Showing 48001 words to 51000 words out of 142577 words

Chapter 17 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

yakeyi ba abin da yake furtawa sai jujjuya kan Usman d'in yakeyi yana cewa.
"Usmaaan ! Usmaaaaaan!."
sai kuma ya k'ara matsoshi jikin shi ganin wani irin yunk'uri da Usman d'in keyi,
shi kuwa Usman k'irjin shi ya rik'e tare da damk'o hannun d'an uwanshi yayi wani irin kakari da
k'arfi har jikin shi na karkarwa ,
aman jini ya rink'a yi bak'ik'k'irin dashi guda-guda sai ya damk'o hannun d'an uwan nashi yayi
kakari,

ita kuwa Ummul gaba d'aya karkarwa takeyi da dafa jikin motar tayi tana tafiya a hankali har ta
isa gaban su hannun ya Usman d'in ta rik'e da k'arfi cikin gigicewa da tsoro ta saki wani irin
k'ara mai k'arfi kawai sai ta fad'a jikin Hamma Umar d'in a sune,
shi ma ya Usman lokaci d'aya numfashi sa ya fara d'auke wa,
Allah sarki Hamma Umar gaba d'ayansu ya had'a ya ruggume su cikin tsinkewar jijiyoyin jikin
shi gaba d'aya ya zame ya zauna a k'asa kanshi ya rink'a murzawa a jikin motar Usman cikin
wani sauti mai tsananin rauni yace.
"Usmaaan kar kayi min haka Usman karka barni ni kad'ai Usman wazai meye min gurbin ka
wayyo Allah wayyo d'an uwana wayyo Ammina ina kike Usman zai tafi ya barmu wayyo Abba
d'an uwana zai tafi ya barni ni kad'ai ba Uba ba d'an uwa."
ruggume Usman da Ummul d'in ya kumayi da k'arfi Abba ya rink'a kira da k'arfi dai-dai lokacin
daya ga numfashi Usman yana ficew....






By
*GARKUWAR FULANI*


*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1⃣9⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*






*Wannan shafi naki ne kad'ai Firdausi Sodaggi ke da members naki na matan k'warai na baku
kyautan wannan shafi gaba d'ayan shi�*



*QAULIKI HAQQUN SAFIYYA HUGUMA ALMUSLIM AKUL MUSLIM ZADAKILLAHU
FIKHRAN WA ILMAN, WAYATTAQINALLAHU JAMI'AN*

*R*uggume su ya K'ara yi cikin tarin firgici yana tallabo kan Usman yana mannawa a k'irjin shi
tare da rumtse ido da k'arfi yana fad'in.
"ya rabbi ! Ya k'adir ! Allah kaine gatana kaine gatan dukan bayin ka Allah kaine mai rayawa da
kashewa Allah kaine mai bada lafiya ya Allah ka jib'amci lamuran d'an uwana Allah ka rayamin
d'an uwana,
shima Usman k'amk'ame Umar d'in yayi cikin fitar hayya cinshi da azabar da yakeji,
Ummul kuwa manne take a jikin Hamma Umar d'in tayi luf a sume,
su Abba kuwa tun k'aran da Ummul tayi na fari sun ka fito cikin mamaki jin muryar Ummul d'in a
gida ya Adam da Sadik kuwa jin muryar Hamma Umar yana kiran Abba da karfine yasa suka
fito a guje gaba d'aya harabar gidan suka nufa,
Hamma Umar kuwa gaba d'aya jikin shi rawa yake tsoro da firgicin zai rasa d'an uwan nashi
gaba d'aya sai ya resa k'arfi jikin nashi haka ya zauna dir sham a k'asa yana ruggume dasu
yana wani irin kuka mai cike da firgici da tsoro da kad'uwa gaba d'aya ya resa halin da yake ciki
duniyar ta mishi duhu, su Abban suna fita da gudu sukayi inda suke jin sautin kukan Hamma Umar d'in da sautin
fuzgar numfashin Usman d'in,
suna zuwa Abba ya durk'usa gabansu cikin tarin firgici da ganin ikon Allah ya kamo hannun
Usman cikin tashin hankali yake kiran shi.
"Usman ! Usman ! Innalillahi."
sai ya kumu kalli Adam da gaba d'aya jikin shi rawa yake cikin rawan murya yace.
"Adam fito da mota mu tafi asibiti."
sai ya kumma kalli Ummul dake kwance luf jikin Hamma Umar d'in tana sume cikin jin tsoron
lamarin ya kalli Umar tare da cewa.
"Umar meke faruwa da sune?."
ina ya kasa magana sai k'ara ruggume Usman da ummul d'in yakeyi,
shi kuwa Usman cikin tarin ya kamo hannun Adam d'aya juya zai fito da mota numfashi na fizga
tare da zarewan idanu yace.
"Ad..! Ada..! Adam Karku kaini asibiti Abbah Ku barni a gida."
sai ya kuma carkewa da tari sai ya rink'a amayo da jini guda-guda bak'k'ik'irin dashi,
cikin a man ya kamo hannun Umar d'aya gama mutuwan zaune yace.
"Hamma na karku kaini ko ina ku barni a gidan ku maidani cikin gida."
Hamma Umar kam kanshi ya kife a jikin Usman d'in cikin rawan murya da baki yace.
"Usman d'an uwana ya za'ayi mu barka a gida a cikin wannan halin da kake kayi hak'uri muje
asibiti."
hannun Umar d'in ya rik'o dan ya fara jin numfashi sa na dawowa tunda ya amayar da bak'in
jinin hawaye na bin fuskarsa zufa na ketomai tako ina
cikin murmushi k'arfin hali yace.
"Toh su asibiti zasu hanani mutuwa ne in lokaci na yayi? nasan dai mutuwa ce kuke tsoro kuma
in lokaci yayi ba makawa Hamma Umar ka tunafa Abba ka sani tun ina yaro kuke fama dani ko
yaushe muna hanyar asibiti ban workeba yanzu kuma ko anje ba lallai a samu nasara ba ko

