Showing 21001 words to 24000 words out of 92772 words

Chapter 8 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17678

ce, bayan ya gama ya shiga wajan Mama ta kalle shi tun kafin yayi magana tace, "Ina kaje d'azu?." Da girmamawa yace, "naje wajan wacce na buge ne."
"Kaje kayi mata me? Ba ka bada komai Dr zai mata meye naka na zuwa inda take?." Shiru yayi Bai amsa mata ba tace, "Sunan ta Rauda iyayen ta talakawa ne suna zaune a unguwa Katsalle tana saida abinci a kasuwa meye naka da zaka dinga zuwa inda take?, wannan ba kalar wacce zaka je dubawa bace Hydar, zubar da kima ne a ganka a wajanta!, Tunda ka bar komai hannun Dr kar ka sake waiwayon ta kayi mata iya k'ok'arin ka."


Kallon mahaifiyar tasa yake da zallar mamaki jin har ta binciko komai a kanta daga jiya zuwa yau kuma wai ya daina zuwa inda take tsakani da Allah ai babu adalci a cikin abinda tace shi kuma bazai iya ba, baice komai ba sai daga baya yace, "In kin min izini zan fita." Ta kalle shi da hannu tayi masa alama haka ya fice taja dogon tsaki tana fad'in, "meye nasa na damuwa akan wata banza y'ar talakawa oho?, har na tsani yarinyar" ta fad'a tana yarfe hannun ta tana tab'e bakin ta.


*GRA.*


Su biyu ne kacal a zaune a falon Sadiya da y'ar ta Jidda suna zaune suna tattaunawa kamar koda yaushe Jidda tace, "Mum u mean zan mallaki Asad matsayin miji na?." Sadiya ta murmusa tace, "of course Jidda, nan kusa bada jimawa ba zaki zama mallakin sa."
"Wow!" ta furta tana juya idanun ta cikin jin dad'in abinda Mum d'in tace. Murmushi mahaifiyar tata tayi tana kallon ta tace, "Wannan kyauwu naki Jidda ai sai sarki, d'an sarki, jikin sarki ne zai d'auka."
"But Mum kina ganin zaiamince?, kin san halin sa fa kamar ba mutum ba."
"Babu abinda zai hana ya amince, yana jin maganar Maman sa fiye da tunanin ki, ko wuta ta nuna masa tace ya shiga zai iya shiga kuma ke kin san yadda take jin maganata ko ta iyayen ta bata ji, duk yadda zanyi sai nayi wajan ganin kin shiga cikin gidan nan matsayin matar sa. Wallahi zan iya k'arar da komai nawa wajan ganin hakan ya tabbata."


Jidda bata ce komai ba Mum ta kuma cewa, "da sannu zan kwace duk wani jin kai da take ji dashi ya dawo hannun ki, da idanun ta zata kasa sarrafa d'an ta sai abinda muka ce shi zaiyi, tana muryar d'an ta zai zama sarki ne ni kuma ina murnar zaki mallaki sarki, zata kasance mahaifiya a gare shi zaki kasance mata a gare shi, duk wani sirrkan sa zai dawo tafin hannun mu daga nan Rabi'atu ta gama yawo."


Murmushi Jidda tayi kyawun ta ya sake bayyana kana kallon ta kasan asalin iyayen ta ba hausawa bane tace, "Mum tana son Asad sosai fa, kina ganin zata bada wata dama kuwa?."
"Nice damar ai Jidda sai abinda nace mata ke kin sani, duk wannan zafin kan da take ji dashi sai na sauke mata. Kin san wahalar da nasha kafin na mallake ta kuwa...? Na kashe kud'i ban san adadin su ba wallahi. Akwai tarin abubuwan da tayi min a baya na tabbata ita ta manta amma ni ban manta ba, kwantan b'auna kawai nake mata so nake ki mallaki Asad a nan zata gane wacec Sadiya."
"Mum indai mallakar Asad ne lokaci ya kusa ai, ina so ma naje gidan na gaida ta."
"Hakan yana da kyau Jidda, kije gobe ki wuni a can ki samu ku keb'e keda Asad duk da baya magana kiyi k'ok'arin ganin kunyi magana dashi."


