Showing 48001 words to 51000 words out of 96677 words
Chapter 17 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt
auran dakyar y daidaita nutsuwarshi don bayason su gane maganar da xaiyi ba gaskiya bace yace ai daddy tunda an riga an daura auran to inason matata daba a daura bane xan iya hakura ta auri wanda take so amma yanxu kam baxan iya sakin matata ba y dada sunkuyar da kanshi domin karsu gane plan ne abin,sukace to Allah yayi maka albarka,wata xabura islam tayi ta mike tana nunashi da dan yatsa sam ta kasa magana,can kuma ta tuntsire da dariya tace wlh karya kakeyi munafinci ne kwata2 baka sona sam *ni da kai* bamu daceba,sai kuma ta barke da kuka dago idanuwansa y jefeta da wani shegen kallan kiyayya,a ranshi yace da wayace miki *ni da ke* mun dace tamkar yadda kikace kinfi kaunar maciji akan aurena to saina shayar dake gubar bakin ciki saina jefa xuciyarki acikin kiyayyar maxa harshi wanda kikayi ikirarin kina sonshi,daddy ne y katse shirun yace to Allah yayi muku albarka ke yanxu islam wanda ikon sakinki yake hannunsa yace baxai iya sakinki ba don haka saikiyi hakuri kiyi biyayya Allah y baku xaman lfy,xaku iya tafiya a sukwane islam ta kwasa da gudu ko takan dankwali batabiba balle mayafi ko takalmi,Aslam ma ficewa yayi,sukuma iyayan suka xauna tattauna ta yaya hakan ta faru,anan kaka ta labarta musu irin rashin jituwar da take tsakanin Aslam da Islam,cikin tsananin mamaki su Abba sukace yaushe al'amarinnan yake faruwa su sam basu sani ba,kaka tace tun lokacin da islam ta koma gurina suke wannan rashin jituwar daddy yace Allah y kyauta sukace ameen taron y watse.
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ
[11/21, 4:17 PM] βͺ+234 703 751 0996β¬: (21/11/2016 2:30pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*
*72*
Islam da gudu ta wuce mutane tana kungin kuka ita ko takan mutane da suke kallanta batabi ba direct dakin mommy ta wuce ta fada kan gado tana kuka sosai,cikin tsananin firgici su khausar suke kallanta tambayarta sukeyi menene y faru amma sam taki magana sai kuka da takeyi tana ta shiga 3 ta lalace shine abinda kawai yake iya futowa acikin bakinta,mommy ce ta turo kofar kana kallon fuskarta xakasan akwai tausayi aciki su Amira ne suke tambayarta me akayiwa islam domin suma xuwa lokacin harsun fara hawaye kallansu tayi tace kuje waje ku jirani tashi sukayi suka futa jikinsu duk a sanyaye,bin bayansu mommy tayi tasawa kofar key ta dawo.
Dawowa mommy tayi ta janyo islam ta rungumeta,shafa bayanta ta farayi a hankali sautin kukannata y fara raguwa xuwa can kuma mommy taji saukar numfashi a hankali,dubawa tayi taga islam hartayi bacci komar da ita tayi ta kwantar taje ta bude kofar takira su Amira tace su xauna mata da islam inta farka suxo su kirawota.
