Showing 24001 words to 27000 words out of 92772 words

Chapter 9 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17682

k'afa na zai cire, kaina zai fashe ku taimaka min" ta fad'a cikin tsananin azaba tana juya kanta. Gaban Hydar fad'uwa yake jin yadda maganar ta take fita tausayin ta ya sake kama shi jikin sa yayi sanyi matuk'a ganin duk fa da bai buge ta ba da hakan bata faru ba.


Allura likita yayi mata ya d'aura mata ruwa har lokacin juya kanta take yi sabida ciwo. likitan ya kalli Umma yace, "Kiyi hak'uri Mama zata daina jin ciwo in sha Allah, sai a hankali zaki ga kamar batayi ba" Kai ta d'aga kai daga nan suka fita Hydar ya kalli Dr yace, "tana cikin ciwo sosai babu wani taimako da za'a yi mata?."
"Prince daman ai sai a hankali zata samu sauk'i, yanzu farkawar ta kenan dole taji ciwo a jikin ta amma yanzu zai lafa."
Hydar yace, "Dr ayi abinda ya dace please."
"In sha Allah prince zata dawo kamar batayi ba."
"Thanks" yana fad'a ya bar wajan da sauri shi kuma ya koma office.


Haka Hydar ya koma gida gabad'aya jikin sa ya gama mutuwa tausayin Rauda yake ji na shiga jikin sa sosai, da ya kulle ido sai yaga yadda take kuka tana kiran k'afar ta sai hakan ya sake tayar masa da hankali sosai, muryar ta da kukan ta kawai yake ji a kansa da kunnuwan sa hakan ya sake saka jikin sa yin sanyi yana ji kamar yayi mata kuka.
Lokacin da ya shiga b'angaren su Asad baya nan sai Aliyu yana zaune yana tauna chewing gum ganin yadda Hydar ya shigo ya saka yace, "lafiya kai kuma?."


Hydar ya zauna yace, "yarinyar dana kad'e ce tana cikin ciwo abin tausayi."
"Mtswww and so? I think y'ar talakawa ce ko?."
"Ita y'ar talakawar ba mutum bace?."
"Bata da banbanci da matattaciya."
"Ban san me yake damun ku ba, shi d'an talaka ba mutum bane ba ko me?, ko kuma kai ka zab'i taka rayuwar a haka?."


Aliyu ya tab'e baki yayi masa banza bai kuma kula shi da dan a ganin sa bashi da hankali in shine ya buge ta ko k'afar sa zasu gani ne balle ya dinga zarya haka akan kanta. Shima Hydar d'in banza yayi masa dan ya lura Aliyu da Mama halin su guda ne.


A b'angaren waziri da Hajiya suna zaune kamar yadda suka saba a inda suka zaba had'uwa a sirrance waya na hannun waziri an saka speaker muryar mace babba mai cike da kamala tana fita daga cikin ta, Waziri yace, "kamar yadda na fad'a miki anyi komai an gama gashi har mai martaba yana cewa an jinkirta komai." Murmushi tayi mai sauti tace, "na raina wayon ka da kai da ita kanta Sa'adatun, yanzu ku har kun amince da abinda yace?. Wasa yake muku da hankali ya d'auke hankulan ku daga kan sarautar gabad'aya rana tsaka sai dai kuji sanarwa Asad ya zama sarkin ku dole ku duk'a ku gaishe sa. Kun manta tare suka fita ne a jiya?."


Kallon juna sukayi kafin Waziri yace, "Haka ne, amma bakya ganin kamar wannan karon da gaske yake?."
"Ina baka kana mik'o min hannu. Kai kasan babu wanda ya san sirrin mai martaba sama da Asad sai kuma Mubarak k'anin ka, ko lokacin da suka je Kano da shi Mubarak d'in suka tafi tare aka tattauna aka cimma matsaya ku baku san komai ba. Ku a ganin ku mai martaba zai bada dama kayi sarauta ne? Kuyi tunani dakyau zaku gano kwantan b'auna ne."


