Showing 6001 words to 9000 words out of 142577 words

Chapter 3 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt


Yaran sun tashi cikin k'aunar juna baka gane cewa Nenne ba ita ta haifi su Umar ba,
Sai dai kowa da halinsa dan shi Umar mishkili ne baya wasa da yara kuma kasan cewarsa
shine babba a family d'in su yasa k'annenshi suna girmamashi
shi kanshi Umar yana jin haushin yadda yake halinshi, yayinda hakan ya jamishi kiyeyyah a
uzuciyar Ummul ita kuma gani take yana takura rayuwarta a, zahiri Umar yana jin zafin yadda
wasu lokutan ake gaza gane cewa wannan halin fa ba yin kanshi bane Allah ne ya halicce shi a
hakan.
Sun tashi cikin gata da kulawa inda Umar a yanzu haka shi babban doctor ne yana d'aya daga
cikin yerdeddun governor damaturu shine doctor dake duba lafiyar governor nasu kuma shine
babban doctor dake aiki a general hospital damaturu,
Usman kuwa shi accounter ne sai .

Sai
Adam Airforce ne yanzu haka a Kaduna yake
sai in yazo ziyara.

Sai Sadiq shi kuma yana aiki a ministry of justice.

sai Halimatu Sadiya ita kuma nurse ce tana aiki anan cikin garin potiskum.

Sai
Ummul khairi ita kuma bayan ta gama primary school d'in ta aka jona mata secondary school
GGC damaturu inda ta koma cikin damaturu da zama a cikin makaran ta,
yayin da shi kuwa Alhaji Hassan Abban Ummul kenan shi yana aikine a offishin gwamna a
damaturu hakan yasa Abba yana da gida a can inda yake zama yana aikin shi sai alhamis ya
taho week end cikin garin patiskum d'in,
hakan yasa idan anyi hutu Ummul takan zauna a gidan shi dake gidan jen maikata na ministry
of works and housing dake gashua road damaturu dan jira ya gama aikin sa sai su tafi tare su
koma cikin potiskum tare.

A hakan ne wata rana Ummul ta fita ita da k'awayen ta suna d'an zagawa cikin uguwar,
anan ta had'u da Mustapha saurayin da suke soyayya a yanzu haka,
shima yazo gun abokan shine a unguwar,
dan shi Mustapha gidan su na commissioners quarters dake Maiduguri road damaturu,
haka sukayi ta soyeyya in sunyi hutu yana zuwa har gidan su Ummul d'in dake potiskum,
Haka yasa
ya saba da ita ya saba da y'an uwanta suna yiwa juna so mai tsabta.

Shi kuwa Umar sosai ya zuba ido kan lamuran Ummul, gashi in Abba baya nan kusan shine

uba a gidan,
so yana tsanani sa mata ido dan kare tarbiyar ta ita kuwa hakan yasa ta k'ara tsanarsa da jin
tsoronshi,
dan baya mata da sauk'i.

Usman kuwa mutun ne mai fara'a da sakin fuska yana watsa da kawo dan shi ko da Abba wasa
yake mishi kamar kakanshi,
haka yasa Usman ya kasance wani jigo na gidan in ya fita ko na awa d'aya ne sai anyita ceki
yarshi,
shi da Umar kuwa suna yiwa juna wani irin so mai tsanani Umar yana k'aunar Usman fiye da
komai a rayuwarshi suna yawan kaiwa Amminsu ziyara a gidan kakannin su.

Usman tun yana k'arami ya tashi da ciwon zuciya mai tsanani inda Abba da Daddy Hussain in
Abban kenan sukayi ta jin yarshi,
a haka abin tashi hankali da fari an gane cewa zuciyar Usman tana da d'an hujin dake sashi
ciwon zuciya so anyi ta bashi kula,
amman kuma Usman na girma abin na k'aruwa haka yasa zuciyarshi ta zama ta tsage ,
dole aka fitar dashi Egypt so acan akayi mishi aikin tare da kulawar d'an uwanshi Umar Faruoq
aikin da akayiwa Usman a cikin zuciyar shi aiki ne da yasa an bar wasu na'urori a cikin k'irjinshi
d'an zuciyar tashi tayi raunin da bazata iya harba jininshi ba sai da wannan na'uran haka kuwa
aka k'inda ya mishi dokokin aka hanashi cin duk wani abu green dan abubuwa green suna sa
jinin d'an adam kauri shi kuwa zuciyarshi nada raunin harba tsinkekken jinima bare mai kauri sai
na'urar ke iya harba jinin ,
haka duk bayan shekara 5 yake zuwa a canza na'urar,
ko kusa da kai Usman ya zauna zakaji yedde na'urarnan take aikin a jikin shi tana,
*cak-cak* yana harba amman sai ka matso kusa dashi sosai zakaji sautin a hankali.

