Showing 69001 words to 72000 words out of 142577 words

Chapter 24 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

ta koma kan gadon cikin sanyi ta zauna gefenshi murya can
k'asa tace,
"Na yarda Hamma".
kauda kai yayi,
yayi ta murmushi sannan yasa hannu ya jawota jikin shi,
kayan jikin ta ya zare mata sannan ya zare nashi blanket ya jawo ya rufesu a hankali yasa
hannun shi yana murza al'barkatun jikin ta,
shiru tayi cikin lumshe ido,
ganin bata taimaka maine yace,
"ko dai bakya so ne in barki da cikin ki?".
cikin kasala tace,
"inaso mana ".
murmushi yayi sannan yace,
" toh ki tayani muyi tare duk abinda nayi miki kiyi min inba hakaba in fasa taimakon ".
ba musu ta fara maida mishi martani,
gaba d'aya sun gigice Sun shiga duniyar ma aurata ita kanta Ummul salon Hamman nata na

yau ya wuce zaton ta,
shiko Hamma Umar ya samu gamsuwa iya gamsuwa da y'ar k'anwarshi sai al'abarka yake
samata.

Haka suka kwana mak'ale da juna,
koda gari ya waye yana dawowa masallaci kai tsaye d'akin Ummul d'in ya wuce ya kwashi garar
kafi shayi dad'i,
haka rayuwa tayi ta juyawa tana tafiya gaba d'aya yanzu Hamma umar ya jarabe ya yaraba
Ummul d'inshi wasu lokutan har yana jin tsoron kar dai cikin ya zube dan shida kanshi yasan
jarabarsa tayi yawa,
cikin ko yana nan daram sai k'ara k'awari da lafiya da wintsil-wintsil da yake yawan yi,
Ummul ko har kwanan gobe bata tabajin son Hamma Umar d'in ba haka kuma bata tab'ayin
wani abu dan ta faranta mai raina.


A gida kuwa randa Hamma Umar ya mari Adam suna tafiya,
Adam ya koma parlour Nenne cikin takaici da jin haushin k'anwar tashi ya shafa kumatun shi ya
kalli Sadik dake gefen shi rai a b'ace yace,
"Ni Hamma Umar ya mara a kan na daki Ummul dan tayi mishi laifi".
dogon tsaki Sadik yaja cikin ta kainci yace,
"wallahi tallahi da a bare Hamma Umar ya auro Ummul wallah sai ince ta asirce mana d'an
Uwanmu Kalli fa yadda ta maida Hamma kamar bawanta inajin bak'incin yarinyar nan wallahi
duk randa na kamata sai na b'allata".
ya k'arishe maganar yana nuna yadda zai b'allatan,
Tsaki Adam ya ja cikin ta kaici yace,
"Duk ta meda Hamma Umar shanyeyye soko ya zama tamkar sakarai".
Aliyu ne ya dan yi k'asa da kanshi yace,
"Ni ina jin tausayin Hamma,
Ummul na wahal dashi".

Ajiyan zuciya Nenne ta sauk'e cikin kallon yaran nata a hankali tace,
"Ba Ummul ke wahal da Farouq ba soyayyar Ummul ce ke wahal dashi".
cikin mamaki Adam yace,
"Son Ummul Kuma Nenne Hamma Umar yana son Ummul ne ai ba sonta yake ba had'asu fa
akayi ko kin manta ni dai inaga girman al'k'awarin daya d'aukane ke wahal dashi ko?".
Kai Nenne ta kuma juyawa cikin sanyi tace,
"Farouq yana son Ummul Adam baku gane hakan bane kuma sonda Umar keyiwa Ummul na
asaline tun randa aka aifi Ummul".
sai kuma tayi ajiyan zuciya taci gaba da cewa,
"Tun randa aka haifi Ummul,
Umar ya bata matsayi mai girma a rayuwar shi,
bayan na haifi Ummul Umar shine mutun na forko daya d'aga Ummul yana d'agata ya
ruggumeta cikin tsananin farin ciki sai kuma ya kalleni yace,