Shiru Jidda tayi Mum tace, "zan baki turare ki shafa a jikin ki duk wanda ya shak'i shi sai ya rikice Jidda." Dariya tayi tace, "da alama kin gama shirin ki Mum."
"Murucin kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya, lamarin Rabi'atu ba abu bane mai sauk'i ta wuce inda kike tunani. Kar take kallon kowa kanta na mugun ja sai da dabara da wayo zaka gano lagwon ta." Bata ce komai ba ta cigaba da danna wayar ta amma zuciyar ta cike take da farin cikin zata zama mata ga Asad kyakykyawa, mai aji, mai nutsuwa, mai kud'i, mai ilimi kuma sarki d'an sarki.


*◇◇◇*
K'asa-k'asa take magana kai da kaji kasan duk abinda ake fad'a babu gaskiya a cikin sa tana fad'in, "ka tabbatar Suhail ya saka layar a k'asan kafitar sa?." Daga can b'angaren yace, "na tabbatar domin inda bai saka ba Suhail bazai min k'arya ba."
"Amma kasan ni bana son long process nafi son ayi abu a gama kawai a wuce wajen."
"Ki kwantar da hankalin ki zancen da nake miki ma mai martaba ya jinkirta bayar da kujerar zuwa nan da wani lokaci."


"Kai kamar baka san halin sa ba?, kwantan b'auna zai mana lokaci d'aya sai dai mu wayi gari muji ana bugawa Asad tambari, nifa in ba gani nayi an kawar da Asad ba hankali na bazai kwanta ba."
"Ki kwantar da hankalin ki in abun bai yu ba a wannan karon zamu nemi master planer......."


"Master planer!? Wacece Master planer?" Ta fad'a da mamaki tana jiran amasa. Murmushi yayi mai sauti yace, "Zaki Santa in lokacin hakan yayi, ita take tsara komai kuma yake tafiya yadda ya kamata, in abu ya gagare ni ita nake nema, ta wuce duk tunanin ki ta dame ki ta shanye a hatsabibanci, ta wuce tunanin ki da hankalin ki, in kika ji shirin ta sai kin san naki ba komai bane ba."


Hajiya tace, "wacece ita?, a ina take?, meye alaqar mu da ita...?."
Waziri yayi murmushi yace, "kamar yadda na fad'a miki zaki santa in lokacin yazo amma banda yanzu, ki cigaba da zuba idanu tabbas a kwanakin nan za'a wayi gari ace azo a fitar da gawar Asad, ki rubuta ki ajjiye na tabbatar da wannan" yana gama fad'ar hakan ya yanke wayar ba tare da ya jira yaji me zata ce ba tabi wayar da kallo zuciyar ta na hasaso mata Master planer amma ta kasa gane wacece.................


*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023.


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*007.*


Bayan sallar juma'a aka samu kiran gaggawa daga mai martaba duka iyalan gidan hatta matan da suke gidan mazajen su sai da aka kira su aka taru a fadar cikin gida duk wani da ya kasan jini a gidan sai da aka kira shi. Dukkan su suna zaune ana sauraren abinda mai martaba zaice kowa yayi mamakin kiran.


A kamalance da k'asaita da zallar nutsuwa da hikima ya fara fad'in, "kamar yarda na saka a kira ku nasan da yawan ku kuna tunanin lafiya akayi kiran gaggawa haka kasancewar bai tab'a faruwa ba. Ba wani abun bane an kira ku ne akan murabus da nace zanyi a d'ora Asad." Kallon kallo aka shiga yi dukka mutanen wajan gaban su na fad'uwa matuk'a burin kowa yaji k'arshen maganar.


