Showing 12001 words to 15000 words out of 142577 words

Chapter 5 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

d'an sun kusa k'arewa."

"Toh" yace sannan suka fito suka nufi part d'insu Usman ne ya fara wonka sannan yana fita
Umar ya fitomai da kayan da zai saka,
shima ya shiga yayi wonkan yana fitowa ya shirya tsab,
shiga irin d'aya sukayi shigar shuwa'arab shigar da tafi kama da ta larabawa,
sun fito ras tamkar tagwaye komai nasu irin d'aya hatta tafiyar su farar fatarsu sajen fuskarsu
kamace ta sak da sak suke sun fito ras tamkar taurari sai shek'i da k'amshi suke zubawa,
Suna fitowa Motar Umar suka shiga shi yake jan motar kai tsaye al'ameen restaurant suka nufa,
suna zuwa suka shiga can ciki,
lokaci d'aya aka had'a musu abinci dan sun saba zuwa wurin su maikatan har sunsan iya
abincin da Usman ke iyaci so dama suna zuwa za'a kawo musu komai yadda ya kamata,
kamar yaro Umar ya tasa Usman a gaba saida yaci yayi tik sannan ya biya komai suka fito,

daga nan kuma clinic d'in suka wuce anan ya k'ara duba lafiyar d'an uwan nashi suna fitowa
nan,
kai tasaye katafaren chemist d'inshi suka wuce,
ya had'a komai na maganin Usman d'in sannan,
suna fita Umar ya sake jansu sai dicency super market ,
suna zuwa Umar ya had'e musu duk wani abin buk'atan su sannan aka loda musu a mota suka
fito suka nufi gida.


Ummul kuwa da Mustapha hirarsu sukayi sosai gaba d'aya sun susucewa juna hak'ik'a
Mustapha yana son Ummul so na hak'ik'a haka itama take mishi so da iya gaskiyarta hirarsu
suke basuma san maggariba tayiba saida suka ji kiran sallah,
Mustaphanne ya kalleta cikin tarin so ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya murya can
k'asa yace.
"Ummul idanuna basa gajiya da ganin kekyawar fuskar ki! kunnuwana basa k'osawa da jin
sautin ki mai zak'i ! hancina bayi da wani b'uri daya wuce shak'ar k'amshin ki,
Ummul ina sonki son da bana yiwa kaina."

Tafin hannun ta tasa ta rufe fuskar ta cikin jin dad'i da kunya tace.
"Habeebi dani da murya ta da fuskarta da k'amshi na duk naka ne."
Ido ya tsura mata tare da tasowa yazo gaban ta durk'usawa yayi a guiwowin shi a k'asa ido ya
lumshe sannan ya bud'e su a hankali yace.
"Ina jin tsoro Ummul inajin tsoron karna rasaki Ummul har yanzu baki zama tawaba gashi ban
san yaushe Allah zai mallaka min keba ina sonki inason mu kasance ma'aurata Ummul kimin
al'k'awarin duk rinsi kina tare dani ki min tattalin kanki kada idon wani namiji ya dira a kanki."

Kallon shi tayi cikin murmushi tace.
"Ako da yaushe ina shaida maka kai Habeebi da'iman ne a gareni zuciya ta ba inda wani zai
samu ma tsuguni."

Ajiyan zuciya ya sauk'e sannan ya mik'e yana kallon ta,
itama mik'ewa tayi ta d'an matsa gefen shi,
cikin sanyi tace.
"Sai yaushe zaka kuma zuwa?."

"Ko gobe in kina so zanzo, ina damaturu ina potiskum garin masoyi baya nida."

"Gobe kam ai baka huta bama tukun."

"Hutu kuma Ummul aini bani da wani hutu har sai na ganki cikin gida na."

Murmushi tayi sannan tace,
" toh muje kayi sallan maggariba sai ka tafi kar dare ya maka."

"Kin gaji da ganina ne?."
"Inko zangaji da kallon fuskar ka toh zan gaji da kallon tawa fuskar kenan."