"Nenne da d'a namiji kika haifa da anmin takwara Nenne yarin yar nan dana mijine da na samu
magaji,
amman yanzu ma bai b'aciba Insha Allah zata haifomin takwarana kuma Yerimana".
inajin abinda Umar ya fad'a sai nayi dariya nace ai itama takace,
haka daga wannan ramar Umar ke d'awainiya da Ummul renonta kab shi yakeyi a kwana a
tashi har ta fara girma so shiko a lokacin an kaishi karatu India bayan ya gama ya dawo kuma,
sai ya zama basa shiri da Ummul sabida shi mutunne mai nitsuwa ita ko Ummul tana da kaud'i
da tsiwa ga yawan fad'an da takeyi da Aliyu tana cin zalinshi shiko Umar baya son zalumci da
sowa kuma ya zama shine matsayin mahaifinku in Abban ku baya nan shiyasa yake bada
kulawarshi akan Ummul sosai yayinda ita ko ta d'auki hakan a mizanin k'iyeyya,". kai suka jinjina su duka ita kuma taci gaba da cewa,
"Kuma duk da haka dole ku d'auki mataki kan halin Ummul dan a samu ta gyaru,
amman fa karkuyi a gaban Umar".
toh a haka fa daga ranar suke cike da takai cin Ummul d'in a rayu kansu,
kwanaki sun ja makonni sun ja watanni sun ja ya Usman kuwa kullum sai yasa ranar dawowa
sai ya d'aga a haka har cikin Ummul ya cika wata 7 ,
yayin da a gefen Umar kuwa kullum cikin tashin hankali yake da matsamai da Ummul take akan
a cire cikin ya samu dai yanzu ya lallab'a ta a kan sai cikin ya cika wata 7 da kwana 7...

Yau Monday tun sassafe Hamma Umar ya shiryo da Ummul enshi suka nufo gida dan Ya
Usman yau zai dawo a cewarsa yau kam bazai d'aga dawowar ba dan jin kewar Umar yakeji
tamkar sun shekara 10 basu had'uba,
Abin mamaki suna isa gida a harabar gidan Hamma Umar ya haggo Usman d'in ya nufo gunsu
cikin sauri yana murmushi mai cike da farin ciki,
Hamma Umar kuwa da Ummul har rigerigen fitowa sukeyi,
a motar suna fita Ummul ta ruga a guje cikin ihun farin ciki da sowa da rakad'i tana,
"Oyoyo ya Usman na ya dawo Hamma Umar Kalli ya Usman nawa ya dawo".
shi ko Umar zuciyar shice ta rink'a bugawa da k'arfi yana kallon yadda Usman ya rame sai farin
daya k'ara shiko,
Usman ganin Ummul da yayi da k'aton ciki a take jikin shi ya Kama rawa cikin tsananin firgici da
tsinkewar zuciya gaba d'aya gabban jikin shi suka rink'a rawa zuciyarshi na harbawa da karfi,
dafe k'ahon zuciyarshi yayi a da-idai lokacin da Ummul ta fad'a jikin shi dai-dai lokacin kuma
Hamma Umar ya k'araso garesu bud'e hannayen shi yayi ya had'asu gaba d'aya ya ruggume
su,
Lokaci d'aya yaji wani irin karaya a zuciyarshi abin mamaki saiga Hamma Umar yana kuka
cur-cur ruggume da k'aninshi da matarshi kuka sosai yakeyi yana shinshina wuyan Usman ,
kukan Hamma Umar d'in ne ya k'ara tono dafin zuciyar ya Usman d'in cikin wani irin yana yi
yace,
"Hamma kuka Kuma? ".
sai kuma tari ya sark'a fe mishi tarin yakeyi da k'arfi yana numfashi sama-sama,
a gigice Hamman ya tallabo d'an uwan nashi dai-dai lokacin usman yayi wani irin yunk'uri da
kakari sai ga....

