Showing 33001 words to 36000 words out of 96677 words

Chapter 12 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

74065

ne yace kaci gidanku hajiyar tamu kakewa shakiyanci haka,Aslam yace Allah daddy kyaleni da tsohuwarnan inma tana tsoro ta mutune ta kwantar da hankalinta na rokar mata Allah insha Allah har bikin tattaba kunnenta xata gani,Abba ne y dauki pillow din kujera y jefa masa yace sai dai kaika mutu amma hajiya xama daram,da mamaki Aslam yace Abba ai gwanda ta tafi tunda taci xamaninta taci na yaya dannaci na jikokin ma tace sai taci,kakace ta tashi ta tafi gadan2 wai dukanshi xatayi da sauri Aslam y tashi yana dariya y fice a palon,su aunty amarya ma kawai kunshe dariyarsu suke,komawa kaka tayi ta xauna tana haki tace xakaxo ka sameni ne mutumin banxa ta kalli su daddy tace nafada muku ku kyaleni naje kauye na auro masa ma'u kunki dariya Abba yayi yace hajiya kiyi hakuri kinga Aslam har yanxu yarone baikamata a matsa mishi da xancen aure ba,kaka tace to shikenan dama wai inaso naga yayan jikoki ne kafin sa'i yayi,daddy yace hajiya ai mutuwa lokacice waya fada miki kin kusa mutuwa haka taron y watse kowa cikin farin ciki.


Aslam kuwa yana shiga dakinsa y fada gado yayi murmushi y shafi gemunsa yace waini aure tab ai duk da inada bukatar auran amma baxan iyayi yanxu ba,wayarshi y dauka y kira safwan bayan y daga,safwan yace maxaje y gdan?Aslam yace gda lfy,safwan yace y kowa da kowa,Aslam yace duk suna lfy,sun dade suna hira Aslam y fada masa waisu daddy aure sukeso yayi,dariya safwan y tuntsire da ita sai da yayi mai isarsa,harya bawa Aslam haushi,sannan yace ai sunyi gaskiya y kamata kayi auran,Aslam yace kai ubanwa y hanaka yi,safwan yace aini yarone,Aslam yace lallai fa,shiyasa kake mayan mata budurwar daka gani saika bita,safwan yace eh naji ni ai bawanda yayimin maganar aure,Aslam yace to nima da akamin sainan da 4 year xuwa nan nacika 30 kenan,har xasuyi sallama safwan yace ina jerry dinka? Aslam yace tananan mashirmaciya kasan wai har mafarkina takeyi a dajinnan,anan y lbrtawa safwan yadda ta fada masa kuma harshi safwan din ta gani dan har sunanka ta fadamin,mamakine y kama safwan yace ikon Allah yafi karfin wasa,dariya Aslam yayi yace wai kai mamaki kakeyi,safwan yace eh exartly fa yadda muke a dajinnan ta fada,dan juyawa Aslam yayi yace ni bana mamaki na dade dama ina tunanin yarinyar tanada aljanu saboda rashin jinta yafi karfin hankalinta,to kaga tunanina yaxo dai2 tunda sun fara bude mata ido,dariya safwan yayi a haka harsukayi sallama.


Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘






[11/12, 9:32 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (9/11/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON KAKA*
*54*
Kamar yadda akayi musu alkawari washe gari ko wanne soja yaji alert na 20 million acikin accaunt dinshi,wadanda suka rasu kuma har gda aka kaiwa iyalansu,saboda ba karamin kudi gwamnatin somalia ta bawa nigeria ba,aikuwa kowa yayi farin ciki,safwan ne y kira Aslam yace aboki gaka alert Aslam yace eh,yanxu y shigo tashima nakeso nayi naje nayiwa aunty na albishir safwan yace aboki ankusa fara lissafamu acikin matasa masu kudin duniya dariya Aslam yayi yace Allah y shiryeka masu kudin duniyar akace maka yan milliyoyi ne dasu haka suka karashe wayar cikin barkwanci.


