Showing 57001 words to 60000 words out of 96677 words

Chapter 20 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

74063

akwai hakkokinta
akanka idan ka tauye mata Allah xai iya
tambayarka,siririn tsaki Aslam yaja yace ashe
mai wa'axi ka xama to ai kamata a samo maka
majalasi da loudspeaker kaka wa'axinnaka yafi
armashi,murmushi safwan yayi yace to naji
yanxu saika kaini nayi sallama da amarya tunda
kaga xuwa 5 xan tafi may be nida dawowa
garinnan sai kuma suna nan da 9 month,cikin jin
haushi Aslam yace god forbid ace nixan hada
jikina da banxar yarinyar i can't wlh,cikin mamaki
safwan yace uhm uhm dai kar nan gaba kaxo
kanamin karamar murya,murmushin gefen baki
Aslam yayi wanda har dimple dinshi y loba yace
wannan maganar taka shine babban kuskuren
daxan tafka a rayuwa ta duk ranar dana xo maka
da wannan maganar to ni Aslam na yadda kamin
duk abinda kaga dama,to in banda abinka me
xannema agurin yar tsakuwar nan ai sainaja
tamin rainin dayafi wanda tamin yanxu (nikuwa
nace anya Kuwa )dariya safwan yayi yace to naji
taso dai muje gdannaka Aslam yace wlh sai 4
xanbar gdannan in kaga xaka iya jira fyn in
baxaka iya jira ba ai ba dole,safwan yace to naji
masifaffe gira daya Aslam y dage yace au sai
yau ka sani sukayi dariya a tare daganan sukaci
gaba da magana akana cigaban da Aslam yake
samu a business din motoci da yakeyi,har safwan
yake cewa shima yanaso y fara,Aslam yace ai
hakan yana da kyau.
Su islam sai 2 suka kashe kidan sukayi
sallah,suna idarwa suka futa surrounding din
gdan flowers suka fara tsinka sai da suka cika
dan kwalin khausar,mai kula da flowers din
gdanne y gansu da saurinsa y karasa yana ku!
Ku!!Ku!!,wannan wanne irin iskancine su islam
ganin yadda y xaburo da sauri yanayi musu
tsawa shine y sakasu runtuma ana kare,karasowa
gurin flowers din yayi ganin irin ta'asar da sukayi
shine y saka shi yin tsaki,yace wadannan kannan
amaryar oga din daga ganinsu fitina xasuyi in
banda tsabar rashin ji yaushe anyi Abu domin
kawata gda amma suxo suna batawa,yayi kwafa
yace tabbas dana kamasu yau to bakaramin bugu
xanyi musu ba saboda yadda oga yakeson
flowers dinnan nasan xaiji dadi haka yaci gaba
da mita haryabar gurin.
Su islam kuwa suna shiga dakin sukace me
xasuyi inba dariya ba,dariya sukeyi ba
kakkautawa,islam ce ta tashi ta xura dankwalin
Amira acikin ta, ta tura cikin gaba take
kwaikwayon yadda kurtun sojan y ttumbulo ciki
lokacin daya gansu a gurin flowers dariya suka
dada tuntsirewa da ita daganan kuma suka fara
wasa da flowers din da suka tsinko,cikin 10
minute suka canjawa palon fasali,sukayi kaca2
dashi sun tunkuda center table din palon yayi
gefe sun cicciro pillows din kujerun sun
tarwatsasu a palon garin wasan jefe2,sai da
akayi kiran sallar la'asar sannan suka tashi a
wasan sukayi sallah,islam ce tace kuxo muje
mudan xagaya gdan haka suka fice bayan gdan
ta kofar kitchen sukabar palon kaca2 dan ba
abinda suka gyara.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
December 15, 2016 at 6:4
[3/7, 8:48 AM] ‪+234 703 962 5239‬: na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*86*
Cikin jin dadi suke kallan gdan can idansu yakai
wajen sweaming pool da sauri suka karasa (islam
nagani tayi wani tsalle ta fada ruwan da sauri na
xaro ido nace nashiga 3 harna bude baki da
