Showing 72001 words to 75000 words out of 92772 words

Chapter 25 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17688

zata wuce Rauda tace, "Ina zaki je da magariba?."
"Zan je wajan Bala na karb'o miki magani Umma tace ya k'are."
"Koma anjima sai muje tare."


Ba musu ta koma ya kalle ta yace, "Ina ne wajan mai maganin na karb'o miki?." Rauda ta kalle shi tace, "babu nisa bakin titi ne, wajan wanda ka tura aka bawa kud'in maganin nawa fa." Anas yayi jim kana yace, "wanda na tura aka bawa kud'in magani? Yaushe kenan?." Rauda da mamaki ta kalle shi tace, "Wanda ka biya bashin maganin da yake kaina sannan ka siya kace na dinga karb'a har kud'in su k'are....? a ranar ka turo mana da kayan abinci da yawa da kud'i har da alqawarin Baba na keke napep, ka manta kenan?." Anas ya girgiza kai cikin mamaki ya rik'e bakin sa yace, "Rauda bani bane, duk abinda kika lissafa ban san anyi ba gaskiya sai yanzu da kika fad'a. Maganar keke napep d'azu muka magana da wanda zai kawowa Baba amma ban kawo ba tukunna."


Rauda cike da al'ajabi tace, "Wai da gaske kake?." Ya d'aga mata kai yace, "Da gaske nake ban san anyi ba sai yanzu da kike fad'a min, abinda na sani na turo da da kud'i a baki kafin na dawo." Rauda ta sauke numfashi tana girgiza kai cikin tsoro da mamaki tace, "to waye ya aiko da wad'annan abubuwan haka?, duk a tunanin mu kaine shiyasa bamuyi tunanin kowa ba kaine kawai kazo ranmu a lokacin." Anas ya girgiza kai yana tab'e yace, "Damn it! Lallai akwai wani a gefe wanda yake neman shigowa cikin gwamnati na a shirye, tabbas ko waye ya aiko da abinda kika fad'a masoyin ki ne."


Rauda kamar zata zubar da hawaye tace, "to waye?."
"Allah ne ya sanshi Rauda" ya furta a sanyaye yana kallon ta jikin sa ya kuma yin sanyi jin abinda rauni a zuciyar sa. Shiru tayi shima haka tunanin ta waye wannan wanda yasan abinda yake faruwa da ita har yayi mata abinda yayi....? Koma waye tabbas yana bibiyar ta tunda har yasan da abinda Baba yake so yasan yanayin gidan su na rashin abinci yasan kuma da bashi a kanta wajan Bala mai magani, tabbas ya santa ko ya nemi sani a kanta. shi kuma tunanin waye wannan yake k'okarin shigowa rayuwar Raudan sa a b'oye...? Waye wanda yake k'okarin yin kutse a gwamnatin da yake so ya Gina...?, a ina yake? Waye shi?. Babu wanda zai basu amsa haka dukkan su suka rabu jikin kowa babu k'wari kowa da tunanin da yake zuciyar sa.


Asad yana tsaye a jikin window d'akin sa yana kallon mutanen da suke shige da fice a gidan iska na kad'a shi kad'an kasancewar yanayin garin babu iska, ya rasa abinda yake masa dad'i gabad'aya hakan ya saka shi kallon waje ko zai ji dad'i, motsin da yaji a bayan sa hakan ya saka shi ya juyo yaga Hydar ne ya shigo ya k'araso kusa dashi ya tsaya yace, "Deaf akwai abinda yake damun ka tun lokacin da muka baro gidan su yarinyar nan na lura akwai wani abu, meye shi...?."