Wannan larura da Usman yake da ita yasa gaba d'aya zuriyarsu suke tausayawa mishi duk
wata kulawa suna bashi,
yayinda Umar Faruoq kuwa a duniya baida wata matsala sai damuwar ciwon B'iyayen shi,
shi yasa duk wata kulawa ta duniya wacce uwa da una zasu bawa d'an su ya had'eta yana
bawa k'aninshi Usman.

Ummul kuwa da Usman suna rayuwa tamkar abokai,
Anty Halima kuwa tana gidan mijin ta amman duk wata kulawa tana yiwa Ya Usman d'in nasu.

Ya Adam da Usman kuwa su tamkar tagwaye suke tunda dama kwana 12 Usman yake bawa
Adam.

Ya Sadiq kuwa mutumin Hamma Umar ne.

Auta Aliyu kuwa abokin fad'an Ummul ce shima yanzu ya kusa gama secondary school d'in shi
ita kuwa Ummul sune suka gama this year so yanzu tana gida ana sama mata admission a

FCE (T) potiskum zatayi NCE d'in ta akan maths and computer.
toh fa a d'an wannan zaman da takeyi a gidanne take k'ara fuskantar takura fad'a da Umar ke
mata hakan yasa ta k'ara tsanarshi.


Haka Ita kuwa Ummul take da wani irin ciwon mara a duk lokacin da zatayi al'adarta kasan
cewar a makaran ta tafara ciwon cikin sai ba'a santa dashi sosai ba tana dai fad'a tana ciwon
ciki amman Nenne bata san ciwon mai tsanani bane.....
*Tak'aitaccen labarisu kenan*


Mun dawo kan labarin yanzu.


Nenne na dawowa ta lek'a kitchen tana kiran Ummul tana fad'in.
"Ummul kin gama ne?."

Ido ta d'an zaro ganin ba abin da tayi a kitchen d'in cikin sauri ta fito parlour kan dinning table
d'in ma ba komai agogo ta kalla da sauri ta fita ganin har 2:00 pm tayi.

Parlour Hajjajo ta nufa tana kiran Ummul d'in.
tana shiga Parlour ta kalli Umar Faruoq d'in cikin b'acin rai da fushi tace........




By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL'AMARI*

Page 4⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Fatan alkhairi a gareku masoya na da wannan littafi nawa ina godiya da k'aunarku gareni 🙈🙈
kuyi hak'uri nasan wasu zasuce ba zasu fara karatu yanzuba sai nayi nisa sabida basa son

farawa suzo suna jira toh dan Allah kuyi hak'uri duk wacce tasan sai anyi nisa zata fara toh ta
Tarawa kanta kar sai nakai 20 ko 30 azo ayita bina P/C a nace ana so ni banzan iya hanaku ba
sabida ina son mai sona kuma bana iya fiffik'e ido nayi banza da d'an Adam sabida d'an Adam
abin karramawa ne Amman wallahi ina takuruwa gashi inada eyes problem kuyi hak'uri Ku
tarawa kanku ngd Allah bar zumunci da k'auna GARKUWAR Fulani tana al'fahari da masoyan
ta*


Rai a b'ace cikin yana yin kai k'ararta tace
"Umar kaga Ummul tafiya tayi bata yi aikin komai ba ko,
yanzu-yanzun nan kira min Halima kace maza ta turota gida."

Kallon Nenne yayi yace.
"Tafiya tayi gidan Haliman ne? kuma batayi aikin ba?."

