Showing 6001 words to 9000 words out of 92772 words
Chapter 3 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
zai kaita jami'a dole ta jinginar da burin ta badan taso ba. Daga nan ya fara dafa musu abinci yana d'ora musu talla su shiga kasuwa su siyar su kawo masa kud'in ya d'aga pillow ya ajjiye dan babu wanda zai ci kud'in koda abinci ne babu a gidan sai dai a hak'ura.
Dangin sa babu wanda bai masa fad'a akan basu tallan nan da yake yi ba amma ya shafawa idanun sa toka yace shifa ya haife su baiga wanda zai dakatar dashi da neman kud'in sa ba dole aka hak'ura aka k'yale shi. Babban yayan Umma babban malami ne a garin kowa ya sanshi har shi sai da ya yiwa Baba magana a kai amma ya nuna shifa y'ay'an sane yana da iko dasu dole aka zuba masa idanu.
Masifar son kud'in sa ya amince ya ajjiye kud'in kar ya ci kar iyalan sa su ci amma zai ajjiye yayi ta kallon kud'in yana jin dad'i a fad'ar sa yace kallon kud'in ma rahama ne, da kansa yake girka musu abinci suna shiga kasuwa suna siyarwa gudun ma kar matan nasa su b'ata masa rai akan hakan shiyasa yake zagewa ya hura wuta ya dafa.
Rauda yarinya ce y'ar shekara ashirin da hud'u bata da wadaccen kyau haka baza'a ce mata mummuna ba ba laifi dai zata shiga kadaran kadahan, tana da farin jinin samari sabida ilimin addinin ta kowa abinda yake kwad'ayi kenan a tare da ita amma bata sauraron su burin ta karatun jarida ne amma mahaifin ta ya hana shiyasa bata kula su musamman masu kud'i Umman ta takan ce mata kar ta d'ora buri a zuciyar ta domin duniyar ta koma kwarya tabi kwarya.
Rauda wayayyiya ce in suna hira da Umma baza kace babar ta bace hira suke sosai suyi shawara kamar yaya da k'anwar ta. Sam Rauda bata da duhun kai in taga abu bata sani ba zata tambayi wanda ya sani ya fad'a mata sabida gaba hakan ya saka take a waye in taci kwalliya ka ganta baza kace yar Malam Adamu bace ba. Tana da kirki da girmama na gaba amma fa bata da kunya in aka tab'a ta, bata bari ko waye yayi mata sai ta mayar musamman a tab'a mata iyaye bata jure wannan.
Duk girman mutum in ya latsa ta bazata bar masa ba sai ta mayar a cewar in babba bai ja girman sa ba dan k'arami yabi ta kan girman nasa ba wani abun bane, Allah bai halicce ta da tsoro ba ko Baba ne yayi wani abun ba daidai ba zata same shi ta fad'a masa sai dai yayi mata fad'an ya gama tunda ta fad'a shinkenan, halitta d'aya take tsoro a duniya shine doki.
Anas ya jima yana bibiyar Rauda amma bata sauraron sa bai gaji ba duk sati sai yazo k'ofar gidan su koda bai ganta ba zai gama zaman sa ya tafi sabida Allah ya d'ora masa k'aunar ta, nutsuwar ta da ilimin ta yana daga cikin abinda yake sake jawo hankalin sa zuwa gare ta, kowa yana kaf unguwar itace mai haddar alkur'ani sau da dama y'an matan unguwar wajan ta suke zuwa tayi musu k'ari abinda yake sake burge Anas kenan da ita. In Baba yana nan ne yake tilasta mata zuwa wajan sa kawai dai ya bata wani abun ya kwace ya ajjiye gobe ma in ya dawo ya sake turata shine burin sa kawai.
