Showing 90001 words to 93000 words out of 142577 words
Chapter 31 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
gadon dake kallon nata yasanya jinjirin gaba yanata kallo dan
yariga ta farfad'owa,
yayinda Abba ke zaune a kan kujera a gaban gadon Usman kusa dashi kuwa Dr Bashir
ne suna kallon yanda Ummul kedan motsa k'afarta a hankali,
Ammi ko tana zaune bakin gadon da ummul ke kwance tana rik'e da hannun ta idon
ta ya na kanta,
yun kurin bude idonta tafarayi a hankali tanajin yamata nauyi,
da hannu Ammi taiwa Dr Bashir nuni aiko tare suka taso sukayo bakin gadon,
Tana bud'e idonta da kyar ta d'aga hannun ta da kyar ta shafi cikinta dan jin yayi
mata wayam aiko saita d'an kara zaro idonta tabud'e baki da kyar murya nara voice a
disashe a hankali tace,
"In in inaaaa cikin?". Hamdala suka rink'a jerawa cikin tsananin happy dan tunda Hamma
Umar ya rasu sai yau Ummul ta iya magana,
ya Usman kuwa juya kanshi yayi a hankali wasu irin hawaye masu zafi suna bin fuskarsa,
Ammi ce ta mik'e da sauri ta d'auko babyn da yaketa bacci a gaba Usman shiko Usman sai
kallon yaron yake cikin tsananin k'auna yana jin son yaro fiye da kowa a duniyar nan,
a hankali Ammi tace, "gashi nan Ummul, ga d'anki wanda Allah ya azurtaki dashi keda Faruoq
na amman ke Allah ya nunawa shi shi kam Umar ya rasu da begen wannan rana ya rasu da
kumfar rashin ganin d'anshi Ummul ga d'anki maraya zai tashi maraya kamar yadda iyayenshi
suka tashi marayu". Daga kwance tasa hannu ta d'ora akan yaron ta kuramai idanu tanajin k'aunar shi na
ratsa zuciyar ta da dukkan jikinta sai kuma tayi kurui tana kallon Usman dake konce yana
hawaye cikin sanyi yace,
"Ammi yaron nan bazaiyi maraiciba Insha Allah bazai yi kukan rashin mahaifiba Ammi da izinin
Allah indai ina raye yaronan bazai zubda k'ollah".
sai kuma ya rink'a kuka yana rik'e da hannun Abba,
shima Abban kuka yake Ammi kuwa zuwa yanzu hawayenta sun fara k'agewa,
Adam ma gaba d'aya ya zama mai raguwar zuciya abu kad'an sai Kuka amman shi tausayi
Usman ke addabar rayuwarshi,
haka Dr Bashir kuwa da sauran doctors din sukayi ta kula da Usman da Ummul da jaririnta k'ato
fari tas kekyawa, sukaita kula dasu cikin ikon Allah kuwa Ummul da Usman duk Alhamdulillah
jiki yayi kyau Ummul kuwa tun randa tayi magana bata kuma yiba.
Doctors sun bada tabbacin zuciyar Usman zata iya aikin da ake but'ata amman a guji b'acin
ransa sosai sukayi kashedin gudun b'acin ran shi,
a gefen Ummul Kuwa sunce kar a damu da rashin maganarta sunce a koda yaushe maganarta
zata iya dawowa amman kuma a duk randa suka tsinci Ummul na kuka toh karsuyi yunk'urin
hanata a barta domin a cewarsu yin kukan zai iya maida tunaninta dai-dai har ta fara magana
kuma sanyin da zuciyarta tayi harda rashin kukan.
Bayan kwanaki shida dayin aikin aka sallamesu da sharadin kulawa da bawa Ummul da
Usman magunguna don cigaba da samarwa zuciyoyin su lafiya, da haka suka tattaro
suka dungumo sai gida Nigeria.
Randa suka dawo gaba d'aya zuriyar Shuwa sun cika da farin ciki domin samun lafiyar Usman
da Ummul ga jariri da ya zamo magajin Hamma Umar kowa zaizo da Happy amman abin
fargaba har yanzu Ummul bata mgn,
Nenne takan buya tayi ta kuka,
Ummul kuwa in banda bawa yaro nono da da tasashi a gaba tayi ta kallo ba abinda takeyi da
kanta sai an tasa a gaba wani lokacin sai ta wuni ta kwana bataci komaiba inko yaronta na
kuka sai tai ta rawan jiki ta gigice,
in tak'i cin abinci da wonka Usman yakan zauna a gabanta yayi ta magiya har ya fara zubda
k'ollah to da zaran taga yana kuka sai ta zauna ta fara cin abincin.