niyyar ihun a kawo dauki kawai naganota tana iyo
tamkar kifi harwani tafiyar baya takeyi),cikin
tsantsan mamaki su khausar suka kallanta domin
basu taba xaton islam ta iya ruwa ba ita kuwa
cikin farin ciki taci gaba da wankanta sukuwa
xama sukayi a bakin sweaming pool din suka
xura kafarsu a ruwan sai da islam ta dauki kusan
10 minute sannan ta futo tana matse gashinta
daya jike,khausar ce tace islam dama kin iya
ruwa,dariya tayi tace sosai ma ai lokacin a kauye
har gasar tsere mukeyi dasu hanne a rafi,tayi
wani farr da ido tace kuma nice nake xuwa ta 1
don duk nafisu iya ruwa kuma in kunaso mukoma
in koya muku,xaro idanu sukayi sukace a'ah xoro
mukeji,tsaki tayi ta hararesu tace waya fada
muku in xa'a koyi Abu anasa tsoro a rai ai indai
xaku na saka tsoro a ranku baxaku taba iyawa
ba,Amira tace eh munji an fada miki kowa ne
irinki mai wasa da rayuwarsa dariya islam tayi da
gudu sukaga ta kwasa tayi cikin garden mara
mata baya sukayi,suna shiga da sauri tayi ta
kama bishiyar goba ta dare tamkar yar biriya
xama tayi akai tafara cin goba khausar ce tace
haba islam ki tsinko mana mana muma,cikin
masifa tace baxan tsinko ba nice nahana ku
hawowa kuma sai da taci guda 3 tana cillo musu
kwallayan sannan ta tsinko guda 10 ta jefo musu
tana wlh 3,3 xaku diba ku ajiyemin 4 ehe ta
sakko taraf naga ta haye bishiyar mangwaro
nace tofa.
Su Aslam bayan sun dawo daga sallar la'asar
dayake tun 3 sukayi lunch xuwa yayi part din
aunty amarya y dauko abincin daxai tafiwa dasu
islam yaje yayiwa mommy da kaka sallama suka
fice saboda yadda safwan ke axalxalarsa,tafiyar
15 minute takaisu gdan Aslam saboda yadda
Aslam din yake gudu yana xuwa gate man y
wangale gate yanayi masa sannu da xuwa,bayan
yayi packing motar sun futo da sauri mai kulada
flowers yaje yana fada masa irin ta'asar dasu
islam sukayi,cikin jin haushi Aslam yake tafiya
dan harya manta ba basket din abincin sai
safwanne y dauko,yana mamakin saurin fushi
irinna Aslam.
Turus Aslam y tsaya a bakin kofar palon ganin
irin yadda su islam suka canjawa palon
kamanni,a lokacin safwan y karaso ganin yadda
palon yayi kaca2 shine y saka shi yin dariya,yace
lallai kannan amarya sunyi aiki kamar yadda mai
kulada flowers yace kannan amarya ne guda 3
suka futo suka tsinki flowers,cikin jin haushi
Aslam yahau sama da gudu nemansu amma
kwata2 y duba bai gansufa,sai daya sakko y
sannan y duba dakunan kasa nan ma
basanan,shikuwa safwan sai dariya yake
masa,cikin jin haushin dariyar safwan yace dallah
malam ka damu mutane da dariya kamar wani
sabon kamu,dariya safwan y karayi yace nifa
bani nakar xomon ba,guku Aslam y rike yana
karewa palon kallo yama rasa ta ina xai fara
gyarawa,dariyar su islam y jiyo ta kitchen cikin
tsantsar mamaki yake kallan kitchen
din,hannayensu y gani dauke da mangwaro da
goba,islam tana kyalkyala dariya tana danma kun
samu nasan muku shine xaku raina wanine y
hanaku ku iya hawa bishiyar,tsilli2 sukayi da ido
sakamakon ganin Aslam da sukayi,kallansu yayi a
tsawace yace ubanwa y sakaku bata palonnan
haka bama wannan ba wane y baku ikon xuwa ku
tsinkemin flowers,shiru sukayi dukkansu,tsawa y
daka musu yace badaku nake ba,islam ce ta tura
baki gaba tace to nagama ko bamu tsinka ba
dole iska ta kadata ta fado,sai kuma ta
shagwabe fuska tana kallan cikin idanshi tana
