Showing 93001 words to 96000 words out of 142577 words
Chapter 32 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
a hankali tasauk'e idanun ta kan
fuskar Mustapha dake rungume da Umar faruq kallon yaron cikin tsananin k'auna da
tausayawa maraicin shi, lokaci d'aya tausayi shi ya rufeshi tuno Hamma Umar kawai sai idanun
shi ya fara zubda k'ollah, da sauri ta maida kanta k'asa ganin
hawayen Mustapha sai wani irin raunataccen kuka mai zafi ya kubce mata,
Mustapha da kyar ya dai-dai ta nutsu warshi sannan yace,
"Khairi dan Allah kiyi hak'uri banyi haka dan na saki kukaba please ki dena zubdawa
Hamma Umar hawaye Insha Allah muna zata mai rahama gatan da zakiyi mishi addu'a ce".
ai kamar ya dad'a tunzura ta tacigaba da kukan da sauri ta mik'e ta fita daga palour
cikin kuka a zahiri ko fuskar Mustapha bata son gani ji take sanadin shine tayi duk wani
kuskure da taurin kai shiyasa da zaran ance mata yazo sai ta resa meke mata dad'i,
gashi shima in yazo kullum sai Farouq ya sashi Kuka tana fitan,
Mustapha yasake rungume Umar Faruq ya lumshe idanuwa yanajin kaunar yaron na
ratsa duk wata gab'a ta jikin shi,
Dasu Ya Adam sukaita hira har lokaci yaja sannan yaje sukai sallama dasu Ammi suka
kama hanyar damaturu.
Yau asabar wanda yayi dai-dai cika watanni 4 da Farouq yayi,
misalin k'arfe takwas Usman yafito daga b'angarensu sanye da farar jallabiya yanufi
b'angaren Nanne kai tsaye d'akin Ummul ya shiga yasame su zaune da alama nono
Ummul keba Umar Farouq ta yadda yaga tai maza ta sauke rigarta,
k'asa yayi da kai ya tsugunna ya kuma gaida Ammi sannan ya dago kai ya kalli
Ummul yace,
"kawo shi".
mik'a shi tai batare da ta dago kantaba yasa hannu ya karb'e shi sannan yace,
"kinci abinci ne?".
Kai ta girgiza alamar a a d'an juyawa yayi ya kalli Ammi kafin yayi magana Ammin
tace, "kaga abincin nan zataci kenan yaron yafarka daga bacci,
to nabashi ruwa yasha nace taci sannan ta ba shi nonon,
amma saina ga hankalin ta bai kwanta da hakan ba, shiyasa nabata shi yasha
tukuna".
Murmushin karfin hali yayi ya kalli Ummul ya jijjiga kai ya juya rungume da yaron shi,
a parlour su ya zauna ya kwantar da Faruq kan cikin shi ya zubamai ido saikuma ya
fashe da kuka mai cin zuciya da k'unar rai yana kad'a kai wanda hakan yazama
al'adarsa yana dawowa daga aiki zai d'auki Faruq yaje yasashi a gaba yaita aikin
zubda k'ollah yana tuno d'an uwanshi Hamman shi abin begenshi.
Ammi ce zaune tana kallon farcen hannun ta taga yanda suka fito sukai tsayi nan da
nan ta tuna gudan jininta wanda tunda yayi wayo shike yanke mata farce dan haka ta
manta da lokacin da ta yanke farce ta a rayuwar ta, hannu tasa ta d'auko abin yankan
farce sannan ta koma ta zauna kan carpet ta fara gwada yankewan sai abin ya murd'e mata
lokaci d'aya begen Farouq d'inta ya rufeta mutuwar ta dawo mata sabuwa kawai sai ta kifa kai
jikin gado tasaki matsanan cin kuka mai cike da tausayi.
A part d'in su ya Usman Kuwa,
ya Adam na kwance rigin gine ya d'ora dan lelensu Umar Faruq a kan cikin shi
shikuma Ya Usman ya zuro hannu yana daga kwance yakama k'afar faruq yanata murza
k'asan k'afar a hankali shiko Farouq sai dariya yake yana wulla hannaye,
Ya Sadiq ne ya shigo sanye cikin farar shadda yanata zuba kamshi yai sallama suka
amsa sannan yace,
"Ya Adam dan Allah kabani junior zamuje unguwa".