Murmushi yayi ya mik'a mata hannu wai suyi musabaha,
kai ta sunkuyar a hankali tace.
"Da saura."

kai ya juya sannan ya had'e hannu a k'irjin yayi muryar tausayin yace.
"Haka ne toh da wacce Kalmar za'a sallameni?."

Juyawa tayi ta fara fita yana biye da ita a baya sunzo dai-dai inda zatayi cikin gida shiko zaiyi
woje tace.
"Laisa Lee misluka abadan ya habeebi.
gareni bakada damka masoyina,
ina sonka so mai tsananin Habeebi zanyi maka tattalin kaina dan cika zuciyar ka da farin ciki."

Mustapha kam tamkar ya had'iye ta yakeji da tsabar k'aunar da da hali zai nuna mata sonta a fili
amman ba dama,
sai murmushi yayi tare da cewa.
"Anti sururi,
kece cikon farin cikina."

Ya matsota zaiyi magana kenan yaga Hamma Umar dake zaune can gefen yana al'wala,
haka yasa ya sallama ta,
tayi cikin gida shiko yaje kusa da Hamma Umar d'in shima al'awalan yayi sannan suka tafi
masallaci,
ana idar da sallan suka nufi gida a bak'in gate Mustapha ya tsayai da Aliyu ya fito da manyan
lododi guda biyu ya bawa Aliyun yace,
ya kaiwa Ummul .

Shi kuwa ya kama hanyar komawa damaturu

A parlour suka baje tarkacen daya kawo mata kayan k'amshi ne sai atampopi guda 2 da les 2
sai shadda 2 sai yadukan laffaya masu kyau da taushi guda 3 ,
Anty Halima sai kallon Ummul take tana .
"Iyeeh manyan masoya."

Nenne kuma cewa tayi.
"Maza Ummul had'e kayayya kin nan ki adana ko turaren bazaki fesaba."

Fuska a marairaice tace.
"Ayyah Nenne am kullum Mustapha ya kawo min abu sai ki hanani amfani dashi ban san me
yasa ba ko kema bakya sonshi ne Nenne?."

Murmushi Nenne tayi sannan tace.
"Me yasa ina son Mustapha ai yaron kirki ne kawai dai wannan Al',adarmu ce budurwa bata
amfani da kayan saurayi sai in sunyi aure,
mu a gunmu in kiyi amfani da kayan saurayi kamar kasawa ce,
toh kinga ke kuma ba abinda muka regeki dashi."

Murmushi tayi ta tattara kayan,
sannan suka ci gaba da hira,
Abba da Umar da Usman dasu ya Adam kuma saida sukayi sallan ishah sannan suka dawo,
suna shigowa su Usman sukayi parlour Nenne Hamma Umar kuma Abba ya kirashi suka tafi
parlour Hajjajo,
suna shiga suka samu Daddy ma yazo gun Hajjajon.

Su Usman ko suna shiga,
cikin halin girma Usman ya kalli Halima fuska a tsare yace.
"Ke Sadiya har yanzu baki tafi ba?."

Cikin girmamawa tace.
"Ya Usman yanzu zan tafi."

Mik'ewa yayi tare da cewa.
"Muje in maida ki kinzo kin wuni bai kamata ki kai dare ba."

Maza Ummul ta mik'e tare da cewa.
"Yauwa ya Usman muje in rakaku."

Kai ya gyad'a yace.
"Oga Mustapha ya barki ne?."
"Mustapha kuma ji ya Usman fa dama Mustapha ne ke hanani zuwa unguwa?."

Juyawa yayi ya fita Sadiya na biye dashi a baya ita kuma Ummul tana gefen shi,
kallon ta ya d'an yi sannan yace.
"Keda ki kace Mustapha ya fimu matsayi."

Murmushi tayi tare da rufe idon ta,
shi kuma Sadiya ya kalla cikin murmushi yace.
"Shiga baya kinsan Ummal da son zaman gaban mota kamar ba fullatana."

Dariya sukayi sannan suka tafi.