*by*
*GARKUWAR FULANI*


*RUBUTACCEN AL, AMARI*

Page 2⃣6⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*








*INA KUNE MATAN group d'in TABITAL FULAKU tare da AYSHA ALI GARKUWA FANS da
kuma GARKUWAR FULANI Group tare da GARKUWA AYSHA&UMMEE ina Al'afahari daku
ina sonku har raina ko a cikin groups na ku din nan da banne a gareni Fatan Allah ya k'addara
saduwarmu a jannatul firdausi�*






*S*aiga tari ya k'ara turnu k'eshi tarin ya keyi sosai har ida nunshi na firfitowa woje gaba d'aya
jijiyoyin kanshi dana hannun shi suka taso rud'u-rud'u, sai k'ara ruggume Hamma Umar d'in
nashi yake yana wani irin murmushin k'arfin hali,
ita ko Ummul gaba d'aya jikinta rawa yake ta rik'o hannun ya Usman d'in tana zaro ido murya a
hargize tace,
"Wayyo Allah na Hamma Umar kalli ya Usman".
sai ta kuma fara kuka itama tana,
"ya Usman har yanzu kana wannan tarin da aman jinin ko shin doctors basu duba lafiyar ka
bane?".
kai ya rink'a juyawa jikin cushewar numfashi da zufa dake tsatstsafo mishi duk ta inda hutar
gashin jikin sa yake,

hannun na rawa ya tallab'o hab'ar Hamma Umar da hawaye ke zuba tamkar an bud'e pompo
idanun shi kamar zasu fad'o k'asa yana kuka harda sheshshek'a,
ido ya kuma tsurawa Hamma Umar d'in nashi cikin dauriya Ya rink'a juya mishi kai cikin tarin
yace,
"A zatona zuciyar Hamma Umar na tana da k'arfin da zata iya jure mutuwata ma bare dan
tarina,
amman kach sai gashi ina rayema kana min kuka,
ashe in namutu gatan da zakayi min kenan Hamma na? ashe bazaka iya cin jarrabawar da
Allah zai maka ba,
Hamma Umar ka dai sani dole watara zan mutu ko".
Kai ya rink'a juyawa cikin kuka yana k'ara ruggume shi yana cewa,
"Usman bani da kamarka kullum cikin fargaba nake nima da kaina bansan ya rayuwata zata
kasance min ba inba kai,
Usman bazanyi maka gatan kukaba bazan zubdama hawaye ba zan zamema mai gatan yima
sutura da addu'a Usman inajin tsoron jinin da kake amayarwa".
cikin sauk'e ajiyan zuciya dan tarin ya dan lafa sai ya kuma yi murmushi ya kalli Ummul ya
kuma nuna k'aton cikin ta sai ya Kuma kalli Hamman nashi cikin salonshi na abin dariya ya d'an
ture su yaja baya kad'an sannan yayi gyaran murya ya gyara zaman hulanshi ya dan bud'a
kafad'a cikin salon girma yace, "Na zama Baba yanzu na wuce yarinta a dena jimin tsoron mutuwa ko namutu ga magaji na".
sai ya kuma sunkuyowa saitin cikin yace,
"Ni Baba zaka kirani".
cikin jin dad'i Hamma Umar ya kalleshi tare da cewa,
"ai dama kaine baban shi na bar makashi ni dai mahaifinshi ne kawai amman kaine babanshi".
murmushi yayi cikin farin ciki sannan ya kalli Ummul da ta tura baki tana hararan cikin a hankali
yace,
"Allah ya d'aiyiba min Baby maman Baby".
cikin zubda k'ollah tayi murmushi tare da kallonshi tace,
"ya Usman ina sonka yayana".
dariya yayi sannan yaja hannun Hamman nashi suka nufi cikin gaida, yana cewa,
"Allah ya d'aiyiba".

Kai tsaye parlour Abba suka nufa inda gaba d'aya gidan suke zaune a parlour sunata hira,
suna shiga su duka uku suka zauna gaban Abba da Daddy cikin Happy Abba ya kallesu tare da
amsa gaisuwar su,
sannan ya kalli Hamma Umar yace,
"Farouq ya gidan naka ba wata matsala ko?".
kai ya gyad'a a hankali yace,
"Abba matsalar dai cikin yayiwa Ummul nauyi".
ya Adam ne ya watsawa Ummul d'in harara tare da cewa,
"Toh ai haka kowa ke haifar yaranshi har in ba, ayi daceba yar ta nuna bazata yiwa iyayen nata
biyayya ba".
hararan da Hamman ya mishine yasa ya kame bakin shi,

