Showing 18001 words to 21000 words out of 142577 words
Chapter 7 - BAKIN RIJIYA BOOK COMPLETE NA BILLY GALADANCHI.txt
yi tanaji dariya nason kufce mata murmushin
takeyi tuk'uru cikin jin dad'in azabtar dashi da tayi sai wani kad'a kai takeyi tana magana a
ranta.
"Kad'an ma kaji Hamma Umar wannan shine makullin wahalar da zakasha a hannun na,
kaida azabtuwa kun kullah,
Sai kayi kuka cur-cur da hawaye ka sai ka gommace kid'i da karatu sai ka sakeni saki mafi muni
wanda zan haramta maka har sai inna nasake wani auren an sakeni."
Kai ta jinjina taci gaba da maganar zuciyar da bata saniba na yanzun ya fito fili cewa take.
"Tabbacin da nake dashi ko ince yak'ini na sani Mustapha bazai sakeni ba har Abadan zamu
rayu tare."
Da sauri Hamma Umar d'in ya bud'e idanun shi daya rumtse jin sautin Ummul d'in kan gadon ya
tsurawa ido cikin wore idanun shi ,
fuskar ta ya tsare da ido cikin zafin nama ya mik'a hannushi kan gadon,
ita kuwa ganin haka tayi wani irin dira daga kan gadon a guje tayi woje a parlour ta samu ya
Usman da su Hajjajo da Inna tare da Anty Halima da Anty Shuwa k'anwar Nenne,
cikin rawan jiki ta koma gefen ya Usman ta zauna cikin tura baki da tsuke fuska,
Anty Halima ce ta kalleta cikin tuhuma tace.
"Me kika aikata? kika fito a guje haka?."
fuska ta k'ara tsukewa sannan ta kalli Anty Shuwa dake ta danna mata harara cikin son yin kuka
tace.
"Nayi ai ban sani bane."
Hajjajo ta bud'e baki zatayi magana kenan sai kuma tayi shiru ganin Hamma Umar d'in d'aya
fito cikin d'akin nata ,
tafiya yake yana d'ingisa k'afar tashi duk inda ya taka sai jini dake zuba gaba d'aya jijiyoyin
kanshi sun taso kanshi a k'asa yake tafiya hannushi rik'e da laptop d'in nashi yayinda d'aya
hannun kuma yake rik'e da iPhone d'in shi,
Ya Usman ne da Anty Halima sukayi kanshi da sauri cikin rawan baki Ya Usman yace.
"Hamma Umar me ya fasama yatsa yaushe ya fashe kalli yadda jiki ke zubafa."
Anty Halima kuwa gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin duk jini ya wonke mai k'afarsa cikin sanyi
murya na rawa tace
"Hamma Umar a tsaida jinin nan mana ya dena zuba."
kai ya gyad'a musu cikin jarumta da dauriya ya nufi hanyar fita yana ce musu .
"Ba komai fa."
har yake bak'in k'ofar fita,
Hajjajo da Inna sukayi kanshi da sauri cikin kula da tsananin k'aunar jikan nasu suka kalleshi,
kusan a tare suke magana.
"Kai Farouq me ya fasama k'afar?
kayi magana kayi shiru ?."
kai ya jinjina a hankali yace.
"Tuntub'e nayi."
fad'in haka da yayi ne yasa suka rink'a jeromai "sannu-sannu Amman kaji azaba kam ai abinda
ya fasa farce ba k'ara min abu bane."
Su tsoppin sun yarda Amman Anty Halima da Anty Shuwa kam sun gane sarai Ummul ce taji
mai ciwon dan ganin yadda take zare ido da alamun rashin gaskiya Ita,
kuwa Ummul har cikin ranta take jin dad'in ciwon da taji mishi,
a wani sashin zuciyar ta kuwa tana mamakin yadda Hamma Umar d'in ya rufa mata asiri yak'i
cewa Ita ta fasa mishi k'afar,
dan ta tabbaya d'aya fad'a Ita kuwa da ta shiga 9 nema ba 3 ba.
shi kuwa Hamma Umar ko inda take bai kallah ba ya fice yana d'ingisa k'afar,
ya Usman kuwa karb'a laptop d'in Hamman nashi yayi ya rik'e cikin raunin fuskar sa kamar zaiyi
kuka dan tausayawa d'an uwan nashi,
har zasu fita ya juyo ya kalli Ummul d'in cikin raunin da yanayin tuhuma dan ya gane itace silar
ciwon Hamman nashi,
itama kallon shi takeyi cikin sanyi ta rumtse idonta,
shi kuwa juyawa sukayi suka tafi.
