Showing 54001 words to 57000 words out of 142577 words
Chapter 19 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
tana d'an mai da numfashi,
shi kuwa k'ara matsota yayi cikin yanayin tabbaya yace,
"Khairi me a hannun ki?"
bata kula shiba sai d'an mirgino wa tayi jikin shi cikin yanayin yaudara ta d'an konta kan k'irjin
shi hannun tasa ta cusa a bayan shi,
Ido ta lumshe tare dasa hannun tana shafa sajen shi har zuwa kan k'irjin shi tanayi tana lumshe
ido,
shi kuwa gaba d'aya ta zuba mishi kasala duk jijiyoyin jikin shi sun mace,
ganin haka sai ta sake konta wa ta juya mishi baya ta kifu,
shi kuwa sunkuyowa yayi ya rink'a kissing na tsakiyar bayan ta yanayi yana murzata gaba d'aya
ya gigice ya gigitata a haka ya samu abinda yafi kwana 12 bai samuba,
ita kuwa abinda ta saba fad'a mai shi take furta mai,
"Bana sonka ni na tsaneka".
hakan ya tunzura shi ya murzata har saida yaji ya huce ya kuma gamsu,
sannan ya juya mata baya cikin maida numfashi yace,
" Sai ki nemo wanda kike son yazo ya kaiki gidan ko".
rai a b'ace ta jawo blanket d'in ta hard'eshi a jikin ta ta mik'e tana jan shi tana,
"Sai Allah ya saka min tunda saida kayi tayin pakala iya son ranka sannan yanzu kace bazaka
kaini ba".
tana fad'in haka tana k'ok'arin fita d'akin,
shi kuwa har cikin ranshi yake jin dad'i dan ya samu gamsuwa da ita kuma ta d'an sake mishi,
abinda bai saniba boye laifinta take sonyi,
itako har taje bakin k'ofar fita tace,
" Ni kuwa bazan sake zuwa d'akin nan ba kuma mutun ko yazo min d'aki rufewa zanyi".
Murmushi kawai yayi ya bita da ido,
dan sakarcin Ummul yarin tane a ciki,
ba gashi yanzu buk'atar tace ta kawota ba har ya samu shima tasa buk'atar ta biya so yasan
gaban ma hakane.
Haka rayuwa tayi ta tafiya,
Usman kuwa a gefen shi ciwo ba sauk'i kullum sai gaba gaba yakeyi.
Yau Saturday tun safe Usman bai lek'a ko k'ofar parlour suba,
Nenne kuwa gaba d'aya hankalin ta na kanshi ganin har bayan la'asar bai shigo ba yasa ta
mik'e ta nufi part d'in nasu,
a hankali tayi sallama,
shiru bai amsa ba dan yana zaune a k'asa a bak'in gado ya kifa kanshi a jikin gadon yana kuka
mai cushe numfashi,
a hankali Nenne ta rink'a jin sautin kukan nashi,
tare da tari mai yanayin ciwon zuciya,
a hankali ta shiga cikin d'akin kai tsaye bakin gadon taje ta zauna cikin sanyi tasa hannun ta
tadafa kanshi,
da sauri ya d'ago kanshi yana goge k'ollah dake bin fuskar shi,
cikin k'arfin hali yayi murmushi ,
ido ta zuba mai cikin tuhuma tace,
"Usman a zaton ka bansan meke damun ka bako?"
kai ya jinjina tare da yin murmushi yace,
"Nenne bani da matsalar komai".
ido ta sake tsura mishi sannan tace,
" Ummul ce matsalar ai".
cikin sauri ya rink'a juya kai yana jin kunya na ratsashi ya za'ayi ya k'asa control d'in k'aunar
Ummul a ranshi har mutane su gane yana son matar d'an uwanshi,
ita kuwa Nenne kafad'an shi ta dafa a hankali tace,
"Ban tab'a zaton shak'uwar ka da Ummul ya zama so a tsaka nin kuba har aka d'aura auren
Ummul da Farouq duk a zaton shak'uwace kawai a tsaka ninku,
Usman na fara Azargin kana son Ummul ne bayan Umar ya tafi da ita gidan shi,
tun lokacin da ka fad'i ka suma na gane akwai abinda kake b'oyewa a ranka,
ban gaskanta hakan ba sai randa kukaje gidan Ummul kuka dawo nanma kai ta aman jini sai
kuma randa su Umar d'in suka zo manna ka birkice,
sannan tunda suka tafi baka samu sukuni da kowa ba kuma doctor ya shaida mana akwai abin
da kakeso kuma kana b'oyewa,
Usman ni yanzu nasan Ummul kake so".