Numfashi ya sauke baice komai ba ya cigaba da kallon window d'in kafin Hydar ya kuma cewa, "Ka sanar dani abinda yake damun ka ko zan iya maka maganin sa." Asad ya bar jikin Window d'in ya saka hannu a aljihu yace, "Ban san meyasa nake ganin ta ko haushe ba Hydar, even in my dreams I saw her lokaci zuwa lokaci." Jin yadda yayi maganar da rauni ya saka Hydar fuskantar sa yace, "Who is she?." Kallon idanun Hydar yayi kafin ya bar wajan yace, "Forget it."
"Tell me please, bana so na ganka cikin damuwa ka sanar dani."
Asad ya zuba masa ido na wani lokacin kafin ya tsaya jikin mudubi yana kallon kansa yace, "Hydar...." Sai kuma yayi shiru jin hakan ya saka Hydar yace, "Please in baka fad'a min ba wa zaka fad'awa?."


"Ina ganin ta a mafarki Hydar tana taimako na ko yaushe tana bani kariya, after that na ganta a zahiri na tabbatar itace ta cikin mafarkina" sai kuma ya dafe kansa ya sauke numfashi yace, "ban san me nake ji ba but ina jin wani iri." ya fad'a yana dafe kansa ya jingina da bango yana lumshe idanun sa.
"Wacece?." Shiru Asad yayi masa bai amsa ba Hydar ya sake maimaitawa sai daga baya yace, "Rauda!." Hydar gaban sa yayi mugun fad'uwar ya zaro manyan idanun sa waje yace, "What? Rauda!, I think yarinyar da muka je gidan su itace Rauda ba...?, yeah itace, oh my god!" ya fad'a yana dafe kansa yana kallon d'an uwan nasa da mamaki.


Asad bai amsa ba daman yasan bazai amsa ba hakan ya saka yace, "deaf kana nufin kana son ta kenan?" Ya fad'a yana kallon fuskar sa. Ido Asad ya bud'e suka had'a ido yana kallon sa ya cize baki kafin ya girgiza kai alamun a'a, Hydar yace, "meye in ba so ba?." Asad ya d'age kafad'a alamun bai sani ba.


Hydar yazo kusa dashi ya dafa shi yace, "Deaf kana sonta na tabbatar tun a mafarkin ka ka fara sonta naga hakan a cikin idanun ka, lokacin da mahaifin ta yake gabatar mana da wannan mutumin I saw so many changes on your face, like kishin abinda akace nake hangowa a kan idanun ka a kwanshe, that's mean kana son ta Asad."


Zubawa Hydar ido yayi yana kallon sa har ya kai k'arshen maganar sa kafin yace, "A'a Hydar, hakan bazai yu ba."
"It can be deaf, kai mutum ne kana da zuciya kana kuma da feeling ko da yaushe zuciyar ka zata kamuwa da soyayyar wacce ta aminta da ita. Kana son ta Asad ka amince dani." Numfashi ya fesar ya bar wajan ya koma gefen gado ya zauna ya jawo drawer ya d'auko passport d'inta ya bud'e yana kallon hoton jiki.


Hydar ya murmusa ya k'araso gaban sa ya duk'a yace, "believe me your in love deaf, nasan tunanin ka ta ya zaka tunkari wannan yarinyar da batun love, ka bar min komai a hannu na zanyi komai."
"Nooo Hydar ban saka ka ba, ban amince kuma da abinda kace ba." Hydar ya murmusa baice komai ba yana kallon sa taurin kan Asad shine yake cutar sa wani lokacin. Fita Hydar yayi daga d'akin yana murmushi yana kuma neman hanyar da zai gabatar da yayan sa ga Rauda.


"How?" Ya furta bayan fitar Hydar ya kwanta a kan gado yana kallon sama yana jin zuciyar sa na bugawa da saurin gaske. Idanun sa ya kulle amma ita yake gani har lokacin ya bud'e ido sai yake jin sautin muryar ta a cikin kunnen sa hakan ya saka shi ya mik'e zunbur yana zaga d'akin. 'ta yaya zan fara son wacce aure na da ita bazai yu ba?, ta yaya zuciya ta zata so bayan Mama na raye?; oh my God ya zanyi?. firstly sai na cire ta a raina zan samu sauk'i, but itace take zuwa dreams d'ina bani na gayyace ta ba, meyasa take zuwa? Meyasa zuciyata take bugawa nake jinta a jikin ta?. oh my heart.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan ya dafe zuciyar sa da yake mugun gudu furta kalmaan da Hydar yayi ya saka zuciyar sa ta k'ara kaimi wajan gudu.


