Showing 114001 words to 117000 words out of 142577 words
Chapter 39 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
d'auka yace,
"Ki jirani a palour Nanne baijira amsartaba ya katse kiran.
A parlour ya sameta tana kwance akan kujera yana shiga da sallama tamik'e zaune ta
amsamai kusa da ita yaje yazauna yasauke ajiyar zuciya sannan ya kure ta da ido
cikin tsananin so yace,
"gaskiya kin rame baby, dama nayita tunanin hakan".
d'an murmushi tayi sannan ta sunkuyar dakai k'asa tace,
"ya Usman tunda naje a wuraren Ibadan nake tarewa ina yiwa Hamma na addu'a da nema
mishi rahamar Allah ko cin abinci bana son fita,
ranar na d'an fara gyagyad'i sai nayi mafarkin Hamma na yana nuna min kai yana cemin inje
gareka kar in bari ka zubda hawaye".
sai kuma tayi shiru tana zubda k'ollah,
sai kuma tace,
"ya Usman ka gafar ceni".
A hankali ya sake matsota yakamo hannayen ta duka biyu ya rik'e da kasalalliyar murya
shi yace, "bantab'a jin b'acin rai akan duk abinda kike fad'a kinyi ba,
nasha fad'a miki komai kikayi birgeni yake kuma komai kyau yake miki nagode da
kulawarki ga d'an uwana".
Shiru sukayi dukkansu yanata matsa hannunta dake rik'e a hannun shi ya katse shirun
da cewa,
"Fatana ki yarda da aurena".
sai kumu yasa hannu ya d'ago fuskarta tare da cewa,
"Kamar kinada magana ko?".
K'asa tayi dakai murya na rawa a hankali tace,
"inaso ".
da sauri yace,
"kina son me"?.
ido ta lumshe cikin zubda k'ollah tace,
"Ince son ince maka na amince da maganar auren".
Kasa k'arasawa tayi tafashe da kuka,
jiki na rawa ya janyota jikinshi ya had'ata da kirjin ya ruggume ta da k'arfinshi ta yanda har
tana jiyo bugawar da zuciyar shi takeyi ido ya lumshe yanajin wani irin yanayi da bai
tab'a jiba hakan yasa yakasa daurewa shima yafara k'ollah,
kamar ya tuna wani abu yasa tafin hannu shi ya goge k'ollar idon shi yasake matso ta
yace,
"Yi hakuri kinji, kinga narasa mezance maki dan murna amma dai nasan yau matsalata
ta k'are".
Sakinta yayi ya sauka daga kujerar ya durkusa yayi sujjada yayiwa Allah godiya sannan
ya juyo yazauna gabanta ya d'ora kanshi akan cinyarta kamar k'aramin yaro yasauke
nannauyar ajiyar zuciya yace, " inasonki ina k'aunarki". A hankali takai hannun ta d'aya
kan gashin kanshi ta tusa yatsun ta ciki tana d'an tureshi, runtse ido yayi da k'arfi yanajin
wani irin abu da baitab'a jiba kuma bazai iya kwatan tawaba,
itace ta dawo dashi daga halin dayake ciki dacewa,
"Naji dad'in samun Aunty Aysha Garkuwa domin ko yaushe shawararta irin ta Ammi da
Nenne ce kuma in nabi ina jin dad'i".
d'ago kanshi yayi ya kureta da ido hakan yasa tai shiru cikin kunya tafara wasa da
yatsunta,
shi kuwa sake tashi yayi ya zauna gefen ta sannan ya ruk'o hanna yenta murya a raunane yace,
"Nasani my life nasan wannan yafaru da ikon Allah da taimakon ta hak'ik'a ni dai
GARKUWA tayi min rana".
sai kuma ya d'an fizgota cikin tsananin shauk'i yace,
"inna fad'a miki toh ki rik'e mini duk tsanani da wuya zana sakar miki sona kiyi rik'ona don Allah
kar naga kin gajiya,
in dai kikayi haka so zai habaka zamuga kyen tafiyar,
da shak'uwa aka samu yarda har so yassanya muna kama da juna".
shiru tayi tana jin salon son ya Usman d'in ta mai cike da kalamai masu sanyi gaba d'aya ya
kashe mata jiki sai k'ara narke mishi takeyi cikin Shauk'i ya tallabo fuskarta ido ya kashe mata
tare da kashe murya cikin rad'a yace,
"Bisa dukkan alama an yabamini Kumar nasan zanga kyen yanayi domin kinmin halin
mutuntawa duk kin gwada mini su tunda kin amince na zama mijin ki ni kuwa dole na k'arfafa so
da k'auna nayi miki rik'on da ba shayi,
gurin zaman auren mu in kyautata miki domin muyi zama na faran tawa juna rai".
cikin jin kunya murya can k'asa tace,
"Ni nace maka kwarai ina so dan haka karka fidda rebo,
me kake so ya zama alamar sona a gareka don akwai sabo a tsaka ninmu inko yarda ta kake
buk'ata to ka sanya a ranka ka samu,
dan kai gudane da bani da kamar ka nida Hamma na da Farouq a zuk'atan mu".