nasha maganin shi maganin abinda ya samu yake tayiwa in ya samu sauk'i sai ya k'ara sauk'i in
ya samu ajali kuwa tofa ajalin yake tayiwa dan Allah Abba Hamma Umar ku maida ni gida bana
son zuwa asibiti nan."

Haka dole ba d'an suna soba suka koma cikin gida dashi,
shi kuwa Umar Ummul ya ruggume sannan yabi bayan Abba dake tallabe da Usman,
kai tsaye part d'in Hajjajo suka nufa a parlour suka zauna kan 3 str Abba ya kwantar da Usman
shi kuwa Umar ya kwantar da Ummul kan 2 str ,
ya Adam kuwa dama tuni ya fita ya d'auko doctor dake duba Usman d'in.

Bayan yazo ya duba shin yayi duk binciken da zaiyi ya gama sannan ya kalli Usman d'in dake
konce a rigingine ya lumshe ido hawaye na bin fuskar shi sannan ya juyo ya kalli Hamma Umar
dake zaune ya zuba mishi ido yana rik'e da hannun shi sannan ya kalli Abba dake k'ok'arin
gyara wa Usman d'in konciya cikin kula doctor Ibrahim yayi ajiyan zuciya sannan yace. "Alhaji Hassan ko kuna lura da Usman sannan kunsan meke damun shi akwai matsalar da
yake boyewa a zuciyar shi sannan kuma yasan zuciyar shi bazata iya d'aukar nauyin ba Usman
akwai abin da yake matukar so bai samu ba,
domin na duba na'urar dake cikin k'irjin shi tana zaune yadda ake so tana kuma taimakawa
kamar yadda ta saba tana kuma harbawa jinin dai-dai misali kuma zataci gaba da aikin har nan
gaba shekara 1 a lokacin zai cika shekara biyar da sata sannan za'a koma a canzata kamar
yadda aka saba, yanzu wata matsalar ce ta daban kuwa ke damun Usman kuma zata iya jawo komai a rayuwar
shi."
yana rufe bak'in shi Usman ya bud'e idanun shi cikin salon sa na abin dariya ya fara magana
cikin dariya da son badda matsalar tasa yace.
"Uhummm wai ina son wani abu,
toh niko mai zanso wanda Abba da Hamma Umar basu samamin shiba ni ba abin da nake so."
Ido Nenne ta tsura mishi cikin tsananin tunani lokaci d'aya kuma ta fara tuno wani abin,
Hajjajo kuwa ba abinda takeyi sai kuka,
shi kuwa Hamma Umar ido ya tsurawa d'an uwan nashi cikin sanyi yace.
"Me yake saka tarin da a man jini?."
murmushi yayi tare da d'an shafa sajen shi yace.
"You naga Anyi tayin maganin asibiti ba canji shine jiya naje na karb'o na wmzamai shine na
jik'a nasha ,
sai gashi yana k'ok'arin fecewa dani barzaq."
Murmushi ya kuma yi sannan yace.
"Amman fa gsky naji sauk'i dana amayar da jinin."
haka ya rink'a shashantar da abin shi kuwa doctor Ibrahim ya tabbar akwai matsala tare dashi.
su ya Adam kuwa sun d'an samu nitsuwa ganin Usman d'in ya mik'e,
Hamma Umar kuwa har yanzu zuciyar shi na cike da fargaba,
Abba kuwa bayan doctor Ibrahim yabi suka fita tare yana k'ara mishi bayani,
bayan su Abban sun fita ne Hamma Umar ya d'an juyo kusa da Ummul tafin k'afafun ta ya kamo
yasa hannun shi ya rink'a murzawa yana jan yatsun k'afafun nata tare da kiranta.