*☆☆☆*
Aliyu tunda ya bar cikin gidan sarauta ya nufi wani plat house mai kyau da ya tsaru da falayoyi da fitala masu kyaun gaske, yana zaune a falon yayi shiru yana aikin jan tsaki ba komai ne yake k'ona masa rai ba sai zancen mahaifiyar sa akan Asad, pillow da yake ajjiye a kan kujara ya d'auka ya cillar cikin fushi yana jan numfashi zuciyar sa na mugun tafasa sabida bala'in b'acin rai da bak'in ciki.
Cize lips d'in sa yayi ya koma ya jingina da kujera yana jin d'aci yana tasowa daga cikin zuciyar sa har kan harshen sa yana jin sa. "meyasa komai sai Asad?, meyasa ni ba'a maganar zan yi sarauta sai shi?!" Ya fad'a da k'arfi yana d'aukar remote yayi jifa dashi ya daki bango ya tarwatse a wajan.
"Ya dai prince lafiya?" Wani matashi wanda bazai wuce sa'an sa ba ya fad'a yana shigowa falon yana bin sa da kallo, bai magana ba sai sake runtse idanun sa da yayi matashin ya zauna a kujerar da take kallon sa ganin yanayin da yake ciki ya saka yace, "Prince yane?." Nan ma bai masa magana ba bai kuma d'ago ba ganin hakan sai ya ja bakin sa ya tsuke baice komai ba sai da ya ga dama sannan ya d'ago ya sauke numfashi yana kallon sa shima yana kallon sa.
"Sarkin mu na gobe, kaine yarima mai jiran gado, masarautar katagum taka ce, kai sarki, mahaifin ka sarki, kakan ka sarki, mahaifin mahaifiyar ka sarki. Allah ya ja zamanin Aliyu gadanga k'usar yak'i, daga kan ka an gama sarauta, kaine zakayi ko basa so sai ka hau karagar mulkin katagum." Lumshe idanu yayi jin kirarin da yake masa bai san lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba ya kalle shi sai kuwa ya sunkuyar da kai yace, "Duk mai shirin bamu matsala akan hawa karagar mu zamuyi maganin sa ko waye, kar yarima ya damu muna tare dashi za kuma mu bashi goyan baya duk wahala duk dad'i, ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai Aliyu ya gaji katagum koda Za'a rasa rai."
Jin hakan sai Aliyu ya bud'e bakin sa a hankali yace, "Asad."
"Shi d'in wa? Ana zancen mutanen k'arfafa wa yake zancen rago Asad?, mulki naka ne sai dai Asad ya duk'a a gaban ka ya kwashi gaisuwa, shi waye da zamu duk'a masa?, wane mutum balle aljan?. Mulki na k'arfafa ne ba irin Asad ragwaye ba, mulki na madu dakakkiyar zuciya ne ba irin Asad maau rauni ba. Allah ya ja zamanin yarima bai kamata Asad ya dinga damun ka ba domin ta ko ina kaine a sama bashi ba, waye zai d'auki mulki ya bawa kurma...?" wanda yake amsa sunan Hashim yake fad'a yana kallon sa cikin girmama irin wacce ake yiwa sarakai.
Murmushin jin dad'i Aliyu yake yi duk duniya babu abinda yake k'auna sama da hawa karagar mulkin gidan su, babu abinda yake so sama yaga manya da yara suna duk'awa suna gaishe shi duk tsufan su haka duk yarintar su, yana so yaji ana buga masa tambari ana buga masa bindiga ana bud'e masa lema ana binsa a guje ana yi masa fifita. Asad yana neman zama cikas a cikin lamarin sa, burin sa da yake mafarki kullum Asad yana k'ok'arin ganin ya tafi a banza ba tare da ya tabbata basketball, sake kallon Hashim yayi har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya d'auki wani pack a gefen sa ya bud'e ya d'auki kwayar da take bugar dashi yasha ya kora da ruwa yana sauke ajiyar zuciya. Murmushi Hashim yayi ya mik'e ya fita dan yasan ba kasafai yake son magana ba shi kuma ya lumshe idanun sa zuciyar sa na kawo masa abubuwan da ya kamata yayi a kan Asad.