ya Sadik ma sai hararan Ummul d'in yake yana jin tana gaida shi yak'i amsawa,
ya Usman kuwa Hajjajo ya kallah cikin murmushi yace,
"Hajjajo kingafa na girma na zama baba da haka kar ki kuma cemin yaro".
dariya sukayi baki d'aya
sai kuma suka juyo gun Aliyu da yake hararan Ummul yana janye piket d'in abincin gaban shi
yana cewa,
"mitssss wallahi ke dai kin bonu da kwad'ayi kina ta kallona salon na kware ni ba baki zanyi ba
tunda ai ke yanzu ba yar gidan nan bane".
Hamman ne ya kalleta cikin kula yace,
"Zakici abin cin ne".
Kai ta gyad'a a hankali tace,
"eh yunwa nake ji".
Adam ne ya tsuke fuska tare da cewa,
"Uban me ya hanaki kiyi girkin a gidan ki kici?".
hawaye ta fara k'ok'arin zubdawa ganin haka Hamman ya mik'e tare da cewa,
"Taso mu tafi gidan Ammina zata miki duk abinda kike so bar musu abincin gidan su".
mik'ewa tayi dan tasan inya tafi ya barta zasu iya mareta,
shiko Hamma Umar hannu yasa ya kamo na Usman sannan yace,
"tashi mu tafi".
dariya yayi sannan ya mik'e suka fita,
Nenne ko kallonsu take cikin k'aunar yadda suke k'aunar juna tace,
"ku gaida min Ammin kuce sai gobe Aliyu zai kawo mata aiken nata".
"toh ". Sukace sannan suka fita,
suka nufi gidan Ammin nasu,
suna fita Abba ya kalli Adam dake bin bayan ummul da harara yace,
"Adam me kuma Ummul ta aikata? dan na lura fushi kake da ita".
zama Adam d'in ya gyara sannan ya kwashe labarin yadda sukayi da Ummul da Hamma Umar
d'in ya fad'awa Abban,
gaba d'aya parlour shiru sukayi dan yadda Abba da Daddy suka hatsala fad'a sukeyi sosai
tamkar zasu bugi babu daga k'arshe fad'an ya dawo kan Nenne cikin tsananin fushi Abba yace,
"khadija na lura kece kike d'aurewa Ummul gindi takeyin abinda taga dama shin dan na had'ata
da d'an d'an uwana ai bawai yana nufin tayi ta tozartarmin da shiba,
ashe ban saniba ban isa da Ummul ba toh wallahi zan d'auki mataki a kanta".
ita kam Nenne gaba d'aya takaicin Ummul ya isheta,
tunda gashi laifinta ya shafeta,
dama in yaro yayi abu mara kyau tofa koya uwa zatayi sai anga laifinta,
shiko Abba da Daddy kan Adam d'in suka haura da fad'a,
"ai kaima baka da wani amfani tunda ka kasa d'aukar mataki a kanta kuma tunda na dawo baka
gaya min ba sai yau yau d'inma saida na tabbaye ka,
to daga yau ni na baka izini da Umarni in Ummul ta sake yin abu makamancin wannan kayi
mata duka sai ta konta jinya tunda bata jin magana".
Hajjajo ce taja tsaki tare da cewa,
"yarinya sai taurin Kai kamar Arnan forko,

a mata dukan shine maganin ta".
ita ko Nenne,
shiru kawai tayi tana jinsu sunata fad'a,
haka dai sukayi ta fad'a daga bisani suka watse.

