Showing 120001 words to 123000 words out of 142577 words

Chapter 41 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

dawowa daga masallaci,
wanka yayi ya sha kwalliya sai zuba kamshi yake Adam dake kwance kan kujera a
palour yanajin fitowar shi daga bedroom yasa dariya k'asa-k'asa aiko kamar a kunnen
shi yajuyo yace,
"Me kakewa dariya?."
,hannu yasa ya toshe bakin da hannun shi yana b'oye dariyar yace, "Kai malam nifa abu
nake kallo a waya".
Kwafa yayi yafice sai palour Nanne.

Da Ammi yafara haɗuwa tana fitowa zatayi ɓangaren Hajjajo ɗan raɓawa gefe yayi itako
ta kalleshi cikin kaunar ɗan nata tace,
"hmm Usman manyan gari".
Sunne kai yayi ƙasa yana sosa ƙeya,

sannan ta wuce,
shima ya shige,
a palour suka zauna sunata zuba soyayya yanata rikita ta da kalamanshi masu daukar
hankali cikin hirar sukai amfani da wayar ta suka kira Garkuwa kiran na shiga shiya
fara magana,

"Barka da dare Anutyn Ummu".

"Barka dai ,ya kuke yasu Ammi da su babana Aliyu Auta?".

da fara'a yace,
"Suna lafiya lau kowa na gaidaki".

"Na gode matuƙa".

"Daman cewa nayi bari nayi maki godiya akan irin shawarwarin da kike bawa Ummuna
sannan in sanar dake yau ta karb'i sadaki na sannan ansaka rana nan da sati biyu".

"Alhamdullah gaskiya naji dadi sosai nakuma tayaku murna Allah yasa ayi a sa'a,
bani ita nayi mata murna".
hannu biyu tasa tarufe ido tana murmushi shiko sai cewa yayi,
Kin ganta tana jinki tarufe ido wai kunya takeji,
Anutyn Ummu gaskiya kiyi mata faɗa ta rege kunyar nan gudun karta takura mana rayuwa
kuma dan Allah ki mata nasiha ta rege kuka dan naga tana jin maganarki".
Murmushi tayi sannan tace,
"Ummu yau kuma ni ake kunya to shike nan saina jiki anjima a online dan zamu
tattauna inason karin bayani akan labarin kinga zamu fara".

Da haka sukayi sallama sosai Usman yaketa zuba godiya,
Basu jimaba ya rekata ƙofar ɗaki ta shige shima yatafi ɓangaren su.



Shirye-shirye aka fara domin kuwa sati biyu kawai aka saka ranar auren dan haka
Aunty Shuwa da Aunty Halima suka zage gurin gyara Ummul da taimakon Ammi da
Hajjajo kullum cikin tsumata suke da tsumakansu na shuwa'arab sosai suke tsumeta naci
dana sha dakuma na zama a ciki suna murjeta tuni ta murje ta ƙara fari da kyau ko ina na
jikin ta ya ciko tib sai sheƙi takeyi fatar nan tata kamar ta jariri kuma ita da kanta tasan ta tsumi
da tsumin mutan Yobe.

Wata ranar asabar da tayi dai-dai da saura kwanki bakwai d'aurin auren Aunty Shuwa
ta jiko abunda suka saba bawa Ummul kullum tafito palour Hajjajo inda suke zaune ita
da Aliyu da Aunty Halima sai Nanne da Ammi da uwar gaiya Hajjajo,

