Showing 123001 words to 126000 words out of 142577 words
Chapter 42 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
ta tayi hankali ta miƙa hannun ta karɓi Farouq dake ta bacci daga hannun
shi tamatsa a hankali ta kwantar dashi akan 2 seater,
sannan tadawo jikin shi ta ruggume shi a hankali takamo hannun shi ta jashi suka zauna
kan 3 seater,
ruggume shi tayi cikin kuka da rawar murya tafara magana a hankali tace,
"Hamma Umar baida wani fargaba daya wuce ya ganka cikin tashin hankali,
kullum burinsa ya ganka cikin farin ciki,
fatan Hamma Umar baya wuce samun lafiyar ka ya Usman,
ko a lokacin da zai rasu sunan ka dana Ammi ya kiramin amman Allah bai bashi damar
karisa min maganar da yake son faɗa minba sai yayi kalmar shahada,
Abunda ban saniba wata ƙil amanar ku zai barmin ko cemin zai na kula da kune ban
saniba".
Tana kaiwa nan suka daɗa rungume juna suka sake fashewa da kuka jiki na rawa ya
kuma matseta a jikin shi murya na rawa yace,
"Ummu na ni kam Hammana yabar min amanar ki keda Farouq randa yayi zuwanshi na
karshe a gidan nan,
saida duk ya bar mana wasiya amman a lokacin bamu ganeba,
Ummu kituna meyace min nida Adam".
sai kuma ya sake matsota jikinshi yana zubda ƙolla sannan yaci gaba da cewa,
" Hamma na cemana yayi,
"Da inada damar tafiya da Ummul duk inda zanje,
da ko ina zanje zan tafi da ita,
sai dai kach bani da damar yin tafiya da ita dole in barmaka ita Usman kaine ɗan
uwana kuma dole ka kula da family na,
Ummu
kin tuna abinda yacewa Adam
yace Adam zantafi da ita amman zata dawo in tadawo duk maison ɓata min rai ko
tozar tani to ya ɓatawa Ummu rai niya ɓatawa!
Ummu kin tuna abinda Hamma yacewa Aliyu,
yacewa Aliyu kai kuwa Aliyu a zatona kaine abokin kukan ta kaine abokin shawarar ta
Aliyu ko duk zasu dakarmin Ummul a zatona kai zaga zame mata katanga abun jingina azatona
kai mai tayata kuka ne".
Sai kuma ya sake ruggumo Ummun cikin tarin ƙunci ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya yace,
" Kin tuno me yacewa Sadik
Cemai yayi
"Sadiq inta dawo ka kasheta don dole zata dawo badon ina soba dole zata dawo cikin ku ba
yadda na iya,
ya kuma cewa Nanne Ummul fa madadin mutum 3 ce ni Usman da Ammin mu dakuma
ɗan cikin ki ya ware kanshi a lissafi ashe zai tafi ya barmune bamu saniba tafiyar da
bazai dawoba ashe duk maganganun shi wasiyace a garemu,
Ummu dana sani dana hana Hamma na tafiya a wannan ranar,
ashe shike nan mun rabu har abadan,
ashe shike nan yayi zuwanshi na ƙarshe a gidan nan,
Ummu ki tuna a ranar Hamma yace min,
Usman nauyin farin cikin Ahlina yana kanka in bananan".
Sake matsota yayi yaci gaba da kuka har yana shiɗewa,
Cikin tsana nin kuka itama ta ruggumoshi tana cewa,
"Ya Usman kayi hakuri mubar yiwa Hamma na kuka muyi mishi addu'a zaifi farin ciki
damu, kabar kukan nan Hamma bayason kukanka nima banason kukan ka,
ya Usman ina sonka ina son farin cikin ka ka dena kuka".
Cikin kukan ya tallabo kanta ya kalleta da kumburarrun idanun shi ya sakar mata
murmushin dayafi kuka ciwo a hankali yace,
"Allah ya ɗaiyaba min Ummuna,
nima ina sonki".
Itama murmushin tayi wanda hawaye ke bin fuskarta a hankali tasa tafin hannunta tashare
mai hawayen,
shima haka yasa hannu ya share mata nata ya ruggumo ta yana sauƙe nannauyan
numfashi a hankali yace,
"Ummuna zan dawo miki da farin cikin ki keda Farouq ko Hammana zaiyi farin ciki dani".
