Showing 60001 words to 63000 words out of 142577 words
Chapter 21 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
yayi threatening nata yace zai fad'a wa su Ya Adam, ta k'ara
haske sosai sai dai ta d'anyi rama, ga wani son cin abincin da take yanzu tana cin abinci yanzu
anjima kad'an zata fara jin yunwa, koh cikin dare idan taji yunwa zata tashe Hamma Umar ya
had'a mata tea taci da snacks ta koma bacci, da sassafe tana sallah'n Subh zata ci abinci sai
kuma ta koma bacci cikin kasala yau kam kamar abin yafi na kullum dan yau tunda ta tashi
bacci take ta bin bayan Hamma Umar d'in tana rirrik'eshi dan jiri takeji dan tsabar yunwar dake
kwakwularta,
kallon ta yayi a hankali yace,
"tsaya a nan Ummul bari in shiga kitchen in kawo miki abinda zakici".
yana fad'in haka ya janye hannun shi ya shige kitchen d'in,
ita kuwa a take duhu ya rufe mata idanun da wani irin jiri ya kwasheta lokaci d'aya k'afafun ta
suka rink'a rawa sai ko tayi wani irin...
By
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2β£3β£
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Kuyi hakuri sisters da jinkirin da muke samu na Rashin yin typing hakan ya farune bisa wasu
larurai da sukasha kaina nasan ku kanku readers kun san ba haka na sabayi ba so nasan
zakuyi min uzuri ngd da addu'ainku gareni Allah bar zumunci da k'auna*
*I*tako atake duhu ya rufe mata idanu da wani irin jiri ya kwashe ta lokaci d'aya kafafuwan ta
suka ringa rawa sai kuwa ta fad'i kasa a sume. Hamma Umar ba k'aramin birkice wa ba yayi
daya fito a kitchen ya ganta cikin irin wannan halin, a rikice ya cincib'ota ya kaita d'aki ya
kwantar da ita akan gado. Ruwa ya d'auko da sauri a fridge ya yayyafa mata nan take tayi wani
irin ajiyan zuciya tareda bud'e idanuwan ta, cikin tashin hankali Hamma Umar yake tambayar ta
lafiya tareda shafo fuskan ta, wani irin kuka ta fashe dashi tace "Yunwa nake ji ga kuma ciwon
kai". Take ya d'auko mata Indomie'n da ya dafa ya mik'a mata, cikin five minutes sai gashi ta
cinye shi tas ta wani tura bakin ta tace "Hamma Umar nifa ban k'oshi ba", bud'e baki yayi yana
kallon ta da yasan Ummul bata iya cinye indomie k'anana biyu gashi yau ta cinye shi tas kuma
tana kukan bai ishe taba, yace
"Toh bari naje na k'ara dafa miki wani", turo bakin ta tayi tace
"Ni yanzu
wainan kwai nake so na.." bata k'arasa taji wani irin mai na zuwa mata take ta tashi tana son fita
a d'akin taje toilet da gudu nan take Hamma Umar ya rik'e sai kawai ta fara aman a jikin sa, yi
take har sanda ta amar da Indomie'n gaba d'aya a jikin sa, hankalin sa tashe sai sannu yake
jero mata, a hankali ya kaita band'aki ya mik'a mata towel ta cire rigan jikinta ta wanke fuskan ta
da hannun ta, bayan ya kwantar da ita akan gado shima ya fad'a toilet yayi wanka. Bayan ya fito
ya saka jallabiyar sa sai baza k'amshi yake amma kallo d'aya zaka masa kasan hankalin sa a
tashe, matsowa yayi kusa da Ummul dake kwance ta lumshe idanuwan ta, shafo fuskan ta yayi
yace
"Ummul bakya jin dad'i ashe, meh da meh yake miki ciwo?", hawaye tafara tace
"Hamma ciwon kai kuma ni yanzu yunwa sosai nakeji ni gaskia ka kaini gida", shafa fuskan ta
yayi yace
"Yi hak'uri zan kaiki gida kinji yanzu meh kike so kici", shuru tayi na d'an wani lokaci tace "Bread
da shayi", Allah ya so shi akwai biredi a gidan ya had'a mata da shayi taci. D'akin sa yaje ya
d'au kayan aikin sa ya k'ara dawowa d'aki, cire allura yayi ya lallashe ta kan ta yarda ya d'au
jinin ta, canza kayan sa yayi ya saka ash shadda wanda ya amshe sa ya masa kyau sosai yace
"Ummul yanzu meh kike so kice dan ni zanje na bada jinin ki a lab suyi test"
Take tace masa "D'anwake da alale", fita yayi ya siyo kan ya dawo har ma tayi bacci, ajiye mata
yayi a d'aki a flask na tea ya fita.
