Showing 102001 words to 105000 words out of 142577 words

Chapter 35 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

Dr Umar Ibrahim Umar Shuwa( Hamma Umar)*





*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣4⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





*RESA TUM MARA TUM HEB'A TUM SEYA TUM JOD'E BE GAYOMA WOD'I NAFU*





*I*do suka zubawa Daddy tare da shafa Kai da sauri Usman ya sauk'e kanshi k'asa,
Adam kuma ya yunkura zai tashi sai kuma ya koma ya zauna ganin shiko Daddy ya saki
labulen daya d'ago ya juya ya fice,
batare dayace musu komai ba,
saida suka tabbatar da ya tafi Adam yatashi ya lek'a sannan ya dawo yazauna cikin
zolaya yace,
"Allah yasa Daddy yaji zancen da mukai".
Nura ya gyara zama cikin wasa yace,
"basai in fara kiran abokina da angoba". dukan wasa Usman yakaimai yana murmushi.

Shiko Daddy kai tsaye gidan shi ya wuce haka ya kwana da tunanin abinda yaji yaran
nasu na tattaunawa wannan yasa gari na wayewa tun da suka fito daga masallaci suka
d'unguma b'angaren Hajjajo,
samunta sukai tana lazimi a kan sallaya ganin haka suka samu gefe suka zauna har
takai inda zata tsaya ta d'aga hannu sama tai addu'a suka shafa tare sannan suka
gaisa cikin so da k'auna, kallonsu tayi da alamar tambaya,
Daddy ne ya sake tonk'oshe k'afa yafara magana cikin nutsuwa yace,
"Ummie jiya bayan nafita daga nan sai naje b'angaren yaran nan dan zan aiki Adamu to
ina zuwa kunnena yaji Adam yanata rok'on Usman,
wai yabar shi ya fad'a mana yanason Ummulkhair".
da mamaki Hajjajo ke kallonsu shiko Abba cikin jin dad'i yace, "Alhamdullah Masha
Allah,
in haka ta kasance tabbas muna farin ciki dan naji dad'in wannan magana sosai".
Sannan ya maida duban shi ga Hajjajo da itama da ganinta kasan taji dad'in maganar
yace,
"Ummie kinji ko? yanzu izininki kawai muke nema dan aiwatar da abinda ya dace tunda
dama ita Ummu tak'i kowa kuma inaga shak'uwarsu da Usman zatayi tasiri wurin sa ta amince
dashi".
Ita love Hajjajo sunkuyar da kai tayi tana b'oye k'ollar data fito mata wadda ta fito da
manufofi biyu tace, "namuku izini,
kuyi duk abinda ya dace,

Allah yai muku albarka yasa k'udirin mu yazamo alkhairi amman a nemi yardar Ummu dan
yanzu ita ba budurwa bace ku bata dama tayi zab'in da ranta keso gudun kar a maimaita abinda
ya faru a baya".
had'a baki sukai suka amsa da, "Amin".
sannan Daddy ya kuma gyara zama tare da cewa,
"Insha Allah baza a maimaita abinda ya faru a baya ba dan tabbas munga illar auren dole da
illar auren cushe duk da muna da damar da zamuyi mata zab'i kuma mun mata amman
zuciyarta bata soba gashi sai a k'arshe rayuwar ta katse mana cikin nadama ita kuwa sanin din
kafiyarta ta d'auke farin cikin rayuwar". cikin sanyi Hajjajo tace,
"Allah ya tsare na gama".
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati ".
suka amsa a tare, Matsowa Abba ya sakeyi kusa da d'an uwan shi yace,
"Hussain ina nemawa yarona Usman auren yarinyarka Ummulkhair". Hannunshi Daddy
ya rik'o cikin jin dad'in yadda d'an uwan nashi kemai kara akan yaransu yace,
"Nabaku nabaku Ummulkhair bisa amana da k'auna Allah yasa ayi cikin sa'a kuma
Allah ya sanya alkhairinsa".
Hajjajo da Abba suka amsa da, "Ameen".