Hajiya tace, "duk abinda kika ce haka ne tabbas tunani na bai kawo haka ba sai yanzu, tabbas kwantan b'auna mai martaba yayi mana yana so hankalin mu ya d'auke daga kan Asad ne shiyasa yace haka. Ya fahimci akwai masu nufi irin namu shiyasa yayi saurin dakatar damu." Murmushi tayi mai kyau tace, "Dad'ina dake kina da saurin fahimta. Ku nutsu ku kuma dawo hankalin ku in ba haka ba kuna ji kuna gani komai zai lalace muku. Suhail kuma tabbas ya sakawa Asad layar nan dana baka kuma ta fara shiga jikin sa zancen da nake muku yanzu ma zaman gidan ya fara neman gagarar sa, ciwon Hydar zai tashi a cikin kwanakin nan, ga Aliyu kuma daman ba zaman gidan yake ba. Matuk'ar bamu d'auke hankalin Rabi'atu ba to tabbas shirin mu bazai tab'a tafiya yadda muke so ba, rashin lafiyar Hydar da barin Asad gida ya isa ta fasa tafiyar da tace zatayi, dan matuk'ar taje Kano sai komai ya lalace."


Waziri ya girgiza kai yace, "Wannan shine shirin mu na gaba kenan?."
"Shiri na gaba a kan Asad ne ya zama dole ya bar gidan nan kota halin k'ak'a, ko kuma ya bar duniyar gabad'aya barin sa da numfashi barazana ne ga namu numfashin."
Hajiya tace, "Abinda nake nuna masa kenan tun farko amma ya kasa ganewa, a kawar da Asad shine abu mafi mahimmaci a wajan mu."


Tace, "kwantar da hankalin ki Hajiya baza mu gaggawa ba, a hankali zamu tafi da lamarin in muka ba bar Asad da Aliyu ma komai zai tafi yadda muke so, zakuyi mamaki idan nace Aliyu yana neman hanyar da zai bi wajan ganin ya zama sarki a garin nan, tabbas Ali zai iya kashe Asad abu ne mai sauk'i a wajan sa indai burin sa zai cika wannan ba komai bane ba. mu jira muga yadda wasan zai kaya."


"Abinda nake so dake Sa'adatu ki cigaba da nuna k'aunar Asad a gaban mahaifin sa, ki jawo sa jikin ki yadda baya sakewa da uwar sa ke ya sake dake, kiyi duk abinda zakiyi ya fara cin abin hannun ki ana zuwa wannan gab'ar mun kamo wuyan sa, na bar ku lafiya" tana fad'a ta datse kiran wayar. Hajiya tace, "kirata naji ta yaya zan jawo shi jiki na, dan Allah ka kira ta."


Waziri yace, "Bana tab'a samun ta a waya sai dai in ina taso zata kira ni sai ta bani lokacin da zamuyi magana."
"Gaskiya ta cika babbar master planer, amma wacece ita? Naso na gane maganar ta amma na kasa ganewa, na santa kuwa?."
"Ba lallai kin santa kedai kiyi abinda tace ta kai k'arshe wajan iya tsara plan. Ta wacce hanya zaki bi Asad ya zo hannun ki?."


Numfashi ta sauke tana girgiza kai kafin tace, "Salad, zogale, lansir, wad'annan shine abinda Asad yafi so yaci tun mai babban d'aki tana raye, duk juma'a sai ta aiko masa da d'aya daga cikin su an masa lafiyayyen had'i zai ci kuma hankali a kwance. Bayan shi sai kunun tsamiya mai lemon tsami, sai kuma shayi ko coffee ko kuma chips Asad yana son wannan abubuwan dasu zanyi amfani na meye gurbin mai babban d'aki wajan aika masa dashi duk juma'a, babbar matsalar ita Rabi'atu kana ganin zata bada damar da zan jawo Asad jikina?."


"Tabbas kinyi tunani mai kyau Asad yana matuk'ar son abubuwan da kika lissafa kuma shi halinsa daban ne dan kin bashi karb'a zaiyi yaci bazai kawo komai ba, yadda zuciyar sa take fara gani yake ta kowa fara ce, yarda baya nufin kowa da sharri gani yake kowa ma haka ne. Matsalar dai ita uwar sa kamar yadda kika ce."