Direct yana futa part din aunty amarya y shiga akace tana part din mommy acan yaje y sanesu ya fada musu sunyi murna sosai sun kuma tayashi farin ciki,yace toh yanxu bari su daddy suxo naji shawarar da xasu bani akan kudinnan aunty amarya tace gaskiya kayi tunani me kyau,mommy kuwa murmushi kawai takeyi,aunty amarya ce tace mommy bakice komai ba,mommy tace to me xance uwa da da suna shawara,dariya aunty amarya tayi tace addu'a mukeso kiyi mana,mommy tace to Allah yasa albarka,aunty amarya tace ameen,ta kalli Aslam tace jeka fadawa uwar gdan taka dariya yayi y tashi y futa,kaka kawai y tarar dan su islam sun tafi makaranta yaje y fada mata itama ta tayashi murna kuma tayi masa addu'a.


Dasu daddy suka dawo y fada musu sunji dadi,sukace dama mun riga mun siya muku fili kai da amir na kowa 1.5 million aka siyeshi to da munso mu gina muku dama karshen shekara muke jira tunda kai kudi yaxo saikaje ka fara ginawa inaga cost din da aka bamu na ginin gran 10 million ne babu furnishing ragowar ka fara kasuwanci ko sai da motocine,farin ciki sosai Aslam yayi yadinga yiwa su daddy godiya da addu'ar Allah y kara budi,suma sunji dadi sosai.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya,Aslam y saka anfara gina masa gidansa ginine mai kyau ginin xamani,kuma y fara kasuwancin motoci ta computer yana ganin albarkar abin dan lokacin da yayi order sukaxo 2 millions y samu riba.


Wannan karan basu fiya haduwa da islam ba,shiyasa duk rashin kirkin da takeyi baya sani,yauma kamar ko yaushe,friday ce Aslam y dawo daga masallaci sallar la'asar yaga yara maxa da mata sunata shiga gidansu,mamaki y isheshi yace to me akeyi haka yana shiga yaji sauti natashi a part din kaka karasawa yayi hayaniya yaji ana tayi,islam y hanko sanye da body hug red mai dogon hannu da three quarter pensil tayi packing din gashinta da red ribon kwalli kawai ta saka sai red lipstick amma tayi bala'in kyau irin dressing din Amira tayi amma rigarta yellow khausar ma haka tata pink,rawa islam takeyi tanata wani kada kugu tamkar babbar mace yara kuwa sai ihu sukeyi,su Amira suna lika mata yan 5 naira da yaya sagir y canjo musu,hannun ko wanne yaro yana rike da biscuit da lemo wata muguwar tsawa Aslam y sakar musu tuni kowa y nutsu,islam kuwa sororo ta tsaya kallasa dakawa yaran tsawa yayi yace kowa y fice,da gudu suke futa kowa yana rige2,islam ce cikin daga murya tace ku Ku tsaya mana inaruwanku dashi shine y gayyatoku koni dan Allah karku tafi,ganin da tayi yaran basusan ma tanayi ba shine y kular da ita ganin kowa y waste,a tsiwace ta karasa gaban yaya Aslam,tace yaya ina ruwanka da patyn da nakeyi,kawai xakaxo ka tsorata min kawaye da wannan jan idonnaka da kuma katuwar muryarka kamar xata fasa gda,mamakine y ishi Aslam y kasa magana islam tace wai baka jinane inayiwa yata birthday ka tarwatsamin tarona ta karashe makanar tana harararsa tana murguda baki,bakinnata y kama y murda da xafi y rankwasheta yace ke ko kadan baki dace da sunan islam ba danshi musulunci xaman lfyne,amman ke duk inda tashin hankali yake nan kikafi kauri,ai dama nine nasaka miki islam to xansiyo rago nacanja miki ki koma duduwa,y hankada ta gefe y fice,ihu ta kwalla ta fadi tana wayyo wlh ba wanda y isa y canjamin suna nakoma duduwa mai kan bari,duk da xafin da bakinta yake mata batashi takeyi ba,suna da akace xa'a canja mata shiyafi mata ciwo.
wannan page dinnakine *53 & 54* aunty jameela Marapha 💃💃


Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘
[11/12, 9:32 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (12/11/2016 2:00pm) *na umma yahya musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON KAKA*
*55*
Ihunta taci gaba dayi hawaye kuwa shabe2 a fuskarta,sai hakuri su Amira suke bata amma takiyin shiru,kakace ta dawo daga gdan makotansu akwai tsohuwa a gdan,tana yo hanyar part dinta tajiyo ihun islam ai da sauri tayi part din nata harda hadawa da gudu.