Haka sukai ta tattauna yanda zasu tsara,
daga k'arshe Abba ya d'auko wayar shi ya latsa yasa a kunnen shi,
Usman dake zaune kan sallaya yaji wayarshi na k'ara yamik'a hannu Adam dake kan
gado kwance yasa hannu yad'au wayar ya mik'amai dasauri Usman ya amsa kiran
yasa a kunne ya russuna kamar yana ganin me kiran yace, "Assalamu alaika,
Abba ina kwana?". Adam dajin Usman yace Abba ya mik'e daga kwanciyar da yake ya
zauna tsakiyar gadon ya zubawa Usman ido wanda ya saurara yana jin abinda Abban ke
fad'a yana jiran karin bayani,
"To". Usman yace sannan ya sauke wayar ya kalli Adam yace, "Abba na kiranmu a
palour Hajjajo".
daga haka ya tashi ya ajiye wayar yafice,
cikin happy yayi d'an k'ara tare da cewa,
"yes". sannan ya sakko daga gadon yafita cikin zumud'i da addu ar Allah yasa abinda
yake zato ne.

A palour Hajjajo Usman yayi sallama suka amsamai yasami k'asa gefen Abba ya zauna
sannan Adam ma ya shigo yasami gefen Daddy ya zauna,Usman ne yafara gaida
Hajjajo sannan yakuma gaida iyayen nashi sannan Adam ma yayi tashi gaisuwar sai
kuma suka saurara cikin nutsuwa Abba yafara magana dacewa, "Usman banji dad'in yadda kuka waremu kaida d'an uwanka Adam kuke b'oye
damuwarku ku kad'ai ba,
duk da nayar da komai lokacine kuma ga lokacin yayi dan haka inaso ka shaida
sannan d'an uwanka ya shaida kamar yadda mahaifiyata ta shaida d'an ni mahaifinka
na nema maka auren y'ar d'an uwana Ummul khairi".

sanyi, dadi, fad'uwar gaba gabaki d'aya suka ziyarci zuciyar Usman da haka ya kasa jin
komai da gane komai da suke fad'a,
Abbane ya dawo dashi daga duniyar daya tafi ta hanyar dafa kafad'ar shi yace,
"Allah yamaka albarka Allah ya baka ikon kula da d'an d'an uwanka". Cikin nutsuwa da
kwantar da kai k'asa Usman murya a sanyaye yace,
"Daddy nagode Allah ya saka da alkhairi". sai kuma yakai dubanshi ga Adam da dad'i
ya cikawa ciki yanata murmushi yace,
"Adam katayani godiya gun Abba".
Shiko Adam washe baki yayi kai kace shi akaima kyautar matar yace,
"Daddy mun gode Allah ya k'ara girma".
Usman yasake matsawa kusa da Abban yai k'asa da murya cikin biyeyya da yace,
"Abba nagode Allah ya k'ara arzik'i,
amin godiya gun Daddy".
sai kuma ya d'anyi shiru kai ya kuma sunkuyarwa a hankali yaci gaba da cewa,
"Sannan inaso in nemi wata alfarma agurin ku".
Abba ne ya sa hannu ya shafa kan Usman yace,
"a shirye muke mu samar maka da farin ciki kada ka damu ka fad'i duk abinda kake so
insha Allahu zamuyi maka danko munada yak'inin bazaka nemi abinda bazamu iyaba".
sauke ajiyar zuciya yayi sannan murya na rawa yace,
"Abba dan Allah kumin alfarma kubani dama in nemi yardar Ummul,
da kaina kar ayi mata dole a bari ta amince dani da kanta,
Daddy inaso inganta cikin farin ciki sannan hakan shizai bani damar k'arasa kula da ita
da yarona cikin jin dad'i, ina nufin zatafi jin dad'i idan anyi komai da yardar ta".