A parlour Hajjajo kuwa bayan su Abba sun d'anyi hira Abba yayi gyaran murya cikin kula ya kalli
Daddy sannan ya kalli mahaifiyar su Hajjajo sai ya kuma kalli Hamma Umar cikin wani irin

yanayi yace.
"Farouq ina maganar aure da mukayi da kai?."
Kai ya sunkuyar yayi shiru,
ido Daddy ya tsura mishi tare da cewa.
"Farouq shi fa aure dolene a gareka tunda Allah bai hanaka yadda zakayi ba,
shin a zatonka munajin dad'in zaman ka hakan ne,
Farouq ka sani duk girman mutun da darajarsa da matsayinsa matukar baiyi aure ba toh bai
cika mutun ba."

har lau dai baiyi magana ba sai sunkuyar da kai ya k'ara yi,
a hankali Daddy yace.
"Farouq me kake jira ne? da har yanzu baka fara maganar aure ba."

Kanshi a sunkuye murya can k'asa a hankali yace.
"Daddy ina jiran......





By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 7⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




*"Abba* ina jiran Usman ne."
ido Abba da Daddy suka zuba mishi Hajjajo ko kai ta jinjina cikin mamaki tace.
"Usman kana jiran Usman kuma? toh ka jirashi a kan me? me zakayi mishi da kake jiran shi?."
shiru bai amsa mata ba bai kuma kalleta ba sai zaman shi da ya d'an gyara,
juyowa gaban shi Abba yayi cikin son fahimtar sa yace.
"Farouq!
Usman kake jira? meyasa kake jiran shi d'in? ko so kake kuyi aure rana d'aya?."

kanshi ya d'an d'ago cikin tok'k'oshi wuyanshi kan kafad'arsa cikin sanyi ya kalli Abba da Daddy
murya a raunane yace.
"Abba ina jiran Usman ne ! Abba inaso inga Usman ya samu mai kula dashi kafin nayi nesa
dashi ! Abba in nayi aure yanzu wazai kula da Usman kaga baya son shan maganin shi kuma
baya son bin dokokin doctors kuma kaga inba ana samishi idoba komai ya samu zaici,
gashi ko yau saida yace min k'irjin shi na mishi nauyi."

Sai kuma yayi shiru dan muryarsa da ta fara rawa,
dan har cikin ranshi yake jin tausayin d'an uwanshi da yana da damar karb'awa Usman ciwon
daya karb'a mishi.

Abban ma shiru yayi tausayin 'yay'an d'an uwan nashi na ratsashi yana son Usman da Umar a
ranshi fiye da yaran shi.

Daddy ne ya d'an gyara zama cikin kallon Hajjajo da ta fara zubda k'ollah cikin k'arfin haki yace.
"Farouq aure rahama ne meyasa kake ganin aure zai nesan taka da d'an uwanka Allah shike
kula da Usman ba wayon mu ko dabararmu ba."

Kai ya sunkuyar a hankali yace.
"Daddy inajin tsoron barin Usman shi kad'ai dan baya son shan magani gashi dole dai in nayi
aure zan koma cikin Damaturu da zama,
Abba gashi bansan matar da zan auraba,
gashi matan yanzu basa son dangin miji sai k'alilan ake samun masu son dangin mijin su,
tayiwu nayi aure matar ta nuna bata son Usman yana rab'ata ko taga na fifita Usman a kanta
har azo ta fara tunanin shiga tsaka nina da d'an uwana."

Gaba d'aya parlour shiru sukayi cikin nazartan kalaman Hamma Umar tabbas matan yanzu
k'alilan ke son dangin miji,
kuma kamar yadda ya fad'a Usman tamkar yaro yake a gaban Umar,
a hankali Abba yace.
"Toh kai Farouq yanzu haka zakayi ta zama kenan?,
ko dai auren ne baka so Farouq?."

Kai ya jinjina cikin sanyin murya da tausayawa kanshi a hankali yace.
"A,a Abba bawai auren ne bana soba!
Abba ni bansan matar da zan aura bane ,
Abba ban san ya zanyi in samo matar da zata tayini kula da Usman ba."