Shiru tayi tana kallon shi cikin jin tausayin shi,
Shiko ido ya lumshe cikin sanyi yasa hannun shi yana shafe fuskarta tare da gashin kanta
hannun yasa ya ƙara jawota jikin shi cikin salon lallashi yasa hunnun shi yana shafa jikinta
yana sunsunarta tare da goga sajen shi a kumatun ta,
a hankali ya rinƙa fese mata iska mai sanyi cikin kunnen ta,
hannun shi yarinƙa cusawa cikin rigarta yana yiwa kirjinta wani irin salo mai wuyar faɗuwa
yana sunsunar wuyanta yana wani irin numfashi gaba ɗaya ya gigitata ya gigita kanshi,
itama sai sake narkewa take jikin shi tana mika tana ɓoye fuskarta a jikinshi cikin tsananin
kunya,
haka suka kasance cikin yanayin rarrashin juna da kyar ta zame jikinta,
ta koma gefe tana gyara rigarta da ya cukuikiye a hankali takai dubanta ga agogon dake
manne a palour 12 dai-dai
shiru tayi a wurin tana satan kallon shi yadda
ya kife kanshi a jikin kujerar yana maida numfashi gaba ɗaya yayi wani iri,
da kyar itama ta saita kanta a hankali tace,
"Ya Usman tashi ka rakani zan koma cikin gida kar Ammi ta farka taga Farouq baya kusa da
ita".
riƙo hannun ta yayi murya na rawa yace,
"a,a dan Allah kibar shi mu kwana anan". miƙewa tayi tana girgiza kai,
"a,a gaskiya nidai tafiya zanyi wallahi ni kunya nakeji bazan iya kwana anan ba".
Shima miƙewa yayi ya kamo hannun ta ya lonƙoso kai yace,
"Ki taimaka min habibty zan shiga wani hali in kika barni cikin wannan yana yin ina buƙatarki
kusa dani,
ki kaishi saiki dawo in kinga kowa yayi bacci kinji plssss".
Dakai ta amsa mai alamar "Toh".
dan ya Usman yana bata tausayi kuma tana tsoron karta kuma irin kuskuren da tayi a baya A
hankali ta ɗauki Farouq ɗin ta fita kai tsaye ta wuce ɗakin su inda ta samu tuni Ammi tayi
bacci.
Kwantar dashi tayi akan gado a kusa da Ammin,
sannan taje tayo wanka tashafe jikinta da turaruka masu ƙamshi da sanyaya zuciya sai
kuma
itama tazo ta kwanta gefen shi,
Addu'a tayi ta tofa mashi ta tofe kanta sannan ta kwanta tajanyo wayarta ta buɗe data
dan taga ya Usman nata kiranta kuma bata son ɗagawa kar Ammi ta tashi,
tana buɗe datan
saƙon shi ta gani,
"ina jiranki a kofar Nanne ki fito mutafi kinga kowa yayi bacci".
Amsa tamaida mai,
"kayi haƙuri kaje ka kwanta saida safe".
"gaskiya bazan iya baccin ba kizo ki taimaka min in kuma bakizo ba kuka zanyi tayi har
gari ya waye, daman ni nasani ba mai sona sai Hammana".
Jiki na rawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta lallaɓa dan kar Ammi tafarka ta fice,
a bakin ƙofar palour ta taddashi tana fita yasa hannu ya ɗauketa cak ya ruggume ta a
jikin shi,
bai sauketa ko inaba sai sai akan gadon shi,
A hankali ya kontar da ita cikin wani irin yanayi ya konta gefenta a hankali ya jawota jikin shi
yana maida numfashi hannun shi ya cusa cikin rigar baccin jikin ta yana mata wani irin salo mai
taɓa zuciya a hankali yake sarrafata da salo mai cike da so da ƙauna haɗe bakinsu guri
guda yayi yana mata wani irin tattausan kiss, hannun shi nakan kirjin ta yana murzawa dukkansu sun rikice sunyi nisa cikin duniyar
masoya a haka sukai ta fama har bacci ya ɗaukesu suna ruggume da juna cikin happy.
A zabure Ummu ta farka,
aiko tare suka mike yana daɗa matseta kamar zaa kwace mai ita,
"Ya Usman kabarni intafi kafin kowa ya farka kaga an fara kiran salla ".
Wani irin kallo yake mata kamar zai haɗiye ta baice komaiba ya saketa,
dasauri ta fice bayanta yabi da kallo badan yasoba banɗaki yashiga yayi wanka sannan
ya fito ya fara nafilillin shi.
