Showing 3001 words to 6000 words out of 142577 words
Chapter 2 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
sai ya tsaya ganin yadda ta karya wuya ta tsura mishi ido tana murmushi gaban ta ya
matso dai-dai lokacin Nenne da Aliyu kuma suka shigo parlour,
ita kuwa Ummul kai ta k'ara d'agowa cikin koikoiyar muryar Ruk'ayya budurwar Nuru tace.
"Ya Usman ina son ka."
Murmushi yayi tare da k'ara matso ta ya tura k'afa d'aya gaba d'aya kuma ya maida shi baya ya
d'an rink'a sonkuyowa kanta sannan ya koikoiyi muryar abokinshi Nuru yace.
"Allah d'aiyiba ."
Gaba d'aya su Nenne da ya Adam da ya Sadiq kam sai dariya suke Aliyu harda rik'e ciki Hajjajo
kuwa sai binsu tayi da ido tana murmushi dan tasan shek'iyan cin Usman yawa ne dashi.
Shi kuwa Usman ko a jikin sa sai tea d'in shi yaci gaba da sha,
Itama Ummul sai murmushi takeyi ta zauna gefen shi tana sa mishi abinci.
dai-dai lokacin Dr Umar Faruoq kuma yayi sallama duk da yana jin yadda suke ta dariya,
yana shiga ya gaida Nenne ya Adam da Sadiq kuwa suka gaida shi,
gefen Hajjajo yaje ya zauna tare da tonk'oshe k'afafun shi kanshi a sunkuye yace.
"Hajjajo an tashi lfy."
Juyowa tayi tana fuskan tarshi tare da zubawa kekkyawar fuskar sa ido,
shi kuwa bai bita kan ta amsa mishi gaisuwar ba ya sunkuyar da kai yana b'allo magungunan
Usman d'in.
Ido Hajjajo ta lumshe cikin k'aunar jikan nata da takeji tamkar ranta donko ya kasan ce shine
jikanta na forko da ta fara mallaka uwa uba ga tsananin kamar da ya keyi da mahaifin shi gashi
takwaran mijin tane hakan yasa take masa wani irin so mai tarin yawa gashi da halaiyar girma
Doctor Umar Ibrahim Umar shuwa kenan.
Cikin kula tace.
"Umaru sanda kafi mata yanga Umaru kafi k'arfin kab'i mace sai dai ta bik'a Ummaru sanda mai
k'amshin al'miski sanda babuga mai taimakon na gida da woje ,
Ummaru tsiyar ka rigima da mishkilanci ko maganar ka tsada gareta."
Kanshi a k'asa ya d'an lumshe ido har ga Allah shi wannan halin nashi halittar sa ce haka Allah
yayishi bai san ya zaiyi ya canza kanshi ba haka yake, a ranshi yace.
"Ya zanyi da Rubutaccen al'amari haka Allah ya halicceni bazan iya canza kaina ba".
Ita kuwa Ummul tuni ta tsuke fuska dan sam bata jin Hamma Umar Faruoq d'in nasu kamar jinin
ta haka kuma ya samo asali ne da yanayin halin Faruoq baida shiga harkar da ba tasaba bayi
da yawan magana baya kuma son raini da hayaniya yana da girmama na sama dashi har
ranshi kuma yake jin son y'an uwanshi a ranshi yana kuma kula da yanayin tarbiyar k'annen shi
a matsayin shi na babban yaya,
suma kuma suna son d'an uwansu sai Ummul ce da sam bata ko son su had'a inuwa d'aya da
shi.
Tsuke fuska Ummul ta kuma yi jin yadda Hajjajo ke wani bashi kula ta musamman shiko ya wani
shareta.
Su Adam da Sadiq da Aliyu da Usman sai murmushi sukeyi.
Shi kuwa yana gama b'allo maganin ya mik'awa Usman tare da bud'e mishi ruwan ya bashi
yasha sannan ya had'a maganin wuri d'aya tare da mik'ewa ya fita a hankali yana zuwa bakin
kofar woyarshi ta fara tsuwa cikin wani sautin wak'ar India kaal hoh nan hoh sautin ne da ya
kasan ce ko ba,a ga Umar Faruoq a wurin ba matukar akaji sautin toh tabbas yana kusa da
wurin sauti mai cike da sanyi da tausayi.