A daren ranar Asad ya tabbatar da son Rauda yake ba tausayin ta yake yi ba, ya tabbatar da maganar Hydar tun ganin da yake mata a farki Allah ya ajjiye soyayyar ta a cikin zuciyar sa, ya tabbatar da itace macen da ta samu nasarar d'aukar kambun soyayya a zuciyar sa. A cikin daren ya fara tunanin nemo hanyar da fidda ta daga zuciyar sa tun kafin dare yayi masa.


Washe gari.


Mama na zaune tana karyawa ita kad'ai a falon ta Aliyu ya shigo ya zauna kusa da ita ya jawo kayan breakfast na gaban ta ya fara sha shima, bata ce masa komai ba sai da ya had'a tea yasha kana ya kalle ta yace, "Mamana kin san me Asad yake shirin yi kuwa?." Ta kalle shi tace, "kamar ya kenan?."
"Mama ina wannan yarinyar da Hydar ya buge kika ce babu shi babu ita?."
"Ina jin ka."
"Itace dai yarinyar da ta kira ni da mahaukaci, at the end kuma kullum Asad sai yaje gidan su wajan ta, ya mata passport ita da iyayen ta zai kaita Egypt" ya fad'a yana kai grape bakin sa yana taunawa.


Mama ta ajjiye cup d'in hannun ta tace, "Me kake fad'a ne haka Aliyu?." Aliyu yace, "Abinda mahaifita taji shi nake fad'a, ina da tabbacin Mamana tasan bazan mata k'arya ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me ya had'a Asad da y'ar talakawa y'ar tallah har yake zuwa gidan su?."
Aliyu ya kalle ta yayi murmushi yace, "sabida yana sonta ne, yana kuma tunanin auren ta!."


"What? Aliyu kasan me kake cewa kuwa? Bana son shirme fa, wanne irin yana sonta Aliyu?." Aliyu ya mik'e tsaye yace, "Ba k'arya nake yiwa Mama ba, in kuma Mamana bata yadda ba zata iya sakawa a bincika zata gane maganar Aliyu gaskiya ce. but yana da kyau Mamana ta yiwa tufkar hanci tun kafin abun yayi nisa, mahaifita tasan in Abba yaji maganar nan babu abinda zai hana bai bashi ita ba. Faruwar hakan kuma daidai yake da Fulani mahaifita matar sarkin Katagum y'ar sarkin Kano jikar sarkin Kano zata zama inlaw d'in gurguwa, baka, kuma y'ar talakawa. At the end ita kuma zata zama matar sarki zata kasance a saman take Mamana, before Asad yayi sharawa da mahaifita sai ya fara da ita tunda itace sirrin sa!. Zata san abubuwa nasa da yawa kafin Mamana ta sani." Yana gama fad'ar hakan ya fita yana cize bakin sa alamun samun nasara dan yasan Mama ta cika tayi fammmm.


#Vote
#Share
#Comments.


*KWANTAN ƁAUNA*


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*021.*


Hankalin Mama in ya kai miliyan ya tashi jikinta har rawa yake sabida tashin hankali ta tashi ta bar wajan da sauri ta nufi ciki hankalin a tashe sosai. Bata tab'a jin abu mai munin abinda Aliyu ya fad'a mata ba gabad'aya ya gigitata ta rud'e jikin ta har rawa yake yi sabida rud'ani. Kallon agogo tayi taga k'arshe sha d'aya na safe ya kusa ta saka takalmi da sauri ta fita zuwa b'angaren y'ay'an nata dan tana so ta tabbatar da abinda akace mata. Gab da zata shiga falon taji sautin muryar Hydar yana cewa, "Deaf in love, ban tab'a amincewa zaka fara soyayya da wata mace ba duba da yanayin ka da yanayin maganar, sai gashi ka fad'a ba tare da ka shiryawa hakan ba, wannan soyayyar taku itace silar accident."