Ta daki kujerar da take kai tace, "Amma bar ni da ita nasan abinda zanyi zan biyo mata ta k'ark'ashin k'asa sai burin mu ya cika."
"Ki dai yi a sannu kin san tana da wayo kuma ta dafu da magani ne tun tana yarinya ta kuma dafa y'ay'an ta, ki duba wahalar da muke ta sha tun suna k'ananu har yanzu akan abu guda muke, amma zamu kamo bakin zaren in Allah ya yarda."
Hajiya ta mik'e tsaye tace, "ni na koma zaka ji bayani daga baya" tana fad'a ta fita shima bai jima sosai ba ya tashi ya tafi.......




*ni kaina na shiga confuse fa, wacece Master planer kuma?.*πŸƒπŸΌβ€β™€οΈπŸƒπŸΌβ€β™€οΈπŸƒπŸΌβ€β™€οΈπŸ€£πŸ€£


*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*008.*


Washe gari ta kama ranar Asabar kamar jiya da wuri Hydar ya d'auki mota ya tafi asibitin da Rauda take duk da ciwon kan da yake fama dashi haka ya jure dan da ita ya kwana a ransa. Dak'yar ya iya k'arasawa yayi parking motar ya shiga cikin asibitin kansa na sara masa sosai. D'akin da take ya fara shiga da sallama a bakin sa cikin takun nutsuwa da izzar sarauta da k'asaita da take yawo a cikin jijiyoyin jikin sa.


Yana shiga idanun sa ya sauka a cikin na Rauda da take kallon wanda ya shigo, bai d'auke idanun sa daga cikin nata ba ganin yadda idanun ta sukayi ja duk da bai san su a yadda suke a baya ba amma yadda ya gan su ya san sun canja. Kwarjini da fad'uwar gaban da ta ziyarci k'irjin ta ya saka ta janye idanun ta ta saukar k'asa duk da tsananin azabar da take ciki.


Babu kowa a d'akin sai ita kad'ai ya k'araso yana yatsine fuska sabida kansa ba k'aramin sarawa yake yi ba, ko takawa yayi sai yaji takun har kwakwalwa sa. Kallon ta yake yi ganin yadda take juya kanta kana gani kasan tana cikin azaba jikin ta har rawa yake ga k'afar tata a d'aure goshin ta manne da flasta, k'arewa fuskar ta kallo yake a karon farko k'irjin sa ya cigaba da bugawa yayi saurin d'auke fuskar sa yana kallon gefe guda.




Bud'e k'ofar akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Dr ne da kuma mahaifin ta ganin sa ya saka Dr k'araso yace, "barka da zuwa." Idanun sa ya lumshe ya bud'e kafin ya kalli Baba kafin yayi magana Baba yace, "Barka da safiya, da fatan an tashi lafiya."
"Ya mai jiki?" Ya furta a nutse yana kallon Baba.


"Mai jiki da sauk'i" Baba ya bashi amsa jikin sa har rawa yake yi. Hydar ya kalli Dr baiyi magana ba hakan ya sake yace, "Komai zai tafi dai-dai in sha Allah." Kai kawai ya girgiza ya juya zai fita cikin takun isa sai kuma ya tsaya cak ya juyo yana kallon Baba kafin yace, "ba wani damuwa?."
Sai kuwa Baba ya gyara tsayuwa yace, "To Alhaji kasan lamarin abubuwan sai a hankali, ga gida ba abinci ga kud'in motar zuwa asibiti ga kuma......." hannu Hydar ya d'aga kawai baice komai ba ya saka hannun a aljihu ya d'auko d'aurin dari biyar guda biyu ya mik'awa Baba ya k'araso jikin sa har yana rawa ya karb'a baice komai ba bai kuma bari Baban yace komai ba ya fita.