A hankali ya fito a barandar Hajjajo ya koma gefen baya kad'an tare da zauna wa kan kujerun
dake jere a wurin.
Woyarshi ya zaro a hankali yayi picking ya fara magana a hankali.
Su kuwa a parlour Usman ne ya mik'e tare da cewa.
"Nenne bari in tafi gwadago."
Murmushi ya Sadiq yayi tare da cewa.
"Tab ai kai kam aikin wuya kam baka cikin kai da zuciyar ka take rabi ai sai dai kaje back kana
shan rab'a."
Hannun shi yasa ya d'an dafe k'irjin shi cikin lumshe ido yace.
"Da kenan ya Sadiq yanzu nayi lafiya zuciya ta kamar taka take ko buhu zan iya d'agawa."
Adam ne ya d'an kalleshi yace.
"Sai dai buhun kam amman damuwa da firgicin da zuk'atan mu zasu iya jurewa taka zuciyar
bazata iya d'auka ba."
Murmushi sukayi baki d'aya ita kuwa Ummul maya finta ta gyara cikin fara'a tace.
"Yauwa ya Usman dama zanje gidan Anty Sadiya dan tunda akayi sallah ban jeba."
Hannu ya mik'a mata tare da cewa.
"Zomu tafi yar k'anwata zan kaiki."
Aliyu ne ya kalli Nenne da sauri yace.
"Nenne kina ji wai zata tafi gidan Anty Sadiya kuma batayi girkin ranaba."
Da sauri Nenne tace.
"Ehh haka nefa Autana kaga har na manta,
kai kam Usman tafi kawai abinka kar ka makara,
Ita Ummul sai tayi girkin rana."
Lokacin d'aya idanun Ummul suka ciko da k'ollah tib hannu ta rink'a yarfawa a hankali tana d'an
buga k'afafun ta tare da yin kan Aliyu tana cewa.
"Ma gulmacin yaro dan munafurci Aliyu duk k'asa min ido a rayuwa ta shi yasa wallahi na
gomma ce ina school ba mai takura wa rayuwa ta."
Sai ta kuma juyowa gun Nenne cikin muryar lallashi tace.
"Ayyah Nenne na kiyi hak'uri ki barni naje wallahi zan dawo da wuri inyi aikin dare."
Kai Nenne ta girgiza alamun bazata jeba.
Sai hawaye car-car a fuskarta.
Shi kuwa Aliyu dariya ya fara yi cikin jin dad'in ya d'ana mata tarko.
Kanshi tayi a fusace tana.
"Munafuki wallahi sai na dokeka."
Cikin dariya ya zille ya fara gudu ita kuma tana binshi a baya ta kasa kamashi.
Shiko Aliyu gudu yake tare da cewa.
"Yoh ai laifin ba nawa bane tunda bani nace duk randa kika dawo Hutu ko weekend kece zakina
yin girki ba,
Hamma Umar Faruoq ne ya fad'a, kuma kice ni zaki daka, kije ki ce mishi bazakiyi girkin ba
mana,
ni me nawa a ciki?."
Kuka ta farayi tana binshi tana cewa.
"Ai shima mugun tace kawai ya hanani hutawa a rayuwa ta, ga masu aikin Amman don
mugunta yace ni zanke yin girki mugu kawai mai bak'in hali."
Dariya Aliyu ya kuma yi harda yi mata gwalo yace.
"Shifa Hamma Umar yana tausayawa mijin da zaki aurane shi yasa yace ke zakina aikin ,
don karkije baki iya girkiba,
a ga laifin iyayenmu."
Binshi tayi da sauri shi kuma ya nufi woje da gudu yayi gefen da ya hoggo Hamma Umar d'in
nasu yana gudu yana juyowa yana kallon ko ta kusa kamoshi.
Shi kuwa Dr Umar Faruoq tun da ya katse kiran woyan da yake yin,
yake jiyo hayani yarsu shi Aliyu a hankali yake tsokanar ita kuwa Ummul sai mita da kuka take
yana jin tana ta cewa Aliyu munafuki,
Kalmar da baya k'aunar yaji an suffanta mutun da ita.
