Showing 111001 words to 114000 words out of 142577 words

Chapter 38 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

D'an d'agowa yayi ya
lek'o kan gadon yace, "Khairi mik'omin wayar ki".
Dana sauri Ammin tace, "Haba Usman kace in mik'omaka mana saika tayarmin da ita
daga baccin tun d'azufa kuka take yi da kyer na samu tayi shiru".
A hankali ta d'an d'ago kanta wadda daman tana jin duk zancen nasu ta d'auko wayar
tayi ta mik'o mai,
Kanshi a sunkuye yasa hannun zai karb'i woyar cikin hikima ya had'e wayar da hannun ta ya
rik'e yana murza yatsunshi biyu kan yatsunta cikin salon lallashi da so,
da sauri ta zame hannun ta tana kallon Ammi,
Itako Ammo batama ga abinda suka yiba, Dialling number yayi bata jima tana ringing ba
ta d'auka sannan ya mik'awa Ammi ta karb'a tasa a kunnen ta sannan tace,
"Assalamu alaikum". Cikin muryarta mai sanyi da saisaita zuciya ta amsa sallamar
sannan tace,
"Wa alaikissalam ina kwana".
gyara zama Ammin tayi tana fara a tace,
"lafiya lau d'iyar albarka, ya yaranki ? da mai gidan ? ya kuma gurin manya?".
Cikin ladabi ta amsa da, "lafya lau Alhamdulillah".
cikin girma Ammi taci gaba da cewa,
"Y'an nan Ammin Ummul ce".
jin hakan Garkuwar cikin tausayawa tace, "Ayyah Ammi kece ya hakurin mu na rashin
Hamma Umar? Allah ya jik'an shi yamai rahama yasa can yafi masa nan ku kuma Allah
ya k'ara maku juriya da hak'urin rashin shi".
Cikin sanyi Ammi ta amsa mata da,
"Ameen nagode Allah ya bada lada".
sannan tayi ajiyan zuciya tare da ci gaba da cewa,
"Usman ya sanar dani yadda duk kuka yi akan rubutun littafin kuma yace kinaso ki
k'ara tabbatar da sahihancin labarin shiyasa nasa baki kuma nake fatan zaki karb'i abun
dan taimakawa".
Shiru tayi dan sauraren amsarta inda cikin girmamawa tace,
"Insha Allah Ammi babu matsala zanyi iya k'ok'arina inga munbada sak'on da labarin
yake d'auke dashi, duk da ina da wasu ayyukan banda wanda nakeyi a yanzu amma da
yardar Allah zan aje komai idan na k'arasa wanda nake aiki akai yanzu Insha Allah shi
zan fara." Cikin jin dad'i tace,

"To y'ar nan Allah yamiki albarka ya jib'anci dukkan lamuranki yakuma biyaki da gidan
aljannah".
Daga ita har Usman da Ummul da,
" Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati ".
suka amsa cikin sakin fuska Ammi tasake cewa,
"To sai hakuri da k'anwar taki gatanan kuka koyaushe takasa daina shi sai ki cigaba da
d'orata kan hanya dan tabbas had'uwar ta dake ya kawo canji a yanayin ta da".
"Insha Allahu" Garkuwa tace sannan Ammi taciga da cewa,
"Yauwa Aisha nagode sosai Allah ya bada sa a Allah yabaki ikon aikin alkhairin da
kikayi niyya Allah ya miki al'barka".
"Ameeen". da haka sukayi sallama Ammi ta mik'awa Ummul wayar ta mik'e tana kallon
Usman cikin k'aunar d'an nata tace,
"Fita zakayi ko?".
yana inda yake zaune yace,
"eh me kike buk'ata? in kawo miki?".
tana tafiya tace, "bakomai Allah ya kiyaye ka ya dawo dakai lafiya".
Yana sosa kai kamar mara gaskiya yace,
"Amin".
Tashi yayi yakoma bakin gadon ya zauna ya k'ura mata mayan idauwan shi sannan cikin
rad'a yace,
"Wai ina yarona ne?". Kanta a k'asa tana wasa da yatsunta tace, "Yabi Daddy tunda
yazo gaida Hajjajo".
K'ara sunkuyowa kanta yayi cikin lumshe ido yace,
"To amma dai bawata matsala ko?".
Murya na rawa tace, "bakomai".
hannu shi yasa ya ruk'o nata yana d'an murza yatsunta a hankali yace, "To aimin rakiya
mana irinta masoya".
nan da nan ta kwab'e fuska ta tayi rau-rau da ido alamar zatayi mishi kuka,
Ganin haka ya sake daburcewa jiki na tsuma mik'ewa yayi sannan ya sunkuyo dai-dai
kunnen ta ya tsurawa k'irjin ta ido murya a cushe yace,
"Kiyi baccin ki mai dad'i tare da mafarki na ina lasar wad'an nan lips en na ki masu taushi
Ummu na ina begen randa zaki zamo mallaki na".
Fusge hannun ta tayi ta rufe idonta cikin kinda da mamakin ya Usman d'in,
shiko ko ajikinshi dan daman haka yake baya b'oye abinda yakeji,
juyawa yayi har yaje bakin k'ofa yace,
"please ki ajiye wayarki a kusa".
Sannan yasa yatsunshi biyu a kan lips d'in shi yai kissing d'insu ya hura mata da bakin
shi sannan ya fice.