Suna zuwa part d'in su Hamm Umar d'in yayiwa yatsar tashi dressing sannan yawa kanshi
allurar ya kuma sha magani.
Ita kuwa Ummul suna fita Anty Shuwa da Anty Halima suka jata d'akin dake gefen na Hajjajo
suka rink'a yi mata gyare-gyare tare da tsumata da irin tsumukansu na shuwa'arab ,
Anty Shuwa ce ta b'alle marfin wani roba sannan ta jijjiga tare da mik'ewa Ummul d'in cikin
tsuke fuska tace.
"Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar."
Kai Ummul d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace.
"Ni dai amai nakeji dan Allah a barni hakanan."
A fad'ace Anty Shuwa tace .
"Sai kinsha muguwar banza yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da
baya magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta."
kai Halima ta jinjina sannan tace .
"Gaya mata dai Anty wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Hamma Umar d'in."
Haka suka rink'a yi mata fad'a da nasiha sunayi suna tsumata tare da dilketa da murjeta.
Haka nan kullum Sai sun murjeta sun tsumata,
ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta kuma tamkar auduga komai
nata yasha gyara sai wani k'amshin mai sanyi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya
ratsa wurin
gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman k'afafun
ta da hannayen ta kuwa an musu zanen Lalle na mu samman komai na Ummul ya fito rasa ta
fito a shuwa'arab d'in sak.
A gefen ago Hamma Umar kuwa ,
komai Ya Usman ne yake gudanarwa gaba d'aya ya gayyato abokon Hamma Umar d'in nashi ...
Yau ta kama Jumma haji babbar rana Wanda ya kasance gobe asabar ne za'ayi d'aurin aure
Ummul da Hamma Umar .
Toh a rayuwar shuwa'arab akwai wata al'adar da sukeyi a duk lokacin da zasuyi bikin su ,
suna yin wannan al'adar tasune kamar gone za'a d'aura aure ,
kuma wannan al'adar tasu tana kunshe da wata al'adar kuwa Wanda a halin gaskiya a yanzu
haka gaba d'aya shuwa'arab sunbar yin wannan al'adar ta biyun na farin dai sunyi Amman na
biyun kam ,
a shuwa'arab d'in ma na zamanin yanzu da yawa basuma san al'adar ba dan tuni anbar yin
al'adar duk da dai a zamanin da d'in ma a cikin aggwaye 100 da wuya a samu aggwaye 5 masu
yin wannan al'adar domain al'adace mai nuni da d'auka alk'awari da kuma rik'o da amana suna
kiran al'adar da sunan *Nad'in uwar gida*
So shiyasa aggwayen yanzu basa wannan al'adar ta biyun kenan fa,
Amman na farin kam har yanzu shuwa'arab sunyi kuma in an gama na farinne akeyin na biyun,
so Yau jumma'a tun safe aketa shirin wannan al'adar tasu na. farin wanda dama asan dashi shi
kuwa na biyu ba wanda yake da tabbacin za'ayishi a cikin shuwanma wasu basu san da
wannan ba,
tun safe aka k'afa tantuna a harabar gidan nasu aka shimfid'a kilisai na al'farma aka ajiye kujera
na gani na fad'a kujera masu taushi gaba d'aya an zagaye wurin da kolliyoyin zamani tare dana
al'adun shuwa'arab d'in,
cikin kujerun kuwa a tsakiyar kujerun akwai na aggo da amarya wanda sunayen su ke rubuce a
Kansu sai na k'awayen Amarya da abokin aggo suma duk sunayen su na rubuce akan kujerun
nasu.