Shirune ya ratsa palour na y'an mintina sannan Daddy yai gyaran murya tare da cewa,
"Usman Allah yayi maka albarka, hak'ik'a wannan kalaman naka sunkai ayi maka uzuri
kamar yadda ka buk'ata kuma hakan ya dad'a tabbatar mana da cewa kaine kad'ai
zaka iya dawo mata da farin cikin ta, Allah yamaka albarka Allah yabaka ikon kulawa da iyalinka".
"Amin". Suka amsa sannan Abba yace,
"to duk abinda zance Daddyn ku yafad'a dan haka indai babu wata maganar sai kuje
kuyi abinda zakuyi,
Allah yayi muku Albarka ya jikan yayanku yakai haske kabarin shi".
duka suka amsa da, "Amin".
Daddy yace to Adam kayi mana addu'a mu tashi,
daga haka taron ya tashi kowanne zuciyar shi na cikin nishad'i.

Suna fita Adam ya kama hannun Usman yace,
"congrat bros". Murmushi yayi yace, "nagode".
Adam yasake matse hannun Usman dake rik'e a hannun shi yace, "nidai naso kabari
ayi auren nan kasan yadda Ummul take balle yanzu yaza ai kace saida amincewar ta".
a hankali ya janye hannun shi ya shafa kanshi ya kalli Adam cikin lumshe ido da sauk'e
sassanyar numfashi yace,

"Adam hak'ik'a inason kasancewa da Ummul ina son rayuwa da ita k'ark'ashin inuwar sure,
amma kasani a yanzu soyayya hud'u nake mata, nafarko inamata so irin na ma a bota
soyayya da kauna wanda Allah ne ya dasamin hakan a zuciyata,
na biyu inason Ummul soyayya ta yaya da k'anwarsa, na uku itace abinda Hammana
yafiso da k'auna, sannan itace tafara haifamin d'ana jinina,
kaga wad'annan suke jana kuma suke bani tabbaci da kwarin gwiwar insha Allah zanyi
nasarar samar mata farin cikin data rasa a baya".
ajiyar zuciya yayi sannan yacigaba da cewa,
"Zan jure duk wata damuwa akan haka,
nasan burinka insami farin cikine amma inaso kacigaba da tayani addu'a Allah ya sanya
sona a zuciyar Ummu".
Magan ganun Usman ne suka kashe wa Adam jiki ya sa hannu ya rungumo shi suka
rungumi juna suka juya zasu tafi b'angarensu Keenan,
muryar Nanne c ta tsai dasu suka juyo inda take,
ita ko cikin jin dad'in ganin su a haka tace, "y'ay'an Abba me kuka samu ne? na ganku
a cikin nishad'i".
K'asa sukai suka tsuguna a tare suka ce "ina kwana".
Ammice ta amsa da, "lafiya lau". Kasancewar indai Ammi naguri Nanne bata amsa
gaisuwar da za ai daga farko,
sannan suka sake gaida Nanne ta amsa cikin sakin fuska tace, "kuje abinku muma
zamu gaida mai sunan Ummul ne".
Da haka suka shige sukuma suka kama hanyar b'angarensu.

Dab da zasu shigene Usman yasaki hannun Adam daya rik'o yace, "kaga jeka ni bazan
iya komai ba saina dubo Noor hayati name da my son".
dariya Adam yasa harda rik'e ciki,
shiko Usman ko kallo bai ishe shiba ya juya yai tafiyar shi.

Hargowar Farouq yajiyo tun kafin ya shigo,
yana k'arasowa ya sauke idanuwan shi kan Ummul dake zaune a bakin gado rik'e da
rigar Farouq a hannu ta shagwab'e fuska kamar zatai kuka,
inda take kallo shima ya kalla Farouq ne tsaye ya mak'ale kafad'a ya turo baki gaba
yana zare ido, abin nasu dariya yaso bashi amma saboda gudun rigimar Ummul ya
b'oye dariyar yazauna bakin gadon kusa da Ummul yace, "meya had'aku ne?". Kafin tai
magana Farouq ya taho yafad'a jikin Usman yace, "Abee imma ne".
k'ara rungume shi yayi a jikin shi yace, "Ummuna wai menene?".
Itama k'ara shagwab'e fuskar tai tace,
"tun dazu kowanne kaya na d'auko sai ya gudu yace bashi ba ni har nagaji".
Murmushi Usman yayi yana jinjina aikin gaban shi na rarrashin y'an shagwab'a biyu
sannan yasa hannu yakarb'i rigar daga hannun Ummul yace,
"yaron kirki yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login