"Ummul ! Ummuuul !."
sai kuma ya dawo ta kanta hannun shi yasa ta k'asan wuyanta yana d'an murzawa,
nanma shiru sai ya manna hancin shi da nata sannan ya rufe bakinta da nashi,
cikin lumshe ido ya rink'a fesa mata numfashin sa sannan yana zuk'o numfashin ta bak'in ta
gaba d'aya nashi numfashin ya rink'a fesa mata cikin sa'a tafizgo numfashin sannan a razane ta
kamo wuyan shi baki ta bud'e da nufin zata sake k'ara,
sai yayi maza ya rufe mata bak'in da tafin hannun shi,
haka yasa ta bud'e idanun ta sannan ta rink'a kallon su d'aya bayan d'aya,
zame bakin ta tayi cikin sanyin muryar tace.
"Ya Usman ! ya Usman ."
ido ya d'an rumtse sannan yace.
"Na'am Ummul ."
jin muryar shi ta mik'e da sauri taku d'aya tayi ana biyun ta koma ta zauna ido na zubda k'ollah
dan azaban ciwon da raunin jikinta ke mata,
cikin sauk'e ajiyan zuciya Hajjajo tace.
"Ke kuma meya sumar dake? sannan yanzu tafiya ma na gagararki."
batayi magana ba sai kawai ta kama kuka,
ganin haka Nenne tace.
"Toh sarkin kuka ya isa haka taso mu tafi kiyi wonka sai kici abinci kiyi bacci."
mik'e wa tayi cikin zubda k'ollah tafiya ta farayi cikin d'ingisa k'afafun ta tana d'an waresu tare
da cije lips d'in ta,
ganin haka tuni Nenne tayi gaba dan ta gano matsalar yartata itama Hajjajo shiru kawai tayi dan
ta fahimci matsalar,
shi kuwa Hamma Umar kanshi ya sunkuyar cikin tarin kunya da tausayin Ummul d'in sai
hawaye yaji yana bin hab'arsa dan gani yake kamar ya gwada mata rashin tausayi tunda yasan
yarinya ce,
kunya yakeji ta rufeshi kamar k'asa ta tsage ya shiga,
ganin hakan yasa su ya Adam duk suka zame suka fita itama Hajjajo kitchen d'inta ta shiga ta
fara had'a wa Ummul had'in su na tsoffin shuwa'arab sannan tayiwa Usman d'in ma had'in shi
na musamman ta kuma dafawa Usman abincin da zaici da kanta.

A part d'in Nenne kuwa suna shiga kai tsaye bedroom suka wuce kan gado Ummul ta konta ta
kife kanta tana kuka,
ita kuwa Nenne toilet ta shige ruwan d'umi ta had'a mata mai k'unshe da sinadarai na gyaran jiki
sannan ta had'a mata wani juk'o na musamman a cikin buta,
tana fitowa taje kusa da ita cikin kulawa da tausayawa irin ta uwa da yarta ta kamo hannun ta ta
zaunar da ita kafad'an ta ta dafa a hankali tace.
"Ummul Allah ya miki albarka kiyi hak'uri mamana ki d'aure kinji ko ki denan kukan nan ya isa
yanzu kin girma ya kamata kiyiwa kanki fad'a tashi kije kiyi wonka ki zauna cikin ruwan d'umin
sannan kiyi amfani da ruwan butar nan."
kukan ta kumayi cikin shogwob'a dan ganin Nennen ta na lallashin ta,
da kukan ta shiga tayi wonkan sannan ta k'asa kanta lokaci d'aya taji jikinta duk ya wore,
tana fitowa ta samu Nennen ta jona borner a ajikin wuta tana fitowa ta zuba mata wasu turaruka