"Babu batun ta a yanzu mu janye, amma nan da wasu kwanaki maganar zata dawo matuk'ar ina raye kuma abinda nace baza'a canja shi ba, in kunga abinda na fad'a bai faru ba ku tabbatar k'asa ta rufe fuska ta." Shiru fadar take ko masu kirari babu kasancewar magana ce ta cikin gida su kad'ai babu damar magana kuma sai ya bada dama. Fuskokin mutanen dake wajan zaka kalla zaka hango zallan farin ciki akan abinda yace, fuskar Mama ce kawai a d'aure cikin akasin farin ciki amma bata ce komai ba.


"Bana son na sake jin wata magana akan wannan na yiwa tufkar hanci, in lokaci yayi komai zai bayyana amma banda yanzu." Nan ma shiru suka kuma yi kafin yace, "Akwai wanda yake da magana a cikin kuz?." Shiru akayi babu wanda yace komai sai daga baya babar y'a kaf gidan mai Maimuna wacce taci sunan mahaifiyar mai martaba ake kiran ta da Mummy tace, "Allah yaja da zamanin mahaifin mu, Allah ya kare mahaifin mu a duk inda yake. Hukuncin mai martaba shine hukunci a ko wanne lokaci, babu mai magana a cikin mu."


Kai ya girgiza kafin yace, "Kowa zai iya tafiya." Kai k'asa sukayi da kansu a tare dukkan su suka furta, "A tashi lafiya." Dukkan su suka fita kowa ya nufi b'angaren sa zuciyar kowa fari kar sab'anin Mama da take cikin mayuwacin hali.


Tunda ta shiga b'angaren ta take zagaye hankalin ta a tashe ta matuk'a ta kasa zama sai kai kawo take, ta d'auki waya hannu na rawa ta kira Sadiya tana d'auka tace, "Sadiya akwai matsala babba."
Daga can b'angaren tace, "Ranki ya dad'e me ya faru?."
"Mai martaba ya janye batun murabus d'in sa haka kawai babu wani dalili."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Ranki ya dad'e munyi sake gaskiya, duk yadda akayi wani abun aka yiwa mai martaba kuma ya shiga jikin sa. In fulani zata tuna akwai wanda zasu shiga su fita wajan ganin an tarwatsa mana abinda muka saka a gaba."
"Shiyasa nace miki ina buk'atar zuwa Kano, dole ne na shiga garin Kano a kwanakin nan, babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da mulkin Asad, babu shi ko waye" tana fad'a ta yanke wayar hannun ta na rawa ta kira Asad.


Yana zaune yaga kiran ta daman yasan sai Mama ta neme shi ya d'auki wayar baiyi magana ba ya sauke daga kunnen sa ya tashi ya tafi b'angaren nata, can ciki ya shiga inda ya kasance babu mai shiga sai su yana shiga kafin ma yayi magana tace, "a tafiyar da kuka yi dashi me kuka tattauna har ya canja shawara lokaci guda?." Ya d'ago ido kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin hakan sai ranta ya sake ya b'aci tace, "bazan lamunci wannan shirun naka ba Asad! Ka fad'a min kaine kace masa baka ra'ayi?."


Kai ya girgiza alamun a'a kafin yace, "wallahil azim Mama bamuyi magana irin wannan dashi ba, ki amince dani bazan yi k'arya dan na kare kaina ba" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'asa. remote ta d'auka tayi jifa dashi ya tarwatse a wajan tana wuci tace, "koma dai meye Asad baka isa kak'i karb'ar mulkin nan ba indai ina da rai, Asad kaine zaka mulki garin nan babu wanda ya isa ya shiga tsakanin ku da mulkin nan, dole ka cika min burin." tana fad'in hakan ta wuce zuwa d'akin ta tana fad'in, "A shirya min tafiya gobe zan wuce Kano." Kai ya girgiza sai da ta shiga ciki sannan ya juya ya fita zuciyar sa gabad'aya babu dad'i ko kad'an.


