Showing 27001 words to 30000 words out of 96677 words

Chapter 10 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

73992

*GOYON* *KAKA*
*46*
Da sauri safwan ma y futo y rufe motar yabi bayan Aslam side din safwan suka shiga pallo ne sai kayan kallo sai kujeru brown & milk sai center carpet da center table sai bedroom kuma bedroom din Aslam y wuce jakarshi y ajiye y dauro alwala y futo y shimfida sallaya sai da yayi nafila raka'a biyu sannan yayi sallar la'asar safwan kuwa dayake y riga yayi kawai kwanciya yayi akan gado,sai da Aslam ya idar da sallarsa yayi axkar kamar yadda yaxo a sunna y dade yana kwararo addu'a sannan y shafa y kalli safwan yace tashi mu tafi gurin canal kasan daxu y kirani nace masa yau xan shigo,safwan yace gaskiya kam gwanda muje kaima a jikaka da naira dan yanzu accaunt dina taff yake,Aslam yace kai haba maxa tashi mu tafi da sanyin safiya ake kamun fara,dariya safwan yayi yace dan wadannan farin babe ne dan 1 million ake sakawa duk wanda aka xaba a tafiyar da sauri suka futa sai da suka biya suka gaida aunty (mmr safwan)ta tambayi mutanen gda yace duk lfy suna gaisheku tace tom ina amsawa sannan suka futa.


Sai da suka nemi permission sannan suka shiga office din canal yunusa safana kamar yadda nagani a karamin allo an sakala a kofar kafin ka shiga,suna shiga suka sara masa suka kame time din yana duba yadda akayi ta'asa a somalia a laptop dinshi y dago kyakykyawan dan fulanine yana da siririn bille a kumatunshi,yadan manyanta xai kai 55 year y nuna musu kujera yace have a seat dada kamewa sukayi suka sara masa sannan sukace tnx sir suka xauna.


Kallan Aslam yayi yace haba umar y kake wasa da damarka,kasan yawan sojojin da sukeso a turasu aikinnan saboda in harkun yi nasara a aikinnan bakaramin girma xa'a kara muku ba,sunkuyar da kai Aslam yayi yace sorry sir wlh gocewar kashi nayi to lokacin da safwan y fadamin ina kwance shiyasa banxo ba,murmushi canal yayi yace haba Aslam karka bawa sojoji kunya mana common gojewar kashi ta kwantar dakai to ina wadanda afilin yaki xasu karye amma saboda tsabar tashin hankalin da suke ciki basa sanin sun karye karka bani kunya mana ina maka kallon jarumi shiyasa na xabeka dan ku sani in kunyi bajinta to tamkar ni kuka kare,suka hada baki sukace insha Allah baxamu baka kunya ba,yace to Allah y tai aka xaku iya tafiya sukace ameen suka mike,yace kaje ka bawa cashier accaunt number dinka xakaji alert insha Allah yau,yace OK sir tnx suka ficw direct cashier office suka wuce y bada accaunt number dinsa sannan suka koma gda.


Suna xuwa gda safwan yace eyya dan'uwa Ashe gocewar kashi kayi,yace eh safwan yace garin yaya,Aslam yayi tsaki yace inna fada makama dariya xakamin cikin yanayi na tausayawa safwan yace y xa'ayi nayi maka dariya,anan Aslam y lbrtwa safwan abinda y faru tun ranar daya koma har ranar da islam ta fada masa itace ta xuba masa karkashi,da kuma xaman da yayi najira ta dawo yayi mata hukunci sai kuma canal y kirashi,dariya safwan yake babakawa sosai harda faduwa banda kwalla data taru a idonsa yace kai amma yarinyarnan ta birgeni wlh kajifa sunan data saka maka wai dan gurgu😂,Aslam yace to dallah menene na dariya kuma ciki safwan y kama yace saboda kasan xanyi dariya shiyasa kaki bani lbrn da farko ai tsaki Aslam yayi y bude fridge y dauko faro y balle murfin y kafa a baki ko takan cup baibi ba saboda yadda xuciyarsa take tafarfasa ji yakeyi tamkar yanxu islam ta xuba masa karkashi.