Ita kuwa sam bata lura da Hamma Umar d'in a wurin ba.
Shi kuwa Aliyu ya zo dai-dai gaban Hamma Umar d'in ya sule yayi wani irin mugun fad'uwa a
k'asan tayis,
gum ya buge bak'in shi a take sai ga jini,
cikin wahala ya saki kuka mai k'arfi, wanda yasa su Nenne fitowa a guje.
Shi kuwa Hamma Umar da sauri ya mik'e ya d'ago Aliyu ranshi a b'ace ya kalli yadda bak'in
yaron keta zubda jini,
ita kuma tsayuwa tayi jikinta nata rawa ganin yadda jini yake zuba a bak'in k'anin nata ga wani
irin mugun kallo da Hamma Umar ke watsa mata.
Ganin su Nenne sun fito tayi maza tayi bayan ya Usman dan shi kad'ai ne mai kareta su ya
Adam ma kullum fad'a suke mata da biyewa Aliyu da takeyi tayi ta jibagarsa.
Ita kam Nenne da sauri ta k'arisa gaban Dr Umar Faruoq da ya tallab'e hab'ar Aliyu cikin fad'a
tace.
"Ummul zaki kashe min yaro a banza ga yadda kika fasa mishi baki akan zuwa uguwa."
Ita dai Ummul sai hawaye hannun Usman ta rik'e da k'arfi ganin Dr Umar Faruoq ya kirata da
hannunshi cikin rawan murya tace.
"Ya Usman dan Allah ka bashi hak'uri wallahi bazan sake ba Allah ban san zai fad'iba."
A hankali Usman yace.
"Hamma tace kayi hak'uri."
Fuska ya tsuke murya a fad'ace yace.
"Zo nan."
K'ara k'ak'k'ame hannun Usman tayi tana zubda k'olloh,
shi kuwa Usman hannushi yasa a hankali ya b'amb'areta a jikin shi cikin rad'a yace.
"In baki jeba zai k'ara hatsala kije ki k'arb'i hukun cinki."
Cikin zubda k'olloh tayi gaban shi a hankali take taku har zuwa gaban shi tana zuwa ta durk'usa
a gaban shi.
A hatsele yasa k'afa ya tureta tare da cewa,
" taso."
Da sauri ta mik'e ta tsaya a gaban shi.
Mari ya watsa mata cikin fad'a ya nunata da yatsa yace.
"Kika kuskura kika k'ara cewa wani munafuki wallahi sai na fasa miki baki,
ke kullum bakya jin magana,
kiyi ta munafurta mutane kuma kece mai halin muna fukan,
kalli yadda kike kuka tun ba'a tab'aki ba, ko shi da kika fasawa bak'in baiyi wannan kukan ba,
kuma kiji daga baki na ba inda zaki je sai shegen son yawo."
Sai ya kuma watsa mata mari tare da cewa.
"Ki wuce kiyi cikin gida ki fara akin ki tun wuri."
Baki na rawa tace.
"Toh"
Ta fice ta tafi tana kuka Usman ne yabi bayan ta da sauri yana lallashin ta har saida ta d'an
huce ya kalleta cikin kulawa yace.
"Allah ya d'aiyiba."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ya Usman Ina sonka."
fuskarta ya shafa tare da koikoiyan muryar Nuru yace.
"Allah ya d'aiyiba
Dariya sukayi baki d'aya sannan ya fice ya tafi.
Hajjajo kuma da Nenne da su ya Adam parlour Nenne suka bita,
Nenne da su ya Adam fad'a suke mata,
ita kuwa hajjajo lallashinta take yi.
Shi kuwa Dr Umar Faruoq yana rik'e da hannun Aliyu har suka shiga parlour su,
kan kujera ya kontar da Aliyu dressing na wurin yayi mishi tare da bashi maganin ya sha,
sannan ya kunna mishi A,C da TV.
a hankali Aliyu ya rink'a sauk'e ajiyan zuciya tare da lumshe ido,
lokacin d'aya yayi bacci,
shi kuwa Dr Umar Faruoq wonka yayi tare da kimtsawa ciki shigarsu irin ta manyan doctors sai
k'amshi yake zubawa ya fito ya nufi katafaren chemist d'inshi mai suna Baba aura chemist
dayake kusa dasu,
yana zuwa dai-dai bakin wurin yayi wani irin.......
