Showing 3001 words to 6000 words out of 92772 words

Chapter 2 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17676

kafin ka samu mai irin ta sai ka tona. Dak'yar yake taka k'afar sa sabida sarautar da ta gama ratsa jijiya da tsokar jikin sa, kamar yana tausayin k'asa haka yake tafiya bakin sa na motsawa a hankali yana furta kalmar da ta zame masa jiki a koda yaushe wato Astagafirullah.


Zubewa ake ana gaishe shi sai dai ya kad'a kai ko ya d'aga hannu amma magana koda motsa bakin sane baya yi sai lazimin da yake yi, Ba jimawa ya k'araso k'aramar fada yasan tabbas mahaifin sa yana ciki ya shiga da sallama cikin muryar sa da bata fita sosai.


Ga mamakin sa mahaifin nasa baya nan sai dogarai da alama bai jima da tashi ba, "barka da shigowa Yarima mai jiran gado, barka da zuwa magajin masarautar katagum, Allah ya tsare mana kai, ya kare ka daga dukkan makiyan ka, takawar ka lafiya......" D'aga masa musu hannu yayi hakan ya saka su jan bakin su sukayi shiru ya kalli kujerar mahaifin sa ya kalle su nan take suka gane mai yake nufi cikin girmamawa suka ce, "mai martaba ya shiga ciki" suka fad'a suna sunkuyar da kansu suna yi masa jinjina.


Baice komai ba ya juya yana ji suna kwara masa kirari ya yatsine fuska ya nufi babban falon sa na cikin gidan, da gajeriyar sallama ya shiga mahaifin sa na hango shi annunirin fuskar sa ta bayyana yana zaune su biyu kacal daga shi sai k'anin sa da suke ciki d'aya wanda ya kasance wambai katagum suna tattaunawa, k'arasowa yayi da girmamawa ya gaida mahaifin nasa ya amsa yana fad'in, "Asad zaki na, barka da zuwa."


Murmushi yayi wanda ya k'ara saka fuskar sa annuri da kyau ta fito da zallar k'uruciyar sa amma baice komai ba, wanda yake a zaune shima murmushin yake yace, "Asad ikon Allah." Mai martaba yana kallon sa yace, "ya akayi ne Asad? Akwai wani abun ne?."
Kai ya girgiza kai alamun babu komai yana murmushi amma baice komai ba, "in anjima kazo ina neman ka." Kai ya d'aga kafin yace, "to in sha Allah zan amsa kira."


Mahaifin nasa yace, "Zaka iya tafiya." Ya sake duk'ar da kansa yace, "Godiya nake. A tashi lafiya" Daga haka ya mik'e ya fita suka bishi da kallo kafin mai martaba yace, "Mubarak ya kake ganin ranar dana ajjiye sarautar nan Asad zai iya mulkin nan kuwa?."


Wanda aka kira da Mubarak yace, "zai iya mana ranka ya dad'e, Allah ya ja zamanin mai martaba ai kaf dangin mu Asad shine ya cancanci kujerar sarautar katagum sabida ilimi da halayen sa masu kyau. A madina fa yayi karatun addini suka rik'e shi suka hana shi dawowa sabida tsabar ilimin da ya tara, gana zamani gana addini. Allah yaja da ranka ina jin an manta da cewa Asad shine wanda k'asar Saudia ta yiwa takardar shaida zama d'an k'asa dan akwai basa so suyi asarar sa?."
"Haka ne wambai, amma baka duba yanayin sa na k'in magana, ta ya shugaba zai kasance baya magana da wanda suke k'ark'ashin sa?. Sai abu ya k'ure sannan yake iya furta kalma guda d'aya fa."


Murmushi Wambai yayi yace, "zai koya ne koya ne mai martaba. Allah yaja da ranka ai a haka ma maganar tasa ba kamar daba, tunda ya dawo Nigeria ai yana magana a can fa in ba karatun alkur'ani ba to yana masallacin madina yana limanci." Murmushi yayi mai cike da izza kana yace, "Sai yanzu nake ganin ganganci da nayi wajan furtawa y'an uwana Asad zan barwa mulkin Katagum, tabbas nayi kuskure a wannan b'angaren dana bar abin a zuciyata sai dai aji na aiwatar hakan zaifi."