Kai tsaye yawuce FCE(T) inda yake koyar da masu koyan computer duk juma a da
asabar.

Office d'in Mallam Bashir Bala abokin aikin shi yashige kai tsaye kasan cewar nan yake

zama in yaje saboda yakan jene sabida nemanshi da sukai yarink'a taimakawa,
bayan sun gaisa Malam Bashir yace,
"To bari inje kafin ka huta".
Yana fita shiko ya d'aga kafafuwan shi ya d'ora akan kujerar dake kallon wadda yake
zaune ya ciro waya yakira number Ummul ya saka a kunne,
saida ta kusan katsewa sannan ta amsa murya can k'asa tai mashi sallama,
"wa alaikissalam Hubby, ykk".
Jin abin tai wani iri sabida ganinta yanzun nan yafita amma yana tambayar ya take,
shiya dawo da ita daga tunanin da take da cewa,
"Allah yasa ba bacci kika fara na tasheki ba, kiyi hak'uri wallahi soyayyar ki ce take
d'ibana nake kasa jurewa shiyasa zakiga ina irin wannan abu buwan".
baki ta tura tare da cewa
"hmmm". Kawai shikuma yaci gaba,
"Gaskiya Baby ki dena min rowar muryarki dan Allah ki karb'eni kiban dama nashigo
rayuwarki na cika zuciyar ki da farin ciki pls".
Yasan da wuya tabashi amsa dan haka yaci gaba da cewa,
"Kice wani abu dan Allah, indai kinaso nayi aikin danazo yi".
shiru dayajin ne yasa d'an sauke k'afar shi k'asa yazura takalmin shi ya mik'e yana
mak'ale da wayar yafara tafiya yana cewa,
"Ganinan dawowa tunda bazaki min magana ba nima babu abinda zan iya yi gwara
indawo inta zamana a gida". Dai-dai nan yabud'e murfi motar shi yashiga ya rufe kofar,
k'arar rufe motar yasa ta tabbatar dagaske zai dawo da sauri cikin sanyin murya tace,
"Ya Usman dan Allah karka dawo". Komawa yayi ya jingina da jikin kujerar motar yayi
murmushin jin dad'i yace,
"kin barni na fito bakimin addu'a ba kuma yanzu nakira kink'i kimin magana gashi duk a
matsa nake wane irin aiki kikeso nayi a hakan?".
Katseshi tai da,
"Kayi hakuri Allah yabada sa'a ya kiyaye ka".
Wani irin sanyi yaji a zuciyar shi yasa hannu yabud'e motar ya fita ya maida murfin ya
rufe sannan yace,
"Amin, to ko kefa, yanzu ne zanyi aiki ki kulamin da kanki saina fito".
"Adawo lfy".
tace sannan ta katse kiran tabi wayar da kallo tana jinjina hali irin na ya Usman shi sam
ya fiye zalama daga dukkan alamu shi ba irin Hammanta bane mai hak'uri.