Baba yabi kud'in da kallo yayi murmushi yana shafa fuskar sa yace, "To ke Rauda ai sai ayi fatan ki ta zama a asibiti wannan abin arzuk'i haka?, tunda nake na d'auka zan rik'e kud'i manya haka nawa na kaina ni kad'ai? Ai ban tab'a ba sai silar kwanciyar nan taki. Yo ba sai nayi ta addu'a kita zama ba indai irin wannan zasu zo hannu."


Rauda kallon Baba take yi duk da ciwon da take ciki hakan bai hana jin takaici da bak'in ciki a zuciyar ta ba, ji ta kud'i ma yake bata lafiyar ta ba gashi da ya shigo ko ya jiki bai mata ba dan ta fahimci shine ya buge ta.
Hydar dak'yar ya iya zuwa office d'in Dr ya zauna kansa yana juyawa a ya saka duka hannayen sa biyun ya dafe kansa, ganin hakan hankalin Dr ya tashi dan masomin tashin ciwon Hydar kenan hakan ya saka shi ya rud'e yace, "Prince lafiya? Me yake damun ka?."


Kansa yake nuna masa jikin sa har rawa yake hankalin Dr ya tashi ya kalle shi yace, "Prince kana buk'atar drip." Kai ya girgiza alamun a'a kafin kuma ya ja dogon numfashi jin yadda kansa yayi mugun sarawa daga nan idanun sa duhu ya mamaye su amma duk da haka yak'i kulle idanun nasa.
"Prince! Prince!! Kana jina?, Prince!!!" Dr ya fad'a hankali a tashe amma lokacin idanun Hydar ya rufe ruf yana zaune idanun sa a kulle jikin sa ya saki duka.


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abinda Dr yake maimaitawa kenan jikin sa na mugun rawa ya bud'e k'ofar Office d'in sa yana fad'in, "Nurse!, Ashiir kana ina?!" Ya fad'a da k'arfin gaske wanda yake kira ya tawo a guje. "Zo ka taimaka min" ya fad'a yana komawa ciki suka shiga tare suka d'aga Hydar da jikin sa yake a sake kamar gawa suka d'ora shi akan gado Dr hankalin sa tashe suka tura gadon Hydar zuwa babban d'aki na musamman.


Ta underground aka shiga babu wanda zaice akwai wani d'aki ko hanya a wajan aka shiga da Hydar aka jona masa ruwa na'urori sai da ya tabbatar yayi masa abinda ya kamata sannan ya fito da sauri yana kiran wayar Mama amma bata d'aukar wayar.


Dafe kansa yayi hannun na rawa ya rika number Asad kamar yadda yayi zato bazai d'auka ba bai kuma d'auka d'in ba, "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta yana danna layin Aliyu shima bai d'auka ba har kira biyu.
Suhaima ya kira na farko bata d'auka ba sai a na biyun yana ganin ta d'auka da sauri yace, "Princess where are you?."
"At home."
"Ina Mama?."
"Lafiya?."
"Ki sanar da ita Hydar yazo nan wajan yarinyar da ya kad'e kuma ciwon sa ya tashi yanzu haka yana kwance."


"What!" Ta fad'a a firgice tana dirowa daga kan gado ta fito daga d'akin ta cikin sauri, bata yi tafiya mai nisa ba ta iso babban falon mahaifiyar tata bata same ta a shi ba ta nufi ciki ta ganta a tsaye tana amsa waya, "Mama ciwon Yaya Hydar ya tashi" ta fad'a a firgice bata jira ta gama wayar ba ma. Ba shiri ta sauke wayar daga kunnen ta ta zaro idsnu tace, "me kika ce? Ciwon Hydar? Yana ina?."
"Dr Yasir ne ya kira ni yake sanar dani yanzu haka ma yana asibiti."
"Oh my god!" Mama ta fad'a tana yin ciki da sauri.


Ita da sauri ta koma ta canja kayan jikinta da sauri ta dawo ta tarar Mama har ta fita tabi bayan ta da saurin gaske, a mota ta samu Mama da sauri ta shiga kusa da ita aka ja motar aka fita da motar da saurin gaske.