Aslam kuwa part dinsu y shige direct dakinsa y wuce tsaki yayi ganinsu safwan suna dakin wucesu yayi ko magana baiyi musu ba y cire babbar rigar jikinshi y balle bottle din ta ciki y cire y daura towel y shige bandaki y sakarwa kanshi shower ko xaiji saukin xafi da radadin da xuciyarshi takeyi masa,haka yadauki tsawon 20 minute y futo yana tsane kanshi da towel mai y xauna y shafa sama2 armless y saka da short nikker y kwanta y runtse idanuwansa,safwanne yace haba ango kasha kanshi ya xaka saka wadannan kayan bayan kasan yau ranarka ce mu bama ka fada mana wace amaryar taka ba,y karashe maganar da dariyar shakiyanci,banxa Aslam yayi dashi domin yasan yadda xuciyarsa take tafarfasa xai iya yiwa safwan komai akan maganar nan daya fada masa,y dada runtse idanunsa xuciyarsa kuwa banda furucin islam da yakeyi masa amsa kuwa a kunne inda take cewa *wai itace matar hero ita yadda ta tsani hero hartafi son mutuwarta akan shi,ita har gwanda a aura mata maciji tasan saranta xaiyi da ace hero ne mijinta*,runtse idanuwansa yayi da karfi y mike cikin karaji yace wlh karya kikeyi xakiyi danasanin furucin da kikayi a gareni sai gdana y xame miki kabari saboda duhun da bakin cikin da xaki tarar warwaxa gashin kansa y farayi tuni yahau jifa da komai y dauka (nikuwa nace tab ran maxa y baci allurar sojoji ta motsa)da sauri su safwan suka matsa suna subhanallah mai yayi xafi haka jikinshine y koma yana bari tamkar dan gangi,a hankali Amir y fara magana haba big bros abinda hakuri bai bayarba rashinsa baxai taba sakawa ba daga yadda naji lafuxanka hakan yana nuni akan matar da aka aura makace karka manta biyayya ga iyaye wajibice kuma mai yinta baxai taba tabewa ba,karka manta aljannarka tana karkashin iyayanka kaga kuwa komai na duniya mai saukine tunda xamane na temporary kayi kokari ka gyara permanent dinka ma'ana lahirarka tayi kyau,a hankali Aslam yaji hankalinshi na kwanciya xuciyarshi tana rage radadi sai kuma y fara kuka wiwi tamkar karamin yaro kyaleshi sukayi saboda sunsan hakanne kawai xai rage masa xafin xuciya,safwanne yayi karfin halin magana yace haba Aslam y kakeyin kuka saikace ba namiji ba abinda bakayi shi a filin yaki ba sai yanxu akan cammond karamin Abu xaka tashi hankalinka rinannun idanuwansa Aslam y ware akan safwan yace cikin dashashshiyar murya auran yarinyar nanne karamin Abu kasan kuwa wa aka auramin to ba kowa bace illah aljanar yarinyar nan ta wajen kaka,wani dadine y lullube safwan domin yasan duk daran dadewa sai Aslam yaso islam.
A hankali islam take bude idanuwanta jin yadda kanta yayi mata nauyi a hankali abinda y faru daxu y fara dawo mata,su khausar basusan tashinta ba sai kukanta sukaji da sauri khausar ta tafi kusa da ita Amira kuma ta tafi kiran mommy.
*assalamu alaikum plz masoyana kuyimin hakuri narashin samun posting jiya hakan y farune sakamakon unguwa da naje,sannan masu kirana suji lfy ngd masuyimin massage kuma ngd sannan dan Allah wadanda sukaga sunyimin massage banyi reply ba kuyi hakuri ba'ason raina haka ta faruba sai don matsalar da wayar take bani wani lokacin massage na tsakiyar shigowa sai whatsap din y goge gaba daya,sai nayi sabon downloading kuma saiya xama wadancan massage din nayi missing dinshi nima ina kaunarku a duk inda kuke ngd dftn xakuyi min uxiri ngd,insha Allah yau xa'a kaimin gyaran wayar*
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ
[11/22, 4:22 PM] βͺ+234 810 749 9249β¬: (22/11/2016 2:00pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*
*73*
Mommy ce ta karaso da sauri tacewa su Amira su futa,tana haba my daughter kukanne har yanxu bai kareba,kiyi shiru kiji me xance miki shiru islam tayi duk da har lokacin tana hawaye,mommy tace daughter na saurareni da kyau kiji abinda xan fada miki,nima nasan an tauye miki hakkinki amma sam banxata dake xa'ayi aurannan ba saboda daddyn ku bai sanar mana ba,amma shawarar daxan baki yanxu kiyi hakuri ki daure a gama bikinnan lfy nasan bakyason Aslam kuma shima baya sonki don duk abinda y fara karyane,cikin mamaki islam ta dago kai tana kallon mommy,mommy tace eh yanxu abinda nakeso dake kamar yadda yayi pretending y nuna yana sonki to kema kiyi hakuri a karasa bikinnan da kaina xansaka y sakeki,cikin jin dadi islam ta dago kanta hawayen da suke sauka tasa hannu tana gogewa don yanxu bbn abinda y dameta dama bai wuce wannan kallagaggen auran ba,to yanxu kuma mommy tace xata saka y saketa,mommy tace yauwa daughter na ki share hawayenki ba sagir kikeso ba cikin jin dadi islam ta daga kanta harda murmushi kumatunta suka lotsa,itama mommy murmushi tayi tace yauwa my daughter yanxu kije kiyi wanka mai makeup xataxo tayi miki an jima xa'ayi kamu,fes islam taji ranta yayi saboda batad sauran damuwa ta shiga bathroom ta sakarwa kanta shower mommy ta futa su Amira suka dawo dakin.