Wambai yace, "Allah yaja da ranka abinda aka riga aka furta ya wuce, sai dai dole mu dage da taya Asad da addu'a dan wannan maganar da mai martaba ya furta wasu suna nan da ita suke kwana suke tashi burin su bai wuce su samu hanyar da zasu kawar dashi ba dan cikar burin su."


Mai martaba yace, "Nasan da wanann, makusanta na sune suke wannan k'ok'arin na san da hakan. Amma in Allah ya amince babu abinda zai faru sai alkhairi. Dan ma Asad d'in ba baya bane wajan addini da yanzu sun haukata shi. Allah zai kiyaye."
"Da izinin Allah." Daga haka suka canja hirar zuwa wata daban.


A guje ta shiga cikin babban falon jikin ta na rawa sosai ta zube a gaban wata babbar mace mai ji da jiki mara haske sosai tana fad'in, "Allah ya ja zamanin uwar gidan mai martaba, Allah ya ja zamanin ki, Allah ya ja da ranki ya saka ki fi haka, Allah ya albarkace ki da iyalan ki. Ranki ya dad'e" ta fad'a tana mata jinjina hannun ta na k'asa. Kallon ta tayi daga inda take zaune tace, "Ramma lafiya?."
"Ranki ya dad'e yarima mai jiran gado na gani........"
"Duk sanda na sake jin kin kira shi da wannan suna sai na saka an k'ona bakin ki" ta dakatar da ita a fusace.


"Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake, nabi Allah na biki ki yafe ni." Tsaki ta ja sannan tace, "Ina jin ki."
"Asad na gani a k'aramar fada shi da mai martaba sunyi ganawar sirri."
"Ganawar sirri?" Ta fad'a tana mik'ewa zaune sosai tana kallon ta.


"Na tabbatar ranki ya dad'e, domin daga shi sai wambai a ciki ko dogarai babu, kuma ya jima a ciki kafin ya fito." Jinjina kai take yi kafin ta mata alamu da hannu taje ta mik'e tana godiya ta fita. Tashi tayi tsam ta shiga cikin d'akin ta ta d'auki waya ta kira number Waziri.


Duka biyu aka d'auki wayar yana d'auka tace, "Kana da masaniyar ganawar sirri da mai martaba yayi da Asad?." Daga can b'angaren yace, "Bani da masaniya, meya faru?. Waye ya kawo miki wannan labarin?."
"Na tab'a kawo maka mara tushe ne?."
"Baki tab'a ba."
"Nifa kwata-kwata bana son mulki yaje hannun jinin Rabi'atu, tana yi mana kallo y'ay'an talakawa dan kawai ta kasance jinin sarauta, da zarar d'an ta ya zama sarki tabbas mun shiga uku zaman gidan nan sai ya gagare mu, dole nida kai mu san abin yi domin kuwa Asad ne kawai burin ta shima mai martabar shine burin sa ya zama dole muyi maganin sa."


Dariya wanda ta kira da Waziri yayi yace, "Ina raye, ina numfashi, ina da wayo, ina ji, ina gani, ina da lafiya, wani bai isa ya mulki masarautar katagum ba face ni. Nine na dace kuma nine zan yi, babu wanda ya cancanta sama dani. Rabi'atun banza da wofi balle wasu y'ay'an ta?, ki bar ni dasu zaki ga yadda zan b'ullowa lamarin matuk'ar ina raye karagar nan tafi k'arfin ta!?."