Murmushi yayi cikin jin dad'i yace,
"Ummu na ina da matsala fa ban sani ba ko zaki iya d'aukar nauyin yawan buk'atata gaskiya
gwara na shaida miki tun yanzu kar sai munyi aure kice na matsa miki ko na fiye jaraba,
kuma ko a Shari'ance dama in gaya miki kisan irin mijin da zaki aura".
kanta ta sunkuyar cikin jin tsananin kunya hakan yasa ta kasa maga sai kai ta gyad'a mai
murmushi yayi cikin tsananin jin dad'i yace,
"Dole in gwada miki farin cikina gaskiya kinyi na yaba miki al'k'awari kuma zan rik'e miki wurin
zaman aurenmu wallahi bazan matsa mikiba zan sakaki a cikin farin ciki zuciyar ki na cire mata
bak'in ciki da duk wani k'unci tunda kema kin yimin halacci domin kinyi rik'o da amana tunda kin
amince dani". ido ta lumshe cikin sanyi da jin kasala da kalaman ya Usman d'in nata,
a hankali tace,
"Lallai shak'uwa tana sanya yarda a tsakanin mu tabbas idan nace maka a zuciya ta kai na
zab'a ka gaskatani ka bani dama,
amman in dai sone har gobe Hamma nane kawai nake so a raina ya Usman sai kayi hak'uri
dani".
Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya kamo hannun ta ya tsaida ita cikin mayen so da juyewar
idanu yace,
"zan rayu dake cikin aminci son da kikeyiwa Hamma na ma kawai ya wadatar dani ko baki
soniba ba matsala tunda kinso d'an uwana Kuma nasan nima wata rana zaki soni".
Haka suka kasance cikin hirar su ta soyayya duk da bakomai take amsamai ba amma
saida suka raba dare suna hira sai k'arfe 3:15 ya rakata har bakin kofar d'aki ta shiga
yanajin kamar kada su rabu sannan ya juya ya tafi part ensu.
Yana shiga bedroom ensu yasami Adam yayi d'ai-d'ai a gado yana baccin gajiya kasa
hak'uri yayi yasa hannu yad'an bugi k'afar shi, da k'yar ya bud'e ido yad'ago kai yace,
"yadai?".
zama yayi kusa dashi a kan gadon yace,
"Tashi kasha labari naci zab'e Dr Bashir da Mustapha duk sun fad'i jam'iyata ta kafu
k'ark'ashin jam'iyar Hamma na naci albarkacin d'an uwana duk da baya raye amman a sana
dinshi nake farin ciki".
"a a dan Allah ka barni nai bacci na kaban labarin da safe".
Adam yafad'a yana gyara kwanciya,
da sauri shiko ya rik'oshi ya k'arasa zaunar dashi yana cewa,
"Gwarama ka tsaya kaji wlh dan bazan barka kayi baccin nan ba". Adam da yakeson
yacigaba da bacci yace, "To menene?".
"Ummul ce". yace shiko katse shi yayi da cewa,
"ai dama nasani koyaushe maganar kenan".
hannu yasa ya toshemai baki yace,
"Kai ba irin wannan labarin bane,
yau da bakinta tace ta amince da aure na".
"congrat Allah sanya alkhairi". daga haka ya juya yaci gaba da baccin shi,
shiko mik'ewa yayi yaje yayi wanka da alwola yazo yayi ta nafiloli da karatun Qur'ani
har aka kira sallah asuba.
Tunda suka fito daga masallaci sallah asuba Abba ya fahimci da magana a bakin yaron
nashi dan yanata bin bayan shi yana sosa kai,
kamo hannun shi yayi suka nufi b'angaren Abban,
ya zauna a kujera shikuma yazauna k'asan kujerar ya ton k'oshe k'afa saida suka
gaisa sannan yafara sosa k'eya kamar mara gaskiya,
"Haba d'an Abba ya aka yine ? ai babu wannan b'oye-b'oyen tsaka nin mu fad'amin me
kakeso?".
K'ara sunne kai k'asa yayi yana murza yatsun kafar shi cikin sanyi yace,
"Daman mun gama magana da Ummul ne shine ".
Sai kuma yayi shiru dariya Abban yayi mai sauti ya dafa kafad'ar shi yace,
"To shikenan nagane anjima zamuyi magana da Ammin ku sai kuma insanar da Hajjajo
inyaso idan Daddy ku ya shigo anjiman sai mu mik'a musu sadakin su kaga sai su
samana rana ko?".
Baisan lokacin daya kamo hannun Abba ba yana cewa,
"nagode nagode". Saikuma ya saki hannu yana sosa kai.