Kai Adam d'in ya d'an d'ago yakalleshi yace "ina zakuje?".
cikin mik'a hannun yace,
" D'azu dana fita zan sayoma Nanne turare ne naga wani takalmi na yara me kyau
shine nakeso inkoma da Farouq in sayo masa".
aiko yana rufe baki Ya Usman ya mik'e yace,
"muje nima zanje,
kuje mota bari inje gun Ummul koda akwai abinda takeso a seyo mata".
Yana fad'in haka ya nufi cikin gidan,
Shigar dayayi tambayar Ummul ne yasa yaga Ammi ita kadai a d'akin ta kifa kai
hannunta rike da abun yankan farce tana kuka mai cin rai,
cikin rauni da sanyin jiki ya zame ya zauna kusa da ita yasa hannu ya karb'i abin yankan
farcen kawai sai ya fashe da kuka mai ban tausayi ya kasa yanke mata farcen da rufe
idonshi sai ya rink'a tuno yadda Hamman shi ke yanke mata farcen.
shirun da Adam da Sadiq sukaji suka gaji da jirane yasa suka shigo dan duba me
ya tsaya yi,
aiko samun su sukayi suna kuka ba me rarrashin wani cikin su ganin haka,
Sadiq ya zube guiwowin shi a kasa ya dafa kafad'ar Usman shima Adam ya rab'a
yazauna bakin gadon sannan yafara bawa Ammi da usman hakuri da lallashin har saida
suka samu suka hakura,
sannan Usman yakama hannun Ammin shi ya yanke mata farce sannan yankan farcen
Umar farouq,
daga ranar yanke music farcen ya zame mashi abun yi duk k'arshen sati.
Ranaku na shud'ewa wattanni sun tafi har Farouq yayi wata 7 B'ngaren Ummul kuwa
kullum cikin kuka dasa mutane kuka tana fad'in irin yadda takejin Hamma Umar da
soyayyar shi mai k'arfi a zuciyar ta yayinda ya Adam ya Sadiq Aunty Halima dake zuwa
daga gidan ta duk kwanaki biyu suka dage wajen kula da y'ar uwarsu dan samar mata
da farin ciki.
Kamar kullum yauma zaune suke a palour nanne suna ta hira Aliyu zaune gaban
Ummul yana b'are mata lemo yana bata labarai masu ban dariya su ya Sadiq na
tayashi, Nanne ce ta fito daga bedroom nata ta zubawa yaran nata ido cikin kulawa
tace to ina Yayan ku Usman? ya Sadiq yace,
"yanzu yad'au Faruq yafita dashi".
ajiyar zuciya tayi tace, "daman yanzuma fitowa nayi ince a d'aukeshi daga koyan
tsayuwar kar ya gaji".
Da haka ta wucesu tanufi bangaren su Usman,
abinda take zato ta gani,
Usman zaune yasa Farouq dake ta wutsil wutsil a gaba yana aikin kuka,
zama tai gefen shi a hankali tace,
"haba Usman, nad'auka zaka sassauta wannan damuwar da kake, nad'auka nasihar da
mukaima jiya nida Inna da Hajjajo zata sa ka sassauta wa ranka, dan Allah kayi hak'uri
ka ruggume k'addararka ka dena kukan nan haka, addu'a Hamman ka yakeso daga
gareka a yanzu ba kukaba, kagafa d'anka yanzu yayi wayo yana buk'atar wasa , kuma kaga yafi sabo dakai kaduba yanda yake kallonka ya gane muryarka dayaji yake
woige-woigen neman ka amma kuma saika sashi gaba ka rink'a kuka".
