Showing 78001 words to 81000 words out of 142577 words
Chapter 27 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
k'arisa cewa bata sonshi kenan sai kuma ta juyo suka kalli juna,
murmushi yayi yace,
"Ina sonki Ummul khairi na so mai tarin yawa zanci gaba da sonki har gaban Abadan".
bata kulashi ba ta wuce cikin d'akin,
shima masallaci ya wuce,
bai dawoba har saida akayi sallan ishah sannan ya dawo,
yana shiga d'akin ta ya wuce kan sallayan ya sameta tana zaune rik'e da qura,an tana karatu
ganin haka shima ya zauna gefenta sukaci gaba da karatun bibbiyu inda suka karance suratul
bak'ara bak'i d'aya sannan sukayi addu'oin masu tarin yawa,
sai k'arfe 9:00 pm suka shafa addu'oin suka mik'e a tare,
hannun ta ya kamo suka fito parlour abincin daya seyo musu bayan fitanshi masallaci ya zauna
ya bata da kanshi taci kuma sosai,
sannan aka fara darun shan magani wanda inda sabo Hamma Umar ya saba da darun Ummul
a kan shan magani kullum sai tayi tamai gardama da rigina,
haka dai da kyer ya samu tasha,
sannan yaje da kanshi ya had'amata ruwan wonka saida yaga ta shiga sannan shima ya wuce
d'akin shi,
wonkan yayi sannan ya fito yayi shirin baccin 3 qtr ne kawai yasa sannan ya feffasa turare,
kitchen yaje tea ya had'a dan shi baici abincin ba,
d'akin nashi ya dawo ya zauna yana shan tea d'in suna woya da Ammin shi,
bayan sun gama woyar ne ya koma bakin gadon shi ya zauna ranshi da jikin shi duk suna
mamakin sauyawar Ummul hakan yasa gaba d'aya jikin shi yayi sanyi,
ita kuwa Ummul bayan ta fito ta kimtsa har ta konta sai taji gaba d'aya d'akin nata ba dad'i yayi
shiru,
haka yasa ta mik'e ta nufi d'akin Hamman nata,
sallama tayi cikin sanyi,
a hankali ya amsa mata tare da bud'e mata hannayen shi
ba musu ko wani gardama ta fad'a jikin shi tare da sauk'e ajiyan zuciya a jere a jere kamar
wacce tasha kuka ta k'oshi,
jin hakan yasa ya k'ara ruggumota a jikin shi a hankali yace,
"Ummu na ina sonki".
ido ta zuba mai tare da cewa,
"Uhummmm".
gyara zaman su yayi a kan gadon tare da shafa fuskarta ya kuma cewa,
"duk duniya bani da kamarku".
lumshe ido tayi tare da shafa sajenshi tace,
"hahhhm nida waye? ".
murmushin farin ciki yayi dan wannan wani ci gabane ace yau shida Ummul ne suke hira duk da
ba amsa take bashiba sai dai tace
Uhmmmm ko ahammm a hakan abin ya mishi dad'i gashi wai Ummul ke shafa wani sashi na
jikin shi,
ganin hakan yaci gaba da cewa,
"Ammina da Usman da ke da Baby nan da zaki haifa min".
"uhmmmmm". ta sake cemai,
shiko jawota yayi suka konta suna fuskantar juna har lau hannun ta na kan fuskarshi,
shi kuwa cusa hannun shi yayi cikin rigarta yana murza k'irjinta amman kuma bata hanashi ba
saima hannun ta d'aya data saka ta kunce igiyar rigar baccin nata ta yadda k'irjinta ya fito fili,
amman tak'i yarda su had'a ido sai k'irjinshi ta zubawa ido,
ido ya lumshe cikin jin dad'i yace,
"Ummul ina sonki,
nima zaki soni ko? ".
batayi manana ba sai lumshe idonta tayi,
shiko mirginowa yayi ya k'ara shiga jikin ta a hankali yace,
"Khairi kinsa wani abu kuwa wallah da takarduna zasu amfaneki da nabaki su kema ki zama
Doctor Rabi'atu Hassan Umar,
tunda na lura a fushin nan da akeyi dani a cikin laifukan nawa harda batun kara tunki da Abba
ya hana a dalilina".
