Showing 108001 words to 111000 words out of 142577 words

Chapter 37 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

amsa da, "Wa alaikassalam, ya Usman ka
fitane?". saida ya sake kashe murya yace,
"waneni infita banyi sallama da ruhina ba,
inzone?".
Dasauri tace,
"a a ina zuwa".
bata jira amsar shiba ta katse wayar ta tashi ta fito.

Juya kai Usman yayi ya harari Adam cikin wasa yace,
"meye ka zuban ido, kake wata dariya kamar mara gaskiya".
k'asa da kai Adam yayi yana danne dariyar dake shirin fitowa da k'arfi yace,
"ni menace?".
tsuke fuska yayi yace, "Daman me ka isa kace,
fita zaka yi daga d'akin Ummuna zatazo".
Adam baisan lokacin da dariyar ta kwace mashi ta fitoba,
shiko Usman yunk'ura wa yayi ya kawomai dukan wasa Adam ya kauce yace,
"kuda zakuyi maganar ku a palour ina ruwana ina nan".
Kai ya kad'a yace,
"Allah saika fita d'an sa ido kawai".
Wayarshi ya d'auka yasauko daga gadon yana dariya yace, "intai tsami naji".

"inba tagi tsaminba kuma kai sai kayi tsamin ko".
Adam yana fita yasami Ummul bakin k'ofa tana sallama ya amsa cikin kauda kai sannan
suka gaisa ya wuce yanufi b'angaren Nanne.

Usman yana jin ta ya fito yana amsa sallamar ya k'arasa inda take tsaye ya kamo
hannunta,
ta biyo bayan shi saida yazo ya zaunar da ita a kujera sannan shima ya zauna gefen
ta yad'an matse hannun ta dake rik'e a hannun shi yace,
"kinyi kyau Baby".
janye hannunta tayi daga rik'on da yayi mata tace,
"ina kwana?".
sosa kai yayi sannan yace,
"lafiya lau sweetheart musamman ma dana tashi cikin sa ar ganin kyakykyawar fuskar
ki".
Kauda kai tayi gefe cikin jin kunyar shi sannan murya can k'asa tace,
"Ya Usman daman inaso muyi wata magana ce".
komawa yayi jikin kujera ya jingina ajiyan zuciya ya sauk'e tare da yin magana cikin rad'a yace,

"Ina jinki ya habeebati me bum'arki?".
Shiru tayi dan wata iriyar kasalar da voice d'in Ya Usman d'in ya sakar mata cikin sanyi tace,
"Labarin rayuwar mu nake son a rubuta shi ya zama novel ne dan inaga akwai darussa
da wasu mutane zasu samu da izina da WA'azantarwa a ciki shine ya Sadiq yace in fad'a
maka".
D'ago kai tayi danjin yayi shiru na d'an lokaci aiko da sauri ta maida kanta k'asa dan
yanda taga irin kallan da yake mata tamkar zai cinye ta duk ya susuce a kanta a hankali cikin
zurfin nazari yace,
"Tabbas akwai darasi a rayuwar mu kuma babu wani aibu ga abinda mutum zaiyi dan
nuni da tunatar da wasu wani Illa ko alfanu ko gargad'i ko izina ga Al'umma,
dan haka ina goyan bayan hakan".
Sai kuma yasa hannu yasake kamo hannun ta yace,
"Abin damuwar shine waye zai rubuta tunda kinga mu ba iyawa mukayi ba".
D'an murmushi tayi ta d'ago kanta dan jin dad'in yanda yabata goyon baya tace,
"ai akwai group da Aunty Halima ta sakani a Whatsapp to shine akwai Admin na group
d'in dana fad'amai har na bashi labarin kuma yace,
akwai marubuciyar danaga novel d'inta zai mata magana akan labarin,
toh amman ya mata magana ,
amman yace min ta nuna gaskiya ita bazata karb'i aikin labarin nawa ba tace,
ai yanzu haka ma tana typing novel nata mai suna *Bandirawo* bata gamashi ba kuma tace ko
ta gamashi tana da wasu aiyu kan rubuce-rubucen da yawa,
nima ya bani number ta na mata magana amman ta nuna gaskiya nayi hak'uri bazata yiba,
toh na gayawa Yahaya hayat d'in yadda mukayi yace kar in damu Insha Allah zai k'ara rok'onta
kuma zai tura mata labarin yana kyautata zaton in taga yadda labarin yake zata karb'a kuma
zata gyarashi ta yadda zata maidashi littafi mai zaman kanshi ta yadda ask'on da ake son
isarwa zai isa ga Al'umma ya kuma cemin aikin typing wuyane dashi bare maida labarin gaskiya
ya zama littafi aikine mai but'atar nazari da fasaha dan abu kad'an zaisa a kauce tsarin labarin,
don haka kaima kayi mata magana kuma mu gayawa Abba da Ammi in sun yarda ba matsala
yace sai,
zuwa anjima zaimin magana in sun gama maganar da ita".
Idonshi a lumshe yace, " to Allah yasa ta karb'a dan na lura hakan zai saki farin ciki
kuma yanzu zanje in gayawa Abba da Ammi jirani yanzu zanje in dawo sai mu kirata".
Murmushi ta k'arayi tace,
"nagode ya Usman". Shiko mik'ewa yayi ya nufu cikin gida Kai tsaye part d'in Abba ya wuce
inda ya sameshi shida Daddy da Ammi da Nenne suna maganar batun auren nasu,
A nan ya zauna yayi musu bayanin yadda sukayi da Ummul batun rubuta labarin ta,
murmushi Abba yayi shida Daddy da Ammi sukace sun yarda Allah ya sanya al'khairi rubutun
Allah Kuwa yayiwa marubuciyar albarka komai za'ayi da yardarsu sun yarda a rubuta labarin ko
suna yensu a saka kuma kar a canza labarin,
sosai Usman yaji dad'i cikin happy ya juya ya fita kai tsaye part ensu ya koma,
yana shiga ya zauna gefen Ummul nashi
sannan ya
d'anyi baya ya jingina da kujera yace,