Islam ce ta futo wanka amma idanunta sunyi ja sun kukkumbur,Amira ce tace 6* wai kukan me kikayi ne kinga yadda idanunki yayi ja y kumbura,xumbura baki gaba tayi ta shagwabe fuska tace wai aure akayi min cikin firgici da mamaki suka maimaita aure,siraran hawaye ne suka xubo mata ta goge tace eh cikin xakuwa sukace dawa,ta tabe baki tace hero,dariya suka tuntsire da ita suna tab Ashe kece amaryar yaya Aslam lallai xa'asha luv,cikin masifa ta tashi ta dauko pillow ta fara jifansu dashi tana balbalin masifa ganin sun mayar da ita mahaukaciya sunci gaba da dariyarsu yasaka ta koma ta xauna ta bude shafin kuka tana shure2,mommy ce ta shigo itada makeover ganin islam na kuka da sauri ta karasa tana subhanallah islam kukanne har yanxu,cikin kuka tace basu Amira bane sukeyi min dariya ba dannace nice matar hero ta karashe maganar da kuka,cikin fushi mommy tayi kansu kamar xata dakesu sukuwa ganin haka suka kwasa a guje suka fice a dakin suna dariya.
Dakyar mommy ta lallabi islam tayi shiru bathroom mommy ta jata da kanta ta wankewa islam fuska sannan suka futo,make up akayi wa islam sosai tayi kyau wani hadadden material white da touch din peach colour mommy ta dauko gown ne rigar ta kama islam ta sama ta bude daga kasa sosai ba karamin kyau tayiwa islam ba nada mata head makeover din tayi,sosai tayi kyau fashion dankunne da sarka aka saka mata peach colour occasion bag mommy ta dauko peach colour dayake takalmin hill ne sai islam ta kara tsayi,ba karamin kyau tayi ba duk da fuskarta ba annuri mommy tace xauna ki jirani,gaban dressing mirrow islam tayi ganin kyawun da tayi haryafi na safe amma maimakon tayi dariya ko murmushi saita karkace baki tayi tsaki tace aikin bands duk akan hero akayimin kwalliyar nan sai kuma tace dama da sagir akeyi min aurannan da nafi kowa farin ciki sai ta shagwabe fuska tace Allah sarki sagir dina very soon xan dawo gareka domin ni takace,su khausar ne suka shigo sanye da purple din material an masa kwalliya da light pink flowers sun daura light pink head suda wadansu yanmata da basu wuce sa'anninsu ba su 4,islam ganinsu ta hade rai sunata xolayarta ta musu banxa,mommy ce tace ku futo saka islam sukayi a tsakiya rigarta kuma tana sharar kasa.
Lokacin dasu islam suka futo yayi dai2 da futowar su Aslam saboda dokunan da xasuyi kilisa sun iso idanuwan sune suka hadu cikinna juna dam kirjin Aslam y buga islam kuwa ko a jikinta illa murguda baki da tayi ta dauke kai,Aslam ma kansa y dauke,harsun shiga mota safwan y karasa da sauri y mikawa khausar whapper ta 100 guda 2 yace gashi kubawa amaryarmu 1 tayi liki kuma ku raba 1 godiya su khausar sukayi islam kuwa nunawa tayi tamkar batasan akwai wata halitta a gurin ba.
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ
[11/22, 4:34 PM] βͺ+234 810 749 9249β¬: (22/11/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*
*74*
Driver yaja motar su islam sukabar gurin domin dama su kadai suka rage kowa y tafi,safwan ma komawa yayi gurinsu Aslam yace ku muje kallan kasan ido Aslam yayiwa safwan yayi tsaki yace mutum sai shegen shishshigin masifa dariya safwan yayi yace eh naji suka futa suma.