bud'e idonta tayi a hankali tana kallon fuskarsa,
shiko ruggumeta yayi ya d'agota ya d'aurata kan ruwan cikin sa ya d'an kaikace ta yadda basu
matse cikin taba a hankali yace,
"In kin haifi namiji duk sunan da kike so shi za'a saka,
inko mace kika haifa duk sunan da nake so shi zan saka".
hannu tasa tana shafa kanshi tace,
"toh ko sunan Mustapha ka yarda in saka?".
Murmushi yayi tare da laso lips nata yace,
"Hmmmmm meyasa kikace ko sunan Mustapha ma na yarda?".
a hankali tace,
" babu ".
kai ya juya cikin sanyi yace,
"ai shima Mustapha d'an Uwana ne meyasa zank'i yarda,
sharad'i d'aya ne kan sunan,
ina sone ki sawa d'anmu sunan wanda kikafi so a duniyar nan baki d'aya in har shi mustapha
kikafi so toh na yarda ai shima madadin k'ani yake a gareni,
Khairi Mustapha da kike gani mutunci mukeyi sosai har aurenshi naje d'aurin aure".
ido ta lumshe a hankali tace,
"Kai waye kafi so a duniyar nan?".
murmushi yayi a hankali ya zuba mata ido yana murza k'irjin ta da hannu bibbiyu cikin rad'a
yace,
"Ammina nafi so amman keda Usman ku nake sawa a Next of kind na a account na kune a
wurin aikina ma keda Usman na saka".
ya k'arishe maganar cikin rad'a sosai tare da cewa,
"kar Baby na taji ba ita na saka a Next of kind tayi fushi da Daddyn ta".
murmushi Ummul tayi dan ya bata dariya a hankali tace,
"Hamma yaron dake cikin mamanshi kuma yana jin magana ne?".
gira ya d'aga mata tare da cewa,
"zaiji mana ".
murmushi sukayi dukan su,
farin ciki a zuciyar Umar kuwa baya fad'uwa bakin shi ya manne da nata harshen shi ya zirama
ta a bakinta,
ba zato ba tsammani yaji Ummul na kissing nashi,
wayyo gaba d'aya Ummul ta gigitashi da kis d'aya tak sabida bata tab'ayi mishi hakan ba,
duk ya susuce ya susutata,
murya na rawa yace,
"Khairi kin yarda na rab'i jikinki?".
karo na forko da ta kasa cemai a a kenan sai rufe idonta tayi ta kasa magana sai k'ara shiga
jikinshi takeyi,
hakan ya bawa Hamma Umar damar d'ibar gara domin yau ita kanta Ummul tana taima ka
mishi a harkar,
haka ya bashi damar gamsuwa da ita ba musu,
kuma yau Ummul bata iya furta mai kalaman da tasaba yi mishi ba in yana mu'amalantuwa da
ita duk da dai har cikin ranta bawai tana jin tana sonshi bane,
haka yayi ta murzata duk da cikin dake jikin ta,
da kyer ya sararamata,
sannan ya sake jawota sukaci gaba da hira duk da ba tanka mishi takeyi ba,
a haka sukayi ta hira har zuwa k'arfe biyu na dere sannan ya kuma nuna mata cewar yana son
k'ari,
haka Ummul ta kasa hanashi ya murjeta son ranshi saida ya gamsu iya gamsuwa ya jawota
jikin shi yana ta sa mata al'abarka ita ko tuni gajiya da zazzab'i mai zafi gaske ya fara rufeta
lokaci d'aya ta fara karkarwa,
jikin ta kamar uwata sai duk'unk'unewa takeyi a jikin shi ga zucuyarta dake harbawa da k'arfi
kamar zata fashe,
gaba d'aya Hamma kam ya rud'e k'aramin towel ya d'auko da d'an ruwan sanyi ya rink'a jik'awa
yana goge mata jikinta har saida jikin yayi sanyi sannan ya bata magani tasha,
lokaci d'aya jikinta ya sake ganin hakan ya jawota jikin shi,
a take bacci ya saceta,
shiko sai k'ara ruggumeta yayi yana kallon yadda d'an cikin ta ke motsi
fuskarta kuwa tayi fari tas sai shek'i takeyi duk a wunin yau ta canza tayi fiyau,
haka yayi ta kallonta har zuwa k'arfe 3 a lokacin ta farka ido ta zuba mai ganin yadda yake
kallon ta,
cikin baccin ta juya gareshi tasa hannu biyu ta ruggumo shi,
murmushi yayi sannan ya gyara mata konciyar,
sai can k'arfe 4 kuma ta sake farkawa nan ma har yanzu baiyi bacci ba kallon ta yakeyi kamar
zai had'iye ta,
nan ma juyi tayi a jikin shi cikin sanyi ta shafa sanjen shi har zuwa k'irjin shi a hankali ta sauk'o
da hannun ta har kan mararshi cikin magagin baccin tace,
"Hamma har yanzu bakayi bacci ba,
me kake so ne? ".