"Haka kake cewa koda yaushe amma ka kasa yin komai, da zafi-zafi ake dukan k'arfe amma kana barin sa yana wucewa, tun kafin mai martaba ya furta maganar murabus kake fad'ar haka yau gashi har ya riga ya furta ya kuma ambaci sunan Asad, da zarar an tabbatarwa da Asad mulki nida kai dole mu bi babu yadda zamuyi. A daina d'aukar lokaci in za'a yi kawai ayi bana son a dinga mayar da hannun agogo baya." Daga can b'angaren yace, "ki bani lokaci Asad bai isa yayi mulki ina da rai ba, yaron akwai tsari a jikin sa sosai dama kad'an nake so na samu nayi masa shigar sauri, zamu gani za kuma muji, kema kuma zaki gani" yana fad'a ya yanke wayar tabi wayar da kallo tana sauke numfashi zuciyar ta tana tafasa cike da bak'in ciki da b'acin rai. A shirye take da ta salwantar da duk abinda ta mallaka wajan ganin jinin Rabi'atu bai mulki katagum ba, zata iya salwantar da rai da lafiyar wani domin burin ta ya cika.


*☆☆☆*
K'aramin gida ne kana kallon sa kaga gidan talakawa wanda basu dashi yanayin sa da komai nasa ya nuna zallar talakawa ne suke rayuwa a cikin sa, ko a yanayin unguwar kasan ta masu k'aramin k'arfi ce amma tana da babbar hanya wanda mota zata zo har k'ofar gida. Daga cikin gidan tsakar gida ne mara girma duk turb'awa ko arzuki siminti babu sai d'akuna a tsakar gidan guda uku sai d'akin girki da kuma band'aki. "Rauda! Rauda!! Rauda!!" Gajeren Dattijo mai duhun fata da farar furfura ya ke fad'a yana shigowa gidan.


Maimakon mutum d'aya ta fito kamar yadda yake fad'a sai mata uku suka lek'o, biyu daga d'aki d'aya guda d'aya kuma daga wani d'akin daban. A hankali ta tako ta k'araso inda yake ta durk'usa tace, "Baba gani." Kallon ta yake cikin harara yace, "uban me ya hana ki fita wajan waccan yaron mai mota da yake son ki?." Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa ganin hakan ya saka shi ya fusata yace, "ba magana nake miki ba?."


D'ago idanu tayi ta kalle shi kafin tayi magana yace, "ke ba kyau ba amma ki dinga wulak'anta manyan mutane masu kud'i irin wad'an nan? Dan kin samu zasu d'auki irin ki....? a ka'ida a mai aikin gidan sa zaki je amma yayi miki adalci yana so ya d'auke ki matsayin mata kike ja masa aji, ina aji a wajan talaka..? Nace miki ina aji a wajan talaka...?." A hankali tace, "Baba kayi hak'uri."
"To tashi kije ki ku tattauna bana son jan magana." Bata musa ba ta mik'e taja mayafin ta a kan igiyar shanyar da take tsakar gidan ta saka takalmi ta fita.


D'akin da mata biyu suka lek'o ya kalla sai suka koma ya ja tsaki yace, "haka dai, ke munafuka y'ar ki ma munafuka." Rauda lokacin da ta fita ta tarar da wanda zuciyar ta ta bata tabbacin ganin sa a tsaye a jikin motar sa yana facing gidan su. Yana hango ta ya saki murmushi sab'anin ita da face d'in ta take a cushe ba walwala ko kad'an ta k'araso tace, "Ina wuni."
Sai da yayi murmushi sannan yace, "lafiya lau Rauda, ya gida da mutanen gidan?."
"Lafiya."
"Kiyi hak'uri na saka Baba ya fito dake."


Bata bashi amsa ba daman yasan hakan yayi murmushi yace, "Ina son ki Rauda, Ina burin ranar da zaki ce min kema kina sona" Bata ce komai ba ta kalle shi tace, "Sai anjima." Har zata juya yace, "minti d'aya Rauda." Cak ta tsaya ya zagaya mota ya d'auko leda k'arama ya dawo ya mik'a mata yace, "ga tsaraba babu yawa." Kallon ledar tayi ta kalle shi tace, "na gode" daga haka ta juya ta shiga gida ko waiwayen sa batayi ba.