*Aslm plz kuyi hakuri da rashin posting din _goyon kaka_ kwana 2 hakan y farune sanadiyyar xaxxabi danayi ina*
*bukatar* *addu'arku* *yan'uwa*


Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘
[11/12, 9:30 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (6/11/2016 3:00pm) *na* *umma* *yahya* *musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON* *KAKA*
*47*
Kamar yadda canal yace cikin dare around 9 o'clock Aslam yaji alert dadi y isheshi,sai a lokacin yayiwa safwan magana yace friend kaga nima kudin y shigomin cikin jin dadi safwan y miki,saboda kawai daurewa yakeyi bayason ko kadan Aslam yayi masa fushi danshi akwai san raha,safwan yace to kaxo muje shopping ko akwai abinda kakeso,Aslam yace a'ah ba abinda nakeso nasiyo komai safwan yace shikenan daganan sukaci gaba da hirar yadda tafiyar tasu xata kasance.


Kamar yadda akace yaune ranar tafiyar su Aslam kowanne soja sanye yake da unifoam fuskarnan a daure tamkar a filin yakin suke(nidai da nake a gefe tuni cikina y bada kuuu my Afma kuwa data rakani dauko rahoto tuni ta fara xawo a wando saboda ganin wani soja y saitata da bindiga 😂😂) sai da suka dadayin training sannan aka bawa kowanne soja wata jaka tamkar skul bag amma tafi skul bag girma in da xasu xuxxuba kayan da xasu bukata kowanne da bindiga a gurinshi a hankali kowa yaje yahau motoci xasu wuce airport suhau flight xuwa somalia.


Su islam anata shirye2 xasu shiga j.s 1 yau iyayi ake tayi an fara xama yan mata dayake a primary skul din da suka gama acikinta xasuyi secondary unifoam ne kawai na secondary section white shirt ce mai dogon hannu da skirt maroon sai hijab fari mai hula sunyi kyau sannan suka futo isya y daukesu a mota sai makaranta.


Jere suke a assembly akayiwa dalibai barka da dawowa makaranta dftn sun daura damarar karatu akayi bayanai kowa y wuce class j.s 1A nanne ajinsu islam,again uncle hasheem shine foam master dinsu dadine y ishesu saboda yadda ya iya tallerating students.


Su Aslam suna sauka a somalia,ana saukesu a airport akaxo da manyan motoci aka debesu sai head quater aka babbasu masauki sukayi wanka musulmi sukayi sallah,sannan sukaci abinci,anan shugaban yasa aka kirawo su yayi musu brk da xuwa sannan y fara musu bayanin irin gurin da xasuje da haxarin da yake gurin,da irin ta'asar da yan kunar bakin waken sukeyi,yayi musu fatan samun nasara aka basu taswira ta gurin aka dada hadasu da wasu sojojin na garin duk da akwai wadansu acan jejin,su Aslam tunda suka futa kallan garin suka fara saboda yadda duk yan tada xaune tsaye suka bata garin,wasu gurin an rurrushe gininnika an kokkona,a haka har suka karasa dajin da sauran sojoji yan'uwansu suke suma duk an kakkashe wadansu ga gawarwakinan birjik na sojoji dana yan kunar bakin waken,suka ajiye jakunkunansu suka fara buga runfuna,suka shishshiga ciki musulmi sukayi alwala sukayi sallah.


Misalin 4:00pm sukaji harbe2 da tashin bomabomai nan suka fara shiri suka futa,kurar yan tada kayar bayan suka gano har suka karaso daf dasu nanfa aka fara dauki ba dadi akayita misayar alburushai su sunaso su shigo cikin gari su sojoji kuma sun hana,haka akayita bala'i su Aslam sunga tashin hankalin da basu taba gani ba dan irin wannan yakin sai a film suke gani haka suka kwana ana abu daya sai daf da asuba suka tabbatar da yan kunar bakin wakennan sun koma,dan cikin dare sai sunyi tunanin sun tafi saisu dawo,in lokacin sallah yayi kuwa sai dai musulmi 10 da keister 5 masu gadinsu da haka sukeyin sallah.


Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘
[11/12, 9:30 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (6/112016 4:30pm) *na umma yahya musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON KAKA*
*48*
Sai lokacin su Aslam sukayi sallar asuba sannan suka shishshiga rumfunansu,wadanda sukaji ciwuka akayi musu treatment dinshi Allah y taimaki Aslam da safwan dai basuda rauni ko daya sai gajiya abinci sukaci sai pracitamol suka kwanta,sai axahar sannan mafi yawansu suka tashi wasu rumfunane dai sukayi bathroom dashi nan wasu suka shiga suka watsa ruwa dan sai suyi sati basuyi wanka ba.