A haka rayuwa tayi ta juyawa har sukayi kwana 9 da dawowa,
yau asabar da safe bayan sun gama aiyu kansu,
Abba da kanshi ya shiga d'akin da Ammin ke zaune da Ummul a nan ya samu Usman da
Nenne da Adam Ummul ruggume da yaron,
bayan sun gaisa cikin kula Abba ya kalli Usman yace,
"ni kam Usman me sunan yaron ne har yau baka gaya min
ba? ".
cikin mamaki Usman yace,
"Abba baka yiwa yoron huduba bane dama ni yamin ka gaya mai sunanshi ai".
a hankali Abba yace,
"A a Usman ya za'ayi haka yaro yau kwana 14 kuma ashe ba'a mai huduba ba".
Ammi ce ta kallesu a hankali tace,
"mahaifiyarshi ta mishi huduba tun randa yayi kwana uku amman har yau bata gaya min sunan
shiba".
usman d'in ya zuba mata ido cikin sanyi yace,
"Ummul kiyi hak'uri mana ki ruggumi k'addararki ki rink'ayi mana magana yanzu tsakanin ki da
Hamma kiyi mishi gatan Addu'a ki bawa d'anshi tarbiya to amman a hakan zakiyi wad'an nan
abubuwan"?.
shiru tayi tana jinshi karo na forko da ida nunta suka ciwo da hawaye tab,
Abba ne ya kalleta a raunane yace,
"Me sunan yaron?".
murya can k'asa cikin rauni da tsananin k'una a zuciya tace,
"Washe garin za'a kashe Hamma na yace min in namiji na haifa ya bani dama nasa sunan
wanda nafiso a duniya wanda duk duniya bani da kamarshi".
sai kuma ta saki wani irin kuka ta ruggumo yaron tana kallon shi,
Usman ma kukan ya fara a hankali yace,
"Ummul me sunan yaron?".
cikin tsananin kuka tazo ta durk'usa gaban Abba murya a disashe tace,
"Abba ina sonshi Abba ina sonshi ina sonshi Abba duk duniya bani da kamarshi Abba ina son
Hamma Umar Abba ina zan ganshi Abba sun kashe min Hamma na a gabana Abba ina son
Hamma Umar".
sai kuma ta kife kanta a cinyar mahaifin nata cikin rauni da tausayawa rayuwarta,
shiko Abba a hankali yace,
"Me sunan yaron kika saka? ".
cikin tsananin kuka tace,
"Sunan shi *Umar Faruoq*".
tana fad'in haka Usman ya........
*Sadaukarwa ga Umar Ibrahim Umar Hamma Umar*
By
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 3β£2β£
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*
*Kin kid'i kankad'a damoni na damoni giddo mo fina laramo gaid'omo fina sukoyo ladde Allah
yamad'u benduki yamete ki b'ib'b'e sammete joruki tenete ki d'oidi yalete*
*U*sman ya d'ago jajayen idanuwan shi yazuba matasu sannan ya mik'e yana layi
yaje bakin gadon ya sa hannuwanshi biyu a d'auko Umar faruq ya rungume sosai a
jikin shi yana zubda hawaye mai tsanani da zafi da k'una a zuciya yana shafa kan yaron
dake cike da suma bak'ik'k'irin daya kwanta luf, ita kuwa Ummul cikin kuka taci gaba da cewa,
"Hamma Umar ne rayuwa ta nafi sonshi a kan kowa a duniya, shikad'ai nakeso shine
komai nawa na rasa a lokacin da nake tsananin buk'atarshi".
Tana magana ne cikin matsanan cin kuka, bakajin komai a gun sai shashshek'ar kuka
da duk wanda kegun yakeyi,
shiko Usman yana k'ollah ne idanuwan shi na kan Umar faruq yana mai wani irin
kallo kamar a lokacin yafara ganin halittar jariri,
Itakuwa Ummul cikin kuka taci gaba da cewa,
"Ammi wallahi ina sonshi,
bazan k'ara son wani mutum a duniyar nan bayan Hammana,
ina kaunar shi fiye da kaina Inamai matsanan cin so da duk duniya bamai iya fahimta".
sei ta kuma jan gwiwoyinta data zuba k'asa har gaban Ya Adam dake ta faman zubda
k'ollah tace, "Yaya na kafi kowa yimin fad'a bakamin wasa amman na kasa ganewa,
kuma baka son damuwa ta, nasan kayi iya k'ok'arinka ka d'orani ka turbar gaskiya,
amman taurin kaina da rud'un shaid'an yasa nak'i gane abinda nasan gaskiya ne gashi hakan
ya jazamin nadama ta har abadan na cutar da kaina da kaina naga illar rashin yiwa iyaye
biyeyya, nagode dakaita k'ok'arin nunamin hanyar gaskiya".