A falon Hajiya iyalan ta zagaye suke da ita maza da mata y'ay'an ta kowa ka kalla zaka hango zallar farin ciki a tare dashi barin ma ita da take ta murmushi ita kad'ai alamun hak'ar ta ta cimma ruwa. Wayar ta da taji tana k'ara ya sakata ta mik'e ta shiga d'aki ta barsu a wajan ta amsa wayar tace, "Abu kamar wasa yana ta zama gaske, sai ga mai martaba da kansa ya janye batun nan."
Waziri yace, "Na sha fad'a miki ki kwantar da hankalin ki komai fa a hannun mu yake amma duk sai ki bi damu kan ki."


Murmushi tayi mai sauti tace, "yanzu meye abu na gaba?."
"Master planer tace mu had'u dake waje d'aya zamu tattauna."
"Yaushe zaka shigo to?."
"Zan shigo zuwa dare." Murmushi tayi tace, "Allah ya kai mu" tana fad'ar hakan ta yanke wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane.


*◇*
Amaryar Sarki Hajiya Rukayya wacce ake kira da Ammi a gidan itama tana zaune da nata iyalan babban d'an ta namiji mai suna Nazif a shekaru bazai wuce shekara sha hud'u ba ya kalle ta yace, "Ammi ni na rasa ganewa kamar kina goyan bayan sarautar Asad?." Murmushi tayi ta kalle su dukkan su tace, "To meye nawa da zanki goyan baya Nazif? Kai dai a musulunce baka kai minzalin jan ragamar al'umma ba to meye abin tayar da jijiyoyin wuya akan hakan?."


Babbar y'ar ta mace mai suna Zainab wacce ake kira Yaya Zainab tace, "kin huta Ammi, koma waye zai mulki garin nan mudai burin mu ya kasance alkahiri a gare mu da kuma garin." Wacce take bin ta tace, "Shine kawai fatan mu amma ni banga abin tayar da hankali a lamarin nan ba. Asad kuma kaf gidan nan babu mai kirkin sa kawai shi rashin maganar sa ce illa amma kowa yasan halin sa ga san y'an uwan sa baya lakari da yanayin gidan namu kowa na sa ne. Duk da Mama bata son yana sauraren mu amma shi ko a jikin sa, ga ilimi da kud'i a hannun sa."
Ammi tace, "Allah ya kyauta" duk suka amsa da amin suka cigaba da hirar su gabad'aya maganar mulkin katagum bata gaban su su kam.

Hydar da Aliyu da kuma Asad ne a zaune a b'angaren su babu wanda yake yiwa d'an uwan sa magana dukkan su waya ce a hannun su suna dannawa hankalin su a kwance, waya Hydar ya d'auka ya kira Dr ya sake tambayar sa jikin Rauda ya tabbatar masa da komai daidai. Asad ya dafe kansa da yake mugun ciwo yana yatsine fuskar sa. Hydar ya kalle shi yace, "Deaf ya dai?." Yatsine fuska yayi yace, "nothing" yana fad'a kawai ya tashi ya shiga d'akin sa ya kulle k'ofar ya zaga baya ya bud'e varanda yana kallon harabar gidan ana ta hidima da shige da fice.


Allah ya sani baya k'aunar mulkin da ake son k'ak'aba masa ga jifa da yake sha tun daga fara maganar sarautar nan yake ganin mutane da yawa wanda baiyi tunani ba a mafarkin sa ina ga an bashi sarautar?. Burin sa kasancewa a madina ba'a Nigeria ba a can yake burin yin aiki kuma burin sa ya cika amma Mama ta hana.


Lumshe idanun sa yayi mafarkin da yayi a jiya ya dawo masa kansa ya wara idanun sa yana k'ok'arin tuno fuskar yarinyar da ya gani ta taimake sa a mafarkin amma ya kasa, furzar da iska yake yi jikin sa na kyarma hankalin sa ya tashi ji yake gidan gabad'aya yana juya masa sam baya son zama a cikin sa, duk yadda yaso daurewa kasawa yayi ya fito ya d'auki makullin mota ya fita har lokacin Hydar da Ali suna zaune.