Yadda ake al'adar tasu kuwa bayan an gama kimtsa wurin aggo zai fara zuwaya zauna da
zugar abokan shi sai bayan ya zauna da mintuna kad'an sai a fito da amarya,
fito da amaryarna kuma 'Yar uwar amaryar ce ta jini zata fito da amariyar rik'e da hannun ta ,
sai ta mik'a hannun amariyar ga hannun y'ar uwar aggo ko d'an uwan aggon,
daga nan sai shiko d'an uwanshi ago yaja hannun Amarya ya kaita kusa da aggon ya ajiyeta,
so y'an uwa da abokin arzik'i zasu tashi sunyi ta yiwa Amarya lik'in kud'i da gudumowowinsu,
bayan duk an gama lik'inne sai shi kuwa aggo ya tashi yayi nashi lik'in,
shike nan itace al'adar su ta farin .
So haka aka tsaba wannan al'adar bayan an sauk'o sallan jumma'a Hamma Umar da
abokanshi duk suka dawo gidan suka d'an huta sannan matayen su kuwa suna cikin gida ,
bayan anyi sallan la'asarne sannan aka fara shirin fita wurin taron,
abokon Hamma Umar manyane masu cikar kamala abokai ne daku masu karatu kun sansu
haka kuwa matayen su,
haka sukayi shiga ta al'farma shiga irin ta shuwa'arab d'in sukayi baki d'ayan su suka fito rasa
tamkar larabawa,
Suma matayen su da k'awayen Amarya Ummul shiga sukayi ta shuwa'arab d'in gaba d'ayan su
laffaya suka yane jikin su dashi suma dama gasu kyawawa. Haka yasa wurin taron ya zama
tamkar a k'asar larabane ,
wani abin burgewa kuwa duk woni sak'o da luggu har cikin fulawowi na gidan an ajiye kaskon
turaren wuta sai wani irin k'amshin ke tashi hakan yasa nishad'i a zuk'atan duk wani bani adam
dake zaune a wurin.
5:00 pm zugar ago da abokanshi suka ido farfajiyar gidan Ya Usman ne a gaba yayinda
sauran abokon ke binshi a baya ,
Hamma Umar kuwa yana tsakiyar su yasha sutura ta al'farma ya fito cikin haiba da cikar zati
sajenshi sai wani irin shek'i yakeyi farar fatarshi ta fito ras tamkar balarabe sumar kanshi kuwa.
yayi luf gwanin sha'awa ya murza hula a kan nashi yayinda gashin nashi yabi k'eyarshi da
zagayen fuskar shi,
idanun shi kuwa wani d'an siririn glass ne mai haske irin na Doctors ke manner a fuskar sa.
dai-dai lokacin da suka fito a dai-dai lokacin kuma matayen abokan aggon suna suka fito ,
gaba d'aya wani taku suke a jere kamar yadda kujerun ke Jere kowa da matarsa a gefen
Hamma Umar ne ya fara zama sai babban abokin shi ,
Hamma Yusuf da Ayshar sa sai Hamma Hassan da Fateemar shi sai kuma. Hamma Bashir da
Ruk'ayyar shi
Sai Hamma Mahmoud da Khadija shi sai kuma Hamma Aliyu Haydar tare da Minalin shi,
A d'aya gefen kuwa
wasu manyan abokan Hamma Umar d'in na gani da matayen su, Amadi da Nadiyar shi,
sai Abuturrab da Batul d'in shi sai kuma Salim da Tawa
Sai Abdullahi tare da Maryam d'in shi,
daga gefen su kuwa Fauziyya ce da Al'ameen sai Aisar tare da
Bintun shi
sai kuma Abbah da Ruky pinkyn shi,
ga kuma Ridwan da Zakiyya
can kuma kusa dasu Ahmad Ana Muslim ne tare da khadijan shi
sai kuma Assadiq da Safiyyar shi tare Hibbah da Faheem.
Gaba d'aya sun zauna cikin nitsuwa da al'farma suna zaune cikin cikar haiba sun fito tamkar
taurari sai shek'i sukeyi da wani irin k'amshin da suke zubawa zamane sukayi na masoyan
gaske.