*ASAD.*
A zaune yake a k'aramin falo ya hard'e yatsun sa waje d'aya yana kallon wani wajan daban idanun sa a kulle kamar mai tunani, wanda yake zaune kusa dashi kallon sa kawai yake yi kafin yace, "Asad hak'uri zaka yi fa babu yadda zakayi." Numfashi ya sauke ya buɗe idanun sa ya kalle shi kamar zai magana sai ya fasa ya koma ya jingina da kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa.
"Kai kad'ai ne ka dace da sarautar garin nan ka fi kowa ilimi da girmama talakawa, kai kad'ai ne kaf gidan nan baka yiwa bawa tsawa sai dai murmushi koda bakayi magana ba, kai kad'ai ne zaka cigaba da gunadar da mulki kamar mai martaba, matuk'ar sarautar nan ta bar hannun ka sarautar garin ta lalace gabad'aya" wanda yake zaune kusa dashi ya fad'a yana kallon sa. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe ya kalle shi a hankali ya furta, "ni kuma bana so, why sai ni?."
Jin yadda yayi maganar ya saka Suhail yayi murmushi yace, "kamar ba yanzu na gama fad'a maka qualities d'in ka ba?, bazan b'oye maka ba ko mahaifi na da yake k'ani a wajan mai martaba matuk'ar ya karb'i sarautar nan sai ya lalata komai, domin kansu kawai suke hange ba talakawan su ba, kaine ka dace dole ka hak'ura." Jijiyoyin kansa ya dafe yana murza wajan a hankali zuciyar sa na kawo masa abubuwa da yawa. _Meyasa ma suke zancen shine zaiyi sarki bayan mahaifin sa na raye kuma yana kan mulkin?._ ya tambaya a zuciyar sa yana so ya furta a bakin sa amma baya tunanin zai iya hakan ya saka shi ya sake yin ajiyar zuciya baice komai ba.
Mik'ewa Suhail yayi ya k'arasa wajan fridge ya d'auko fresh milk ya had'o da glass cup ya dawo kusa dashi ya zuba masa madarar ya mik'a masa yace, "karb'i ka sha zaka ji dad'i a zuciyar ka." Bai motsa ba kuma bai karb'a ba hakan ya saka Suhail yace, "please ka karb'a." Baya son magana hakan ya saka shi ya karb'a ya rik'e a hannun sa ba tare da ya sha ba.
Cigaba da magana Suhail yayi yace, "burin Mama ne ka daure ka cika mata shi nasan an tauye ka da yawa, burin ka na zama babban malamin addini a k'asar Saudia ya rushe ta dalilin sarautar nan amma ya zakayi abinda Mama take so ne, kayi hak'uri ka dinga bin abinda tace in Allah fa yayi baza kayi mulkin nan ba sai kaga baka yi ba."
Dai-dai lokacin da ya kai kofin madarar bakin sa zai kenan daga bayan sa aka ce, "Asad!." A firgice ya fasa sha ya juyo yana kallon wanda ya shigo ya juya idanu dan daman yasan sai shi d'in ya d'auke ido daga kan sa dan ya tsorata shi. Abokin sa Hafiz kuma MD na kamfanin Asad ya fad'a yana shigowa cikin falon yana kallon sa yana kuma kallon Suhail. Zama yayi a nesa dashi yana kallon sa yace, "lafiya kake?."
Fuska ya d'aure sosai domin yasan Suhail da Hafiz basa jituwa ko kad'an koya suka had'u zasu so suyi hayaniya shiyasa baya so su kasnace waje d'aya suna bashi ciwon kai, ganin hakan sai Suhail ya murmusa ya mik'e yace, "Deaf zamu had'u anjima." Fita yayi daga falon Hafiz ya kalle shi yace, "u know what deaf?, sam zuciya ta bata amince da wannan Suhail d'in a kusa da kai ba, u have to be very careful kasan yanzu kowa kai zai dinga hari tunda mai martaba ya furta zai sauka a mulki ya baka kowa burin sa yaga ya kawar da kai."