"amma fa gaskiya Ummul auren mu shine cikar burina da kuma k'arshen littafin Ummu na ina
sonki ina sonki kusa dani ina da buk'atarki kusa dani".
kauda kai tayi cikin sanyi tace,
"Toh yanzu mu kira Aunty Aysha Garkuwa kayi mata magana da kanka".
"To" yace sannan ya Karb'i woyartata yasa Hf cikin sanyi ta fara magana a hankali tace,
"Anuty Aysha kiyi hak'uri na matsa miki Ummul ce wanda kukayi magana jiya dama ya Usman
ne yake son kuyi maga".
cikin tausayawa GARKUWAR FULANI ta fara magana dan yahaya hayat ya tura mata labarin
ta karanta cikin tausayawa rayuwarsu tace,
"Ayyah Ummu sannu Allah ya jik'an Hamma Umar Allah yasa ya huta rabbi ya karb'i
shahadarsa Allah yasa Al'jannace makomarsa muko in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani
da kalmar shahada,
Allah ya bawa Ya Usman lafiya da nisan kwana Allah ya raya Farouq k'arami".
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati".
suka amsa a tare ita kuwa garkuwa tuni take kuka cur-cur tunda ta karanta labarin nasu ta kasa
tsaida hawayen ta,
cikin sanyi ya Usman yace,
"Mun gode da Addu'arki ga d'an uwanmu Aysha Ummul tace min kince baza ki amshi aikin
labarin namu ba gashi yanzu tana kuka kuma mun gayawa iyayen mu sun yarda Insha Allah
anjima zan had'aki da Ammin mu ta gaya miki da kanta".
cikin sanyi da rauni tace,
"Ba komai ya Usman na yarda in dai naji daga bakin Ammi na yarda zan rubuta labarinku ina
gama *Bandirawo* kafin Sallan layyah bayan sallah zan fara labarin ku,
zan ajiye duk labaraina sai na gama rubuta labarin ku dan tabbas labarin Ummul akwai izinah a
ciki darasi mai girma a ciki".
Godiya suka rink'ayi ita kuwa Ummul sai kuka takeyi,
bayan sun katse kiran ne Usman yasa hannu a hankali cikin wani irin salo ya j.........




*SADAUKARWA GA DR UMAR IBRAHIM UMAR SHUWA (HAMMA UMAR)*





*By*
*GARKUWAR FULANI*


*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣5⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*




*Kin kid'i kankad'a, damuni na damoni, gid'd'omo fina laramo, gaid'omo fina sukoyo, ladde Allah
yamad'u, ki b'ib'b'e samme te, ki d'oidi yalete, b'end'uki yamete, yoriki tenets,*





*Ina mik'o sak'on ta aziyata ga yan uwana Fulani ma zauna Numan dake jihar Adamawa Yola
Allah ya isan mana ya saka mana cikin gagga bisa kisan gillan da k'abilar B'acamawa sukeyi
mana, Allah ya jik'an wadanda suka kashe Allah ya karb'i shahadarsu Allah ya saka mana
yadda suke tozarta mu Fulani ma zauna cikin rigogi suma Allah ya tozarta su Allah ya isa Allah
ya isa Allah ya isar mana kuma shi zai saka mana zalumin ci da ake mana, ina kuma kira ga
ugiyar TABITAL FULAKU ta jihar Adamawa tare da Ugiyar MI YETTI ALLAH da su hamzarta
shiga cikin wannan Al'amari domin kawo k'arshen wannan zalumcin da akayi mana shekaran
jiya da jiya a kwana biyu ace an kashe mutun kusan arba'in wannan zalumcin dame yayi
kama*