tunda Nenne ta fara magana yayi shiru yana kallon ta,
saida ta furta "Ummul kake so".
sai ya kife kanshi kan cinyarta ya saki wani irin kuka murya a hargitse ya rik'o hannun ta ya
rink'a juya mata kai a birkice yace,
" Asiri na ya tonu naji kunya har gaban Ubangiji na tunda matar aure zuciya ta ke so ina zankai
wannan zunubin? naji kunya a idanun duniya na rasa wacce zanso sai matar d'an uwana
shak'ik'ina wanda bayi da b'uri a duniya daya wuce farin ciki na".
sai kuma ya kuma kife kai yayi ta kuka mai tarin firgici cikin rawan murya ya durk'usa gaban
Nenne a hankali yace,
"Nenne ki rufa min asiri ki tayani b'oye wannan sirrin nawa kodako zai zama ajalina dan Allah
karki gayawa ko daga ni sai ke ".
itama Nenne kuka takeyi sosai dan Usman ya zama abin tausayi,
a hankali tace,
" kana ganin a haka zakaci gaba da boye abin a ranka ne?"
Kai ya jinjina a hankali yace,
"Nenne taima kona zakiyi kisa baki Abba da Hamma Umar su barni intafi India inbar k'asar gaba
d'aya na tabbatar zan samu sauk'in abin a raina in nayi nesa da Ummul".
kallon shi tayi a hankali tace,
in dai haka zai sama maka sauk'i toh ba matsala".
Haka kuwa akayi Nenne ta ajiye Hamma Umar da Abba tayi ta rokawa Usman d'in a barshi ya
tafi ai yace ya samu lafiya kuma daga can zai k'ara ganin doctor,
shi kam Hamma Umar har cikin ransa baya son tafiyar da d'an uwanshi zaiyi amman Abba da
Daddy sun yarda dole shima ya yarda,
shi kuwa Usman ya fara shirin tafiya cikin happy da kewar d'an uwanshi da Ammin su abar
k'aunar su ji yake kamar ya fasa tafiyar dan gani yake kamar shike nan ya rabu dasu kenan har
abadan,
haka dai ya d'aure ya tafi.
Gidan Alhaji Bello kuwa mahaifin Mustapha gaba d'aya rayuwar Mustapha ta juya ta canza
Mustapha ya zama abin tausayi dan tabbas har cikin ransa yake son Ummul mahaifin shi kuwa
ganin ya rasa Ummul d'in ne yasa yace zai had'a shi da y'ar k'anwar shi,
yau tun safe aketa fama da Mustapha iyayen shi sun sashi a gaba kan batun auren amman sai
ya d'ago ya kallesu fuska cike da k'ollah yace,
" Daddy ni ba zanyi aure ba Daddy dan Allah kuyi hak'uri ni bana son auren ,bazan iya auren
bafa".
Ido Daddyn ya zuba mishi cikin sanyi yace,
"Mustapha shin kana fushi da hukuncin Ubangiji ne? ya za'ayi kace bazaki yi aure ba bayan
kuma kana da damar yin auren ashe dan ka rasa Ummul bazaka so y'ar uwarka Amina ba shin
ko zakaci gaba da son matar aure?"
kai ya rink'a juyawa yana zubda k'ollah yace,
"Daddy bana son Amina kona aureta bazata ji dad'in zama da niba Daddy bana son cutar da
ita".
Mahaifiyar shi ce ta kalleshi cikin tausayawa tace,
" Mustapha wata rana zaka so Amina na kuma tabbata zatayi ma biyayya tunda dama ita tana
sonka kuma indai mun isa da kai toh ka aminci da auren nan".
a hankali ya mik'e cikin rawan murya yace,
"Shike nan Daddy na aminci indai hakan zai saku farin ciki".
murmushi Daddy yayi cikin jin dad'i sannan suka bishi da Addu'a,
shi kuwa yana fita d'akin shi ya nufa a parlour ya konta a k'asa yayi shiru yana tuno irin shirin da
yakeyi na auren Ummul kawai sai ya rink'a kuka yana istgifari dan tuno cewa Ummul fa yanzu
matar aure ce,
haka akayi ta shirin auren Mustapha da Amina..
