar zuciya.
Ya jima a haka sosai har magariba tayi a nan yayi sallah kafin ya mik'e ya d'auki key da wayar ya fita ya shiga mota ya fita daga gidan.
Baiyi gida ba babban company sa ya wuce ya tarar da Hafiz yana ta kai kawo har lokacin ganin sa ya shigo ya saka shi bin bayan sa zuwa office suna zama Hafiz yake cewa, "Asad what happened?." Bai bashi amsa ba yayi shiru ya jawo laptop d'in dake kan table d'in gaban sa yana dannawa. Ganin hakan sai Hafiz ya bar shi ya fita bai jima sosai ba ya fita daga office d'in yaja motar ya fita gabad'aya.
Gida ya wuce kai tsaye wajan Mama ya shiga kasancewar magariba ce bai same ta ba Suhaima take sanar dashi tana d'aki ya shiga wajan Hydar yana nan kamar yadda yake koda yaushe ko hannun sa baya motsawa yayi masa addu'a ya zauna a kan kujera yana kallon sa. A nan ya kwashe lokaci da yawa har i'sha tayi ya fita yayi sallah ya sake dawowa a nan ya ga Mama a wajan Hydar ya k'araso gaban ta ya tsuguna da girmamawa yace, "Barka da dare Mama."
"Ina kaje yau?" Ta tambaye shi ba tare da ta amsa ba. Kallon ta yayi sai kuma ya d'auke idanun sa wannan tun yana ganin wani abu kan tambayar nan da Mama take masa ta ina kaje, ina zaka, me zakayi in ka fita, wa ka tambaya har ya daina ma domin ya saba.
"Naje Abuja" ya bata amsa a tak'aice. Bata ce komai ba tayi jim kafin tace, "yaushe zaka je wajan Jidda kasan dai ita zaka aura ko?." Kallon Maman yayi baice komai ba tace, "in baka ce ba nasan ai ka jini, nan da lokaci kad'an za'a d'aura muku aure ta." Kai ya girgiza kafin yace, "Mamaa......" Sai kuma yayi shirun jin hakan sai tace, "kar kace min baka sonta ko baku dace ba, itace zab'ina ya zamar maka dole ka sota." Kai ya jinjina alamun gamsuwa kafin ya mik'e jikin sa a sab'ule ya fita.
Sallama akayi aka shigo falon ana fad'in, "y'ar sarki, jikar sarki, matar sarki, babar sarki kuma k'anwar sarkin garin Kano in sha Allah." Jin muryar tasan wacece k'anwar mai martaba kenan Rabi'a kaf cikin dangin mai martaba tasu ce tazo d'aya suna shiri sosai ta juya ta kalle ta ta fad'ad'a murmushi tace, "babbar bak'uwa." Murmushi tayi mai sauti itama ta k'araso tana fad'in, "Zaman kujera ya gagare ni ni Rabi in dai har gimbiya na zaune a kai." Kan Mama ya sake fashewa izzar ta ta ninku ta saki murmushin k'asaita tace, "keda kika b'uya ko ganin ki ba'a yi."
"Yanzun ma dole ce ta saka na taso nazo domin naji abubuwa suna ta faruwa marasa dad'in ji." Mama ta sauke numfashi tace, "bari kawai Rabi'a komai yana neman lalace min lokacin da ban shirya ba."
"Shiyasa nazo ai naji ya akayi hakan take faruwa."
"Sharrin Hajiya ne, itace ta bama Asad guba a ganye yaci." Murmushi Tayi tace, "Zata aikata ai, in kince badaqalar da suke yi da waziri kare bazai ci ba. Waziri yayana ne amma bazan b'oye miki ba baya son ki baya son me son ki, kinga dashi da galadima dama kawai suke jira a kan ki su kawar da y'ay'an ki sabida a lalata maki goben ki."
"Na sani takwara, na sani. Duk abinda suke yi a kan idanuna suke yin sa. Nan Suhail fa ya kira Suhaima yana bata wani abu wai ta bawa Asad na tsarin jiki ne, kiji rainin wayo da y'ar uwar sa yake son yin amfani yaga bayan sa." Tace, "shiyasa dana tashi tawowa na biya wajan malamin nan na karb'o garin magani da rubutu, kinga lamarin Aliyu ma wallahi saka masa hannu akayi haka Hydar ma. Asad ya gagare su ne kawai sabida ibadar sa amma shima zasu iya nasara a kansa nan gaba tunda ya kasance mai rauni ta wani fannin."