Sai ya kuma juyawa ya kalli Daddy da Hajjajo da take ta zubda k'ollah a hankali yace.
"Ni da zan samu sai Usman yayi aure ya samu matar da zata kula dashi,
in yaso daga nan sai na nemi auren,
amman yanzu ina tsoron nayi aure nabar Usman gashi ni bansan ya zan fara neman auren
bama bare na nemi wacce zata tayani kula da Usman."

Gaba d'ayan su shiru suka yi kowa da tunanin dake ranshi.

Cikin sanyi Abba yace.
"Umar ba dai so kake ka auri matar da zata taya ka kula da Usman ba.?"

Kai ya jinjina tare da murza yatsun hannun shi.

Shiko Abba sai juyawa yayi ya fiskan ci d'an uwanshi Daddy kenan,
Hajjajo kuwa shiru tayi cikin zurfin tunani...


Su Ya Usman kuwa suna zuwa k'ofar gidan Anty Halima suka had'u da mijin ta zaije d'auko ta,
ganin ya Usman ya dawo da ita suka gaisa,
da mijin k'anwar tashi sannan suka juya shida Ummul suka nufi gida.

Suna juyawa Ummul ta kalleshi cikin murmushi tace.
"Yauwa ya Usman ya batun koyamin tuk'in ne? tun da muka fita sau 2 bamu kuma fitaba."

Juyawa yayi ya d'an kalleta a fakaice yace.
"Ke da kike da Mustapha ai shi zai koya miki."

Baki ta d'an tura tare da cewa.
"Wai ya Usman kaima ka tsani Mustapha ne kam? wai me yasa bakwa son bawan Allah nanne
kam?."
Baki ya d'an tab'e yace.
"A,a Hajia ni bance ba,
bance miki bana sonshi ba."

"Toh ka koya min kaji ko Ya Usman na,
Habeebi Katir katir."
dariya yayi tare da cewa.
"Allah ko Ummul kin rainani watoma Mustapha shine Habeebi da'iman ni kuwa Habeebi
katir-katir na zama.?"

murmushi tayi tare da cewa.
"Ina sonka ya Usman dinnan."
Murmushi yayi yace.
"Allah d'aiyi ba."
sai kuma sukaci gaba da dariya,
suna cikin dariyar phone d'in Usman ya fara suwa a hankali yana d'agawa yaga Nuru ne,
juyawa yayi ya kalli Ummul dake ta kiciniyar murza siterin motar tare da taima konshi,
a hankali yace.

"Ga lailamajanun yana kirana."
Murmushi tayi tace .
"Toh yauma zaku je zancen kenan?."
Kai ya gyad'a mata tare da amsa kiran
yana d'agawa Nuru yace.
"Kai Gwanja ina kake ne? gani nazo gida Aliyu yace ka fita."

Dariya yayi tare da cewa
"Toh d'an anace naga jiya mafa kaje shine yauma zaka wani takura ni,
toh yau nima na fara zuwa zance gani ga Baby na tana ta cemin,
Ina sonka niko nace Allah d'ai yiba."

Shiko Nuru tsaki yaja yace.
"Kai da Allah ka same ni a k'ofar gidan su."

"Toh" yace sannan ya katse kiran,
hannu yasa ya d'an ture hannun Ummul dake kan nashi yana kallon titin yace.
"Bari sai gobe zamu fita da rana zan koya miki yanzu muje in maida ke gida dan zanje gun Nuru
inban jeba zaita damuna."
"Toh tace sannan tace.
" Ya Usman ina son fruits."
Kai ya gyad'a sannan ya tsaya a gefen titin yaje ya saya mata sannan ya dawo suka tafi,
a bak'in gate ya sauk'e ta da nufin zai juya,
da sauri tace.
"A a ya Usman zomuje na yanka maka fruits d'in kasha kafin ka tafi."

"Ki bari sai na dawo."
"A a wallahi ni dai kazo mu shiga inya so na gyara maka ka tafi dashi ko a cikin mota zaka ci."

Binta yayi suka shiga cikin gida kai tsaye kitchen d'in Nenne suka shiga , gaban sink ta tsaya
tare da
wonke su tsab sannan ta jawo wata yar roba mai kyau ta zuba mishi,
suna fitowa Aliyu ya kalli Ummul yace.
"In anga kina kiciniya dai toh kinga kayan zak'ine,
nanne za'aga k'wazon ki."