A cike su islam suka tarar da hall din da xa'a gudanar da kamu,suna xuwa sauran yan mata masu anko suka furfuto suka marawa islam baya,suna shiga d.j y saki kida.
Su Aslam ma sunyi kilisar inda wanda yaxo na 1 kyautar lefan aka bashi na 2 kuma t.v plasma sai na 3 shikuma waya iphone cikin jin dadi kilisa ta watse sabanin ango dayake jin ranshi bakikkirin tunanin irin axabobin da xaiwa islam yakeyi don kullum y tuno da karkashin data xuba masa sai yaji tamkar a lokacin taxuba masa.
Islam bayan an kamata mai d.j y bukaci amarya ta futo itada kawayenta,tuburewa tayi tace ba inda xata dakyar mommy ta lallameta ta futo anma kikam ta tsaya a filin wajan dukkuwa da yadda duma take ratsata su khausar kuwa rawa sukeyi sosai,aikuwa iyaye da abokanan arxiki suka futo ana barin nerori (nikuwa nace watako wasu ba ruwansu da buhariyyar nan π)bayan nan anci anyi rabon sevoniars sannan taro y watse kowa y koma gda cikin jin dadi,amma fa banda islam.
Suna komawa gda islam tayi jifa da head dinta da takalmin da jakar ta juya tacewa Amira ni xugemin kayan xafinnan Amira ta xuge mata,xama islam tayi daga ita sai vest da under wear ta xauna bakin gado,mommy ce ta shigo rikeda try dauke da abinci kallan islam tayi a ranta tace islam baxaki taba girmaba wai,kallan su khausar tayi tace kuje ku dauki abinci,karasawa tayi ta xauna a gefen islam tace yanxu my daughter a haka kika xauna keyanxu bakisan kin wuce wannan stage din ba,keyanxu matar aurece y kamata ki daina wannan abin yaran,xumbura baki gaba tayi amma batace komai ba dan ita inda abinda ta tsana baiwuce ace tana da aure ba murmushi mommy tayi dakyar ta lallaba islam taci abincin.
Washe gari 2 o'clock aka fara tafiya reception na pretty mommy ce ta shigo dauke da wata leda lokacin an gama yiwa islam makeup ta xaxxage kayan unifoam ne na sojoji riga da wando harda takalmi,mommy tace toh fa yau akeyin ta dama ance matar soja,itama sojace ga kayan da xakisa cikin shagwaba islam tace banaso fa mommy,murmushi mommy tayi tace au yi hakuri,kayan islam tasa subhanallah xanso fans din *goyon kaka*kuxo kuga yadda unifoam dinnan y karbi islam saboda yayi bala'in y mata kyau,yau dankunne barima tasaka aka kama mata gashinta da ribom y sauka har gadon baya ga takalminta tasaka,mommy tace my daughter ke kowanne kaya kyau yakeyi,murmushi islam tayi cikin jin dadi,su khausar ne suka shigo sanye da wandon sojoji da white t.shirt sai hula da takalmin sojoji suna ganin islam sukace wow sis gaskiya kinyi kyau,ai kayannan har sunfi karbarki akan yaya Aslam cikin jin haushi islam tace toh naji kafin ku fada mommy ta tafada ta karashe maganar da murguda dan bakinta daya sha jambaki,dariya mommy tayi tace islam bakida dama.
Futa su islam sukayi wata mota sabuwa ta gani safwan y bude mata baya yace shiga ranki y dade cikin xumbura baki ta shiga har saida ta xauna kanshin turaren da taji shine ya sakata saurin dago kanta Aslam ne xaune fuskarnan tashi tamau tamkar bai taba dariya ba,siririn tsaki tayi tace aikin banxa mutum kullum fuska a daure kamar anmasa bishara da a ranar xa'a dauki ransa,kallan mamaki Aslam yayi mata domin tsaf y jita ita kuwa kanta ta dauke,khausar ce ta shiga gaba Amira kuma tana motar Amir suka wuce country mall.
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ
[11/23, 5:56 PM] π¬ππ°°Salma°°π¬ππ: (23/11/2016 12:00pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*