"To jekai azkar d'inka".
"to ".
Kawai yace yamik'e a kunyace ya fice.
Shi kam Abba mamaki yake dan yana rena shekarun Usman gashi baida wani girman jiki
amman ya lura yana son auren sosai,
Dr Bashir kuwa yau da wuri ya tashi dan zaizo yayiwa Ummun shi sannu da dawowa,
a gefen Mustapha ma harda Ummanshi suke shirin zuwa yau din suwa Ummul barka da
dawowa Lafiya,
Shi kuwa Usman yana shiga part ensu a parlour ya zauna cikin jin bacci ya kira Ummil d'in
tana kan sallaya woyar na gefen ta juyowa tayi ta d'an kalli Ammi dake karatu,
a hankali ta yi mishi sallama,
yana jin muryar ta cikin,
wani irin yanayi yace,
"wash Noor Hayateeeeeeeeeh bacci nake ji kuma kuma b...........
*By*
*GARKUWAR FULANI*
í ½í³í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 3⃣6⃣
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*MOH ALLAH WUJI FURÆŠATA*
```A madadin Member's É—ina na Group É—in
TABITAL FULAKU nake miƙa saƙon gaiduwar ta'aziya ta ga HALIMA Ummu Maryam kano tare
Mu'allima Bauchi Allah ya jiƙan iyayen ku Allah yasa sun huta rabbi ya sanyayya konciyan
ƙaburburansu Mu'allima Allah ya baki haƙurin rashin mahaifiyarki da kikayi a deren jiya Halima
kema Allah ubangiji ya baki haƙurin maihaifiyarki da kika rasa shekaran jiya Allah yasa sun huta
muko in tamu tazo Allah yasa mucika da imani```
*M*iƙa yayi cikin kasala da jin bacci murya can ƙasa yace,
"Washhh Ummu na bacci nakeji,
kuma begen ki ya hanani baccin,
gashi ina jin sanyi".
shiru tayi bata amsa mai ba a ranta kuwa mamaki ya Usman É—in yake bata shi kuwa iska ya
furzar a hankali sannan yaci gaba da cewa,
"Inama an daura mana aure Ummu na in samu d'umin jikin ki".
shiru tayi batace komai ba saidai cike take da kunya,
shi kuwa lumshe ido yayi yaci gaba da cewa, "Laisa liyal'huzni inkunti ma'ee=in kina tare
dani bani shiga kunci, amma yanzu narasa yadda zanyi".
Dakaji yanda yake magana kasan bacci ke damunshi sai faman mik'a yake da
hammah yana magana cikin shogoɓa yana maƙale da woyar yaci gaba,
"Uhhmmmm wash bacci nakeji Ummuna kuma begenki ya hanani lumshe ido".
A hankali ta buÉ—e baki cikin sanyi ta huramai iska a kunnen shi sannan cikin rad'a tace,
"yanzu ina kake?".
ldo ya lumshe sannan cikin shogob'a yace,
"ina palour".
Murmushi ta É—anyi jin yadda yake magana sannan a hankali tace,
"To tashi ka koma bedroom ka konta a hankali saika lumshe idonka".
Tashi kawai yayi yanufi bedroom É—in yana shiga ya kwanta kan gadon ya lumshe ido a
hankali ya furta,
"Nayi yadda kikace É—in". ÆŠan murmushi takuma yi shogob'ar shinna tana bata mamaki a
hankali cikin raÉ—a tace,
"Gani a gefenka, ga hannuna ka riƙe". Hannu yasa ya damk'e filon da yake kai a
hankali yafurta, "Shhhhmm Ummuna Insha Allah sana iyshu ma'aki ma'a habbah=insha
Allah zan rayu dake tare da soyayya".
jin haka yasa tafara sauke numfa shi tana murmushi tana kuma hura mai iska a
kunnenshi a haka yafara bacci ita kuwa taci gaba,
"Kayi bacci cikin nutsuwa hannuna na riƙe da naka kanka yana cinyata hannuna ɗaya
na yawo a cikin suman kayin ka zuwa kunnen ka, ina son kayi bacci kar ya saka ciwon
kai".
Shirun dataji dakuma jiyo saukar numfashin shi a hankali yasa ta kira shi ta tabbatar da
yayi bacci dan jin bai amsa kiran da tayi mai É—inba,
haka yasa ta katse wayar ta konta cike da tunani har bacci ya d'auketa.
Gari na k'arasa wayewa Ammi tazo ta tasheta dan tayi break saida tayi wonka tai
kwalliya sannan taje tagaida Nanne,
bayan sun gaisa tace,
"Ga abincin Usman can ki É—auka ki kai mishi".
Amsawa tayi sannan tajuya ta je ta had'a mai komai akan tire ta É—auka ta fita hannun
ta riƙe da