Direct lab ya wuce ya bada jinin ta ma wani abokin sa yace a mata test na Widal, Mp da PT
emergency neh yanzu yake so.
Cikin awa d'aya kaf aka gama masa tests d'in yana zaune a office na abokin sa aka kawo masa
gaba d'aya uku tests result d'in. Karb'a yayi ya bud'e Widal result d'in yaga bata dashi gaba
d'aya 40% da 80% wanda yake nunin batada typhoid, sannan ya bud'e na Mp yaga +1 tana da
malaria'n amma ba sosai ba, a hankali ya bud'e result na pregnancy tests d'in idon sa yakai ga
Positive, bai yadda da abunda yake gani ba har sanda ya k'ara bud'e idon sa da kyau harda
goge idon sa, matar data kawo masa results d'in tayi dariya tace
"Tabbas idon ka bai maka k'arya ba congratulations matar ka tana da cikin wata uku", nan take
ya d'aga eyes nasa yana kallon ta nan take ya tashi a kujeran da yake zaune yayi sujada ya
d'ago ya d'aga hannayen sa sama hawaye ya cika fal a idon sa yace "Allah nagode maka!
Alhamdulillah Yaa Allah!" Take ya fita a d'akin yaje parking lot inda yayi parking motar sa, shiga yayi cikin motar yana
murmushi yaja motar sai wani babban restaurant, abinci fried rice ya siya da Ice cream ya wuce
gida.
Da sallama ya shiga d'akin ta a lokacin Ummul tana kan sallaya ta idar da sallah, rungume ta
yayi sosai ta baya yana mai shakan k'amshi ta, tura bakin ta tayi tace "Hamma Umar please ka
barni k'amshi turaren ka na tada mun da zuciya", murmushi yayi ya raba jikin sa da nata yazo
gaban ta yana kallon ta with so much tenderness in his eyes yana murmushi yace "Guess what?", tura bakin ta tayi tace "Hamma Umar I ain't good at guessing kawai ka fad'a
mini menene?", k'ara rungume ta yayi sosai cikin rad'a a kunnen ta yace "Ummul kina da cikin
wata uku"
Zuciyan tane taji ya wani irin tsinkewa cikin k'arfi ta raba jikin ta da nasa hawaye fal kwance a
kan kuncin ta tace
"Na shiga uku nah ni Ummul Khairi", tareda aza hannu biyu a kaa, take ta fashe da wani irin
kuka tace
"Wallahi bana so bazan yadda ba sai dai a cire cikin nan, wallahi bazan bar cikin nan a jiki na
ba", kallon ta yake yana ga yadda ta zauna ta mimmik'e k'afafu tana dukan cikin da k'arfi,
ransa a b'ace yace
"Hak'uri zakiyi Khairi dan ni wallahi inason cikin nan",
tasowa tayi tana kuka taci gaba da dukan cikin da k'arfin da Allah ya bata tana,
"Wallahi Allah sai dai ya zube ni bazan bar cikin nan ba sai dai ya zub'e" Tana mai buga cikin
da hannun ta, nan take Hamma Umar ya rik'e hannun ta cikin lallashi yace
"Ayyah Khairi yanzu baza kiyi hak'uri ki rungume k'addara ba, mata nawa suke neman haihuwa
a duniyan nan Allah bai basu ba dan Allah kiyi hak'uri ki haifa min yaron nan ina matuk'ar son
cikin nan fiyeda komai na rayuwa ta".
Kuka take tana mai zubda kayan gaban dressing mirror'n ta tana wasar dasu a k'asa tana
"Wallahi Allah bazan bar cikin nan ba, wayyo Allah na nashiga uku kowa baya so nah zasu
d'aura min hawan jini, wayyo Allah nashiga uku", tana kuka sosai
Kama ta yayi ya zaunar da ita akan gado yana mai rok'on ta Allah da annabi tabar masa cikin
"Khairi dan Allah ki rufa mini asiri dan darajan manzon Allah S.W.A ki bar min cikin nan, a yanzu
inason cikin nan fiyeda komai a rayuwa ta dan Allah Khairi". Cikin kuka tace
"Bazan iyaba Hamma Umar kayi hak'uri nidai kam gaskia a cire cikin nan, idan kuma kaki koh ta
yaya zan cire cikin nan"
Haka zai ta lallashin ta har dare, tun safe data ci abinci bata k'ara ci ba, sosai take jin yunwa har
jikin ta rawa yake yana karkarwa, Hamma Umar rik'e hannun ta yayi hawaye fal a cikin idon sa
yace
"Dan Allah Khairi kici abinci kiga jikin mi har rawa yake yi dan Allah", ganin yadda ya marairaice
ga hawaye ciki a idon sa yasa ta d'an ji tausayin sa tace " Toh ka kawo min". Take ya taso jikin
sa har b'ari yake yayi warming fried rice d'in ya kawo mata, sosai taci abincin tana gama ci ta
fad'a toilet tayi wanka bayan ta fito tayi sallah, kwanciyar ta tayi a k'asa ba yadda baiyi da ita ta
hau kan gado ba amma taki tace ita sam a k'asa zata kwana. Tsaban irin kukan da tayi koh
minti biyar batayi da kwanciya ba bacci ya sace ta. Bayan tayi nesa a bacci ya d'auke ta cak sai
kan gado tareda rufe mata jiki da bargo.