Gidan Hamma Umar kuwa tun randa Ummul taje d'akin Hamma Umar d'in ya kusance ta daga
Wannan ranan ,
rayuwar Ummul ta fara canzawa wani irin abin al'ajabi da tsoro ya rink'a bibiyar Ummul,
tun daga yamma cin wannan ranar Ummul ta farajin hannun ta da akasawa robar family
planning d'in yana mata wani irin nauyi sannan sai taji hannun kamar ba a jikinta yaje ba gaba
d'aya sai zuciyar ta ta rink'a tsinke wa wata iriyar kasala ta rink'a rufeta,
a haka a daddafe tayi sallan maggariba da isha,
cikin kasala ta zame ta konta kan sallayar da nufin zatayi bacci ,
Amman sai ga wani sabon al'amari mai ban tsoro kuma,
bayan ta konta tayi Addu'a sannan ta lumshe ido a hankali bacci ya fara fizgarta,
lokaci d'aya bacci mai dad'i ya d'ebeta,
Amman cikin baccin sai taga Hamma Umar yana rik'e da jariri fari tas mai kyau yaron sai kuka
yakeyi shi kuwa Hamma Umar sai ya mik'e mata jaririn ita kuwa sai ta ture ta juya ta gudu can
gefen su,
shiko Hamma Umar d'in sai yasa yaron a kafad'an shi yana lallashin jaririn yana ta zirga-zirga
shiko jaririn sai kuka yakeyi da k'arfi,
ganin haka ta tashi a firgice al'wala taje ta kumayi sannan tazo ta kumayi Addu'a sannan ta
sake kwanciyar bayan kamar minti 30 bacci ya sake d'auke ta,
still cikin baccin ta sake ganin Hamma Umar zaune cikin jarirai sai kuka sukayi da k'arfi duk sun
cika gidan da kuka,
a hankali ta rink'a ganin jariran sun dawo gareta sunata kuka shima Hamma Umar ya koma
gefen su yana kallon jariran yana zubda k'ollah,
haka ta sake farkawa a firgice,
Toh fa haka Ummul take rayuwa ba bacci data rumtse idanun ta sai taga ana binta da jarirai
suna kuka har abin ya fara zame mata ko a gyegyed'i takeyi sai tayi tajin kukan jarirai ga
hannun ta kuma yamma nayi yake fara ciwo ta kuma k'i ta gayawa kowa Hamma Umar kuwa ko
sabgarta ya dena shiga , sai ya kwana nafilfilin shi yana mai rok'on Allah ya azurtashi da haihuwa kullum Addu'ar sa Allah
yasa Ummul ta samu ciki dan yana son haihuwa tare da ita
sai azumi da yake yawan yi dan ya rege k'arfin sha'awarsa tunda yasan ba kulawar Ummul zai
samuba,
itako Ummul zuwa yanzu har tsoro take dere yayi da zaran yamma tayi bata da sauran
kwanciyar hankali.
Yau juma'a tun safe Hamma Umar yake d'akin shi yana ta karatun qura'an har zuwa 12 sannan
yayi wonka ya shirya sab cikin fararen tufafi sai k'amshin turaren shi na du'a'ul jannah yake yi
sannan ya fito hannun shi rik'e da sallaya a parlour ya samu Ummul zaune cikin yanayin bacci
dan yau koda safen da zaran ta rufe ido sai taga ana mik'o mata jarirai gaba d'aya baccin sai
yasa mata ciwon kai ga hannun ta da takeji kamar ba nataba gashi dai ba kumbura yayi ba
amman jin hannun take kamar dutsi,
tana ganin shi ta matso gaban shi cikin yin mik'a ido a lumshe tace,
"Hamma Umar a bani maganin bacci mana".
bai kalleta ba bai kuma yi magana ba har yaje bakin k'afa sannan yace,
" sabida me? zan baki maganin bacci?"
"Bana samun bacci ne shiyasa".
" baki da lafiya ne?"
"A a ni lafiya ta lau".