aiko tana ganin ta da cup ta ɓata fuska ta marairaice kamar zatayi kuka tajuyar da kai
tace,
"Ni gaskiya nagaji wallahi cikina a k'oshe yake yanzufa Aunty Halima taban wani
nasha".
Itama Anty Shuwa ɗaure fuska tayi ba wasa tace,
"Kuma wannan ma yanzu zaki shanye shi ba,
ni banson shirme ki amsa kishs kawai".
Bubbuga ƙafa tafarayi a ƙasa tana yarfa hannu da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa dai-dai lokacin
shigowar Usman da Adam da Sadiq sun dawo daga gaida Inna,
Dasauri Usman ya ƙaraso cikin palour yace,
"Wai meye, Halima ce ko?".
Ɗauke kai Aunty shuwa tayi kamar bata jiba itako Aunty Halima cewa tayi,
"kai ya Usman to bani bace itada Auntyn ta". ɗan juyawa yayi ya kalli Aunty Shuwa
data ɗaure fuska babu alamun wasa tace, "kyaleni da ita, abu nabata wai bazata shaba
ta k'oshi".
ɗan leƙa cikin kofin yayi sannan ya tambaya,
"Magani ne?".
"eh maganin ciwon ciki ba".
Inji Halima,
ganin yadda yajuyo yana kallonta yasa Nanne tashi ta fice dan ta gane sarai Usman ya
gane maganin menene ake batan,
dan tasan halin shi zai iya faɗan komai,
a hankali ya ƙarasa inda take zaune yace, "Ummu na yi haƙuri kisha mana kinji kinga
yanada amfani".
Noƙe kafaɗa tayi alamar taƙi a hatsale Aunty Shuwa tace,
"Matsamin dan Allah intafi ana baki kinawa mutane yanga wazai amfana? ni ko Halima ko
ke?".
Dasauri yamiƙe ya karɓi kofin ya tsura mata ido fuskar shi babu alamun wasa yace,
"Ke wallahi sai kinsha ko in ɗura maki, wannan ai shirme ne,
au tukun ma wai shin ko dai baƙin ciki zakimin?".
da jin haka Ammi ma ta tashi ta fice tabarsu ganin taƙi karɓa yace, "Sadiq riƙe min cup ɗin
Allah saina ɗura maki zakiwa mutane asara da baƙin ciki inke bakya so ni inaso kuma dole
kishi".
Yana faɗa yana matsowa kusa da itan sanin halinshi yasa ta miƙa hannu Sadiq ya miƙa
mata kofin tana ɓata fuska takai bakinta,
"Gwara miki dan wallahi ba abinda zai hana in d'ura maki shi". Saida ta shanye tas
sannan tasauke kofin tana dama fuska kamar zatai amai,
kallon Aunty Shuwa yayi wacce kunya ta rufeta har ta kasa ɗaga ƙafarta wato Usman yama
gano me ake bawa Ummu,
shiko ko a jikin shi yace daga yanzu in taƙi sha dan Allah ku kirani".
Yajuya zai fita Hajjajo datake kallon ikon Allah tace,
"fitsararre".
Juyowa yayi kafin yaba ta amsa idon shi yasauƙa kan Ummul da taketa kakarin amai

kallon ta yayi tare cewa,
"Kada kiyarda ki amayar da abinnan dan sai an ƙara maki wani".
Ficewa yayi suko duk sukayi shiru suna kallon juna itako tashi tayi tafice tana buga ƙafa.




Yau asabar da misalin ƙarfe 10:30am na safe dubban jama a suka shaida daurin auren
USMAN IBRAHIM UMUR SHUWA da amaryar shi RABI'ATU HASSAN UMAR SHUWA ciki
da abokan Hamma Umar wanda dayawa suka sami gayyata daga Dr Bashir da kuma
Mustapha shima da mahaifinshi, Ango kuwa Usman lokaci ɗaya tunanin ɗan uwanshi ya faɗo mai a take ida nunshi suka fara
zubda ƙolla mai tsananin zafi yana tuna a yau ds Hamman shi na raye da zaifi kowa farin ciki
da yau zaiga gata mai tarin yawa cikin kuka yake gaisawa da abokan Hamman nashi,
bayan ya shiga cikin gida kuwa Ammin shi ya tasa a gaba suna wani irin kuka mai cike da ƙuna
a zuciya da kyer aka samu Abba da Hajjajo suka tausasu.

Haka abin ya kasance a cikin gida mata nata nasu hidimar ga matar Dr Bashir da
matar Mustapha da Ummanshi,
ita kuwa Ummul yau mutuwar Hamman ta takuma dawo mata ruggume Farouq tayi ta durƙusa
gaban Adam da Sadik tana kuka mai tarin nadama da dana sani,
Shima yaro ganin yadda mahaifiyarshi ke kuka sai ya fashe da kuka mai ƙarfi
ayyah Adam shma gaba ɗaya ya kasa control en kanshi sai hawaye cur-cur ya kasa magana
Aliyu kuwa jawo Farouq yayi ya riƙeshi gam a jikin shi suna kuka,
Sadik ne da Anty Shuwa sukayi ƙarfin halin lallashin su da yi mudu nasiha,
saidai Amaryar kam da kyer aka samu aka rarrasheta saboda kuka da takeyi mai
tsanani dan tunawa da masoyinta Hamma Umar.

Haka jama'a sukayi ta tayasu murna har zuwa dare aka fara watsewa.

Ango yanata sintiri dan yana son ya lallashi Ummul enshi da kanshi kuma shima yana buƙatar
ta tausayawar ta a gareshi dan yau gaba ɗaya begen Hamman shi yake,
karo na 3 yashigo yasami Nanne da Ammi sai Aunty Shuwa da Aunty Nafisa yasami
gefe yazauna gaisawa sukayi tare da ƙara yimai addu'a kai yafara sosawa yakalli Aunty
Shuwa cikin rauni yace, "Ina take?".
Haɗe fuska tayi sannan kuma abin nashi ya bata dariya ya kuma bata tsusayi a hankali
tace,
"To anace tanada bak'i".
D'agowa yayi ya kalleta sannan ya saci kallon Ammi daketa ƙoƙarin maida ƙollar ta a
hankali yace,
"Dere yayi fa kuma zamuje wani wuri da ita Ayyah dan Allah a bani matata".
Ammi ce ta karb'i zancen da cewa,
"A,a baza a baka ba Usman,