Shak'uwa mai k'arfice take shiga tsakanin Ummul da sabuwar Auntyn ta Aysha Aliyu
Garkuwa, wanda sukan yi waya sannan suna dadewa suna chat, hakan na debewa
Ummul kewa kuma tasami nutsuwa saboda irin rarrashi da shawarwari datake samu
daga gareta saidai kusan koda yaushe dukkansu da kuka hirar tasu take k'arewa
musamman idan GARKUWAR tayi mata wata tambaya game da rayuwarta ta baya,
ranar wata asabar Ummul ke fad'awa Auntyn nata zasu tafi Saudi dan gudanar da aikin
Hajji ita da Ammi da Ya Sadiq kuma zasu tafine ta international air dan haka Dubai

zasu wuce sannan daga can su dawo k'asa mai tsarki. Addu'a tayi mata sannan suka
rabu.

Kamar yau aikin hajji ya k'are dan haka suka d'unguma sai Dubai inda zasu kwana
kafin da safe suwuto gida Nigeria,
Wannan yaba Ummul damar bud'e data ta tayi sa a Auntyn ta tana online taji dad'in
ganin ta saboda hakanan taji tana buk'atar su tattauna akan abunda yake damunta,
sallama ta yimata bayan su gaisa sosai ne Ummul tafara tambaya kamar haka, " Aunty
dan Allah dagaske ne yanzu idan nasake aure shikenan na rabu da Hamma Umar na
rabu da aurensa na tashi a matsayin matar Hamma Umar?". Tambayar ta bawata tausayi
duk da tasaba da shirmen Ummul d'in, cikin sigar lallashi data saba da yimata tace,
"Meya kawo wannan tambayar dear?". Shagwab'ewa tayi kamar zatai kuka tace, "Ya
Usman ne yadameni kan maganar aure nikuma gaskiya banason kowa kuma banaso
inzauna da kowa sai Hammana Aunty Aysha wallahi ina son Hamma na duk duniya yanzu shi
nake so".
Ajiyar zuciya tasauke sannan tace,
"Haba Ummuna, tun kafin kiyi tafiyar nan muke magana guda d'aya kuma kinga dukkan
mu burin mu mu samar maki da farin ciki wannan shiyasa zakiga kowa nada burin kiyi
aure saboda auren shine kad'ai hanyar da zaki sami nutsuwa kuma kisamar wa
Hamman ki kwanciyar hankali dan in kinyi aure zaki rege zubarmai da hawaye, kuma ta hanyar auren Usman ne zaki samu farin ciki mai d'orewa, k'anwata auren Usman
shine kwanciyar hankalinki dana iyayenki dakuma na yaronki kai harma dana Hamman ki
Allah yamai rahama".
"Amin" ta amsa sannan taci gaba,
"Zai kasance cikin farin ciki kina kulamai da d'anshi da k'anin shi sannan iyayenku su
kasance cikin farin ciki kuma su manta da duk abinda ya faru a baya da yafe maki
kuskurenki na bijire musu da kikayi a baya".
Sannan taci gaba cewa, "Ki d'aure zuciyar ki nasan dole zakiji babu dad'i kuma dole
akwai ciwo a zuciyar ki amma ki daure kiyi hak'uri kinji k'anwata ki yarda da auren
Usman".
Hannu tasa tashare k'ollah dake zubowa daga idonta sannan ta fara typing amsa,
"To Aunty Aysha insha Allah zanyi hakan sabida farin cikin Hamma na da iyayena,
nagode da kulawarki gareni".
hakanan daga nan kuma hirar takoma rarrashi saboda kukan da dukkansu sukeyi.


K'arfe 12 na dare jigin su yasauka a filin sauka da tashin jirage na Aminu kano a cikin
birnin kano,
a Tahir guest palace suka kwana sannan da safe suka d'auko hanyar Potiskum, ya
Usman da ya Adam ne sukaje d'aukosu haka suka dungumo misalin k'arfe 10:08 suka
iso gida,
Sunsami kowa cikin k'oshin lafiya Umar Farouq tunda suka iso ya haye jikin
mahaifiyarshi yanata bata labari na abubuwan da suka faru bata nan haka suka wuni

cikin nishad'i sai bayan sallah isha'i ya Usman yamaida Halima da yaranta gida shima
Adam yamaida Aunty Shuwa da Inna tunda unguwarsu d'aya,
Adam na dawowa yawuce b'angarensu dan yana buk'atar hutu, shiko gogan Ummul
daman Allah-Allah yake bak'in su tafi ya gana da masoyiyar shi tun yana mota yakira
wayarta tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login