hannun ta ya rik'o a hankali yace,
"Pakala nake so kuma naga kin gaji gashi baki da Lafiya ko zaki iya da buk'atuna?".
a hankali tace,
"Uhum".
jawota yayi ya ruggume cikin jin dad'i yace,
"Nagode Khairi Allah ya miki al'barka amman yanzu kiyi baccin ki sai na dawo masallaci sai ki
bani kafi shayi tunda yanzu biyar ta kusa".
kai kawai ta juya sannan taci gaba da baccin shikoh tashi yayi yaje yayi wonka sannan yazo ya
d'anyi nafila ana kiran salla ya tafi massalaci,
bayan ya had'a mata ruwan wonka ya kuma tasheta,
itama wonkan tayi sannan tazo tayi salla ta d'an tab'a karatu zuwa k'arfe bakwai ta koma ta
konta,
shiko bakwai da rabi ya shigo gidan yana shiga ya lek'ata ganin tana bacci ya wuce kitchen
kasan cewar yau Monday sauri sauri ya had'a musu breakfast sannan ya shirya musu komai
kan dinning table,
wonka yaje yayi a gaggauce yana fitowa k'ugunshi d'aure da towel ya nufi d'akin Ummul da
nufin ya tasheta tazo taci abinci ya kuma bata magani,
yana shiga ya wuce bakin gadon a hankali ya yaye blanket da ta rufe jikin ta,
murmurs yayi ganin daga ita sai borgon duk zanin jikin ta d'in ya gudu hannu yasa ya shafo
kirjin ta wanda hakan ya tayarmai da buk'atarsa,
kawai sai ya rab'a gefen ta ya konta cikin sanyi ya fara lalubarta,
koda ta bud'e ido batayi yunk'urin hanashi ba,
haka ya murzata har saida ya samu gamsuwa sannan ya ciccib'e ta ya wuce da ita toilet nata,
tare sukayi wonka,
sannan suka fito d'akin shi ya koma ya shirya tsab sannan ya fito,
koda ya fito parlour yayi mamakin ganin bata fitoba,
dan haka ya wuce d'akinta yana shiga ya sameta sai rawan sanyi take kar-kar gaba d'aya
zazzab'i mai zafi ya rufeta duk jikin ta kamar wuta,
da sauri ya ruggumeta cikin tsananin k'auna da kulawa yace,
"Ummu na sannu zazzab'in nan yana bani tsoro wallahi".
ita dai ba magana sai hawaye da rawan sanyi ganin haka,
yaje ya had'a mata tea sannan ya kwaso magungunan ta yazo ya bata,
a Karo na forko kenan Ummul ta karb'i maganin tasha ba musu sannan ta shanye tea d'in ya
kuma k'aro mata tea d'in tashanye tsab,
sannan ya kontar da ita ya d'an rufe mata jikin ta kis ya manna mata a goshin ta sannan ya
shafa fuskarta a hankali ya zaro babbar woyarshi ya ajiye mata gefen pillown ta cikin kula yace,
"Ummu na fitar nan ta zame min dole ne badon hakaba da bazan fita in barki baki da lafiya ba
amman karki damu yanzu zan dawo bazan dad'eba,
ga wayata na ajiye miki zan fita da k'aramar dan zan kiraki inji ya jikin".