Gari na wayewa misalin 8:00 Usman ya shirya tsab yaje yagaida Abba da Hajjajo
sannan ya shiga ɓangaren Nanne, a kitchin yaji motsin Nanne dan haka ya tsaya ya
gaidata sannan ya wuce ɗaki, zaune yasami Ummul a kan sallaya Ammi kuma na
bakin gado ta zuba mata idanu, kamar jira take ya shiga tana ganin shi ta zuba mai ido
cikin son gano halin da ɗan nata ke ciki,
Shiko Usman a hankali yazo ya zauna a gefen ta yana gaida ta,
ɗago kai tayi tana kallonshi,
sai kuma ta sunkuyar da kanta ido cike da kolla a hankali ta fara zub da hawaye sai
sautin kukanta dayake fita a hankali dasauri sukayo gabanta suka durkusa suna
tambayar ta ko meya sameta suma idonsu tab kollah, cikin kuka tace,
" Usman wato wannan shine gatan da zakuyiwa Umar kenan ko Usman? sai ku taru
kuyita mishi kuka?
An haɗaku aure dan a nazaton zaku samawa juna sanyi da sassaucin zafin rashi shi
amman ashe bamu saniba hakan an baku damar ku zauna kuyi ta mishi kukane".
Usman ta kuma kalla da duk jikinshi yayi sanyi tace,
"Usman bakaso hankalina ya konta ko? Kasan bana son tashin hankalin ku kaida Ummu
kuma shine kake ƙarawa ga yadda fuskokin ku suka kubbura,
Usman har sai yaushe zamu bar kukan rashin Umar?
Usman ai kukan rashin shi bazai kare manaba har sai randa muka konta damarmu
daurewa zamuyi mubar zubda ƙollah muyita mishi Addu'a,
amman hakan ya gagara da sai ka tasa Farouq a gaba kaɓuya kayi ta kuka yanzu kuma
Ummul zakake tasawa a gaba kana kukan kenan?".
Shiru sukayi cikin sanyi da yarda da nasihar Ammin,
A haka Abba da Adam suka shigo suka samesu suma suka ɗora tasu nasihar har
saida sukaga sun sake suka je sukayi break cikin wolwola.
A ranar bayan sunci abincin dare ne suka zauna a palour Nanne dukkansu suna kallon
news a tashar TVC News suna zaune kowa da abinda yakeyi amman ita Ummul gaba ɗaya
hankalin ta na kan tv sai Aliyu dake zaune gefenta ta saman hannun kujerar da take zaune
Usman kuwa yana gefen ta a kan kujerar suna cikin hirar kawai sai sukaga Ummul
ta miƙe cikin tsananin razana da firgici gaba ɗaya jikinta sai rawa yake cikin gigita ta damki
hannun Aliyu dake kusa da ita sannan ta nuna tv da hannunta ɗaya baki na rawa murya
a hargitse take nuna tv tare da cewa,"
"Ammi gasu Ammi sune ya Usman kallesu wallahi sune Ammi sune suka k..".
Bata ƙarasa maganar ba tayi baya a sume ta faɗa kan Usman,
wanda ya taso tunda yaga yanda jikinta ke rawa,
dukkan su kanta sukayo kowa yana addu'a da jimamin damuwarta da gudu Sadiq
yaɗebo ruwa ya mikawa Ammi jikinta na rawa ta yayyafa mata sannan ta shafa mata a
fuska,
Lokaci ɗaya tayi wata irin ajiyar zuciya sai takuma razana tana ɗago kai idanu wanta a
zazzare
cikin tsoro Ammi tace,
"Wai meke razanata ne haka fa in baku mantaba hakan yafaru da ita cikin azumi ta
suma".
sai ta kuma kallon ta cikin tausayawa tace,
"Ummu na faɗamin me ke faruwa?".
Cikin firgici jiki na rawa tare da rera kuka mai cike da ƙuna a zuciya ta nuna fuskokin da ake
nunawa a tv tace ,
"Ya Usman kallesu sune suka yankamin Hamma na a gabana sune suka kasheshi wallahi
har abadan bazan manta waɗan nan fuskokin ba bazan manta fuskokin suba wallahi sune".
Gaba ɗaya jikinta na rawa,
sosai Usman yasake matsota ya tare mata fuskar ta daga kallon tv shima yana rumtse
idanun shi da ƙarfi dan har abada bazai so ƙara kallon waɗannan mutanen da suka kashe mai
Hamman shiba,
Adam dayake tsaye jikin shi yana rawa yafara musu bayani,
"Hakane cikin azumi wani azumi daya wuce ankama waɗanda suka kai harin bomb a Jos!
Kano da Zaria a gurin da ake verification na malaman makaranta, an kamasu ne a hanyar
komawar su a Daɗin Kowa ta jahir Gombe, wannan da take nunawa yanzu dashi a
cikin su yanzu kuma dasune akayi musaya suka bada y'anmatan Chibok da