Asad dai baice komai ba Mama jin abinda ta jiyo ta sake firgicewa ta kuma tabbatar Aliyu bai mata k'arya ba abinda ya fad'a gaskiya ne tunda gashi har Hydar ya sani yana kuma kiran soyayyar da silar accident, har zata shiga falon sai kuma ta koma da baya da sauri ta koma b'angaren ta ta shiga cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya ta kira Mum. Buga biyu Mum ta d'auki wayar kafin tayi magana tace, "Sadiya in kina da time ki shigo yanzun nan." Daga can b'angaren Mum tace, "An gama ranki ya dad'e, bani mintina goma zan iso." Mama bata kuma jin me tace ba ta yanke wayar ta cillar kan gado tana zaga d'akin hankalin ta yayi mugun tashi.


Zagaye take daga nan zuwa nan ta kasa zama abinda bata tab'a tunanin zai faru ba shine yake k'okarin faruwa jinin ta wanda ya fito daga jikin ta shine da son y'ar talaka, jinin talakawa kuma nakasashshiya. Jinin nata ma kuma Asad da ta k'wallafa rai a kansa ace shine yake son y'ar talaka gurguwa mummuna wannan ba k'aramin abun kunya bane a wajan ta. Shigowar Mum ya saka Mama ta juya Mum ta k'araso da sauri tana fad'in, "Ranki ya dad'e lafiya kuwa?."
"Ina fa lafiya; zauna mu tattara" Mama ta fad'a tana zama itama Mum d'in ta zauna.


"Me ya faru?."
"Meye ma bai faru ba Sadiya. Wani abu naji wanda yayi bazanar tarwatsa min zuciya ya jefa ni cikin wani hali wanda ban shirya tsintar kaina a cikin sa ba." Mum tace, "Ranki ya dad'e meye wannan d'in haka?."


Mama tace, "Ace wai jinina wanda na haifa da kaina ne zai so jinin talakawa, y'ar talakawar ma y'ar tallah a titi bak'a kuma gurguwa? Ta yaya hankali na bazai tashi ba?." Mum ta dafe k'irji ciki da firgici tace, "mun shiga uku, gaskiya dole hankalin ki ya tashi domin kuwa wannan babban cin mutunci ne da cin fuska a gare mu duka ba ke kad'ai ba."
"Bari kawai, yanzun nan naji maganar yanzun nan na tabbatar da ita amma zafi nake ji a k'irjina kamar ana tafasa min zuciya."


Mum tace, "Amma waye da wannan d'anyen aikin? Nadai san Aliyu bazai aikata hakan ba sai dai Hydar dan nasan shine zai iya b'allo mana wannan ruwan." Mama tayi murmushin takaici zuciyar ta na sake cika taf da k'una da b'acin rai tace, "Wanne Hydar ana zaune qalau...? inda Hydar ne ai hankali na bazai tashi haka ba. Babbar giwar fa Asad; wanda yake jiran kujerar masarautar nan wai shine yake soyayya da yarinya irin wannan." Gaban Mum yayi mugun fad'uwa jin wanda aka ambata ta dafe k'irji cikin tashin hankalin da ya bayyana akan fuskar ta itama ta zaro idanu tace, "Asad! Mun shiga uku." Mama ta girgiza kai bata ce komai ba Mum tace, "Kuma kin tabbatar da maganar? In kika duba yanayin sa ranki ya dad'e sai naga kamar ba zai saurari irin su ba, Anya maganar nan daga majiya mai tushe take?."