Cikin takaici Nenne tace.
"Ehh tafiya tayi mana tunda bata gidan nan tun dazu nake kiranta ban jita ba,
gacan kitchen d'in kuma ba abinda ta tsinana."

Hajjajo ce tayi tsaki dan ko ita bata san Ummul na cikin d'akin nata ba,
cikin mita irin ta tsofaffi tace.
"Wannan yarin ya akwai lalaci da k'in aiki,
fisabillahi yanzu a haka za aurar da ita a kaiwa wani yayi ta famar yi mata bauta."

Wani dogon tsaki Hamma Umar d'in ya ja,
sosai yakejin zafin rashin jin maganar ta.

Ita kuwa Ummul tuni ta fara had'a zufa dan tun dazu take son fita jin Hamma Umar d'in a parlour
Hajjajo ya hanata fita,
gashi yanzu kuma tanaji Nenne ta kawo kararta gun shi dama ya lafiyar kura a dawa bare an
tab'oshi,
hannu ta yarfa cikin sanyi da rawan murya tace.
"Nenne nifa gani nan ba inda naje fa,
kuma wallahi zanyi girkin."

A hatsale Nenne tace.
"Toh me kikeyi a cikin d'akin da kika kasa fitowa?,
me kike aika tawa?
wato ke har kullum indai batun aiki ne sai kin b'ata min rai ko?."

Taku ta farayi a hankali tana fitowa parlour murya a hankali tace.
"Ayyah Nenne kiyi hak'uri wallahi zanyi aikin yanzu zan gama."

Hajjajo kam salati ta rink'a yi tana tafa hannu cikin mamaki tace.
"Ke takwarata yanzu yaushe kika shigo ban ganki ba? kuma uwar me kikeyi a d'akin?."

Baki ta d'an tura cikin kallon kakar tasu tace.
"Wani abu nake yi."

Harara Nenne ta watsa mata cikin jin haushi tace.
"Bar min aikina zanje nayi abina,
ki zauna nan ki gayawa Hamman ku dalilin ki na k'in yin aikin."

Tana kaiwa nan ta fice part d'inta ta koma
kai tsaye kitchen ta wuce ta fara aikin ta cikin sauri da tsanaki.

Shi kuwa Hamma Umar tunda Ummul ta fito bai kalli inda take ba har Nenne ta fice ,
yana komce kan 3 str sai y'ar k'aramar k'orya da ke gaban shi mai cike da kindirmo mai kyau
fari tas,
konce yake rigin gine sai laptop d'in shi dake kan ruwan cikin sa ya hard'e k'afafun shi.

Ita kuwa Ummul cikin tsarguwa ta tsuguna gefen shi kad'an tayi k'asa da kanta tana d'an satan
kallon shi,

Hajjajo kuwa mik'ewa tayi ta kalli Hamma Umar d'in cikin kula tace.
"In dama maka da furane? ko insa maka dakkere ne?."
Baiyi magana ba sai lumshe
ido yayi,
ita kuwa ganin haka ta shige d'aya d'akin ta fara dama mishi da fura.

Shiru parlour su duka biyu ba wanda yayi magana har zuwa wani lokacin ganin haka Ummul ta
gyara durk'usuwan da tayi don guiwowin ta sun fara tsami,
fuska ta marairaice ta lokk'oshe kanta a kafad'ar ta tai rau-rau da ido murya can k'asa tace.
" Hamma kayi hak'uri wallahi bazan sake ba".

Shiru bai kula taba,
itama shirun tayi dan ta sani da ta k'ara magana toh ta k'ara laifine dan zaice ta cika mishi
kunne da hayani yarta."

Haka yasa kawai sai ta rink'a jujjuya guiwowinta dan sun tara jini,
gashi ta fara jin ciwon marar da yake mata duk wata,
haka yasa ta fara zubda k'ollah tana d'an gogewa da tafin hannun ta,
murya na rawa tace.
"Hamma kayi hak'uri."

Sai yanzu ya bud'e idanun shi a hatsale yace.

"Uban me ya hana ki yin aikin?,
wacce tsiyar kike aika tawa a cikin d'akin tun da safe?."