ainan ba gidan ka bane kuma da bakinka kace sai kaje course kadawo zata tare".
Da hannu ta nuna mai hanya alamar ya tafi, marairaice fuska yayi kamar zaiyi kuka
yace, "Nanne".
Bai ƙarasaba tace,
"Jeka kayi wanka ka huta babu mai hanaka matarka".
Ɗan murmushi ya ido cike da ƙollah yatashi yafice yana ƙoƙarin cire babbar rigar jikin shi,
Ammi ta kalli Nanne tace,
"Bafa zan yarda da wannan tsarin ba". ƙasa Nanne tayi dakai cikin girmamawa tace,
"Kiyi haƙuri Addana dan tun ɗazu Abban su yace kada a hanashi matar shi ,
dan duk su biyu kukan da sukeyi na abu ɗaya ne tuno Umar ne kuma su duka kowa zai tsaida
hawayen shi dan ɗaya yayi shiru,
kuma ai banga laifin hakan ba tunda mutune dayawa suna aure su tare gidan iyaye
nasu kinga shima yanada damar hakan kuma kinga yama kusa yin tafiyar".

Aunty Shuwa ce ta kalli Ammi tare da cewa, "Ammi ki kyale ɗan Abba yasha sha anin
shi dan wallahi dagashi har Ummul sun ban tausayi ga yadda ƙaddara ta haɗasu bawan Allah
Farouq shima yau yayi kukan rashin Uban da bai saniba".
Itako Ammi baki ta d'an rumtse hawaye na bin fuskarta tace,
"Hmmm to Allah yayi musu albarka Allah ya jiƙan Umar Allah ya mishi rahama Allah ya raya
abun da ya bari".
"Amin Amin Ameeeeeeeen ya rabbil izzati"
suka amsa baki ɗayan su,
Aunty Nafisa matar Daddy wacce tunda aka fara magana tayi shiru tace,
"Au shiyasa naga Adam da Halima sunata shirya Ummul ɗin".
Ammin ce ta miƙe tana tafiya tace,
"eh mana ai duk bakinsu ɗaya har da Adam kamar mace,
nidai baruwana kuma bame takuramin yarinya.


A ɗakin su Usman kuwa Adam ne da Nuru sukayi ta lallashin Usman,
miƙewa sukayi
jin muryar Anty Halima wacce ta shigo ruggume da Farouq Ummul na biye da ita a baya,
A hankali tace,
"Ga Farouq tun ɗazu yake kuka sai a kawoshi gun Abeen shi".
hannu Usman yasa ya karɓeshi sannan ya ruggemeshi
suko Anty Halima da Adam da Nuru fita sukayi suka bar part ɗin gaba ɗaya.


Shiko Usman suna fita yasa hannun ya ruggum.....



*By*

*GARKUWAR FULANI*


[12/5, 9:42 PM] +234 808 364 9787:

*RUBUTACCEN AL,AMRI*

Page 3⃣7⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*





*MOH ALLAH WUJI FURƊA TA FULLO BE FULAKU KOSAM EH DAN GOL*



*Wannan shafi naki ne ke kadai k'anwata ta kaina Queen Hafsi Allah bar zumunci da k'auna
dear *








*H*annu yasa ya jawa Ummul ɗin ta faɗo jikin shi cikin sauƙe ajiyan zuciya ya haɗasu da
Farouq ya ruggume su tsam a jikin shi yana jin wani irin yanayi mai cike da tarin rauni,
tabbas wani abu sai mutuwa inba mutuwaba ya za'ayi ya auri Ummu matar ɗan uwanshi gaba
ɗaya begen ɗan uwanshi ya rufeshi zuciyarshi ta cika da rauni a hankali wani irin kuka ya kufce
mai,
kuka mai cin zuciya har jikin shi na rawa sai ƙara ruggume ta yake yana sheshsheƙa
hawaye na bin fuskar shi,
itama Ummu sai kara lafewa tayi a jikin shi tacigaba da kukan dama tun safe take yinshi,
Kuka suke sosai bame rarrashi wani a cikin su sai ruggume juna sukeyi suna kuka mai cike
da ƙuna a zuciya,
sun ɗau lokaci mai tsawo suna cikin yanayin tuno da jigonsu gaba ɗaya zuƙatansu sun cika
da rauni,
Cikin kukan Ummu ta ɗago kanta fuska cike da ƙollah ido ta ɗan firfitar ganin yadda numfashin

ya Usman ke fusga yana neman ɗaukewa sai karkarwa yake ida nunshi sunyi jazir ƙirjinshi
na bugawa da ƙarfi ,
janye jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login