*A* hankali ya janwo ta jikin shi ya d'ora kanta a kan kijinshi sannan yasa hannun shi ya
ruggume ta sai wani irin numfashi yake fitarwa a hankali yana lumshe ido da sauk'e ajiyan
zuciya yana mai jin k'aunar ta da wani irin sonta,
itako sai lafe tayi a jikin shi tana kuka mai cin zuciya dan tuno Hamma Umar d'inta da tayi,
yayinda shikuma yakejin kukan ta har cikin ranshi gaba d'aya ta hargitsa shi yana jin
tausayi kanshi da kanta cikin lallashi yace, "wayyo Allah ba Ummu na dan Allah ki rufamin
asiri kidena kukan nan zuciya ta tana harbawa da k'arfi".
Sake cusa fuskar shi yayi a wuyanta yasa bakin shi a saitin kunnen ta cikin sigar
rarrashi da rad'a ya hura mata iska mai sanyi cikin kunnen nata murya a narke yace,
"Ki taimakawa zuciyar data dad'e tana muradin samunki, ki tausayawa ran daya dad'e
yana kwad'ayin ganin farin cikinki ki jik'aina kidena zubda hawayen ki,
kiyi min son da ako yaushe kika tuna Hamma na kiyi mishi Addu'a,

Wallahi Allah Ummul kece burin raina,
kece zab'ina,
Kece farin cikin ruhina kuma muradina,
zanso kiban dama in gwada miki yadda nake azab tuwa da cuter k'aunar ki da rad'ad'in
rashin d'an uwana kece kad'an zaki samamin farin ciki,
ina kaunar ki k'auna mai tarin yawa,
wallahi Ummul idona baya gani sai ko wacce mace da sigar aure sai ke,
kunnuwa na basa jin zak'in muryar ko wacce mace sai muryarki,
Noor qalbee wallahi idan nace ina ganin sauran mata kamar maza kar kiyi mamaki
wallahi bazan iya rayuwa babu keba".
ya k'arishe maganar tare da sa hannun shi ya shafo wuyanta numfashin shi na fita da kyar
muryar shi na rawa yace,
"Ummuna kaunar ki zatamin illah in dai ban same kiba,
dake nake kwana dake nake tashi numfashi na da bugun zuciyata duka nakine,
bazan iya jure rashin kiba, ki taimakeni ki yarda da aurena wallahi hakanne kawai
mafita guna kinji ka'nwata abar k'aunata".
Zuwa lokacin Ummul tafa ra tsorata da Usman gaba d'aya yanason b'atar mata da
hankali,
sai wani irin fesa numfashi yake yana lumshe ido da laso lips enshi kamar wanda yake cikin
maye,
ganin yadda yake ta k'ara matsowa jikin ta yasa ta d'an juya kai ta fuskarta ta fuskanci tashi
hakan yasa hancinsu ya had'u guri guda sannan ta sauke ajiyar zuciya da hakan yasa
iska fitowa daga bakinta kamar da gangan tayi,
aiko Usman najin iskar kasala ta sauka mai jikin shi ya mutu hakan yasa shi sassauta
rik'on dayayi mata ya koma jikin kujerar ya jingina yana lumshe ido yana bud'esu da kyer gaba
d'aya ya sake sai wani irin shu'umin kallo yake mata,
Ita kuwa hakan yasa tasami dama ta fusge jikinta daga rikon dayayi mata da k'arfi cikin
sassarfa tafice daga parlor tana kuka cikin sanyin sauti.

Kai tsaye d'akin su ta nufa tana shiga tafad'a kan gado tacigaba da rairo kukan ta,
dakyar Ammi dake gefenta ta rarrasheta cikin kukan da tuno Hamman ta tayi lamo akan
gadon kamar mai bacci,
ganin tayi shirune Ammin ta fita ta barta.

A parlour kuwa dakyar shima ya yunk'ura a daddafe yashige bedroom din ya fad'a kan
gado hannun shi rik'e da marar shi yayita mirginawa yana juyi hawaye na bin fuskarshi
pillow ya jawo Ya rungume da k'arfi yanajin wani irin yanayi na shigar shi,
yad'au lokaci a haka sannan ya tashi dak'yar yafad'a bathroom yasakarwa kanshi ruwa
sannan yafito ya shirya tsaf ya d'au mukullin mota yayi b'angaren Nanne .


Kwance yasami Ummul kan gado kamar me bacci Ammi kuma da shigowarta d'akin
kenan tana ajiye kayan data shigo dasu ya rusuna k'asa yasake gaida ta amsa tayi

sannan tasami bakin gadon ta zauna saida yayi kamar zai tashi sai kuma ya zauna
yace,
"Yauwa Ammi akan maganar rubuta littafin da Ummul takeso d'azu munkira ita
marubuciyar munyi magana shine nace mata zan had'aku da ita tasake ji daga bakin ki
saboda tad'au abin da muhimmanci duk da dai daga yanayin yanda mukai magana da
ita baza a samu wata matsalaba kuma bisa ga dukkan alamu Ummul ta k'ara samun
Aunty dan bakiga yadda tayita rarrashinta d'azuba".
Nan da nan Ammi taji k'aunar marubuciyar na ratsata kasancewar a yanzu bata da
burin daya wuce ganin samun kwanciyar hankalin Ummul d'in ta da murna tace,
" To madallah kirata muyi magana kaga sai nasake mata godiya".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login