Hajiya tana tsaye jakadiyar ta ta shigo a guje tana haki ta zube a gaban ta, da sauri ta juyo ta kalle ts tana fad'in, "ke kuma lafiya zaki fad'o min ko sallama babu."
"Tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ki."
"Lafiya?."
"Wato ranki ya dad'e ciwon yarima Hydar ne ya tashi yanzu zancen da nake miki gimbiya ta tafi asibiti wajan sa." Waje Hajiya ta samu ta zauna tace, "yanzu kenan abin ya faru?."
"Yanzun nan ranki ya dad'e dan yanzu ta fita a gigice da ta shirya tafiya Kano amma a halin yanzu tafiyar ta watse."


Kyakykyawan murmushi tayi tana cize baki tace, "jeki."
"Na gode ranki ya dad'e, ki huta lafiya" ta fad'a tana fita jiki na rawa ta bita da kallo tana murmushi.


"Master planer!" Ta furta a bayyane tana murmushi ganin duk abinda ta tsara ya tafi nan take taji farin ciki yana mamaye mata zuciyar ta. Y'arta Khaleesat sa'ar Suhaima ce ta shigo ta kalle ta itama ita take kallo tace, "Khaleesat kin san me nake so dake?." Kai ta girgiza kai Hajiya tace, "Jeki ki samo min zogale yanzun nan."
Wara idanu tayi tace, "zogale? Hajiya a ina zan samo zogale yanzu?."
Tsaki taja ta shige ciki ita ma tabi bayan ta da sauri.


B'angaren Mama a gigice suka isa asibitin b'angaren da aka ajjiye shi shiru wajan babu motsin komai tsittt ko tsuntsu baya bi ta wajan ta shiga inda Hydar yake kwance, yana kwance sanb'al kamar koda yaushe ko ina na jikin sa baya motsi an jona masa na'ura a kan sa idanun sa a kulle ko wanne lokaci. Kallon Dr tayi ta kalli Suhaima da take gefen ta ta dawo da kallon ta ga Dr tace, "me yazo yi asibitin nan?."
"Ranki ya dad'e yazo duba yarinyar da ya buge ne."
"Yarinyar da ya buge? Kana so kace min a wannan asibitin ya ajjiye y'ar talakawar da ya kad'e?."


Suhaima tace, "Mama muje waje kin san ba'a yi masa hayaniya." Ba musu duka suka fito ta kalli Dr tace, "Kai nake sauraro."
"A nan ya ajjiye ta ranki ya dad'e, yau d'in ma yazo duba ta ne."
"Ita wacece da zai zo duba ta da safe ko wajena bai shiga na gansa ba?, me take dashi?."


Dr yace, "Bata da komai ranki ya dad'e." A fusace tace, "a kan me za'a ajjiye ta a nan? Meya zo yi wajan ta ko wajena bai shiga ba?, me yake nufi da yarinyar nan?." Shiru Dr yayi ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba tace, "akan ta Hydar ya kwanta rashin lafiya, yasan ba'a son ya cika zirga-zirga mussmman da safe amma sabida ita yake fitowa har hakan ya kai shi ga kwanciya, y'ar gidan uban wacece?."


Dr yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ba y'ar kowa bace hasalima iyayen ta talakawa ne." Dogon tsaki taja takaici da bak'in ciki na damalmale mata zuciya tace, "Ayi gaggawar sallamar su daga asibitin nan su koma asibitin gwamnati suje can su k'arata, bazai yu yana kwance a nan itama tana nan ba matsayin su ba d'aya bane ka gane ko?." Kai ya girgiza alamun eh cikin girmamawa tace, "a shirya komai zai tafi da Hydar gida" ta fad'a tana niyar komawa d'akin Suhaima tace, "But Mama zaman sa a nan zaifi samu kulawar da ake nema." Hararar ta tayi hakan ya saka ta yin shiru bata ce komai ba domin an gama magana ta shiga ciki.


Suhaima ta kalli Dr tace, "please Dr ka bar yarinyar ta samu sauk'i in yaso sai ku sallame ta, a bata kulawar da ya kamata please" tana gama fad'a tabi bayan maman ta shima ya bisu da kallo. K'irji ya dafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login