Showing 105001 words to 108000 words out of 142577 words
Chapter 36 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
hakuri kasa wannan yanzu anjima kad'an sai in canja maka wasu ko?".
d'aga kai yayi yace cikin gwaranci, "ambuma". hannu Usman ya mik'o ya mak'ale yatsu
guda biyu yace,
"e". aiko dariya Farouq yasaka sannan yasa yatsanshi tsakanin na Abeen nashi ya raba
yatsun da Usman d'in ya had'a,
sannan ya mik'a kai Usman ya sakamai rigar yajuya ya fice da gudu,
ido suka rakashi dashi sannan Ummul tasuke ajiyar zuciya tai k'asa da kai tace,
"Ina kwana".
Ido ya zuba mata na tsahon 20 second sannan yace,
" waya ce maki a haka ake gaida masoyi?".
d'an turo baki tayi ta turo lips d'inta gaba ta mik'e zata fice daga d'akin,
cikin zafin nama ya rik'o hannunta abinda yajine ya ratsa dukkan sassan jikin shi yasa
yayi saurin sakin hannun nata itako tacigaba da tafiya,
ganin hakan ya dafe kirjin shi da hannun shi d'aya yace,
"washh". da sauri ta juyo ta dawo kusa dashi ta zauna tad'ora hannunta akan nashi tai
rau-rau da idanu kamar zatai kuka tace, Ya Usman meke damunka? k'irjin ko? ". zame
hannun ta yayi daga nashi yace,
"so, soyayyarki ce take damuna Ummul soyeyyar kice take son min illah a zuciyata da jikina".
Yanda ya kafeta da idanuwan shi masu zuba kasala yasa tai k'asa dakai ta marai raice
fuska cikin sanyin murya tace,
" dan Allah kadena min haka kaga kaban tsoro nazaci ciwo kakeji". murmushi yayi cikin
jin dad'i tare dayi mata wani solon kallo mai cike da k'auna sannan yace, "Ummuna bakyaso
inji ciwon ne?".
Dakai ta amsamai alamar "eh".
sannan ta tashi zata fice,
da sauri ya taso yasha gaban ta ita kuwa ta rink'ayin baya-baya har ta isa jikin gini,
ido ya tsura mata cikin laso lips enshi murya can k'asa yace,
"Ina sonki so mai tarin yawa ina son rayuwa dake da Farouk na wuri d'aya ki kijik'ana ki
tausayawa tuzurun yayanki Ummul na gaji da zama ba mata na matsu da yin aure ki tausayi
min nida Farouq kar muyi maraici biyu ba Hamma na kema kuma kiyi nesa damu baza muji
dad'in rayuwa ba". k'ara matsowa kusa da ita yayi cikin yin k'asa da murya yace,
"Ummuna ina son aure wallahi na fa gaji da zaman gidan ina son mace kusa dani hak'uri na ya
fara gazawa kiyi hak'uri ki yarda dani ki bani dama zan dawo miki da farin cikin ki kinji
Ummuna".
rab'awa tayi gefen shi cikin jin tsananin kunya da tsoron ya Usman d'in dan ta lura baida sauk'i
ficewa tayi ta barshi a d'akin,
shiko murmushi yayi yamik'e yafice.
A ranar bayan ya tashi daga aiki,
kai tsaye ya wuce Ahlul bhait communication ya seyowa Ummul d'inshi waya k'irar
Iphone 6,
sannan ya nufi gida yanajin farin ciki sosai a ranshi dan ya tabbatar ta woyar zai k'ara
samun damar isar da sok'onnin soyeyyarshi.
A gida kuwa yana isa kai tsaye part d'in kakarsu ya nufa,
zaune ya samesu a palour Hajjajo yana shiga ya d'an rusuna ya gaida Hajjajo da Ammi da
Nanne,
sannan ya zauna a k'asan carpet,
Sadiq ne yafara gaida shi sannan Aliyu Ummul ce k'arshe sannan ya dubi Nanne yace,
"Ina Farouq fa?
Murmushi Nenne tayi sannan tace,
"Sun fita yanzun nan da Adam,
kasan shi dason yawo". hannu yasa cikin ledar daya shigo da ita yaciro kwalin wayar
ya mik'awa Aliyu dake kusa dashi yace mik'ama Ummul saika saka mata sim card d'in ,
murna Aliyu yake yasa hannu biyu ya karb'a ya mik'ama Ammi ta juyata tace,
"to angode Allah yayi albarka".
sai ta mik'ama Nanne tace,
" Gashi asamana albarka Ummu na tayi woya".
hannu tasa ta karb'a tayi godiya sannan tamik'a ma Hajjajo,
da sauri Hajjajo takama kwalin da kokawa,
sai kuma Aliyu yayi saurin kwacewa yace, "ke tsohuwa karki mana b'arna fa ya Karo'arma
sai da dambe".