Bayan sun zauna da kamar minti 5 Dangi da k'awayen Amarya da sauran mutane sukazo suka
zauna,
cikin nitsuwa da lumana,
Jim kad'an,
suka fara jiyo wani irin k'amshin na k'ara ratsa hancin su gaba d'aya sai wani irin shauk'i ya
ziyar cesu ido suka lumshe tare da jin dad'in k'amshin dake k'ara bud'e su wanda Anty shuwace
ke rik'e da kaskon turaren wuta,
Anty Halima kuwa na biye da Ita a baya tana rik'e da hannun Ummul wacce tasha gyara iya
gyara an yaneta cikin laffaya mai tsadar gaske ta fito a shuwa'arab d'in sak ta fito tamkar
tauraruwar zarah dake kusa da wata,
Anty Halima na rik'e da hannun ta suka iso farfajiyar gidan yayinda ita kuwa Ummul kanta ke
sunkuye idanun ta na zubda wasu irin wahaye masu zafi da tafasa zuciya tafiya takeyi tamkar
hawainiya,
suna isowa Ya Usman ya mik'e cikin happy yaje gabansu ya tsaya cikin wani irin salon al'darsu
ya d'an kife guiwarsa d'aya a k'asa sannan ya d'an d'ago hannunsh sama kad'an ya ware tafin
hannushi cikin sanyi yace.
"Halima samin hannun matar Hamma na cikin tafin hannuna ni zan kaiwa Hamman matarsa
kusa dashi."
murmushi Anty Halima tayi tare da kamo hannun Ummul d'in ta d'aura cikin tafin hannushi,
wani irin nanauyan ajiyan zuciya ya sauk'e tare da
rumtse idonshi da k'arfin,
yatsun hannushi ya cusa cikin nata ya rik'o hannun ta sannan ya mik'e tsaye ya fara taku a
hankali itama Ummul takun takeyi tamkar hawainiya a haka har suka isa gaban kujerar da zai
zaunar da ita suna zuwa ya kamo kafad'unta ya juyota tana fuskantar shi yayinda ta bawa
kujerar baya, cikin sanyi ya zaunar da Ita kan kujerar dake manne data Hamma Umar,
a hankali ya fara tasowa daga sunkuye da yayi a kanta,
Ita kuwa Ummul kanta ta kuma sunkuyarwa tare da sakin wani narkekken sautin kuka can
k'asa,
Sai kuma tayi shiru cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Ya Usman d'in nata jin kamar y'an
watsa mata ruwa,
abin mamaki da Ummul ta gani ba ruwan bane ya Usman ke watsa mata ,
Hawaye ne ke bin fuskar sa har yana diga cikin tafin hannun ta ,
ido ta zuba mai cikin yanayin tabbaya da tsantsar. mamaki a fuskar ta,
shi kuwa cikin jarumta yasa tafin hannushi ya goge k'ollah dake zuba a idanun shi,
murya na rawa yayi murmushin da yafi kuka k'una a zuciya murya can k'asa yace mata.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi cikin zubda k'olloh murya a disashe tace.
"Ya Usman ina son ka".
ido ya lumshe da sauri cikin raunin murya yace.
" Ummul nima ina sooonki."
Ido Ummul kam ta kuma rumtsewa dan tasan ba haka suka saba cewa juna ba,
Ita tasan in tace mai ya Usman ina sonka shiko sai yace Allah ya d'aiyiba Amman Yau kuma
shima sai yace mata "Ummul nima ina sooonki " a madadin yace Allah ya d'aiyiba Sannan ga
hawaye dake bin fuskarsa,
tana cikin nazarin ne taji ya fara yi mata lik'in da Sabin kud'i na gudan dubu-dubu'
gaba d'aya wuri aka fara tafi marok'a na .
"Kaji k'anin aggo Usman d'an Maliki mai ruwan nare."
lik'in sosai Ya Usman yayi mata yanayi yana zubda k'olloh cur-cur sai yasa tafin hannushi yana
gogewa ganin haka yasa Ummul tayi murmushi cikin d'an d'aga murya kad'an yadda zai iya
jinta tace.