"Da Aliyu ya fad'a min ban amince sosai ba amma da naje na riska suna magana da abokin sirrin sa Hydar a sannan na tabbatar da Aliyu baiyi min k'arya ba. Sadiya jinina tafasa yake yi bazan lamunci wannan lamarin ba gabad'aya." Mum tace, "ni kaina jinin nawa tafasa yake ranki ya dad'e balle ke. Amma fa abinda mamaki anya kuwa ba asiri tayi masa ba? In ba asiri ba a yadda kika lissafo ta meye abin so a wajan ta har da yarima mai jiran gado guda zai d'aga kai ya kalle ta?."
"Babban tashin hankalina kenan Sadiya."
"To shi kin ji ta bakin sa?, ina nufin kun tattauna dashi akan lamarin?."
"Bai san ma na sani ba."
"Amma yana da kyau shima a tsawatar masa a kanta tunda yana jin maganar ki."


"Wannan ba komai bane ba Sadiya na fara maganin yarinyar shi ba wani abin damuwa bane in nace bana so zance ya k'are; ita yarinyar ita nake so na jawa kunne ko dan tasan wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa. Ina so tasan ruwa fa ba sa'an kwando bane, ta banbance tsakanin zare da abawa." ta girgiza kai cikin gamsuwa tace, "Haka ne, yana da kyau mu tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. Amma wanne mataki kika d'auka a zuciyar ki wanda kike gani zamu aiwatar dashi?."


Mama ta kalle ta tace, "Shiyasa na kira ki domin inaso ko meye a aiwatar dashi yau bana son b'ata lokaci." Mum tayi jim tana tunani kafin tace, "Mu saka a d'auko ta a sace ta mu bata wahala sosai a sake b'alla k'afar ta ta kinga in aka mata haka zata shiga hankalin ta." Mama ta girgiza kai tace, "Shawara ce mai kyau wannan amma bazata yu ba, in labarin ya bayyana daga baya sunan mai martaba zai b'aci a garin nan za'a dinga yawo dashi ace nice na aikata hakan. Canja wata."
Mum tace, "Haka ne. Mu tura mutane su je gidan ayi mata dukan tsiya ita da iyayen ta inda dama a b'alla ta a b'alla iyayen ta a kuma yi musu kyakykyawan warning wanda zai shiga jikin su, kin ga zasu ji tsoro dukkan su bama ita kad'ai ba har da iyayen ta."


Mama tayi murmushi cikin jin dad'in maganar tace, "Wannan shawarar tayi d'ari bisa dari da kuma ita zamuyi amfani; amma fa bana son aje da wani dogari daga gidan nan dan tonuwar wannan maganar ma b'ata suna ne a idanun mutanen gidan nan balle mutanen gari, k'askanci ne a wajena ace yaron dana fi so cikin y'ay'ana yana bibiyar wata y'ar talakawa. Inaso aje dake domin kiyi musu kyakykyawan warning wanda zasu shiga hankalin su." Mum tace, "Wannan ki d'auka an gama ranki ya dad'e, zan samu mutane a waje muje muyi duk abinda kika ce ai abu ne mai sauk'i."


Mama ta girgiza kai tace, "kuje a fara aiwatar da komai yanzu bana son b'ata lokaci Sadiya ke kin sani." Ba musu Mum ta mik'e tace, "An gama ranki ya dad'e" tana gama fad'ar hakan ta fita daga gidan da sauri.


Mum na fita gida ta koma Jidda bata nan gidan babu kowa jikin ta har rawa yake dan tama fi Mama son d'aukar mataki a kan Rauda ta d'auki abinda zata d'auka ta fita daga gidan da sauri. Mata da maza ta had'a duka ta biya su aka tafi gidan su Rauda lokacin rana ta bud'e sosai.


Rauda na zaune akan kujerar da ta saba zama ita da Umma da Inna bata nan sauran sun tafi makaranta, Baba ne ya fito daga d'aki bai fita da wuri ba Umma tace, "Malam kaji ashe duk abinda aka kawo gidan nan ba Anas ne ya bayar ba?." Baba ya kalle su yace, "kamar yaya kenan?."
"Jiya take yiwa Anas mganar magani yake cewa shi duk abinda aka kawo bashi ya bayar ba, hankalina duk ya tashi ban san abin wanda muke ci ba wallahi, da alhairi yake neman mu ko akasin sa duk bamu sani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login