"Eh d'in me ruwan ka da ni d'an sa ido kawai."

Kitchen d'in ya shige yana cewa.
"Uhum shazumami kawai kin iya shan zak'i kin iya yi mana kuka in cikin ki ya fara ciwo,
kita b'are mana baki."

Kanshi tayi da sauri zata kai mishi duka,

shi ko zillewa yayi ya koma bayan Ya Adam dake harararta yace.
"Ai gaskiya ce Aliyu ya fad'a kike wani fiffik'ewa ke zakiyi duka."

Shi dai Ya Usman dariya yayi ya jawo hannun ta ya nufi parlour Hajjajo da ita yana cewa.
"Ko Hamma Umar mai son kalota miki laifi bazaice fruits zai saki ciwon ciki ba,
k'anwata sha abinki."

ba tare da tunanin su Abba na cikan d'akin ba suka shiga tare da sallama.

Suna shiga Hamma Umar ya d'ago kanshi fuska a tsuke ya d'an harari Ummul dake rik'e da
Apple a hannun ta tana ci,
baki ta tura tare da kauda kanta da sauri a ranta tana.
"Mugu ko yaushe fuska a tsuke."
Shi ko Usman cikin dariya yace.
"Abba yau mitin kukeyi da Hajjajo da d'an jikinta a gefe ne."

Kallon shi kawai su Abba sukayi zuk'atan su cike da alhinin irin son da Umar keyi mishi,
shiko Usman ganin yadda suke zaune daga dukan alama magana mai mahimmanci sukeyi sai
ya d'an zauna tare da gaida su,
itako Ummul dama tuni ta fita ta tsaya a barandar ganin bai fito bane tace.
"Ya Usman bari in kai maka robar cikin motar ko."
"Toh muje nima gani nan zuwa."

Juyawa tayi ta nufi harabar gidan nasu,
shima yana gaida su ya fito yabi bayan ta,
robar ta ajiye mishi sannan ta koma cikin gida, tana shiga Mustapha ya kira dan shaida mata ya
isa lafiya,
daga nan kuma sukaci gaba da hira,
shi kuwa ya Usman wurin abokin shi Nuru ya nufa,


A parlour hajjajo kuwa cikin zurfin tunani Abba yabi bayan Usman da kallo a hankali ya sauk'e
ajiyan zuciya sannan ya kalli Hamma Umar cikin nitsuwa,
shiko Hamma Umar kanshi ya sunkuyar,
kai Abba ya juya ya fuskanci Daddy da Hajjajo ajiyar zuciya ya kumayi sannan cikin yanke
hukunci yace.
"D'an uwana Hussani da maifiyata Ku zama shaida a gareni na bada auren Ummul khairi ga
d'an d'an uwana ,
na bada auren ta ga shi.....

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 8⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Fans na fatan alkhairi a gareni baki d'aya ina mai Baku hak'uri kwana biyu zaku jini shiru
sakama kon tafiyar da zanyi gobe zanyi tafiya YOLA 2 KANO kuma biki zani ba damar yin
typing sai Allah ya dawo dani lafiya ina barar addu'arku gareni*



*INA kuke masoyan yan gaskiya Firdausi Sodaggi tare da Hassana d'an larabawa Wannan shafi
nakune INA al'fahari daku*


*TABITAL FULAKU group GARKUWAR FULANI group AYSHA ALI GARKUWA fans GARKUWA
AYSHA&UMMEE novels tare da BANDIRAWO fans kun zamoni na zamo Ku Kusani kab groups
na inajin daku kamar yadda kuke ji dani bani da kamarku a duniyar gizo-gizo🤝�😘*



*"N*a bawa Umar auren Ummul khairi,
ku sani na bashi auren ta na kuma yanke hukuncin za,ayi bikin nanda wani d'an lokoci domin
aurar dasu ga juna shine mafita da zamu sama musu ."

Daddy kam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login