Mama tace, "ta b'angaren yarda da mutane Asad yana da rauri, ta b'angaren magana Asad yana da rauni. Amma fa wani abun kwantan b'auna yake yi kallon kowa yake kawai bar shi da rashin maganar sa. Amma wani lokacin in yayi wani abun sai ki d'auka Aliyu ne." Mama Rabi tace, "na sani, namijin duniya kenan kallon su yake yi ta wani b'angaren na san da hakan. Ga rubutun da maganin ko wanne da bayanin sa akwai na Asad akwai na Hydar dana Aliyu harda Suhaima."
Mama ta ja ledar kusa da ita tana dubawa tace, "ai yanzu ma zan tashi na shafawa Hydar nasa dan wancan lokacin rubutun da kika kawo aka shafa masa yayi amfani sosai."
"Mai martaba baya aiko da nasa?." Mama tace, "Da kansa yake zuwa ya bashi kin san gidan ya yake baya barin kowa yazo da kansa yake zuwa, shi da Asad kuma kin san ai ba'a jin sirrin su."
"Haka ne. Wai kuwa Rukayya da Sa'adatu sun zo duba Hydar kuwa?." Mama ta tabe baki tace, "Sun zo."
"Ki dai kula da Sa'adatu zata iya goga masa wani abun a hannu ko a k'afa wallahi." Murmushi tayi tace, "na sani fa rasss nake kallonta." Mik'ewa tayi tace, "ranki ya dad'e ki shafa masa zan shiga ciki na dawo." Kai ta girgiza kawai ita kuma ta fita.
*Bayan Kwana biyu.*
Babu abinda ya ragu ta b'angaren harin da ake kawowa Asad bai kuma fasa addu'a ba mafarkin da yake kullum k'aruwa yake, tunda aka zana masa fuskar ta kuma sai ya koma ganin fuskar a mafarkin amma yak'i bari mafarkin yin tasiri a zuciyar sa yana k'ok'arin mantawa dashi koda yaushe. Fuskar ta ta zama masa tamkar hoto a idanun sa da ya kulle sai ya hango ta hakan ya saka yake jin wani iri a zuciyar sa.
Hydar na kwance har lokacin amma an samu cigaba dan zuwa lokacin yana motsawa alamun ya kusa farfad'owa kenan.
A zaune take a babban d'akin ta wanda aka k'awata shi da kayan gado na alfarma waya na hannun ta, kamar wacce aka tunawa ta danna number Dr ta kira shi bata jima tana ringing ba ya d'auka yana fad'in, "Allah ya ja da ran Mama."
"Ka sallami yarinyar nan kuwa ko tana nan?" Bata amsa gaisuwar ba abinda ta fara tambaya kenan. D'an dabarbarcewa yayi kana yace, "Na sallame ta Mama."
"In ka min k'arya na gano gaskiya kai kasan sauran."
"Ba k'arya nake ba tun lokacin na sallame ta."
"Ka kyauta. In Hydar ya farfad'o kasan sometimes yakan manta wasu abubuwan na baya sai daga baya ya tuna in ya manta batun ta koda zai tambaye ka bana so ka sanar dashi kace komai bai faru ba ka gane ko?."
Kamar yana gaban ta ya girgiza kai alamun to kafin yace, "zanyi in sha Allah." Bata kuma cewa komai ba ta yanke wayar yabi wayar da kallo yana sauke numfashi. "Wannan mata masifaffiya ce, ta yaya zan iya sallamar Rauda bayan har yanzu bata ji sauk'i ba?. In kuma na barta ta gano na shiga uku." Tsaki yaja ya mik'e ya tafi d'akin da Raudan take ya same ta a zaune tana karatun alkur'ani a bayyane. kallon ta yake da birgewa domin da wuya yazo ya same ta haka kawai bata karatu ko lazumi.
Sallama yayi ta katse karatun ta kalle shi tace, "Dr shigo mana." Umma da bacci ya fara d'aukar ta ta mik'e zaune ya k'araso ya tsaya yana kallon k'afar tata yace, "Ya k'afar?."
"K'afa da sauk'i yanzu bata min ciwo ai sai dai gajiya da zama." Ya sauke numfashi yace, "Rauda kud'in wanda ya kawo ki asibitin nan ya k'are kuma shima yana kwance babu lafiya tun zuwan sa na k'arshe nan shine na rasa yadda zanyi." Gaban Umma ya fad'i itama Raudan haka ta rufe alkur'anin tace, "To sai mu koma gida."
"Eh ko kuma ku biya kud'in."
Umma da take gefe tace, "mu biya me likita? Ina muka ga wannan halin?, gwara dai mu koma tunda Allah yayi k'afar tayi kyau."
Jikin sa sai yayi sanyi ya sauke