kai ta gyad'a mai,
jiki a mace ya juya ya fita koda yaje dinning table d'in ya kasa cin komai haka ya fita,
tana jinshi ya rufeta ta baya tanaji har ya tashi motarsa sai kuma taji ya kashe motar,
jim kad'an sai ta kuma jin ya bud'e k'ofar parlour nasu ya shigo,
tana ganin shi yazo ya tsaya kanta yana ta kallon ta,
sai kuma ya shafa fuskarta ya fita,
a karo na uku ya kuma dawowa ya zauna gefenta a hankali yace,
"Ummu ina sonki ciwonki na tayar min da hankali".
kai ta juya a hankali tace,
"meyasa kakeke ta zirga-zirga ka tafi mana ko meyasa kake kallo na?".
mik'ewa yayi ya shafa fuskarta cikin sanyi yace,
"wallahi kinmin kyaune yau d'in bana son d'auke idanuna a kanki".
murmushi tayi tace,
"Hamma kaima sai kaga yadda kayi kyau wallahi kamar oggo".
murmushi yayi yana fita tare da cewa,
"ai yau nake oggon Ummu yayan Usmanu d'an Ammi da baban Ibrahim jikan Hajjajo da Inna
dan gatan Abba da Daddy da Nenne yayan Adam da Sadik da Halima da Aliyu".
binshi tayi da kallon har ya fita,
yana fita fita ya shiga motarsa ya tafi kai tsaye asibitin su ya nufa jikin shi a mace gaba d'aya ya
rasa sukuni.
A gida kuwa Usman ne ya kalli Adam dake gefen shi cikin sanyi yace,
"Adam zan tafi damaturu zanje naga Hamma na tun shekaran jiya bamuga junaba yanzu zan
tafi".
cikin sanyi Adam yace,
"Ni dai bazani ba sai Hamma ya huce ".
haka yayi shirin tsab ya fito ya sallami su Nenne da Hajjajo sannan ya fito ya bud'e motarshi ya
shiga.
Ita Kuwa Ummul Hamma Umar na fita wani irin zazzab'i mai zafi ya rufeta a take taji wani irin
yunk'u ri... ..
*By*
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2β£9β£
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*JAMU NA HOLARE BALD'E*
*Y*unk'uri tayi cikin gala baita dan aman da takeyi tun bayan fitan Hamma Umar d'in nata amai
d'in take tayi har jikin ta na rawa gaba d'aya ta gala baita intayi yunk'uri sai taji zuciyarya taja ta
tsinke ras gaban ta na fad'uwa,
a wahalce ta tashi cikin layi da rawan sanyin zazzab'in dake bibiyarta tattare wurin da tayi amai
d'in tayi ta goge filin sannan ta kashe A/C dan sanyin da taji ya rufe ta sannan ta sassake
labulayen windows nata har ta konta ta kuma mik'ewa da kyar taje ta rufe k'ofar bedroom nata
d'in sannan ta dawo ta konta ta gudundune cikin blanket tana jin yadda d'an cikin ta ya tattare
ya dawo k'asan k'ahon zucuyarta,
yayi cus ya dena motsi,
itako lokaci d'aya wani irin fargaba da razani da tsoro mai tsanani ya rufeta haka kawai taji
jikinta kamar an rufamata d'anyen fata duk zuciyarta ta raunata a hakan cikin kad'uwa da ciwon
wani irin bacci ya saceta.