Alwala yayi yafara jera nafiloli bayan ya idar ya d'au Al Qur'anin sa yana reciting. Shi bai
kwanta bacci ba dai kusan k'arfe uku da rabi.
Washegari da safe Ummul da wani irin yunwa ta tashi, Hamma Umar dake kwance akan
cushion ganin ta tashi tana juye-juye ya taso ya same ta yace
"Khairi lafiya kuwa", kuka ta fashe dashi tace
"Ni Allah nagaji da cikin nan sai wani yunwa yake sa nakeji kamar wata mayya ni gaskia Allah
bazan yarda ba sai an cire cikin", rik'e hannayen ta gam yayi yace
"Eyyah Khairi hak'uri zakiyi kinji, ciki ai rahama neh daga Allah"
Sabon kuka ta fashe dashi tace "Toh ni haka zan ta fama a yunwa kullum, ni kuma bason cikin
nake ba gaskia dole ka cire shi". Sosai yake kallon ta idan tayi maganar zub da cikin ji yake
kamar an tsoka masa kibiya a zuciya, shafo fuskan ta yayi yace " Yanzu bara na kawo miki
shayi kici kinji?" D'aga kai tayi ba tareda ta amsa masa ba, tashiwa yayi ya had'a mata tea ya
soya mata kwai ya kawo mata tareda bread. Sosai ta ci tana ci tana hawaye shi kuwa na kallon
ikon Allah, bayan ta gama ci ya kwashe su flask d'in ya kai kitchen ya d'aura alwala itama haka
sukayi sallah'n asuba. Suna idar wa ya fara karanta Al Qur'ani ita kuma tabi lafiyan gado ta
kwanta dan wani irin bala'in bacci neh ke addaban ta, shi kuwa Hamma Umar sanda tana ta fito
kan ya rufe ya kwanta a k'asa kan carpet shima cikin minti biyar bacci ya d'auke sa dan jiya bai
samu yin bacci da wuri ba...
Misalin k'arfe goman safe ji yake kamar ana bubbuga shi cikin mafarki, a hankali ya bud'e
idon sa yaga Ummul hawaye kwance fal a kuncin ta, ganin ya bud'e idon sa cikin kuka tace
"Hamma Umar ka tashi ka shirya ka kaini asibiti a zubar da cikin nan dan ni bazan k'ara kwana
d'aya da cikin nan a jiki nah ba", pillow ya d'auka ya rufe kansa gaba d'aya dan sosai yake jin
baccin, ganin haka ran Ummul ya b'aci sosai taja pillow'n tana kuka tace
"Hamma wallahi wulakanci bashida kyau ina maka magana harda wani janye pillow koh? Ni ka
tashi ka shirya muje asibiti a yanzu ji nake bazan iya k'ara koh awa biyu neh da cikin nan ba",
tasowa tayi daga kwancen da yake yace
"Kinsan wulakanci bashi da kyau amma baki san kisan kai yafi shi muni ba, abunda kike
k'okarin aikatawa ke kanki kinsan kisan kai neh, kin sani amma kin taka sani, kiji tsoron Allah
Khairi idan baki so nah ai bai kamata ya shafe d'an cikin ki ba, na yarda na amince baki so nah
baki k'auna ta amma dan Allah", ya durkusa har k'asa "Dan Allah kiso d'ana Khairi, ina son cikin nan, ina matuk'ar son cikin nan, ki taimaka min ki
taimakawa rayuwa ta, ina bala'i da masifan son cikin nan", d'auke kanta tayi daga ganin sa tana
hawaye tace
"Kai dai kayi hak'uri Hamma Umar, ni kuma wallahi Allah bana k'aunar cikin nan, bana so na
k'ara kwana da cikin nan a jiki nah, kayi min rai a cire cikin nan, ina alk'awarin daka d'auka wa
iyayen mu akan zaka rik'e ni amana and you'll never deprive me of my rights yanzu ka tabbatar
min da ka cika alk'awarin nan, a zubar da cikin nan"...