By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL'AMARI*
Page 3⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
*Wannan shafi d'ugguruggum dinshi naki ne ke kad'ai Mamyn Najmah ina al'fahari dake ina
sonki har cikin raina Allah ya bar zumunci ngd da k'aunar ki gareni *
*A*jiyan zuciya tare da lumshe ido,
ganin mutane da suke cike a harabar bakin chemist d'in mata da maza manya da yara,
cikin ranshi yake fad'in,
"Allah ya bashi ikion dubasu baki d'aya".
Fitowa yayi cikin nutsuwa ya nufi wurin da ya kasance wurin zaman shi a ko wacce rana
matuk'ar dai ya shigo potiskum toh shi baya samun hutun weekend d'in.
Yana isa yaranshi da ke aiki chemist d'in suka yi mishi barka da safiya,
sannan ya zauna ya fara duba marasa lafiyan d'aya bayan d'aya yana mai basu kulawa yadda
ya kamata duk da ba sakin fuska yake yiba amman a fili za'a gane fuskarsa mai ciki da tausayi
ne da jink'an marasa lafiyan,
dan bashi da surutu maganar sa a k'aiyade take .
Haka ya yayi ta dubasu har zuwa azahar daga nanne ya tashi tare da sa yaran nashi suka rufe
chemists d'in sannan sukayi alwala suka nufi masallaci dan yin sallan a jam'i.
Bayan an idar da sallah su suka koma bakin aikin su shi kuma kai tsaye gida ya nufa dan gaba
d'aya ya gaji ga yunwa ga baccin da yake ji.
Ita kuwa Ummul bayan ta shiga kitchen ta fara aiki kenan ,
woyarta ta fara suwa tun kafin ta d'aga tasan waye ne dan sautin kiran kawai ke shaida mata
Mustapha ne ke kiran ta haka yasa cikin shauk'i da k'aunar juna suka fara magana a woyar,
gas d'in ta kashe sannan ta fita cikin takunta mai cike da nitsuwa,
kai tsaye ta nufi part d'in kakarsu Hajjajo bedroom ta wuce tana zuwa ta d'ale kan gadon ta mai
rumfa cikin sanyin muryar da ko kana gefen ta a kan gadon bazaka ji abin da take fad'i ba,
Ido ta lumshe cikin sauk'e ajiyar zuciya tace.
"Habeebi"
"Na'am."
Yace mata tare da cewa.
"Ummul kina sani d'imuwa soyayyarki tana cazamin kai da jinin jikina k'ok'olwata na cushe in
banji muryar ki na awa 3 ba Ummul ki daure ki soni ko rabin yadda nake sonki."
Ido ta kuma lumshe wa cikin hura mishi iska a kunne murya can k'asa tace.
"Ya Habeebi ka kontar da hankalin ka Ummul taka ce jiki da jini da duk wani motsina kana cikin
raina ko bacci nake fuskar ka itace k'awan yata."
Mustapha kam k'ara sakewa yayi kan kujerar da yake konce gaba d'aya tsikar jikin shi yana
mik'ewa lokaci d'aya kalaman ta suka sakar mai wani kasala da shauk'i k'aunar ta yakeji na
ratsashi har cikin k'ahon zuciyarshi,
yayin da ita kuwa Ummul take jin duk duniya ba yanayin da take so da jin dad'in shi kamar
kasan cewa a haka suna musayan zantukan so masu sanyi,
ji take matuk'ar babu Mustapha a rayuwarta toh gani take kamar ba nunfashi tare da ita.
Haka sukaci gaba da soyewa kamar su shiga jikin juna,
ita kuwa Ummul gaba d'aya ta manta da wani batun girkin da aka sata,
haka yasa tayi ta woyarta sune basu katse hirar ba sai 12:23 pm tana katse kiran kuma bacci ya
kwashe ta,
bata farka ba sai yanzu da taji muryar Hamma Umar a parlour HaJajjo.
Ita kuwa Nenne dama ta shiga mak'o tansu duba mara lafiya so batasan me Ummul tayi ba.