D'an d'aga kai yayi ya kalli Umar Farouq da girman sa da wayon shi keba kowa
sha'awa dan yarone bulbul dashi fari tas kamar balarabe ga dimple dake kumatunshi
inka gan shi kace yayi shekara amma watan shi 7 ne,
shi Kuwa Usman sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya d'auki yaron ya rungume yana shafa
bayan shi,
Ita Kuwa Nanne kanshi ta shafa tace,
"Allah yayi maku albarka".
hawaye ya zubda masu zafi sannan yace,
"Amin Nenne".
Haka rayuwa taita tafiya da Ummul da dad'i ba dad'i dakuma samun kulawa ta
musamman daga iyeyenta yayunta kaninta da uwa uba ya Usman wanda duk lokacin
shi natane ita da yaron shi wanda komai nashi ke kanshi inko yajiyo kukan shi har
yana gudu da tun tub'e dan so da k'auna, sau da yawa yakan cewa su Adam idan
suna hira,
"inajin nafison Faruq junior a kan kowa a duniya ciki harda Hamma na dan so kala da
yawane a kan Junior son da nakewa mahaifinshi ma ya dawo kanshi".
Daga b'angaren Mustapha kuwa abin ba a magana da duk k'arshen sati yana hanyar
potiskum yayin da mahaifiyarshi ke rakoshi bayan sati biyu ko uku, Dr Bashir ma ba a
barshi a bayaba domin kuwa baya wuce sati bai ziyarci Ummul da Umar farouq ba.
Haka abin yake agun Inna da daddy abun saidai hamdala dan kuwa Ummul da d'anta
suna ganin gata tako ina matsalar Ummul d'aya rashin abin kaunarta hasken
idanuwanta Hamma Umar wanda har yau bata dawo dai-dai ba ita da Usman Ammi kuwa
yanzu tasa dangana a ranta.
Ranar wata asabar misalin k'afe hud'u na yamma ne Mustapha ya iso gidan su Ummul
kamar yadda ya saba duk sati, da Aliyu yafara had'u a farfajiyar gidan yana zaune kan
kujerar roba yana karatu cikin girmamawa yataso ya karb'i lodojin hannun shi yakuma
gaida shi sannan yamai jagora zuwa palour sannan ya wuce ya sanar da Ummul, ba afi minti ashirin ba Ummul ta shigo sanye da hijabita k'ato har k'asa tana rike da
Umar faruq da yaketa zullowa yanason sauka tai sallama ya amsa mata cikin kulawa
sannan tasami kujerar gefe ta zauna, Farouq ko yanata kiciniyar sauka Mustapha yai
d'an murmushi yace, "sauke shi mana". Bata d'aga kantaba ta sauke Farouq aiko kamar yana jira ya rarrafa da saurinshi
kasancewar shi mai kuzari da lafiya kuma yana ji da k'arfi ya je wajen Mustapha,
aiko shima hannu ya bud'e yana zuwa ya d'auke shi yana dariya
tare da d'agashi sama yana sumbatar goshin sa,
Sheshshek'ar kukan Ummul ne ya tsagaitar da Mustaphan daga wasan da yakema
Farouq ya d'ago kan shi cikin damuwa da kid'ima a hankali murya can k'asa yace,
"Khairi wallahi da kin san yadda nakeji akan kukan nan naki wallahi dakin taimaka min
kin dena".
sai kuma yayi shiru tare da cire glass d'in idon shi ya mik'awa Farouq da yaketa kokuwar
karb'a sannan yaci gaba da cewa,
"Ummul bana jurewa banajin dad'i kuma bana iya bacci ko cin abinci aduk lokacin da
natuna wannan kukan da kike, kiyi hak'uri khairi dan Allah ki daure".
Haka yayi ta aikin rarrashi kamar yadda ya saba duk sati dako duk yanda zaiyi Ummul
bata cewa komai sai aikin kuka a haka ya zauna yana ta lallashin ta cikin salon tsumin
tsohon so,
Wani irin abune ya ziyarci zuciyar Usman daya shigo daga unguwa ganin motar
Mustapha da yayi a cikin gidan wanda shima ya rasa dalilin hakan ya resa meyasa yake
jin zafi a ranshi in Mustapha yazo gidan, da kyar ya tsaida motar shi ya bud'e cikin
mutuwar jiki