Kallon Hafiz kawai yake yi kafin ya tab'e baki yace, "I trust him."
"Kai ai daman zuciyar ka ta amince da kowa shiyasa ake cutar ka a ko wanne lamari, lamarin sarauta ba abu bane mai wasa kar ka manta mahaifin sa na neman mulkin nan za'a iya had'a baki dashi a cuce ka." Kallon sa yayi har ya bud'e baki zaiyi magana sai ya fasa ya d'auke kansa kafin ya d'auko waya yana dubawa.
Hafiz ya kuma cewa, "ya dai kamata ka nutsu kasan abinda kake yi yanzu da kake gani kowa neman ganin bayan ka yake yi. Baka san komai ba a gidan kasancewar rayuwar ka Madina ka yita shiyasa kake d'aukar yarda ka bawa kowa."
Nan ma bai amsa masa ba yasan daman bazai bashi amsa ba hakan ya saka shi baice komai ba shima ya cigaba da danna wayar sa. Gajiya da zaman Asad yayi ya mik'e ya shiga ciki bai sake magana ba shima kuma Hafiz bai kuma ba.
Da daddare kamar yadda mai martaba yace yana neman sa bayan sallar i'sha ya tabbatar yana cikin gida ya nufi cikin gidan da yake da girman gaske, tun daga k'ofar da zata kai ka B'angaren mai martaba dogarai ne bila adadin har da jami''an taaro da suke gadin wajan sabida abinda zai zo wanda zai cutar dashi. Tunda Asad ya doshi wajan ake kwasar gaisuwa sai dai ya d'aga kai kawai har ya iso babbar k'ofar da zata kai shi falon mai martaba, Sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama a nutse yake takawa har cikin falon.
Bai ma kula da wacce take zaune ba ya duk'a ya kai gaisuwa kafin ya zauna har lokacin bai d'ago ba, "Asad!" Mai martaba ya kira shi ya d'ago yace, "Na'am, Allah ya ja da ranka."
"Gobe in Allah ya nuna mana zamuyi tafiya zuwa Kaduna dakai."
Kai ya d'aga kafin yace, "Allah ya nuna mana goben."
"Amin. Kaje shine neman da nake maka daman."
"Nagode, a tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya fita.
Da kallo uwar gidan sarki ta bishi tana murmushi ta kalli mai martaba tace, "Takawa in Asad ya karb'i mulkin garin nan talakawa zasu huta zasu ji dad'i domin kuwa har ya fika zuciyar tausayi." Murmushi jin dad'i yayi babban burin sa a nuna masa kulawa ga Asad shiyasa koda yaushe Sa'adatu take burge shi tana son Asad sosai tana kuma yabon kyawawan halin sa yace, "Shine fatan da nake yiwa masarautar nan domin Asad shine kad'ai zai gyara duk wata b'arakar da take cikin ta, amma sam baya so shiyasa na dakata da batun ajjiye sarautar zuwa nan gaba."
"Zai so ma tunda yana jin maganar ka na tabbata zai so, mu kam mu Asad ya karb'i mulkin garin nan ai jin dad'in mu ne balle kuma talakawan sa." Murmushi mai martaba ya kuma yi yace, "zai kasance in sha Allah."
"Muna fatan hakan, shiyasa tun yanzu na fara nema masa maganin tsari daga garin mudan maganar da ka furta na zaka bashi mulki Allah kad'ai yasan magautan da suka sako shi gaba. Nasan mai martaba yana nema masa shima kuma yana yiwa kansa tawa gudunmawar nake so na bayar."
Mai martaba yace, "Shiyasa nake alfahari da kasancewar ki babba cikin matana, kinyi tunani mai kyau dan a yanzu haka Allah kad'ai yasan adadin jifan da ake masa."
"Allah zai kare mana shi koma waye zai koma kansu."
Shiru tayi kafin kuma tace, "Takawa in an bamu izini zan shiga gida na dawo." Kallon ta yayi ya d'aga kai tayi godiya ta tashi ta fita.