kada idanuwan ta tamkar yar tsana tace Allah
hero karya yakeyi ba tsinka mukayi ba a kasa
muka debo,ta kalli su khausar tace ko 6*s cikin
rawar jiki sukace eh eh a kasa muka debo,Aslam
kuwa ji yayi jikinshi duk y mutu saboda yadda
idanuwan islam suka saukar masa da
kasala,safwan dayake a xaune yana jiran yaji
matakin da Aslam xai dauka kawai sai yaji yace.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:54 AM] ‪+234 703 962 5239‬: na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*87*
Safwan dayake xaune yana jira yaji wanne irin
mataki Aslam xai dauka kawai sai yaji yace,cikin
kasalalliyar murya to shikenan naji dama
safwanne xai tafi yace yanaso yaxo kuyi
sallama,amma bayan wannan y kamata ku gyara
palonnan,cikin tsantsar mamaki safwan yake
kallan Aslam a ranshi yace tabbas nan da 2
years islam xata ladabtar da Aslam,dariya safwan
yayi yace toh amaryarmu ni xan wuce,xumburo
baki gaba islam tayi tace nifa gaskiya ba
amaryarku bace,dariya safwan y karayi yace to
amaryar captain A.U sai munxo suna,cikin
masifa tace Allah y sauwake nifa ba xama xanyi
a gdannan ba xamana na temporary
ne,permanent yana gdan sagir,cikin jin hsushin
kalaman safwan da kuma abinda islam tace yasa
xuciyar Aslam xafi cikin hargowa y danko islam
lokacin idanuwansa har yayi ja yake banyi miki
warning akan karna karajin kinyi xancen
banxannan ba,buge hannunsa tayi tace wlh sagir
ba banxa bane kaje can kanemi banxan ka kwafa
yayi ganin kallan dasu Amira sukeyi masa y kalli
safwan yace tashi mu tafi,safwan y ciro 20k y
mikawa islam 10k y bawa su khausar ma 10k
yace su raba kowa yadauki 5k,godiya sukayi
masa suka fice.
Amira ce tace islam gaskiya abinda kikeyi sam2
bai kamata ba,kin daisan yanxu in kika yiwa yaya
rashin kunya to xunubi kike debarwa kanki,bama
wannan ba ai naxata yanxu y kamata ace kin
manta da yaya sagir saboda ke yanxu matar aure
ce,khausar tace gaskiya kuma kinsan annabi
yace *aljannar mata tana karkashin diga2 mijinta
idan tayi masa biyayya y daga mata ta wuce in
kuwa sabanin hakane to dama tasan inda
makomarta take* y kamata kidinga tunani saboda
kin sani kin karanta hakkokin miji akan mata
harda dadadan kalamai in tayi masa lada xata
samu,jikin islam ne yayi sanyi tace ngd da
tunatarwar ku 6*s insha Allah xan kiyaye,sai
kuma tayi rau2 da idanuwa xatayi kuka tace wlh
ko kadan banason hero saboda tun tashina bai
taba nunamin soba,ko laifi nayi da duka xai yimin
gyara,Amira ce tace kiyi hakuri a hankali xakiji
sonsa a ranki.
Su Aslam kuwa suna xuwa suka shiga
mota,dariya safwan yake yace abokina irin
wannan soyayyar da kake nunawa islam tana
birgeni,a gaskiya na dade banji lbrn masoya irin
kuba,kaga wani tsantsan kishin islam dana gani a
idanuwan ka,cikin jin haushin kalaman safwan
yace to wai innayi kishin ta haram ne naga dai
mata tace,dariya safwan yayi yace haka nakeso
abokina,gajiya Aslam yayi da surutan safwan y
kunna kira'ar sheik sudes cikin suratul maryam
yahau bi,ko xaiji saukin radadi da xugin da
xuciyarsa takeyi masa.
Gyaran palon su khausar suka fara,islam kuwa
takasa yin komai tunani kawai takeyi yanxu inta
mutu wuta kenan xata shiga,ganin batada amsar
tambayar ta yasa ta kalli su Amira tace 6*s bari
naje nayi wanka nacire jikakkun kayannan
nawa,sukace toh ta wuce stair.