*Asalin dengar takan su, Zuriya d'aya ce duk su jikokin Alhaji Umaru shuwa'arab ne*
Alhaji Umaru Shuwa'arab asalin sa shi da matarsa Rabi'atu Hajjajo kenan su Shuwa'arab ne
asalin ma zauna garin patiskum cikin unguwar tudun wada yamma da fce,
kowa yasan shuwa'arab kyewawane kuma masu jin larabci ne,
Alhaji Umaru da Hajjajo suna da yaran su 3 duk mazane babban d'ansu Alhaji Ibrahim Umar
shuwa sai k'anneshi biyu tagwaye ne Hassan da Husaini sun tashi cikin gata da tsantsanr
k'aunar juna,
Alhaji Ibrahim shine babba kuma ya kasan ce mutun mai tausayi da k'aunar k'annenshi yana
musu so mai tsanani,
iyayensu kuwa sun basu tarbiya mai inganci tare da ilimin addini da na zamani
sun tashi cikin tsabtacecciyar rayuwa,
da kulawar iyayen su bayan sun girma ne Alhaji Ibrahim yayi aure ya auri matarsa Amina ba
fullatanar potiskum d'in,
mace mai mutunci da kara da sanin ya ka mata,
bayan anyi auren bada jimawa ba Allah yayiwa Alhaji Umaru Shuwa rasuwa,
daga nan ragamar gidan ya zama a hannun Alhaji Ibrahim yake ya rik'e k'anneshi da amana ya
basu dukkan abinda uba zai bawa ya ranshi sunci gaba da karatu su .
Yana zaune da matarsa da mahaifiyar shi a gidan shi da k'annenshi baki d'aya,
Ranar da Alhaji Umaru Shuwa ya cika shekara d'aya da rasuwa a ranar Amina matar Alhaji
Ibrahim ta haifi d'anta fari tas kekyawa dashi mai kama da babanshi,
ran suna yaro yaci sunan kakanshi Umar Faruoq kenan.
Yaro ya tashi cikin gata da kulawan mahaifiyar shi da kakarshi da k'annen mahaifinshi Hassan
da Husaini,
yaro mai farin jini da kwarjini.
bayan shekara 4 Alhaji Ibrahim, yayiwa k'annenshi Aure rana d'aya,
suka tare a gida jen da ya gina musu a gefen nashi.
Bayan watannni 5 da auren Khadija matar Hassan ta fara laulayin cikinta na fari a lokacin kuma
Amina matar Alhaji Ibrahim itama tana da cikin d'anta na biyu,
matar Hussani kuma bata da ciki tukun ,
Bayan wani lokacin Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta na biyu mai suna Usman a lokacin
Umar Faruoq kuwa ya cika shekara 5 da y'an watanni, Khadija matar Hassan kuma ta haifi
d'anta na fari mai suna Adam wanda tsaka ninshi da Usman kwana 12 ne Usman d'in ya girmi
Adam da kwana 12 haka yaran suka tashi cikin shak'u da juna ko mai tare akeyi musu, Umar Faruoq ya tashi da k'aunar k'annenshi.
Usman da Adam suna da shekara d'aya a duniya Allah yayiwa Alhaji Ibrahim maifin Umar da
Usman rasuwa.
Rashuwa da ta shiga jikin Hassan da Hussain da Hajjajo sunyi kukan rashin d'an uwansu
wanda shine madadin mahaifinsu a garesu.
Amina matar Alhaji Ibrahim mahaifiyar su Umar wacce yaran ke karanta da Ammi tayi kukan
rashin mijinta da rabuwa da yaranta dan tana gama ta kaba ta koma gidan iyayen ta,
Alhaji Hassan wanda suke kira da Abba ya karb'i Umar da Usman ya dank'asu a hannun
matarsa Khadija wacce yaran ke kira da Nenne sannan kakarsu Hajjajo itama tana gidan suka
taru suka raini yaran cikin kulawa da tsantsar gata ta yadda su Umar basu san zafin maraici ba.
Nenne kuma bayan ta haifi Adam ta kuma haihuwa yaran 4 Sadiq sai Sadiya sai Rabi'atu
wacce take takwarar Hajjajo ce amman suna kiranta da Ummul khairi sai kuma d'an autanta
Aliyu.