Juyawa yayi ya d'an kalleta sannan ya girgiza kai ya fice,
koda akayi sallan juma'a potaskum ya nufa kai tsaye gidan Inna ya nufa ranar ko lek'a gidan
Abba baiyi ba dan tunda Usman ya tafi baya son zuwa gidan sosai,
yana zuwa ya wuni da Ammin su sunata hira ya kira Usman d'in ma a woya sun dad'e suna
hira,
shine bai nufi hanyar damaturu ba sai bayan sallan ishah sannan ya kama hanyar,
ita kuwa Ummul gaba d'aya ta birkice bacci na shirin zautar da ita sai zirga-zirga takeyi da zaran
ta konta in tayi baccin minti 30 dai toh sai mafarkin jarirai,
shi kuwa Hamma Umar yana isowa kai tsaye bedroom d'in shi kawai ya nufa,
wonka yayi sannan ya konta rik'e da woyar shi yana magana da Ammin shi yana shaida mata
ya isa lafiya,
ita kuwa Ummul a hankali ta samu baccin ya saceta,
bacci mai nauyi cikin nisan baccin ta fara juyo kukan jarirai ba adadi kukan sai k'ara matsota
yake har taga jariran sun cika kan gadon nata sai kuma taga hannu wani mutun ya yarfa mata
mari sannan ya nuna mata wani fili mai kyau inda ta haggo Hamma Umar yana zaune rik'e da
jariri yana ta kallon ta yana murmushi tana cikin mamaki ina Hamma Umar a samo yaron nan
sai taji an kuma yarfa mata marin tare da buga mata tsawa,
" tashi kije ki karb'i d'an ki".
A firgice ta farka da jin marin tayi kamar a zahiri,
lokaci d'aya wani irin tsoro ya rufeta gaba d'aya jikinta sai zufa ke tsatstsafo mata hannun ta
kuwa sai rawa yake kar-kar,
sai kuma taji kukan kululluka a saman d'akin ta,
haka yasa ta mik'e cikin tsananin tsoro da gudu ta fito parlour sai kuma ta nufi bedroom d'in
Hamma Umar d'in tana shiga ta ganshi zaune kan sallaya hannun shi rik'e da qura'an da gudu
taje ta fad'a jikin shi gaba d'aya jikin ta sai tsuma yakeyi hannun tasa ta ruggume shi da k'arfi
kanta take ta cusawa cikin k'irjin shi tana to she kunnen ta, da sauri ya kalleta cikin mamaki ganin yadda take boye kanta a jikin shi yasa shima ya k'ara
ruggume ta sannan ya rufe qura'an d'in ya ajiye kan mirror ,
ita kuwa Ummul sai kuka takeyi cikin tsananin jin tsoro,
kanta ya d'ago a hankali yace,
"Ummul meke faruwa ne?"
baki na rawa tace,
"Hamma tsoro nake ji Hamma kullum bana bacci mafarkin jarirai nakeyi suna kuka suna hanani
bacci".
Jawota jikin shi yayi ya kara ruggume ta cikin mamaki yace,
" jarirai kuma? toh banda abin ki Khairi kukan jarirai kuma me abin tsoro a ciki?".
K'ara mak'aleshi tayi tana, kuka tace,
"Suna da yawafa kuma yau har dukana akeyi".
ruggume ta yayi ya mik'e da ita kan gado ya kontar da ita sannan ya konta gefen ta ya ruggume
ta yana shafa kanta cikin sanyi yace,
" kiyi shiru kibar kukan ba komai kinji ko".
Ido ta rumtse sai kuma ta mik'e da sauri ganin wani hannun yana sa wuk'a kan damtsen
hanunta dai-dai inda akasa mata robar ,
hannun ta rink'a turawa Hamman tana kuka tana,
"Hamma ka cire min Hamma zasu yanke min hannun Hamma ka cire min".