A bandaki ma haka tayita tunane2 dakyar tasamu
tayo wanka ta dauro alwata,data futo mai
tashafa sai powder ta xixara kwalli sai lipstick ta
mulke jikinta da sihirtacciyar humra ta kara da
body spray,wardrop taje ta bude tadauko swiss
lace purple blouse & skirt saida ta busar da
gashinta da hand dryer ta mulkeshi da mai tuni
gashinnata yadauki shinning saka kayannata tayi
das naga sun xauna mata,kama gashinta tayi da
ribbons purple ta dada fesa turare takalmi ta
xura tafita a dakin,amma bata daura dan kwali
ba.
Lokacin data sauka su khausar harsun gama
gyaran palon abinci sukaci suna gamawa,aka
danna bell Amira ce taje ta bude isya ne yace su
akace yaxo y daukesu,komawa palon tayi
tafadawa khausar anzo daukarsu,jin haka islam
tayi rau2 da ido xatayi kuka dakyar suka lallabata
ta hakura sukace gobe xasu dawo.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:55 AM] ‪+234 703 962 5239‬: a umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*88*
Yau islam kwananta 7 a gdan Aslam amma ko
yaushe cikin fada suke domin mai hali baya fasa
halinsa,saboda shi Aslam yana ganin islam bata
isa tace xata raina shiba,ita kuma koya y fada
mata cuta saita fada masa mutuwa,kullum kuma
su Amira ne suke kawo musu abincin break fast
lunch Aslam y taho dashi dinner kuma isya ya
kawo musu.
Yauma su Amira ne suka kawo break fast,bayan
Aslam y futo sun gaisheshi yayi break Amira ce
tace yaya daddy yace nafada maka wai yau
dukkansu sun tafi gwarxo bb na tsauni ne bashi
da lfy sukaje gaishe shi,yace OK Allah y bashi
lfy,futa yayi y wuce gdan abokanan sa sukuwa
suka fara wasa.
Da misalin 2 o'clock islam tace kuxo muje muyi
girki tunda yau baxa'a kawo mana ba,khausar
tace nidai ban iya girki ba saboda ko a gda
mammy da masu aikine sukeyi,Amira tace wlh
nima ban iyaba,tsaki islam tayi tace a haka
xamuyi ta xama ne baxamu iya ba ni wlh yunwa
nakeji in baxaku xo muje mudafa ba inna dafa ni
kadai xanci,tashi sukayi suka shiga kitchen din
gas cooker suka kunna aka daura ruwan shinkafa
daya tafasa kamar gaske aka debo shinkafa aka
wanke aka xuba dadi duk y ishesu yau suna girki
(nikuwa nace lallai yau manya suna aiki) sannan
aka dora tukunyar miya a dayan gas din dayake
mai 4 ne,kaxa nagani an dakko a deep frizer an
yayyankata aka wanke aka xuba a tukunyar aka
dauko kayan miya nan ma aka xuba aka saka mai
aka barbare maggi duk aka xuba an xuba maggi
cube yakusa 30 sannan aka saka gishiri 1 spoon
har xa'a kara islam tace a barshi haka in an
gama anji gishirin bai isaba a kara dora tukunyar
akayi a wuta,kitchen din kuwa yayi kaca2 dan
komai aka dauko akayi amfani dashi to anan ake
barinsa xama sukayi aka fara musu wannan tana
tafiyin kokari a girkin wannan tana tafita,kansu
ankara sukaji shinkafa ta fara kauri da sauri suka
tashi sukaje suka kashe,bude tukunyar shinkafar
sukayi suka ganta wani batso2 alamar bata dahu
ba,khausar ce tace shinkafar ma ai bata dahu
ba,dariya islam tayi tace ke dahuwar turawa
ce,dariya suka tuntsire da ita gaba dayansu suna
ihu suna eh kuwa,food flask suka dauko suka
juye shinkafar kuwa in banda kauri babu abinda
takeyi,miyar suka bude sukaga takusa dahuwa
Amira ce ta dafa kai tace af mun manta ba'asa
albasa ba islam tace aikuwa da gudu suka shiga
store suka debo albasa manya guda 5 suka bare
cikin sauri suka raba kowacce 4 peaces suka
wanke suka xuba,baifi 5 minute da xubawa ba
sukaji miyar na kamawa da sauri suka dauko
corry da thyme roba daya2 suka juyesu a miyar
ko minti 1 baiyi ba suka kashe gas din miyar ma
juyeta sukayi a flask islam ce takai abincin kan
dining ta koma suka fara gyara kitchen din.