Hannu yasa ya kama hanna yenta duka biyu ya d'an matsesu sannan yace,
"Ummul nasan kina son shi naga sonshi a idonki amma inaso ki nunamai soyayyar da
kikemai inaso ya amfana da ita ta hanyar yimai addu a Ummu ki dena zubda mai
hawaye".
kai ta rink'a gyad'awa cikin rauni da tsananin nadama,
saita kuma juya ta kalli Abba dake tsaye yana kallonsu ido cike da k'ollah,
sannan ta dawo da kallon ta ga Ya Adam dake murza yatsunta a hankali tace,
"Ya Adam Abbana yamin zab'i mafi al'khairi zab'i mai cike da al'kairai a rayuwata amma
ina shaid'an ya hanani ganewa nayiwa iyayena taurin kai gashi zan dauwama cikin nadama da
dana sanin rashin biyayya haka zan k'are rayuwata na kasa yiwa iyayenmu d'a'a kaitona Allah
ya wadaran halina bani da wani abun koyi lallai duk yarda tayiwa iyayenta ba dai-daiba tana
tare da nadama ya Adam na tsani kaina na cutar da Hamma na na b'ata ran mahaifanmu".
sai kuma ta kife kai wani irin matsanan cin kukane ya kwace mata wanda ya hanata
k'arasa kalaman ta ta kife kanta a gwiwar Ya Adam jiki na rawa tana cewa,
"Wallahi ina son shi, inason Hamma Umar Yazanyi Hamma Umar yaga soyayya da
kaunar da nakemai,
ya Adam kullum Hamma Umar yana cewa Ummul zaki soni, zakisoni lokacin da soyayyar
bazata amfane muba ashe wannan lokacin ne Hamma na yake ganemin dana sani dana nuna
mishi so da yake son in nuna mai lallai wannan shine kuskure mafi muni da yarinya tayi dan
iyayenta sun mata auren dole". kuka takeyi sosai tana cike da madama,
Aliyu ne yataho jiki ba kwari yasa hannu biyu ya d'agota ya durkusa gabanta a hankali
yace,
"Aunty Ummul kiyi hak'uri, Hamma yace nine abokin shawararki abokin kukanki kuma
me rarrashinki kiyi hak'uri kidena kukan nan kinga kinsa Ammi da Nanne kuka ga Abban
mu shima yanayi kinga Hamma junior zaiji sautin kukan mu ki dena auntyna dan
Allah". Cikin galabaita da ajiyar zuciya ta kwantar da kanta a cinyar Aliyu tana sheshshe k'ar
kuka tana nannad'e kafafun ta,
hannun Aliyu yasa yana shafa bayanta yana bubbugawa tare da share mata k'ollar cikin
lallashi da haka bacci yayi gaba da ita,
su kuma Abba ya zauna yayi ta musu nasiha Usman kuma sai ajiyar zuciya yake sauk'ewa
yana ruggume da farouq,
a haka rayuwa tayi ta juyawa rana d'ad'd'ayace
basa zama suyi kuka a hankali mutuwar ta fara shiga jikinsu,
lokaci yaja kwanaki sun tafi tuni Farouq ya cika kwana arba'in.
A bangaren Mustapha kuwa a kullum koda yaushe tunanin shi nakan Ummul da
yaronta dan haka ranar Asabar suka shirya da umman shi suka nufo potiskum dan
duba lfy Ummul da jaririnta, dai dai lokacin da motar Mustapha na shirin shiga harabar
gidanne motar Dr Bashir ta sako kai dan fitowa wanda shima zuwa ganin Ummul da
yaronta ya zame masa jiki a duk lokacin da baida aiki,
daga cikin mota suka gaisa da Mustapha sannan ya wuce cikin gidan shiko Dr bashir ya
fita,
Kayane na gani na fad'a da suka had'a da sabulai man shafawa powder, pampers,
wipers da sauran kayan jinjiri Mustapha ya lodo kamar me bud'e shagon mother care, duk
na Umar faruq wanda Aliyu ke kira da junior,
Bayan ya gaisa da su Ammi da Nanne Aliyu yamai jagoranci zuwa palourn bak'i sannan
ya kawomai abin sha sannan ya fita,
a cikin d'akin Kuwa Ammi ce ta maida hankalin ta kan Ummul dake zaune bakin gado
cikin sigar lallashi da bada umarni da kulawa
tace,
"Ummu na ki kaiwa Mustapha yaron nashi ko".
Dakai ta amsa tad'au katon hijab ta saka sannan Umman Mustapha dake rik'e da
Farouq ta mik'a matashi ta karb'a ta fice,
sukuma sukaci gaba da jajantawa juna irin jarrabawar da suka fuskanta.
Mustapha dake zaune yana latsa wayar shi sallamar Ummul tasa ya aje wayar a gefe
yamik'e tare da amsa sallamar yamik'a hannu ya karb'i Farouq dake ta bacci sannan ya
koma ya zauna yad'an dago kai yana kallon Ummul dake tafiya kamar mara lakka a
jiki har ta sami kujerar dake fuskan tar wadda yake zaune ta zauna tai k'asa dakai
tana wasa da yatsun hannun ta sannan yamai da kallon shi ga Umar faruq,
Shiru ya ratsa na y'an muntina sannan Ummul tai k'arfin hali tace,
"ina kwana".
Saida taji shirun yayi yawa sannan ta d'ago kanta