Cikin mamaki ya kamo hannun yana duddubawa tare da cewa,
" Zasu yanke miki hannun kuma? me a hannun naki?"
shiru yayi dai-dai lokacin da yatsun shi suka sauk'a kan inda akasa mata robar,
d'ago hannun nata yayi da kyau ya duba wurin cikin rawan baki yace,
"Family planning kikayi ne?"
kai ta gyada mai cikin zafin da taji hannun yana mata,
tureta yayi da karfi lokaci d'aya idanu shi sukayi jazir gaba d'aya jikin shi sai rawa yakeyi murya
a hargitse yace,
" fita min a d'aki ki koma can d'akin ki kisan hujjar da zaki gayawa ubangijinmu kisan yadda
zakiyi da jariran dake binki suna kuka ki gaya musu dalilinki na hanasu zuwa duniya Ummul kiji
tsoron Allah ki tuba ki koma gareshi tun lokaci bai k'ure mini ba".
sai kuma ya kamo hannun ya matse da k'arfi har saida tayi k'ara mai cike da gigita,
tureta ya kumayi sannan yace,
"Idan Allah yace ehh toh fa ke Ummul baki isa ki ce a,a ba ki sani idan Allah ya k'addara sai kin
haihu dani wallahi wannan robar bata isa ta hana cikina shiga jikin kiba".
ita kam Umml sai zare ido take tana kuka,
gaba d'aya tsoron shi ya rufeta,
shi kuma murmurshin takaici yati wanda yafi kuka ciwo sannan ya nunata da yatsa yace,
" kina so kija da yin rabbi toh gashi kinga ishara tun ba'aje ko inaba kinga duk abunda kikeyi
koni ban saniba Allah ya sani,
wallahi ki shirya me zaki cewa Abba da Adam da Sadik kome zasuyi miki bazan hanaba kuma
zan gaya musu abinda kikayi zan kuma kaiki gabansu in sunga damage su tsireki ki kuma je ki
samu mahaliccin mu tunda bakya tsoron Allah".
kuka ta kamayi sosai tana,
"Wayyo Allah na dan Allah Hamma ka rufa min asiri wallahi ya Adam zai kusan kasheni gashi
ya Usman baya nan ba wanda zai ceceni kayi hak'uri wallahi bazan sake ba ya Sadik zai
karyani Abbana zaiyi fushi dani Hamma wallahi bazan sake ba".
Cikin tsawa yace,
" ki dai ji tsoron Allah,
kuma ki shirya da sassafe zamu tafi abunki ya fara bani tsoro na lura baki da tausayi".
yana kaiwa nan ya fita ya bar mata d'akin,
binshi tayi a baya tana ta magiya da tuba,
bai kulataba ya wuce d'aya d'akin ita kuwa a parlour ta kwana tana magiya bata kuma samu ta
rumtsa ba.
Washe gari bayan ya dawo masallaci yana shiga parlour tabi bayan shi murya a disashe tace,
"Ayyah Hamma na dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan sakeba kaji na rantse dan Allah karka
gayawa ya Adam".
bai kulata ba ya fara shiri ,
ganin haka ta lallab'a ta d'auki woyarshi ya Usman ta kira,
yana d'agawa cikin sanyin murya yace,
" Hamma na ina sonka yauma nayi mafarkin ka nayi kewarku zan dawo".
Cikin sanyi tace,
"Ya Usman dan Allah ka bawa Hamma Umar hak'uri karya kaini gida kasan ya Adam mugune
zai karyani".
Hannun shi yasa ya dafe k'ahon zuciyar shi dake harbawa cikin sanyi yace,
" Allah ya d'aiyiba min k'anwata, me kikayi wa Hamma na har yasashi fushi yace zai hadaki da
Adam Boss?"
Cikin sakarcin ta gayawa Usman abin da tayin,
tanayi tana kuka,
shi kuwa Hamma Umar ido ya zuba mata cikin tsananin bak'in ciki,
shi kuwa Usman gaba d'aya ranshi ya baci bai tab'a jin haushin Ummul ba akan batun auren su
irin na yau rai a b'ace yaja dogon tsaki cikin fad'a yace,
"Ummul ki sani in kin cutar da Hamma Umar toh kin cutar da zuciyata duk duniya bani da
kamarshi amman kike gaya min bakya sonshi bazaki haihu da shiba Ummul d'an uwana kikeyi
wa haka,
bazan hanashi ba bazan bashi hak'uri ba ya kaiki duk inda zai kaiki kuma kiji a bakina,
nida kaina zan gayawa Adam da Abba".
jin haka saita kuma fashewa da kuka ta mik'awa Hamma Umar d'in woyar baki na rawa tace,
" Dan Allah Hamma Umar