Hydar ma fita yayi aka bar Aliyu a zaune yana ganin fitar su ya mik'e ya shiga d'akin Asad yana k'arewa d'akin kallo kamar yana neman wani abun a ciki. Babba ne d'akin sosai komai fari ne a d'akin hatta tiles d'in d'akin fari ne labulaye carpet komai fari ne a d'akin, fari kuma tass babu alamun daud'a a tare da ko ina sai khamshi da yake yi. tab'e baki yake yana girgiza kai yana hasahen abinda ya kamata yayi a d'akin kafin ya fita daga d'akin.


Hydar yana fita asibitin ya koma a lokacin Umma ce kawai a ciki ya shiga da sallama ta amsa tana kallon sa yace, "Sannu Mama, ya mai jikin?."
"Da sauk'i gata bata farka ba har yanzu." Kallon ta yake yi ya runtse idanu ya rasa dalilin da ya saka gaban sa yake fad'uwa in ya kalli fuskar ta sai yaji wani abun yana shigar sa ya rasa meye.


"Allah zai bata lafiya."
"In sha Allah, ban san sunan ka ba."
Murmushi yayi kad'an yace, "Aliyu suna na" ya fad'a yana ajjiye kud'i a gefen gadon ta ya fita bai kuma cewa komai ba. Kallon kud'in take yi ganin su da yawa a zahiri bata tab'a ganin mai yawan su ba balle kuma ta rik'e ta yunk'ura zata d'auka kenan Baba ya shigo.
Idanun sa akan kud'in suka fad'a ya k'araso yana fad'in, "Ikon Allah wannan abin arzukin fa" ya fad'a yana k'arasowa wajan ya d'auki kud'in yana kallo.


Kallon sa Umma tayi lokacin da yake juya kud'in tace, "Wanda ya buge Rauda ne yanzu ya fita shine ya ajjiye kud'in."
"Tooo!" Ya fad'a da murmushi a kan fuskar sa yana sake kallon kud'in.


Tab'e baki tayi tana kallon sa ya zuba kud'in a aljihu yace, "To shi wanne irin mai kud'i ne haka?."
"Ban sani ba" ta bashi amsa a tak'aice tana kallon wani wajan daban.
"Allah sarki daman in arzuk'i zai same ka sai Allah ya kawo silar faruwar sa, sai gashi silar arzuk'ina yazo ta hanyar hatsari" ya fad'a yana cigaba da murmushi ya saka hannu ya dafe kud'in.


Shiru tayi kawai bata ce komai ba tayi tagumi tana kallon Rauda da take bacci har lokacin bata farka ba. Fita yayi yana ta dariya ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai har ya b'acewa ganin ta.
Fitar sa ba jimawa sosai Rauda ta farka rad'ad'in azaba ya kawo mata ziyara ta runtse idanun ta muryar ta bata fita tace, "Wayyo Allah!" Abinda tace kenan tana hawaye.
Jin hakan ya saka Umma tasowa da sauri tana fad'in, "Rauda sannu kin tashi?." Kai take juyawa tana fad'in, "Umma k'afana!, k'afa Ummana!!, zafi take min zata cire" ta fad'a tana kuka sosai ga kanta na mugun ciwo.


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, sannu Rauda, Allah ya baki lafiya." Kuka take sosai Umman ma sai ta fara hawaye tana rik'e hannun ta tana fad'in, "kiyi hak'uri Rauda, kiyi hak'uri." Bud'e k'ofar akayi aka shigo Umma ta kalli wanda suka shigo taga likita ne da Hydar likitan ya kalli Umma yace, "yaushe ta farka Mama?."
Sai da ta goge idanu tace, "yanzun nan."


"Rauda sannu, me yake miki ciwo yanzu?" Dr ya fad'a yana kallon ta.
"K'afana,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login