A kan idanun Baba komai ya faru tana shiga soron gidan ya yi mata dak'uwa yace, "uban me yasa baki karb'a ba?." Kamar zatayi kuka tace, "Umma ta hana ni."
"Keda Umman ba nine a gaba da ku ba? Dallah malama koma ki karb'o, ka ganar min yarinya y'ar bak'in ciki."


Idanun ta yayi rau-rau zatayi kuka tana kallon sa yace, "in baki koma ba sai na fyad'a ki da k'asa, ka jimin yarinya mai bak'in ciki, zaki koma ko sai na b'alla ki?." Juyawa tayi hawaye na zubo mata ta kalli inda motar take taga babu shi alamun ya tafi ta sauke numfashi ta juyo ta dawo ta kalli Baban tace, "Ya tafi."


Harara ya banka mata ya ja tsaki yace, "a nonon uwar ki kika tsotsi bak'in ciki dan ni kam ba haka halina yake ba, na rantse da Allah duk ranar da kika sake aikata wannan kuskuren sai ranki ya b'aci. Banza mummanar banza da wofi, ke ba kyau sai tsinanan bak'in ciki da mugun hali. Duk wanda ya kwashe ki matsayin mata ya shiga uku." Shiru tayi kanta na k'asa yace, "wuce muje ki d'auki d'anwake ki tafi bakin kasuwa rana tana yi."


Babu yadda ta iya haka ta shiga cikin gidan yana bayan ta ya wuce cikin madafar da kansa ya had'o mata kayan abincin ya fito dasu yace, "D'auki maza ki wuce kar lokaci ya k'ure, kuma wallahi kika dawo kika ce min baki siyar ba duk inda zaki nemo kud'i sai kin nemo kin kawo min, domin ke bak'in halin ki har akan kayan sana'a ta yake." Umman ta da ta fito daga d'aki tace, "Malam dan girman Allah ka daina d'orawa yaran nan tallah, yaran nan sun girma sun kai munzalin aure maimakon ka tura su makaranta sai ka dinga basu talla.....? Nace maka ni ka barni zan siyar maka a gida amma kak'i, gani kake kamar baza'a siya ba, tura yara talla kamar su Rauda ba komai zai jawo ba sai lalacewar rayuwar su."


Da kallo yake binta har ta kai k'arshe yace, "to uwar iyayi ita y'ar uwar ki bata yi magana ba sai ke?, yaran nan dai nine na tsuguna na haifi kayana ba wani ya haifar min ba, kema da kike tutuyar y'ar kice nine nayi miki cikin ta ko? To ki saka min matsaya a lamarina da y'ay'ana na amince da tarbiyayyar dana yi musu, in ma bak'in ciki kike dan ina samun arzuki da talla sai dai ki mutu." Shiru tayi Rauda ta sunkuya ta d'auki kular da yake mai marik'i ce kuma bata da girma can ta kalli mahaifiyar ta ta da mahaifin ta tace, "Sai na dawo."
"Allah ya kiyaye" Umma ta furta a sanyaye tana kallon ta ta fita daga gidan jikinta a sanyaye.........


*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023.


©️ *Nana Haleema.*


*002.*


Bayan fitar Rauda Umma ta kalli Baba ta girgiza kai tace, "Dan Allah Malam ka daina d'orawa y'ay'an ka talla ka bar mu mu matan ka mu dinga siyar maka kome kake so a gida, tura yaran nan tallah babu abinda zai haifar sai d'a mara ido."
"Kedai kiyi masa amma ni kam gwara a d'ora musu tallan, yadda za'ayi rububin siya a wajan su mu baza'a yi a wajan mu ba. sune y'an mata wani saurayin ko dan su kula shi ma ya siya a wajan su" wacce take fitowa daga d'aya d'akin ta fad'a tana kallon Umma.