masu tsananin k'amshi sannan ta kalleta cikin kulawa tace,
zoki tsuguna kiyi hayak'i da wannan."
"toh " tace sannan ta matso gaban borner ita kuwa Nenne ta fita parlour,
tsuguna wa tayi a kanshi hayak'in na shiga jikin ta wani irin k'amshi na ratsata,
tana mik'e wa ta Jita garau hakan yasa ta kimtsa sannan ta koma bak'in gadon ta konta cikin jin
wani irin baccin gajiya,
Tana konciya Nenne na shigo wa had'in kaza ta karb'a mata wanda Hajjajo tayi mata sai ruwan
tsumi mai dad'in sha,
ajiye wa Nenne tayi sannan tace.
"Taso kici abinci saiki kontan."
ba musu ta sauk'o taci tasha dan tana jin yunwa,
kuma yau tana jin dad'in yadda Nennen ta ke kula da ita wanda tunda ta nuna bata son Umar
Nenne ta dena kulata sai yau d'in,
tana gamawa ta koma ta konta tana kallon Nenne dake shirin shiga wonka cikin sanyi tace.
"Nenne zazzab'i nake ji da ciwon kai."
ba tare da ta kalleta ba tace.
"Toh bari in gayawa Umar d'in yazo ya dubaki."
fuska ta tsuke dan bata son abinda zai had'a ta dashi inuwa d'aya kuma gashi ta jawa kanta,
bayan Nenne tayi wonkan ne ta shirya ta nufi d'akin Abba a tsakar gidan ta kalli Aliyu yana
shirin shiga part d'in Hajjajo kiran shi tayi sannan tace.
"Jeka kira Hamma Umar d'in ku kace Ummul bata da lafiya yaje ya dubata."
"Toh" yace sannan ya nufi parlour Hajjajo yana zuwa ya samu Hamma Umar d'in yana zaune
gefen Usman yana b'are mishi lemu,
gefen shi ya zauna a hankali yace.
"Hamma Anty Ummul bata da lafiya Nenne tace kaje ka dubata."
kai ya gyad'a sannan yaci gaba da bawa Usman d'in kulawa,
bayan ya gama bashi abinci ya bashi maganin sannan suka tafi part d'in su suna zuwa ya had'a
mishi ruwan wonka,
har cikin bathroom d'in ya rekashi kamar zaiyi mishi wonkan,
murmushi Usman yayi tare da cewa.
"Hamma yau wonkan ma zaka min ne?."
"Kanaga ka girma ko?."
kai ya sosa sannan yace.
"Gaskiya dai Hamma na girma mai min wonka zai iya makancewa."
K'eyan shi ya d'an buga sannan ya fita,
shi kuma Usman wonkan yakeyi yana zubda k'ollah cikin tausayawa kanshi da d'an uwan nashi,
bayan ya fito Hamma Umar ya shirya shi sannan ya kontar dashi kan gado ya zauna gefen shi
yana shafa kanshi cikin sanyi yace.
"Ammmi ta kiraka kana wonka nace mata kace min yanzu ka girma."
ido ya lumshe yana jin dad'in yadda d'an uwan nashi ke kula dashi k'aunar shi na ratsa mai
zuciya,
ido ya lumshe cikin jin bacci yace.
"Hamma ?."