Baki na rawa ta d'an matsa baya a hankali tace.
"Hamma har na fara aikin fa,
sai Mustapha ya kirani shine na zo nan d'in."

Daga koncen yasa bayan hannushi ya yarfa mata mari da bayan hannun nashi,
sannan ya tashi zaune ido ya kafa mata tare da cewa.
"Amsa kiran Mustapha yafi aikin da zaki yiwa mahaifiyar ki ko?."

Kai ta rink'a juyawa cikin toshe bak'in ta dan karta saki kuka,
tana juya kai tace.
"Kayi hak'uri Hamma bazan k'ara ba."

Tashi yayi ya mik'e fuska a murtuk'e ya watsa mata harara tare da cewa.
"Mik'e kije kiyi aikin kar in b'ab'b'allaki fitinenniya kawai mara jin magana."

Da sauri ta fice tana zubda k'ollah tare da k'uk'k'ini k'asa-k'asa kai tsaye kitchen d'in ta shiga.
tana zuwa tace.
"Ayyah Nenne kiyi hak'uri'
ki kawo aikin zan k'arasa."

Rai a d'an had'e tace.
"Je kici gaba da baccin ki,
nayi aiki na,
in bakiyi na gidan kuba ai zakiyi na gidan miji inda ko godiya baza'ayi miki ba."

Haka Nenne tayi ta mata fad'a har suka gama aikin,
itako tana bata hak'uri,
Shi kuwa Hamma Umar nonon ya karb'a sannan ya koma part d'insu.


Nenne kuwa suna gama aikin rana taje tayi wonka ta kimtsa d'akin Abba dan yau zai shigo
potiskum d'in,
haka yasa ta barwa Ummul sauran aiyu kan girkin dere da kuma abincin Usman da ban.

Su ya Adam kuwa da ya Sadiq da Aliyu duk suna tare a parlour Nenne suna kan dinning table
suna cin abinci.

Aikin take yi cikin k'arfin halin dan ciwon da mararta keyi ya fara yawa sai ta shiga kitchen d'in ta
d'an yi aikin in matar ta murd'a sai ta dawo parlour ta konta kan kujera tayi ta murk'ususu sai
tayi jigib da zufa dan azaba.

Shi kuwa Aliyu duk abin da take yi hankalin shi na kanta,
dan yana matukar son yar uwarshi haka yasa yana lura da yadda take zuwa ta kontan .

8:00 pm Abba ya iso gida cikin family d'in shi su ya Adam da ya sadik duk suka nufi part d'in
Hajjajo suna zuwa suka tsame shi shida Hussain in shi wato Daddy suna ta hira da dariya
Hajjajo
na zaune a tsakiyar su Hamma Umar kuma yana gaban su Abban kanshi a sunkuye yana
zaune tsakiyar k'annen mahaifin shi,
Abba ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Farouq ya ina k'annen naka? ban gansu ba."

Ya d'ago kanshi zaiyi magana kenan su Adam suka shigo cikin girmamawa suka gaidasu
sannan suka zauna sukaci gaba da hira,
kallon Hamma Umar Abba ya kumayi tare da cewa.
"Usman da ummul fa ina suke?."

Aliyu ne yayi carab yace.
"Abba Anty Ummul bata da lafiya tun d'azu kuka takeyi,
ya Usman kuma yanzu ya dawo bai shigo ba tukun."

Daddy ne ya kalli Hamma Umar d'in cikin yana yin tabbaya yace.
"Farouq meke damun Ummul d'in.?"

Kai ya sunkuyar a hankali yace.
"Daddy ni ban san bata da lafiya bama sai yanzu."

Nenne ya kuma kalla a hankali yace.
"Nenne meke damun ta.?"

Fuska ta d'an tab'e cikin kula tace.
"Hmmm Umar kafa san Ummul da raki tun bayan sallan magariba take kuka wai cikin da
mararta ke ciwo ko tashi tak'i tayi wai bazata iya ba."

Cikin mamaki Abba yace kai Khadija mamana bata da lafiya kice raki ,
duk rakin Ummul indai taji na dawo toh zata zo tamin sannu da zuwa ,
tunda kikaga har ta k'asa tashi toh gaskiya tana jin jiki."