Baba yace, "bar ta Asabe ita ai baza ta tab'a ganewa ba shiyasa, indai akace an tab'a mata Rauda shikenan babu zaman lafiya, ko da yake tun lokacin yayyen Raudan ake fama da ita y'ar bak'in ciki ce bata so taga nayi arzuk'i." Murmushi Umma tayi ta kalle su cikin takaici tace, "Amma bakwa gudun wani abun ya faru dasu ta silar tallan da ake basu?, kun manta y'ay'a mata ne dukkan su sun kai munzalin aure?."
Baba ya nuna ta da yatsa yace, "Kinga Binta bana son mugun fata a kan yarana, ina yi musu addu'a ba dare babu rana Allah zai kare min su duk inda suke, kar na sake jin kin furta wata magana mara dad'i a kan su in ba so kike ranki ha b'aci ba." Umma bata kuma cewa komai ba ta koma d'akin ta.


Tana jiyo shi yana fad'in, "kuma wallahi kika cigaba da hure mata kunne akan yaron nan Anas da yake son ta take k'in sauraron sa ki kiyayi hukuncin da zan miki, ban tab'a ganin uwa y'ar bak'in ciki kamar ki ba. Ace y'ar ki ta samu mai kud'i amma ki dinga bari tana wulaƙanta shi....? ita ba y'ar kowa ba ba kuma jikar kowa ba, gata ita ba kyau ba balle ace shi ya gano ya nace amma ki dinga hure mata kunne."


Tana jin sa tayi shiru ta zauna a kan ledar da take shinfid'e a d'akin tana girgiza kai. Lamarin sa kullum sake gaba yake duk da girman da yake cimma masa, indai akan kud'i ne ba sani ba sabo, ko meye zaiyi indai akace kud'i zance ya k'are, tun lokacin baya haka yake gashi shekaru har sunyi nisa halayyar sa tana nan.


Malam Adam haifaffan garin azare ne mazaunin unguwar Katsalle, y'an uwan sa da kowa nasan y'an Azare ne a nan aka haife su a nan kuma suka tashi suke kuma zaune. Yana da mata guda biyu Asabe da Binta y'ay'a kuma yana da goma takwas mata biyu maza, Asabe tana da guda shida biyar mata namiji d'aya, Umma kuma uku mata d'aya namiji shine auta a gidan gabad'aya. Suna zaman lafiya babu laifi wata ran ka gansu kamar y'an uwa wata rana kuma da kaga yanayin su kasan kishiyoyin juna ne. An aurar da mata biyar uku suka rage a gidan, Rauda wacce ta kasance itace babba wanda suka rage a d'akin su sai k'anwar ta Ummulkhairi sai k'anin ta Khalil. D'aya d'akin kuma sa'ar Rauda mai suna Rahma sai k'anin ta Garzali.


Talakawa ne gidan wani lokacin abincin da zasu ci gagarar su yake sai dai kowa ya san abinda zai ci shida y'ay'an sa, mai gidan Allah ya d'ora masa san abin duniya baya jin kunyar rok'o haka baya jin kunyar cewa a bashi, koda sirikan sa ne mazajen y'ay'an sa indai Allah ya had'a su koda a hanya ne da wahala su rabu bai tambayi wani abun ba duk da suma ba masu kud'i bane ba. Tun y'ay'an nasa mata suna nuna rashin jin dad'in hakan da yake yiwa mazajen su har suka gaji domin ba zai daina ba.


Tunda su Rauda suka kammala secondary school suka sauke a islmaiyya ya ajjiye batun karatu daman dak'yar aka k'arasa shi, dak'yar da sid'in goshi da ya hana su cigaba da karatu yace bashi hali suka koma islmaiyya suna hadda shima dan kyauta ce wani d'an siyaya ya d'auki nayi. Shekarar farko aka kori Rahma ita kuma Rauda ta cigaba da yin haddar ta tana sake sanin littafan addini dan Allah ya bata kaifin basira.


Bayan ta kammala hadda a cikin shekara d'aya ta dawo gida sosai ta samu ilimi ta k'aru ta kuma san abubuwa da yawa a fanin addini, burin ta ta zama y'ar jarida amma kuma Baba ya daqile wannan burin nata domin yace bashi da halin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login