Yamutse fuska tai tace,
"garani ai".
dariya sukayi sannan Ammi ta tashi tana gaba Nanne na binta suka fice,
Cikin zumud'i Aliyu ya had'a waya yana washe baki ya mik'awa Ummul dake zaune tana
wasa da yatsun ta kaita girgizamai alamar bataso,
Shiko Usman da tunda ya shigo ya keta satar kallon ta sai yayi saurin kauda kansa
kamar baiga me sukeba yatashi yafice,
Shi kuwa Aliyu dawowa yayi kusa da Ummul d'in yace,
"Haba Aunty meyasa kike hakane?
yanzu dayaga kinnuna bakya so ai bazaiji dad'i ba,
kuma bakya ganin zata d'ebe miki kewa da tunani,
aduk lokacin da kike ke kadai,
dan Allah ki karb'a kisa albarka".
Batace komai ba sai idanu data zubamai tana zubda k'ollah cikin sanyi ta fara kuka murya
can k'asa tace,
"Aliyu kai gani kake akwai wani abu da zai mantar dani Hamma Umar ne Aliyu gani kake woya
zata ciremin dana sanin dana saka rayuwata a cikine Aliyu gani kuko a shekara uku zan manta
yadda aka rebani da Hamma Umar ne Aliyu bayan qura'an ba wani abu da nake rik'ewa inji
sanyi a raina waya zata tuno min da Hamma na dan ita ce kyautar da ya bani a randa zai rasu
zai fita ya ajiye min woyarshi k'asan pillow na yace min Khairi na ga wannan zai d'ebe miki
kewa kuma zan rink'a kiranki inji ya jikin ki".
sai ta kuma fashewa da kuka ta rik'o hannun Aliyu murya na rawa tace,
"Inama woya zata iya had'ani da Hamma Umar da na gaya mishi ina sonshi so na hak'ik'a ina
sonshi son da bana yiwa kaina da zan dauwama ina mishi zantu kan so amman ina Hamma na
yayi min nisa Aliyu ina son Hamma Umar wallahi ina sonshi Aliyu nayi nadama a rayuwata nayi
laifi mai munu ina ganin sakayyar rashin yiwa iyaye biyeyya ina ganin illar taurin kai ina ganin
munin tsanar masoyi da nabi zab'in iyayena da bazanyi dana sani ba da bazanyi nadama ba".
Cikin zubda k'ollah Aliyun yace,
"Abun da Hamma Umar yafi so shine ya Usman Anty Ummu in kinso ya Usman Hamma Umar
zaiyi farin ciki ki yarda da Ya Usman ku had'u ku reni Farouq ku rabashi da agolanci ki karb'i
kyautar ya Usman ko dan kar ranshi ya b'aci kin san matsalar sa dan Allah ki amshi woyar kinji
ko". shiru tayi ta tsura mai ido dan Aliyu kamar k'awa yake a gareta kuma abokin shawara kuma
abokin kuka kamar yadda Hamma Umar ya fad'a ganin tayi shiru ne,
shiko yasake cewa , " kin yarda?".
saida ta k'ureshi da ido sannan cikin kosawa da nacinshi tace,
"eh".
Hajjajo da kamar jira take Ummul ta amsa tamik'e tace, "gulmammiya kawai kin sa kanki
cikin nadama da taurin kanki".
sannan itama tayi shigewar ta bedroom d'inta tabarsu a wurin ita da Auta,
Aliyu ya k'ara matsowa kusa da Ummul yace, " kinga idan na bud'e miki Whatsapp zaki
rink'a chat damu, sannan facebook kirink'a ganin labaru kinga ai zakiji dad'i".
Kallonshi kawai take yana dannawa yace kinga ga number ki nasaka maki number duk
y'an gidan nan harda Abba,
itadai ta zuba ido tana kallon cikin wayar a haka ya seta komai harda whatsapp da
facebook ya sanya mata hoton Farouq akan dp ta sannan ya kira mata Aunty Halima
tana d'auka yace,
"number aunty Ummul ce,
kisa asata a groups da kike dan d'ebe mata kewa".
Itama murna tayi sosai sannan tai addu'a take tabada number Ummul da aka sata a
group na Hausa novel Aliyu ma yayi adding nata a family group nasu wanda shine
admin,
har magariba ta samesu agun sannan suka tashi suka fito a hanya Aliyu ke cewa
Ummul,
"Idan kinje kin nutsu zakiga number ya Usma saiki kira kice kin gode kinji Anty na?".
Bata cikiyi wa Aliyu musuba dan shiya zama kamar k'awarta haka yasa ta gyad'a mai kai
alamar toh.