"Na'am Usman d'an uwana."
kai ya jinji na sannan yace.
"Ina sonka d'an uwana."
kanshi ya rink'a shafawa yana cewa.
"Usman duk duniya bani da tamkar ka ina sonka k'anina bani da buri a duniya daya wuce inga
ka samu lafiya fatana a koda yaushe in ganka cikin farin ciki."
ruggume juna sukayi sannan a hankali Umar ya kontar dashi sannan ya rink'a yi mishi karatu
qura'ani a cikin kunnen shi murya cike da rauni,
lokaci d'aya bacci ya tafi da Usman d'in,
shi kuwa Hama Umar a hankali ya gyara mishi konciya sannan ya fito kai tsaye harabar gidan
ya koma motar shi ya bud'e ya d'auki magungunan Ummul sannan ya nufi part d'in Nenne,
yana shiga parlour ya samu ba kowa sai kuma yaji muryan Ummul dake magana da Anty
Halima da woyar Nenne,
cikin yin sallama ya shiga yana shiga ya zauna gefen Ummul d'in sannan yasa hannu ya karb'i
woyar ya katse kiran ,
ita kuwa a fusashe ta juyo gare shi a nufin yin tsiwa,
sai kuma tayi shiru jin yadda ya jawota jikin shi ya ruggume ta tsam a jikin shi sai sauk'e ajiyan
zuciya yakeyi murya can k'asa yace.
"Kun bani tsoro keda Usman in na rasaku bansan makomata ba Ummul Khairi ina tsoron
abinda zai rabani daku,
In babu Usman bansan ya rayuwa zata juya min ba."
sai kuma ya k'ara matsota jikin shi d'umin jikinta na ratsa shi,
ita kuwa tureshi takeyi tana k'ok'arin matsawa,
jawota ya kumayi a hankali ya tallabo kanta kissing d'in ta yayi da kyau sannan yace.
"Kiyi hak'uri my Khairi bazan sake wahala da keba."
shiru tayi tana jin yadda yake fidda numfashin da sauri-sauri a haka har ya fara sauk'e ajiyan
zuciya a hankali nitsuwarsa ta dawo jikin shi sannan ya bata maganin ya kontar da ita ya shafa
fuskar ta sannan ya fita.

A haka Hamma Umar ya wuni kula da k'anin shi da matar shi da derema haka ya kwana kula da
Usman yayin da kewar Ummul ke cin jikin shi da zuciyar shi,
koda gari ya waye haka ya wuni kula dasu,
kuma Alhamhadullih duk sun mik'e musamman Ummul dan shi kam Usman k'arfin haline da son
kontar da hankalin Hamman nashi,
bayan Anyi salla isha ne Abba yace Hamma Umar su tafi tunda duk jikin su da sauk'i,
bayan ya fita ne ya d'auko jakar Ummul ya bawa Aliyu ya kai mata cikin gida sannan yace .
"In kaje kace tazo."
"Toh" yace sannan ya nufi cikin gidan,
a parlour Nenne ya samu su ya Adam cikin mamaki ya Sadik yace .
"Jakar nanfa daga ina.?."
"Ta Anty Ummul ce."
Ya bashi amsa ya Adam ne ya kalli Ummul d'in cikin tsuke fuska yace.
"Ba yanzu zaku tafiba?."

Kai ta juya ido cike da k'ollah tace.
"A a ni bazan komaba bani da lafiya."
A hatsale ya bugawa Aliyu tsawa .
"Maza ka meda jakar cikin motar Hamma Umar d'in ke kuma tashi kibi mijin ki ku tafi."
shi kam Aliyu tuni ya juya da jakar ita kuwa hannun ta rink'a yarfa wa tana buga k'afafun ta tare
da bud'e baki da k'arfi tana.
"Ai Hamma Umar d'in ya yarda kuma bani da lafiya shike nan dan an tsaneni sai ayi ta korata a
gidan mu."
Kanta yayi da sauri yana zaro bel d'in k'ugunshi,
ya Sadik kuma cewa yake.
"Yauwa zaneta tunda bata jin magana."
Ihu ta saki jin sauk'ar bel d'in a jikin ta a guje ta fita tana kuka,
bayan Hamma Umar d'in ta tsaya tana tsalle da dire-dire tare da rik'e hannun shi ,
Abba ne ya fito dan jin kukanta yana zuwa ya kalli yadda takeyi sai murmushi yayi dan a fili
yarintar Ummul take ganuwa,
shi kuwa Adam tsawa yake buga mata yana.
"Ki wuce ki shiga cikin mota."
Abba ta kalla dan ko zaice ta dawo sai kuma ta shiga motar ganin yadda ya had'a fuska yana
kallon ta,
shi kuwa Abba cikin bada umarni yace.
"Farouq shiga ku tafi.
"toh."
yace sannan ya shiga,
Aliyu kuwa dariya yayi tare da d'aga tafin hannun shi ya saitasu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login