Showing 141001 words to 142577 words out of 142577 words

Chapter 48 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt

na ririta matar shi da babyn cikinta yana bata kulawa
ta musamman hakan yasa hankalinta yafara kwanciya wanda har takan iya wuni guda
batare da tayi kukaba.

Watanni ukun da zaiyi suka ciki dan haka sukai shiri komawa gida Nigeria cikin aminci
da d'an cikin ta da ya fara girma.

A gida kuwa kowa na murnar dawowarsu Abba da Daddy kuwa tuni sun k'awatar masu
da gidansu dake kusa da gidansu komai yakammalu kowa na farin cikin dawowarsu
musamman Ammi da tayi kyewar y'arta da shogoɓarta Hajjajo da Inna ma sai Happy suke
da d'okin ganin jikokin nasu, Adam da Sadiq ne suka ɗaukosu daga Abuja kai tsaye gida suka kawosu inda auka
tarar da duk familyn su na nan suna jiran isowarsu,
Kowa yaji daɗin ganin yanda Ummul ta gyaru tayi kyau tak'ara cika ga haske da
shek'in da fatarta keyi ga d'an cinkin ta ya taso,
Usman kuwa yana manne da Farouq dayaketa zubamai surutu cikin gwaranci sa,
shiko Usman yanayi yana satar kallon matar shi yana k'arajin k'aunarta na ratsa duk
jikin shi.
Haka suka wuni cikin y'an uwa anata raha da hira.

K'arfe tara na dare Ammi ta tashi Ummul data fara bacci a palour tace ta koma
bedroom ta kwanta badan Usman yasoba shima yaje ya kwana ɗakin Adam amma
yakasa bacci sai juyi yake yana missing matar shi.

Washe gari diTun bayan sallah asuba malamai suka fara karatu dan sauk'e qur'ani a
gidan Usman dake kusa da gidansu domin neman kariya dakuma samun albarka a
gidan, basu wuce 12pm ba suka kammala akayi addu'o'i. Sai bayan sallah isha'i sannan
Ammi da Hajjajo da Aunty Halima sai Anty Aysha Garkuwa suka raka Ummul gidanta.
Satinsu guda da dawowa aka shirya bikin buɗe makarantar da suka assasa kafin su
tafi mai suna
*Dr Umar Faruq learners academy* dake tudun wada layout daura da masallacin juma'a
na jibwis k'ark'ashin kulawar k'ungiyar Fityanul Islam ta jaha reshen k'aramar hukumar
potiskum. bikin yasami
halartar manya daga ma'aikatar ilimi ta jaha dakuma wakilan sarakunan Potiskum da
fika,
yaran dake sanye da farar riga da dark blue wando dogo sai farar hula sunyi kyau
matuk'a ciki harda *Umar Farouq Umar Shuwa* Makarantar zata koyar da yara duka
ɓangare biyu wato boko da arabic a farashi mai sauk'i a duk k'arshen zango na karatu,
Anyi taro an watse lafiya da fatan Allah ya yiwa makarantar albarka.

Haka rayu take tafiya Usman na kulawa da Matar shi da d'anshi dakuma cikin Ummul
daya girma,
Shiko Faruq yazama mai gida Uku gidan Abba ga gidan Daddy dakuma gidan Abeenshi
Usman.

Yau lahadi wanda ya kasance ana cikin bikin auren Rukayyat da Nuru abokin Usman kuma
yaune aka gama shagalin bikin bayan abokai sun reko aggo Nuru sun gama komai sannan
Usman ya d'auki Ummul enshi suka nufi gidan su,
Suna isa Ummul ta wuce dakinta Wonka tayi cikin jin gajiya ta zauna gaban dressing mirror tana
murje jikin ta da turaruka masu k'amshi tana kallon cikin ta da ya fara motsi a y'an k'wanakin
nan ajiyan zuciya tayi tare da yin murmushi tana,
"barka na yau da Farouq yana guna da bazai barni na hutaba da surutun shi".
tana d'aure igiyar rigar baccin ta taji woyarta na suwa,
saida ta gama kimtsawa sannan ta dauki woyar ganin ya Usman ta dan karya wuya ta amsa
kiran,
"Ummuna ina kikene kin barni ni d'aya".
a hankali tace,
"Gani nan zuwa Hamma Usman na".
tana fad'in haka ta katse kiran sannan ta fita ta nufi parlour shi,
zaune ta sameshi kan kujera yana ganin ta ya nuna mata cinyarshi alamar tazo ta zauna
ba musu ta matso gareshi ta zauna kan cinyarshi suna fuskantar juna,
hannun shi yasa yana zare igiyar rigar baccin nata,
kamo hannun tayi sannan ta tallabo kanshi bakinta ta manna kan nashi tamai wani irin zazzafan
kiss sannan tasa hannun ta wore rigar tata cikin lumshe ido ta jawo kanshi ta cusa a tsakiyar
k'irjin ta yayinda tasa yatsunta kuma cikin sumar kanshi tana mai wani salon romancing mai
rud'a tunani,