K'arfe 9:30 na dare Ummul tana kwance ganin zata fara aikin ta na tunani da kuka da
take duk darene yasa ta janyo wayar ta kunna sannan ta lalubo number ya Usman ta
danna kira aiko bugu d'aya ya d'auka daman yanada niyyar kiranta sallama yayi ta
amsamai sannan shiru ya biyo baya, a hankali ta katse shirun da cewa,
"ya Usman nagode". wata irin ajiyar zuciya ya sauke,
tare da lumshe ido a hankali yace,
"Nima nagode da kika amshi keutata,
Ummu ina sonki ina son auren ki kiyi hak'uri ki yarda da k'addararki ta sirens dan inba mutuwa
ba ba abinda zaisa ni Usman k'anin Umar nace zan aureki da haka shima wannan ki sanyashi a
cikin littafin k'addarar rayuwarmu Ummu na ina sonki ki shigo rayuwata ki zame min gurbin
Hamma na nima na zame miki gurbin sa,
Ummu wallahi da gaske ina murad'in yin aure na gaji da zaman kad'aici ina son samun me
d'ebemin kewa da kawarmin da buk'atuna ko zan samu sukuni a rayuwa ta Ummu ina da
buk'atar ki kusa dani". saurin cire wayar tayi daga kunnenta ta katse kiran,
tana jin zuciyarta na bugawa da k'arfi salon maganganun Ya Usman d'in nata suna bata tsoro
dan a hankali ta fara fahimtar yana yin irin tasa halittar Kuma,
Kamar zata ajiye wayar sai kuma ta bud'e data,
aiko sak'onni sukayi ta shigowa saida ta bud'e na sauran groups d'in sannan ta dawo
kan wanda taga sakon shi sunfi yawa mai suna 'COOL NOVELS ' na Hayatu Baba
Zubairu, ta bude magan ganu tarink'a gani anayi a group din daga dukkan alamu a kan novel
suke tattaunawa, wata tace daga cikin members na group d'in tace,
"Gaskiya Meenal ta Hamma Haiydar ce". wasu suce,
"A barwa Dr jabeer".
wasu suce General Aliyu ai shine jarumin amman kuma Allah yasa kar Abdul yaci nasarar
ketawa Meenal haddi". Saida tayi ta dubawa sannan taga suna maganane akan wani
novel dataga antura page d'aya mai suna, *'BANDIRAWO'* na marubuciya nan *AYSHA
ALIYU GARKUWA,* fita tayi tayiwa Aunty Halima magana data tura mata novel d'in
saboda ta faro daga farko,
aiko nan da nan ta turo mata, saida takai k'arfe 1:50 tana karantawa har ta iso inda
aka tsaya sannan ta tashi tayo alwala tayi nafiloli day'an addu o i sannan ta kwanta.
Tunda ta karanta littafin *Bandirawo* tafara tunani da kuma son taga itama labarin
rayuwarta yazama littafin da jama a da dama zasu karanta kuma su ilmantu da sanin
illolin rashi biyayya ga iyaye da rashin karb'ar k'addara sannan da sanin muhimmancin
mutum mai hakuri da illar cutar da masoyi sannan jama a da dama zasuji labarin d'an
kad'an daga cikin illar da boko haram sukayi ga zuciyoyin al'umar dake arewa maso
gabashin Nigeria tana son yan mata su d'auki darasi a rayuwar ta tunda ita kam ta rigada tayi
kuskure da nadamar yin tirjiya ga zab'in iyayenta amman tana son labarin ta ya zama izina ga
yan mata da su guji yiwa iyayen su tirjiya dan nadama zata biyo baya tana son taga irin
muhawarar da mutane zasuyi a kanta da abin da ta aikatawa Hamma Umar tana son taga an
fad'i laifinta ko zata k'ara dauwama cikin dana sani da yiwa Hamman ta addu'a.
Aliyu tafara bawa shawara sannan sukaiwa Ya Sadiq da Adam shawarar hakan shima ya
gamsu amma yace mata ta sanar da ya Usman kafin ta ai watar da komai dan shine
babba kuma shi zai bada shawara mafi dacewa dan haka tai niyyar sanar dashi
buk'atar ta.
Ranar asabar misalin k'arfe sha d'aya na rana Ummul tayi wanka tad'au doguwar
rigarta ta saka tai rolling kanta da mayafin rigar ta feshe jikinta da turare mai kamshi
sannan ta zauna bakin gado ta d'auki wayar ta a hankali tai dialing number Ya Usman
sannan ta kara a kunnen ta,
Usman dake zaune gaban laptop yana d'an danne danne ya d'aga wayar yasa ki
murmushi mai sauti dayasa Adam dake latsa wayar shi juyowa yana kallon shi, ciki jin
dadi ya amsa kiran ya karata a kunne yayi k'asa da murya yace,
"Assalamu alaiki ya noorul hayati na". Ummul ta