Su islam ana tashi aka kamo hanya anata wani yauki (nikuwa nace kaga berayen j.s masu gigi 😂),islam ana shiga aka fara fatali da kayan makarantar sai da akayiwa komai daidai pant dinta kawai ta bari sai best haidar ne a lokacin a dakin kaka shiya fatatakata daki ta dauko xanin kaka danshima ba sauki haka tafuto tanata xumbura baki.


Bangaren su Aslam kuwa abin ba sauki dan yan ta'addan yau sunfi na jiya haka akayita artabu yauma basu samu hutawa ba sai da akayi asuba.


Su Aslam har sunyi 3 month acan kwata2 agida ko an kirasu ba'a samunsu saboda jejin da suke babu sabis sannan uwa uba tashin hankalin da suke ciki baxai iya barinsu su futa suyi wayaba,saboda yanxu ko bacci ma basa samun damaryi saboda yadda yan ta'addan sukaga anayi musu ta'adin mutane sosai to koda yaushe cikin kawo farmaki suke ko sallah sai dai su hada axahar da la'asar magruba da isha'i asuba kuwa sai gari yayi rana,dukkansu kuwa sunyi wani irin mugun rama uwa uba wani mugun baki da sukayi dan rabonsu da watsa ruwan ma da sukeyi harsun manta.


Aunty amarya ce take xaune kuwa takeyi wiwi harda majina,tana haba Abbn amir y xakace baxan tashi hankalina ba kafa gani yau my son watanshi 3 da tafiya amma bamu tabayin wayaba koda yaushe nakira wayarsa a kashe take haka ta safwan din to in banyi kuka ba y kakeso nayi in my son y rasune y kamata ku fada mana ta dada rushewa da kuka,cikin sanyin murya danshima dakewa kawai yakeyi yace haba fateema waya fada miki Aslam y rasu yanayin inda suke aikine haka,sannan kuma gurin da suke ba service cigaba tayi da kukanta,haka y tashi y tafi part din yayansa anan y xayyane musu abinda ke faruwa Fateema duk ta tashi hankalinta,mommy ce tayi murmushi duk da itama dakewa kawai takeyi tace in banda abin auntyn yara ai addu'a itace y kamata tayi musu bata xauna tana kuka ba,kallanta Abba yayi yace nikam nakasa rarrashinta daddy y kalli mommy yace khadeeja jeki kirawo ta mommy tace toh ta futa.


Kukan ta tarar aunty amarya tanayi tana ta kiran waya murmushi mommy tayi ta karasa tace daddy yana kiranki,haka aunty amarya tanajan hanci suka fita.


Suna xuwa suka samu guri suka xaxxauna anan daddy y kalli aunty amarya yace haba fateema y xaki tashi hankalinki akan abinda hasashe kawai kikeyi yanxu acema Aslam din y mutu haka xaki xauna kina kuka baxakiyi masa addu'a ba,kuma kinsan rikicin Hajiya (kaka)kullum muka shiga gurinta saitayi mana xancen Aslam bai taba kiranta ba kuma in itace ta kirawo shi sai yara suce ance a kashe take,kinsan cemata mukeyi mu munayin waya dashi kila ita lokacin da take kiransa y kashe wayarne saboda aikin da yakeyi akwai wahala,to yanxu intaji irin maganar da kikeyi y xamuyi da ita,shiru aunty amarya tayi tana goge kwalla,daddy yace dan Allah ki daina kuma nakira abokina yace yaje head quarter sunce suna lfy kawai jejin da sukene ba service kici gaba dayi musu addu'a kinji tace toh.


Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘
[11/12, 9:31 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (7/11/2016 4:00pm) *na umma yahya musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON KAKA*
*49*
Kamar yadda daddy yayiwa aunty amarya nasiha,haka ta daure tana danne damuwarta duk kuwa data damu,sannan haka ta tsaya tsayin daka ta dage da nafilolin dare akan Allah y bawa su Aslam nasara kuma y karesu daga sharrin duk wani abu daxai cutar dasu.