Suna cikin gyaran kitchen Aslam y dawo,tunda y
shigo palon yakejin kauri da sauri yayi kitchen
ganin sana aiki yasaka shi tambayar su
mesukeyi,islam ce tayi magana tace girki
mukayi,murmushi yayi yace kun kyauta y tafi palo
y xauna,sai da suka gama gyaran kitchen din
sannan suka futo,direct dining area suka
tafi,islam ce tace yaya aslam kai baxaka
ciba,tasowa yayi yace ina tsoro cin jagwalgwalo
ne murmushi islam tayi hade dayin farr da ido
tace aikuwa yayi dadi,don in kaci abincinnan
kunnanka sai y Mora,murmushi y karayi lokacin
yayi dai2 da karasawar Aslam dining area islam
da kanta taja masa kujera,saboda yau jinta takeyi
a farin ciki ta sauke hakkin Aslam dayake
kanta,dakanta tayi serving dinshi shidai kallan
abincin kawai yakeyi saboda yadda yake wani
kanshi mara dadi,shahada kawai yayi yayi
bismillah ya debo abincin a spoon yakai bakin
shi,lokaci daya yaji wani dandano mara dadi
hade da karni y gauraye masa baki furxo da
abincin daga bakinsa cikin tsoro su islam suka
dago kai suna kallansa.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:56 AM] ‪+234 703 962 5239‬: na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*89*
Islam ce ta kwantar da murya kamar mai shirin
yin kuka tace,abincinne baiyi dadi ba,wani kallo y
jefeta dashi data kasa fassara me yake nufi,tsam
y tashi y haura stair direct dakinshi y wuce brush
da maclean y daura y dinga wanke bakinshi,sai
da yaji y dainajin dandanon abincin a bakinshi
sannan y daina,tsaki yayi sai yanxu ma yake
ganin wautarshi yama za'ayi yaci abincin
kaxaman yarannan wani murmushi ne y kufce
mishi da sauri y futo daga dakin yayi down stair.
Tarar dasu yayi kowa da abinci a gaba yana
juyawa y kasashi,murmushi yayi yace a'ah yan
matan kakan ya naga kun tasa abinci a gaba kun
kasa ci,islam ce cikin jin haushi tace abincinne
kwata2 baiyi dadi ba dariya yayi yace koh to ku
jirani kitchen y wuce y dauko katon try y futo
juye abincin yayi acikin try din harda wanda suka
xuba a plate ya dauka yace ku taso ku biyoni
table mat y shinfida akan center carpet yace oya
bismillah maxa kafin na kirga 3 ku faracin
abincinnan,xaro idanu sukayi suka hada baki
sukace me yaya,yace abinda kunnuwanku y jiye
muku,da ubanwa y saka baku iyayin abinci ba ku
dafa dan haka wlh sai kunci,islam ce tace Allah
innaci abincinnan amai xanyi daga kafadanshi
yayi y karasa jikin fridge y bude y dauko lemon
shani na gwangwani y balle yace wlh ko xaki
amayar da hanjin cikinki sai kinci abincinnan,y
karasa yace start mana kuka tsaya kallona ganin
sunki xama shine y sakashi dire lemonnashi akan
center table ya hade rai tamkar bai taba dariya
ba,cikin wata irin kakkaurar murya data xoratasu
yayi magana yace baxaku cibane sai jikin ku y
fada muku baxan dauki asara axubar da wannan
abincin ba belt dinshi y fara kokarin cirewa da
gudu suka xauna suka faraci ganin sun faracin
abincin shine y sakashi murmushi a xuciyar sa
yace wannan hukunci shine daidai daku komawa
yayi y xauna akan kujera ya dauki lemonsa yana
sha cikin jin dadi y dauki remote y kunna t.v.