By
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL, AMARI*
Page 2β£4β£
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*K*ai ya rink'a juyawa ida nunshi cike da k'ollah murya na rawa ya durk'usa gaban ta hannun shi
yasa ya dafa guiwowin ta cikin rawan murya yace,
"Bazan iyaba Ummul bazan iyaba ina son cikina bazan zubda gudan jinina da kaina ba bazan yi
kisan kaiba".
sai ya kuma mik'e yana yarfa hannunshi,
ganin haka ta mik'e itama tana yarfa hannun ta tana kuka tana binshi a baya tare da cewa,
"toh ni dai ka maidani gida,
na gaji da zaman gidan nan ka maidani gun Nenne na".
jin hakan yasa yayi ajiyan zuciya dan yasan indai ya maidata gida bata isa tace a zubda cikin ba
dan tana jin tsoron su Adam hakan yasa cikin kauda kai yace,
"shirya mu tafi".
Hannu ta yarfa cikin dire k'afafunta tace,
"ni a shirye nake mu tafi kawai".
"toh".
yace sannan ya shige d'akin shi,
wonka yayi ranshi cike da takaici,
yana fitowa ya sameta a bakin gadon shi,
bai kulata ba ya zauna gaban dressing mirror mai ya fara shafawa yana murza fatar jikin shi,
a d'aya gefen kuma Ummul ce ta mik'e cikin tura baki tazo bayan shi hannun shi ta rik'e cikin jin
bacci da kasala ta manna kanta a bayan shi a hankali tace,
"Hamma mu tafi bacci nake ji".
juyowa yayi ya jawota jikin shi cikin sanyi ya ruggumeta tsam a jikin shi yana shak'ar k'amshin
ta,
hannun shi ya cusa cikin rigarta yana shafa cikinta zuwa kan kirjinta murya can k'asa cikin
daburcewa yace,
"Ummul kiyi hak'uri kiso d'anki kiso gudan jinina ki barni in rab'i jikin ki ina begenki ki bani
hak'k'ina".
shiru tayi ta lafe a jikinshi tana jin yadda yake murje kirjinta da shafa cikin ta,
ido ta lumshe cikin sanyi da kasalar daya k'ara sakar mata ta ruggume k'ugunshi ta manna
kanta da fatan cikin shi,
a hankali tace,
"Hamma Umar tashi mu tafi,
banda lafiya zan koma gun Nenne na ni a cire cikin".
ranshi a b'ace ya d'an tureta sannan ya shirya tsab fuskarsa a tsuke suka fito,
rufe gidan yayi sannan suka shiga mota,
Kai tsaye hanyar potaskum ya nufa da ita.
A gida kuwa Aliyu ne dasu Nanne ke zaune a parlour ,
Aliyu dake zaune a 1 str hannun rik'e da wayar ya Sadik yana game a wayar,
itako Nanne tana kishingid'e a kan doguwar kujera suna hira da Ya Sadiq dake zaune
rik'e da remote yana kallon TV suna d'an hira kad'an -kad'an,
Suna isa harabar gidan Hamma Umar na tsayawa Ummul ta bude motar cikin kasala da
jin bacci ta shige cikin gidan,
kai tsaye tai parlour Nanne Sallamar ta ce tasa Nanne tashi zaune tana murmushi ta
bud'a mata hannu, Ummul cikin shagwab'a ta fad'a jikin Nanne tace,
"Nanne na ina kwana?". lafiya lau Ummul na,
ya Damaturun ?". Sallamar Hamma Umar ce ta katse su,
cikin sakin fuska Nanne ta amsa mai tana mai sannu da zuwa,
Cikin nitsuwa da cikar kamala ya shigo parlour kanshi a sunkuye zama yayi a k'asa gaban
Nanne yace,
"Nanne ina kwana ? ya gidan?".
murmushi tayi cikin jin dad'in ganin su ta amsa da,
"lafiya lau Farouk ya hanya, ya aiki?".
Kai yasake sunkuyar wa k'asa yace "Alhamdullah".
sannan Ya Sadiq da Aliyu daya matso jikin Hamman na shi cikin so da kauna suka gaida
shi ya amsa musu cikin sakin fuska tare da cewa,
"Ina Adam fa?".
Sadiq ne ya dan kalleshi tare da cewa,
"Yanzu ya tafi d'akin shi, barin kira shi".
Kai ya jinjiga yace,
"kyale shi zamu wuni ai".
Ummul dake kwance kan cinyar Nanne kuwa tuni tafara bacci cikin