B'angaren ta ta koma ranta a matuk'ar b'ace jikin ta har rawa yake sabida bak'in ciki da hassada ta wuce cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya, duka biyu aka d'auka tace, "Matuk'ar ba kawar da Asad mukayi daga doron duniya ba tabbas masarautar nan sai ta gagare mu shigowa nan gaba, mai martaba yana nan a kan bakar sa na bashi mulki ya dakata ne sabida wani dalili nasa amma ko gobe yaso zai sauka ya bashi karagar ya hau, bana fatan wannan bak'in labari ya tabbata ina raye ka san abin yi."
Daga can b'angaren ya sauke numfashi yace, "kawar da Asad abu ne mai sauk'in gaske a waje na, amma bazan yi yanzu ba zamu bari a d'an kwana biyu sai mu kawar dashi bayan shi sai a kawar da mahaifin sa mu siye kwamnatin Bauchi ta yadda dole mu za'a bawa mulki koda bamu cancanta ba."
"Meyasa sai an kwana biyu?, meyasa baza'a yi yanzu ba?, a kawar dasu duka biyun meye amfanin mai martaban?."
"Bana son yin gaggawa domin za'a iya gano mu."
"Babu wanda zai gano mu, kayi kawai mulki ya dawo hannun ka, tunda d'ana namiji ya kasance yaro k'arami banga d'an wacce zaiyi mulki a cikin mu ba, dan haka a kashe su duka mulkin ya koma hannun ka sai me!."
Murmushi yayi mai sauti kafin yace, "kwantar da hankalin ki uwar gidan mai martaba sarki komai zai zo yadda muka tsara, ki cigaba da jan Asad jikin ki kina nuna masa so da k'auna a gaban mahaifin sa ki ture mahaifiyar sa kome zakiyi baza ta gani ba, tasan sarauta tasan makircin dake cikin gidan sarauta, a hankali zamu saka bakin nasa ma ya kulle duka ya daina maganar gabad'aya kowa ya huta, kinga ai baza'a bawa kurma ragamar al'umma ba. Kashe shi ba mafita bace mu bar shi a raye ta yadda Rabi'atu tana ji tana gani y'ay'an ta maza uku zasu zama hoto basu da wani amfani."
Numfashi ta sauke ta lumshe ido ta bud'e tace, "Haka ne, bana so a d'auki lokaci a fara gabatar da komai domin ko wanne lokaci mai martaba zai iya canja shawara."
"Kar ki damu yanzu aka fara wasan ai."
"Sai na jika" tana fad'a ta yanke wayar tana wuci ita kad'ai kafin ta dai-daita kanta ta fito ta koma b'angaren mai martaba.
A can b'angaren Waziri bayan ya yanke wayar da suke yi da ita ya kalli d'an sa Suhail da yake zaune yana kallon sa shima yace, "kana jin duk abinda yake faruwa, meyasa kayi wasa da maganin da na baka har bai sha madarar nan ba?." Suhail da ya fi mahaifin sa jin takaicin hakan yace, "Na bashi har zai sha abokin sa ya shigo sai ya fasa sha ya ajjiye, kasan kuma yana da basira ina na matsa akan yasha zai gano ni shiyasa na fito na barshi. Ka k'yale ni dashi Abbah ya riga ya amince dani a hankali zan shiga jikin sa na lalata duk wata garkuwar jikin nasa."
Dogon tsaki yaja yace, "aikin banza, inda ka san daga inda aka kawo wannan maganin da baka yi wasa dashi ba, yanzu kafin a sake samo shi sai an kwana biyu sabida hatsarin sa ya saka ba'a bayar dashi ko yaushe. Ka lalata komai Suhail."
Suhail ya cize bakin sa yace, "Abba zan gyara komai kada ka damu indai ina da rai mulki ya bar gidan su Asad ya dawo gidan nan, sai ka yi sarkin garin nan nima kuma sai nayi, burina kenan burin ka kenan, kada