Su islam abincinnan sukeci tuni suka fara
hawaye harda majina saboda yadda daddanon
abincin yake rikita musu ciki,Aslam kuwa ko
digon tausayin su baiji ba lemonsa ma yakesha
yana kada kansa saboda selection din dasu islam
suka saka yake kallo,su islam har sunci rabin
plate din tuni kukan da sukeyi na xuciya y fara
futowa kallan try din yayi yaga sunci
rabi,murmushin jin dadi Aslam yayi yace y
bakwacin naman da sauri suka dauki naman
suka faraci,tsananin karnin namanne y saka
xuciyarsu tashi da kudu suka tashi bedroom din
kasa suka shiga,basu tsaya a ko ina ba sai a
bathroom tuni suka fara sheka amai tamkar xasu
amayar da yayan jikinsu dakyar amannan y tsaya
ammafa duk sun galabai ta kuskure bakunansu
sukayi suka futo,kan gadon dakin suka baje suna
mai da numfashi.
Kausar ce tace gaskiya yaya Aslam bashi da
tausayi,islam ce tayi tsaki tace ku sai yau kuka
sani,Amira ce ta nuna islam tace eh amma ai duk
ke kika jamana,cikin masifa islam tace danayi
uban me,tsaki Amira tayi tace wanene y sakamu
dole sai munyi girkin,murmushi islam tayi tace
naji kuyi hakuri,sai kuma tace kunsan Allah
baxaici bilis ba wlh saina rama mana wahalar da
mukasha,cikin jin dadin abinda islam tace
khausar tace me xakiyi masa,dariya islam tayi
tace haryanxu tunani nakeyi amma ayau xan
rama baxqi kai gobe ba kunsanni bana
yafiya,khausar tace gaskiyane,itakuwa Amira
gani takeyi islam karya takeyi ba wani rama
musu da xatayi.
*tofa ko wanne irin hukunci islam xata yanke dan
ramuwa oho kudaici gaba da biyoni danjin yadda
xata kaya*
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:57 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*90*
Da misalin 7:30 o'clock Aslam ne a kitchen yana
girki hadaddiyar jellop rice yake dafawa datasha
vegetables sannan yayi pepper soup na kifi
tarwada,islam da take xaune a kan kujera sai
binsa takeyi da idanu,Aslam sai da y tabbarar y
gama hada abincin y juye su a warmers tuni gda
y dauki daddadan kanshi,kallan islam yayi y
harareta yace oya dauki kikai min kan dinning
murmushi tayi masa tace toh sai daya tabbatar
daya gyara kitchen din tas sannan y futo,kallan
islam yayi yace jirani naxo nayi wanka sai muci
abincin tunda ke kinyi toh kawai tace masa.
Islam tana ganin Aslam yahau sama da gudu ta
tafi kitchen container din gishiri ta dauko har
xata xuba acikin abincin sai kuma tayi tsaki tace
gaskiya inna xuba gishirinnan xai gane,kuma ni
kaina xanwa kaina bakin cikin cin abincinnan dan
da alamu yadda y dumame gdannan da kanshi ba
karamin dadi xaiyi ba,tsaki tayi ta koma ta mayar
da gishirin,futowa tayi ta rafka uban tagumi ta
saka wannan taga baiyi ba tasaka wancan har
Aslam y sakko y xauna batasan y sauko ba,tafi
yayi mata a fuska firgigit tadawo daga tunanin
data tafi,yatsina fuska yayi yace tunanin me
kikeyi sai dataja numfashi tace kaka nakeson
gani ta karashe maganar tamkar xatayi
kuka,janyo plate yayi y fara xuba abincin yace
kibari gobe na kaiki tunda yanxu dare yayi dariya
tayi tace Allah y kaimu.
Aslam ne y faracin abincin da alamu abincin yayi
masa dadi ganin yadda yake lumshe ido,har islam
ta janyo plate xata xuba abincin sai kuma ta fasa
murmushi tayi a ranta tace alhmdllh idea taxo
kura masa ido tayi Aslam yaci abincin rabin plate
y janyo flask din pepper soup y xuba y faraci
anan y lura islam bataci abincin ba,dago
lumsassun idanuwan sa yayi y saukesu akan
islam yace y bakiji abincin ba,murmushi tayi tace
y xa'ayi naci abincin danasa dakakken kyankyaso
aciki,cikin tsoro Aslam y xaro idanuwansa yace
what,murmushi tayi ta kada idanta tace
kyankyaso nace nasan xaka iya kin yadda amma
nidai nasan nasaka lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login