*AFTER 1 MONTH*
Yau su Aslam tashin hankalin da suke ciki yafi na kullum,saboda yau harda shugaban yan kunar bakin waken aka futo musayar wuta kawai akeyi a tsakaninsu da tashin bomb ko ina ka kalla a ko kone gawarwaki kuwa tamkar ba yan adam ne a kwance ba bala'in yayi bala'i tashin hankalin yakai,su har mamaki sukeyi inda wadannan mugaye suke samun kayan fada,safwan ne da Aslam a bayan wata bishiya da aka sare a lafe,cikin nuna gajiyawa safwan yace my friend wlh nagaji yau 2 days ana yaki in banda ruwa babu abinda cikinmu y samu ruwan ma bamusha mu koshi ba wlh nagaji anya xamu iya kama wadannan mutanen kuwa Aslam ne y hango wani dan kunar bakin wake y harbo bindiga a daidai saitin kirjin safwan da sauri y hankada safwan yayi kasa shikuma bullet din y shigar masa kafada ohch yace a lokacin y saita kan dan kunar bakin waken y harbeshi a take y fadi y mutu.


Daidai lokacin islam ta futo daga kitchen din aunty amarya ta dauko wa aunty amarya ruwa a try y fadi glass cup din y tarwatse dafe kirjinta tayi tace wayyo,aunty amarya tace ke kuma lfyrki islam tace wlh aunty amarya kawai ji nayi gabana y fadi,aunty marya tace toh ba addu'a y kamata kiyi ba,islam tace toh kitchen ta koma ta dauko broom da packer ta tattare glass din ta xuba a dausbing ta dawo jikinta duk yayi sanyi,tana shirin futa aunty amarya ta kirata tace xonan islam,komawa tayi ta xauna a gefen aunty amarya ta sunkuyar da kanta,aunty amarya tayi murmushi a ranta tace Allah ngd maka yarinyata tafata hankali (nikuwa nace anya kuwa)tace islam meyake damunki naga yanayinki kwana 2 duk y canja kin xama so silent,kawai sai islam tahau kuka mamaki aunty amarya ta fara tace daga tambaya sai kuwa,dakyar ta lallasheta tace ki fadamin damuwarki koda addu'a natayaki kinji cikin xumburo baki islam tace toba yaya bane,da mamaki aunty amarya tace wanne yaya dan tasan kaf gdan abokin tsamarta 1 Aslam to kuma yanxu bayanan,islam ta kara xumburo karamin bakinta tace yaya Aslam,aunty amarya tadan xaro idonta tace a'ina kika ganshi,islam tace a haccina kullum saina ganshi yana can a wani daji yana tashan wahala saiyace naxo nikuma naji tsoro saina gudu saiya dinga kwalamin kira yana cemin nadinga yi masa addu'a saina saina farka in duba naga bayanan,to yanxuma nafito a kitchen naji kamar ihunsa,hawayene y xubowa aunty amarya ta goge,tace toh kinayi masa addu'ar,girgixa kai islam tayi,aunty amarya tace toh daga yau duk lokacin da kikayi sallah ki dingayi masa addu'a kina Allah y bawa yayana nasara y kuma dawo dasu lfy kinji,murmushi islam tayi har dimple dinta y loba tace to,aunty amarya itama murmushi tayi tace that gud my girl give me 5 ta mika mata hannu suka tafa islam ta tashi tana dariya tace bari natafi gurin kaka ta tashi tatafi da gudu murmushi aunty amarya tayi itama ta mike ta shiga kitchen ta dauko ruwan dan islam bata daukoba(kalubale ga iyaye y kamata aduk lokacin da kuka fahimci yaranmu suna cikin wani damuwa y kamata ku jawosu ajikinmu muji damuwarsu tanan xamu samu su fadamana abinda ke damunsu,amma ba muga yaranmu a damuwa ba kuma mu kasa magance musu karmu manta amanace Allah y bamu kuma saiya tambayemu).


Cikin kidima safwan y dago yace y sameka ganin jini na bulbulowa a kafadar Aslam kuma yanata hada uban gumi shiya sakashi saurin sauko da jakar bayansa y xuge y dauko wata karamar wuka mai dan tsini yayi saurin farke rigar y luma wukar a jikin Aslam,Aslam sai runtse idonsa yakeyi saboda yadda y kaje wani irin xafi yana ratsashi tundaga kwakwalwarshi har xuwa dan yatsanshi,wata kara y saki lokacin da safwan y xaro bullet din sai kuma y lumshe idonsa y jingina da bishiyar yana maida numfashi,daure masa hannun safwan yayi sannan sukaci gaba da yakin danyau abin yayi tsanani (nikuma nace Allah y rabamu da yaki 😰).


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login