Birgima ta tarar islam tanayi da sauri kaka ta karasa ta dagowa tirjewa islam ta farayi,kaka tace haba islam dita ku dana tafi nabarku kuna partyn ku y xan dawo natarar ba yaran kallan su khausar tayi tace ina kawayen naku,khausar tace yaya Aslam y koresu,kaka tace wai yaushe Aslam sai daina shiga harkar islam ne to wlh bari naje na sameshi nasan kila har dukanki yayi ko ta kalli islam.


Islam ta shagwabe fuska tace eh y rankwasheni y murdemin baki yacemin mai idon mayu (nikuwa nace uhm harda kari 🤔)sannan yace wai xai siyo rago y canjamin suna wai nakoma duduwa ta dada barkewa da kuka,kaka tace rabu dashi naga dan iskan daya isa y canja miki suna a gdannan kuma xaixo y sameni y fada min wace mai idon mayu,dakyar ta lallashi islam tayi shiru.


Islam kuwa tun daga ranar kawai hanya take jira danta huce haushin abinda yayi mata y bata mata party.


Futowarta daga part din mommy kenan ta tarar da alkajirinsu nura yana wanke motar Aslam,murmushi islam tayi ta karasa tace nura sannu da aiki yace yauwa,tace mota kake wankewa yace eh wlh yaya Aslam ne xaije bikin abokisa,murmushi islam tayi tace Allah sarki xama tayi tanata yiwa nura surutu harya karasa wankin motar y kwashi bokitai ya tafi part din Aslam yace y gama.


Da gudu islam ta tafi part din kaka kibiya ta dauko ta daidaici tayar motar Aslam ta caka kibiyar tus tayar ta sace da sauri ta kwasa da guru ta shiga part din kaka ta labe tana iya leko waje.


Aslam ne y futo cikin wani dakakken yadi milk colour a kallah xai kai 75k tsadarsa yana sanye da xanna bukar brown da touch din milk a kallah hularnan xatakai 25k takalmin kafarsa ma milk ne mai dan yatsa shima daga gani xaiyi tsada,tafe yake yana sauri waya a kunnenshi y makaleta da shoulder dinsa yana ku bani 15 minute insha Allah xan karaso,hannunsa kuma yana daura hadadden ogogon axurfa na rolex,yana futowa y dannan key din motar da mukullinshi ta bude,shiga motar yayi y tasheta xaiyi reverse yaji motar tayi wani gurrrr kit ta tsaya tsaki yayi y futo kallan tayar motar y fara,ganin tarar tayi faci shine y bashi haushi wani naushi y kaiwa motar yace oh god gashi y duba duk an futa da motocin gdan,Nura y fara kwalawa kira.


Islam da take labe ganin yanayin da y shiga ranshi y baci shine y sakata farin ciki tuni tahau kyalkyala dariya,da sauri Nura y karaso kallanshi Aslam yayi yace Ashe motarnan tayi faci amma baka fadamin ba,Nura yace wlh yallabai lfyr motar qlau yanxu dana gama wanketa,Aslam y harxuka yace ga tayar motar a sace xakacemin qlau take,Nura y durkusar da kansa islam ce ta futo daga maboyarta tace yaya ba laifin Nura bane ta daga masa kibiya a hannunsa tace nicenan na sace maka taya,ramawa nayi ka tuna randa ka korarmun kawayena da sukaxo party,ta kyalkyale da dariya,ran Aslam in yayi dubu y baci Nura kuwa mamakine y cikashi a ranshi yace lallai yarinyar nan shiyasa dama taxo ta isheni da surutu.


Har Aslam y xuciya yayi gurinta,ita kuwa ganin haka ta kwasa a guje sai part din kaka,wayarsa da tahau ringing shine y katseshi ganin abdallah ke kiranshi,yayi picking abdallah yace haryanxu baka tahoba yace eh wlh faci nayi amma yanxu xanyi changing taya nataho,spare taya y dauko a motarshi y saka sai daya bata 30 minute sannan y tafi.

Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘
[11/12, 9:32 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (12/11/2016 2:30pm) *na umma yahya musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON KAKA*
*56*


Da gudu ta shiga part din kaka,bayan kaka ta tafi ta dukunkune kaka tace islam wai meyasa bakya rabo da shirme ne,islam ta turo karamin bakinta gaba tace ke kakannan ba yaya Aslam bane y biyoni,kaka tace ina Aslam din yake dan karya,keda bakyajin kunyar karya,islam tace Allah da gaske nake,kaka tace eh laifi kikayi masa,islam tayi murmushi tace babbama kuwa tayar motaraa na sace masa kuma unguwa xaije,dariya kaka tayi tace meyasa islam wai sam bakya tsoron fitina ne,islam ma dariya tayi tace ramawa fa nayi kin manta randa y korarmin kawayena,kaka tace tab naga ranar da xaki yafiya,murmushi islam tayi tace babu rana dan indai mutum yamin saina rama,tsaki Amira tayi tace wlh islam ina tsoratar miki ranar da yaya Aslam xai babballaki,dan ko kaka da take biye miki tana ganin duk abinda kikayi daidaine baxata iya kwatarki ba,islam ce ta hayayyakowa Amira tace eh naji kuma dadinta ni kikace xa'a ballah ba keba dan haka saiki kama bakinki kiyi shiru,kaka da kike cewa tana biyemin ta biyemin din,to ni naji shishshigi ma ina ruwanki da xancen mu manxan Allah S.A.W yace falyakul khairan au liyasmut ma'ana (kafadi alkhairi ko kayi shiru)dan haka babballawa ki gani a kanki ke tsayama kiji ni ko yaya y ballani wlh sainaja kafata na dana masa tarkon da shima xai dawo y xauna sai dai muyi jinyar tare tayi tsaki Amira kuwa shiru tayi saboda ita sam bata iya hayaniya ba.


Kamar yadda akace after 2 month xa'ayi karin girman su Aslam to yau saura 3 day shirye2 kawai su daddy sukeyi dan dukka gdan xa'a tafi sun gama duk wani shirinsu sunyi dinkuna dan tamkar wani biki haka sukejin abin.


Dukkansu sun shirya kaka,daddy,Abba,mommy,aunty amarya,da sauran yaran gdan dukkansu dan harda khausar xa'aje,lokacin da mommy tace ita ba saitaje ba islam ma tace aikuwa ba inda xata,a gurin mommy xata xauna,saida aunty amarya tayi fushi sannan mommy ta yarda xataje.


Ticket suka yanka dan flight xasubi,Aslam kuwa tun last week y tafi,suna dira a airport Aslam da safwan ne sukaxo daukarsu dansun xata iyasu daddy ne xasuxo ganinsu da yawansu yasa daukan drop din taxi 2 suka cika sai gdansu safwan.


Aunty tayi farin cikin ganinsu sai nan2 takeyi dasu bayan sun gaisa ancicci abinci hankali y kwanta daddy,Abba,daddyn safwan suka futa dan hotel xasu kama.


Islam tace Amira ku taso muje gerden sukace toh dukkansu harda kausar da tasleem suka tafi.


Wannan pages din *55 & 56* nakune murjanatu & hafsert.


Taku har kullum *sisin mama*


💘💘💘
*mrs hamisu taura*
💘💘💘
[11/12, 9:32 PM] ‪+234 803 841 7219‬: (12/11/2016 3:00pm) *na umma yahya musa*


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON KAKA*
*57*


Yaune xa'ayi karin girman kowa y hallara a hall din da xa'ayi sojoji kuwa kala2 sanye da kakinsu kamada sojojin ruwa sojojin sama d.s.


Su Aslam sanye suke cikin kakinsu na army sunyi bala'in yin kyau suna a kakkame bayan bayanai da jinjina da dada wa su Aslam karfin gwiwa akan haxakar da sukayi akaja hankalin sauran sojoji suma y kamata suyi koyi da irin haxakar da yan uwansu sukayi,anan aka fara rabon mukamai Aslam da safwan an basu matsayin captain masu igiya 3 a kafada,sai dai muyi fatan Allah y dada riko,anyi fareti kala2,an bawa canal yusuf safana matsayin general saboda horon da yayiwa yaranshi shine y basu kwarin gwiwa har sukayi nassara,anyi pic an rarraba kyautuka daganan taro y watse.


Washe gari su islam suka kamo hanya suka dawo gda kano ta dabo tumbin giwa.


Kowannen su office aka bashi aiki sukeyi tukuru kuma kowanne yana da yaran da yake horarwa a cikin barreck dinsu an bawa kowa gda mai dauke da katon palo 2 bed room akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login