gaba d'aya ta gigitashi sai juya kanshi yake a k'irjinta duk ta inda yaga dama hannun shi kuwa
na shafa cikin ta da ker ya budi baki a hankali yace,
"Um....! Umm...! Ummu na Allah ya miki albarka kin gama min komai a rayuwa ta tunda kike
samamin farin ciki".
Kai ta d'an d'ago ido cike da k'ollah tace,
"Hamma Usman dole na gyara yanzu na tunda na b'ata bayana nayi kuskure a baya bana fatan
kuma maimaita kuren da nayi danko gashi har gobe ina dana sani,
ya Usman da nayi biyeyye yadda *'YAR FULANI* tayiwa bappan ta biyeyyah da na tabbata
bazanyi dana saniba amman da nak'i yiwa iyayenmu biyeyya yanzu *MI WASMITI*
*NAYI NADAMA*
mai tarin yawa naga illar bijirewa zabin iyaye
tabbas na yarda *NAMIJI BAYA KAD'AN* dan naga jarumta da girman shawarar da Aliyu k'anin
bayana yayi ta bani a lokacin baya tabbas da nabi shawarar Aliyu da a zaman aurena da
Hamma Umar da
*A TAUSAYWA JUNA* yayi tasiri a kanmu amman taurin kai da zugar shaid'an sun hanani
tausayawa *BANDIRAWO* na k'iyeyya tasa na manta cewa Hamma Umar fa *BANDIRAWO*
nane na kasa yarda k'addarata ashe a hankali
*RUBUTACCEN AL,AMARI* na bibiyar rayuwata,
Hamma Usman kalli yadda *rubutaccen al, amari*
da k'addara yadda suka had'amu aure Hamma Usman ina son Hamma Umar ina mai addu'a
aduk wani motsina da numfashina *Hamma Usman ina sonka*".
Murmushi yayi cikin jin dadi da tarin k'auna ya rugumota yana murza k'irjin ta murya can k'asa
yace,
*"ALLAH YA D'AIYIBA*

*Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah*
Na godewa Mahaliccina daya bani rai da lafiya da damar rubuta wannan littafin daga forko har
zuwa k'arshe inda na tubk'e bakin zaren labarin Alhamdulillah

Abinda nayi dai-dai Allah ya taramu a kan ladan abinda nayi kuskure bisa ajizanci na d'an Adam
Allah ya gafarta min.

Masoya na ina alfahari daku zanyi kewarku zakuyi kewata dan ina son hutawa sosai kafin na
faro sabon novel na watakil mai suna *FULB'E Nigeria* ba mamaki kuma na canza sunan,

Godiya mai tarin yawa agareku masoyan Hamma Umar tabbas kunsa zuriyar Shuwa farin ciki
da addu'oin da kukayiwa dansu Usman yace a mik'a godiyarsa gareku

*Afwan Afwan Afwan ina mai neman gafararku mace ko namiji Babba ko yaro na kusa dana
nesa wanda nasani da wanda ban saniba wanda muka tab'a magana da wanda bamu tab'a
magana ba wala Allah ko akwai wani abu da ya bata muku rai a cikin labarin ga dan haka ina
mai neman yafiyar duk wanda na sosawa rai a zahiri banyi komai da nufin batawa kowaba Ina
fatan samun yafiya daga ko wanne sashi ku yafe min tun ina raye inko na nabar duniya

masoyana Addu'arku nake buk'ata ni na yafewa kowa*

Moh Allah wuji furd'ata
Fullo be fulaku Moh Allah saini sunata
Moh Allah hokki b'uri moh baba hokki

*By*
*GARKUWAR FULANI�� Fauziyya Fiji ga salon
mu‍♀‍♀‍♀‍♀‍♀‍♀‍♀‍♀‍♀�*

*Bissalam*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login