"Allah ya d'aiyiba min ya Usman dina."
jin haka sai ya rink'a murmushi tare da kallon fuskar ta,
a haka ya gama yi mata lik'in sannan Ya Adam da ya Sadik tare da Aliyu auta suma suka shigo
sukayi mata lik'in ,
daga nan manyan abokan Aggo kuma jarumai suma suka fito sukayi lik'in ban girma,
daga nan y'an uwa da abokan arzik'i sukayi nasu. lik'in,
bayan duk an gama kowa ya koma mazaunin shi wuri yayi haske,
cikin wani irin yanayi Hamma Umar d'in ya mik'e tare da juyowa gaban Ummul d'in sannan
kanshi a sunkuye cikin sanyin muryar shi ya kalli marok'an yace.
"Ku shaidawa Jama'a yanzu zanyiwa Ummul lik'in ne a matsayina,
na babban Yayanta d'an uwanta."
aiko a take marok'an nan suka rink'a shela suna fad'in.
"Aggo yace a shaida muku yanzu zaiyi lik'in ga Amarya a matsayin shi na babban yayanta kuma
d'an uwanta."
gaba d'aya sai wuri ya ciki da shauk'i ,
abokan Hamma Umar da matan su sai murmushi suke,
shi kuwa Hamma Umar lik'in kawai yake mata da rafa-rafa na dubu-dubu,
haka ya rink'a zubawa Ummul kud'i tamkar ruwan sama,
bayan ya gama ne sai ya kuma komawa kan kujera ya zauna,
sannan k'awayen Amarya suka rink'a tattara kud'ad'en.
Bayan sun gama ne Hamma Umar d'in ya sake tashi tsaye cikin cikar haiba da kamala gaban
Ummul d'in ya kuma tsayawa cikin k'asaita yace.
"Yanzu a matsayin aggo zanyi lik'in."
marok'an ko tuni suka cika wurin da kirari suna.
"Ummaru sand'a babuga mai nera Ummaru mai ado da zinari Ummaru Farouq mai K'amshin
al'miski
kunji Umaru Farouq babban adali doctor mai tausayi da jink'ai."
Shi kuwa Hamma Umar Dolas ya zaro ya rink'a yiwa Ummul b'arinsu a kanta,
Ya Usman kuma na tsaye a gefen shi rik'e da turaren mai suna *du'a'ul jannarh* mai tsananin
k'amshin,
bayan Hamma Umar ya gama lik'in sai ya kuma mik'a hannu ya karb'i turaren dake hannun Ya
Usman,
sannan ya d'an sunkuyo kan Ummul d'in ciki kallon fuskar ta ya fara fesa mata turaren yanayi
yana k'ara matsota har ya isa gab da Ita sannan ya mik'ewa Usman turaren ,
a hankali ya rokk'fo gaban ta sannan ya sunkuye dai-dai kanta,
mutanen wurin kuwa gaba dayasun maida hankalin su sukayi kan Hamma Umar d'in domin son
ganin me zai aika ta,
Hajjajo kuwa da Inna tuni sun fara mamakin abinda Umar d'in yake shirin aika tawa,
sauran mutane kuma gaba d'aya kallon shi suke cikin tarin mamaki dan gano abinda yake shirin
aika tawa,
Ammin kuwa lokaci d'aya taji wasu siraran hawaye na bin fuskata tana kallon Abin da Babban
d'an nata zaiyi,
Abokan Hamma Umar kuwa ido suka zuba mai cikin mamaki su Hamma Yusuf duk an cika da
mamaki sai k'ara rik'e hannun Ayshan sa yake.
Itako Ummul gaba d'aya jikin ta sai kerma yake ido kawai ta zubawa Hamma Umar d'in fuskar ta
cike da k'olloh,
Nenne ma ido ta zuba mishi dan gano abinda zaiyi.
Shi kuwa Hamma Umar cikin wani irin yanayi yasa hannushi ya cire hular kanshi sannan ya
k'ara sunku yowa kan Ummul d'in tare da manna....
By
*GARKUWAR FULANI*ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 9β£
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Alhamdulillah ala kulli halin nayi tafiya lfy na dawo lfy yanzu zanci gaba da typing insha Allah
har k'arshe*
```NI na jinjina muku y'an KADUNA bamai rabani daku jama'ar KANO kui hak'uri ga shafinku
ya iso mun