A gidan Ammi kuwa suna shiga gidan ya Usman ya nufi parlour Ammin yana,
"Ammmmmi! Ammi! Ammina ina kike ne ".
Ammi dake kitchen cikin tsananin mamaki da jin muryar autan nata ta fito,
Inna ma da sauri ta fito daga bedroom nata,
a parlour suka sameshi yana ganin Ammin nashi da sauri ya k'arisa gaban ta cikin tsananin
kewar juna ya ruggumeta itama kuwa sai murmushi take tare da hamdala,
Hamma Umar kuwa da yanzu ya shigo tare da Ummul mamaki yake yadda shi Usman ba
ruwanshi ba kunya ko nauyi yake ruggume Ammin tasu abinda shiko bazai iyaba,
ita ko Ummul cikin sanyi ta matso kusa da Ammin a hankali tace,
"Ammi ina kwana? ".
Da sauri Ammin ta ture Usman sannan ta kama hannun Ummul suka zauna kan 3 str Inna ko ta
zauna kan 1 str tana fuskantar su,
shiki Usman d'aya gefen Ammin ya zauna kamar yadda ya saba,
shiko Hamma Umar a hankali ya matso gaban Ammin ya zauna a k'asa kan carpet sannan ya
rusunar da kanshi tare da cire hular kan nashi,
ya sunku yar da kan nashi,
murmushi Ammin tayi sannan tasa hannu ta dafa kan nashi kamar yadda suka saba cikin
tsananin farin ciki tace,
"Allah yayi muku Al'abarka Allah ya tsaremun ku da zuk'atanku da imaninku Allah ya jibanci
lamuranku".
"Amin Amin".
suka amsa baki d'aya sannan shiko Usman ya juyo ya gaidata cikin happy tace,
"Usman ya jikin naka "?.
da sauri ya kalli Hamman nashi dake shirin yin magana sai ya kuma kalli Ammin yace,
"Ni na samu lafiya plxx adena yawan cemin ya jiki,
indai ba so kuke yaron da Ummul zata haifa shima ya fara cemin ya jikin ba".
dariya sukayi baki d'aya sannan ya kalli Ummul d'in yace,
"A cici akawo miki abincin ko? ".
kai ta sunkuyar itako Ammi tana jin haka ta koma kitchen ta had'o musu abincin ta kawo musu,
Inna ce ta kalli Usman tace,
"Kai aggona tare zamuci fa dan yau amarci zamuyi".
duk dariya sukayi,
shiko Hamma Umar abin cin ya had'a musu a pilet sannan ya kalli Ummul da Usman yace,
"ku sauk'o kuci abincin".
sauk'owa sukayi suka fara ci dan ita Ummul da Ammi tamkar uwa da ya suke,
shiru Ammi tayi ta zuba musu ido ganin Usman da Ummul kecin abincin shiko Umar sai in sunci
ya k'ara musu sannan ya had'a musu tea a hankali tace,
"Farouq kai bazaka ci bene? ".

kai ya jinjina sannan ya kalli Ummul d'in da Usman yace,
"Ammi na nafi buk'atar inga su d'in sunci".
murmushi Usman yayi ya kalli Ummul dake ta faman d'uri ko a jikinta,
itako Ammi sai ta had'a wani tea d'in sannan ta mik'owa Umar d'in tace,
"karb'i kasha kai kullum kan kula da Usman kake k'arewa sam bak'a kula da kanka".
murmushi yayi ya karb'a yana sha tare da cewa,
"To Ammina nagode".
itako Ummul tana gama cin abincin tayi mik'a tare da kallon Ammi tace,
"Ammi bacci zanyi".
cikin jin dad'i Ammin tace,
"taso muje ki hau gadona kiyi baccin ki".
haka taje ta konta,
suko sukayi ta hira,
anan suka wuni har yamma sannan suka sallamesu suka koma a gidan ma suka d'anyi hira
bayan sallan ishane Hamma Umar d'in ya kwashi Ummul d'inshi suka koma gidan su cikin
damaturu.


Lokaci ya juya yanayi ya canza a cikin sati 3 da dawowar Usman yayin da yanzu cikin Ummul
yake da wata bakwai da sati 3
tsakanin Hamma Umar kuwa da Usman wani irin shak'uwane da son juna me tsanani yake
k'ara ratsasu
Usman baya iya yin kwana 2 baije damaturu ba inko ya kwana 1 bai jeba toh Umar zai d'auko
Ummul su zo,
Itako Ummul da Hamma Umar zuwa yanzu abu yaci tura ko gaban Usman Ummul cewa take
aje a cire cikin ya isheta ita ta gaji dashi,
a gefen ciwon Usman kuwa Allah ne yasan halin da Usman yake ciki dan gaba d'aya shida
kanshi yana jin rayuwarshi ce tazo k'arshe shiyasa yake jin son Umar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login