Hajjajo tace.
"Gaskiya kam gwara a dubata."

Daddy ne ya kalli Hamma Umar din cikin bada umurni yace.
"A gaskiya bata da lafiyan ne,

Farouq kaje ka dubata."

"Toh" yace tare da mik'ewa ya fita a ranshi yana cewa.
"Mara lafiya ke zuwa gun doctor ita kuma uwar sakalci da raki doctor ne zaije ya sameta dan
tsabar samun sake."

A tsakar gida ya had'u da Usman murmushi Usman d'in yayi tare da sosa k'eya yace.
"Hamma tun d'azu fa na dawo,
yanzu sai naci abinci zanzo insha maganin."

Kafeshi yayi da ido cikin k'aunar k'anin nashi da tausaya mishi,
hannu yasa ya d'an bugi k'eyarsa tare da matse kunnenshi yana.
"Usman baka jin magana ,
baka kula da lafiyar ka,
baka jin tsoron da nake ji akan ciwon nan naka."

Shi kuwa Usman d'an kara ya saki tare da cewa.
"Wayyo Abba na Daddy kuzo Hamma na zai tsinke min kunne."

Abba ne yayi dariya jin muryar Usman yace.
"Da ka iso wuri ko ido bai ganka ba kunne zai shaida zuwan ka Usmanu shehu sarkin
barkwanci shi kowa kakan sa ne."

Daddy ne yayi murmushi tare da cewa.
"Usman kenan shi shiya d'auki halin Baban mu komu y'ay'anshi bamuyi irin yanayin shi ba
kamar yadda Usman yayi. ,
shiko Farouq koman shi. na Yaya Ibrahim ne har tausayin shi da kulawan shi a kan k'annenshi."

Usman kuwa dariya ya rink'a yi yana juyawa Hamma Umar na binshi da ido yana kallon yadda
k'anin nashi ke harkokin sa tamkar baisan ciwon da ke jikin shiba.

A haka ya wuce ya nufi parlour Nenne,
shi kuma Usman ya tafi gunsu Abba yana zuwa.

Ya gaida su sannan ya kalli Aliyu cikin murmushi yace.
"Kai Auta ina Ummul ban ganta ba?."

Hajjajo ce ta kalleshi tare da cewa.
"Bata da lafiya mai baka duk abinci da kake so kaci d'in,
yau anan zakaci abinci."

Cikin zillewa zancen yace.
"Ni duk abinda doctors suka hanani bana cin karki wani had'ani da su Abba,

kuma ko Nenne ma shaida ce bana cin komai matuk'ar dai green ne,
dan haka karma kiyiwa Ummul lak'el kice ita ke bani komai naci,
kowa yasan ina bin doka."

Aliyu ne yayi carab yace.
"A a kam ya Usman wallahi ko jiya kaci miyar ganye."

Kai ya sunkuyar yana murmushi ganin yadda Abba da Daddy suka tsareshi da ido cikin tsoro
Daddy yace.
"Usman meyasa baka kiyaye lafiyar ka Usman ka rufa mana asiri kake bin dokokin doctors ko
zamu samu ka rabu da ciwon nan."

Murmushi yayi cikin k'arfin guiwa ya kalli Abba da gaba d'aya ya karaya jikin shi yayi sanyi
hannun Abban dana Daddy ya d'an rik'e a hankalin yace.
"Cuta ba itace mutuwa ba ,
lafiya kuma bata hana mutuwa nasan abinda kuke tsoro,
ba haushe yace,
nisan kwana maganin annoba,
karku damu yanzu nayi lafiya jin zuciya ta nake kamar ta k'arfe."

Murmushi su duka sukayi tare da sauk'e ajiyan zuciya sannan sukaci gaba da hirar.

Shi kuwa Hamma Umar a hankali yayi sallama,
a bak'in k'ofar ya tsaya jin ba'a amsa sallama ba sai sheshek'an kukanta da yake ji,
haka yasa ya kutsa kanshi cikin d'akin kan gado ya hoggota konce sai murk'ususu takeyi hanna
yenta rik'e da mararta kuka takeyi sosai cikin wahala gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login