Shiko Hamma Umar da yake Federal Medical center duk da dama ba kullum yake zuwaba sai
akwai imergency dan shi aikin shi duba govnr ne,
so yauma imergency ne ya kawoshi,
aiki sukayi cikin sauk'i shida abakin shi Dr Bashir Ibrahim,
k'arfe takwas da mintu hamsin da biyu suka fito kai tsaye office nasu suka nufa dan office en a
jere suke,
suna tafiya Dr Ibrahim na bin bayan Dr Umar Ibrahim Umar d'in da ido ganin gaba d'aya yau
komai yake jikin shi a mace duk motsin da zaiyi sai yace,
"Sauri nake zan Koma gidana Ummul bata da Lafiya,
kuma inaso muje gida nayi kewar Usman".
murmushi Dr Bashir yayi cikin sanyi yace,
"Dr Umar anya ko kana son kanka kamar yadda kake son Usman da Ammin ku da Ummul? ".
kai ya gyad'a mai a hankali yace,
"ina jin tausayin su ne".
a dai-dai tsakiyar farfajiyar asibitin suka tsaya sukayi shiru suna kallon juna cikin kasa kunnuwa
yayin da gaba d'aya illajirin mutanen dake wurin sukayi cirko-cirko suna baza ido da kasa
kunne.
Ta kasance yau Monday 27 February 2014 ranar da mutanen garin damaturu bazasu tab'a
mantashi a kund'in tarihin rayuwar su da garin ba musamman zuriyar Alhaji Umar Shina
k'arfe tara dai-dai na safiyar wannan rana *BOKO HARAM* sukayiwa garin Damaturun diran
mikiya inda sukayiwa garin zobe wanda forkon shigarsu ta layin uguwarsu Hamma Umar suka
shigo wato gidan Ummul kenan dake nyanya line dake gujba road damaturu,
yayin da suna shiga suka rink'a sake bomb da harbe-harbe duk wanda suka kama suyi mishi
kisan gillah,
lokaci d'aya garin damaturu ya hargitse ya birkice sai gudu akeyi ana neman tsiratar da rai,
ν ½νΈν ½νΈν ½νΈsuko tsinannun Allah ta ala sai bi suke gida diga suna kashe Al'Ummar Annabi sannan
sun datse hanyoyin shiga garin duk motor da tazo su tsare su kashe a bakin mashigar garin,
a haka har suka kusan to gidan Hamma Umar.
Shiko Hamma Umar a asibitin inda suke tsaye a take saiga motoci da mata maza manya da
yara suna shigowa cikin asibitin da gudu dan b'oye rayukan kansu,
abin mamaki sai Hamma Umar yaga gaba d'aya mafi akasarin masu shigowa asibitin yan
uguwarsu ce duk mak'o tansu ne kab a cike cikin tsoro da firgici,
ya kutsa cikin su,
Dr Bashir ne ya rink'a binshi a baya yana cewa,
"Dr Umar ina zaka je Dr tsaya mana".
hannun shi ya fizge cikin tashin hankali da firgici yace,
"Ummul! Ummul! Ummul! Bashir banga Ummul ba bashir kalli nan duk mak'otanmu ne gashi
sun gudo banga Ummul a cikin suba".
sai kuma ya rink'a kutsawa cikin mak'otan nasu yana tabbayarsu d'aya bayan d'aya,
" ina Ummul kunga Ummul ne?".
amman duk sai suce basu ganta ba,
hakan yasa cikin tsoro da fargaba yayi parking lot nasu motarshi ya nufa,
Dr Bashir d'in ne da sauran mak'otan nasu suka bi bayanshi cikin tarin tsoro suka rik'eshi a
firgice Dr Bashir yace,
"Dr Umar ka nitsu ina zaka je kana ga wad'anda suke canma sun gudo nan kaikuma kace zaka
koma can plxx Dr Umar karka koma".
ture Dr Bashir yayi cikin rawan jiki da murya yace,
"Ummul bata da lafiya ga tsohon ciki bazata iya guduba kuma kasan kashe masu ciki sukeyi
plxx Dr Bashir barni inje".
Dr Bashir kam kai ya rink'a juyawa rik'e da hannun Hamma Umar d'in,
mak'ocinsa ne ya matsoshi cikin rud'u yace,
"Dr karka koma uguwarmu wallahi suna can suna ta kashe mutane".
hannun shi ya fizge da