Showing 21001 words to 24000 words out of 96677 words

Chapter 8 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

74039

xauna a kujera kallan ihsan yayi yace kawomin ruwa fridge taje ta dauko masa ta doro a try da cup,ta kawo masa kallan aunty amarya yayi yace Aslam fa bashi da lafiya a kidime aunty amarya tace me yake damunsa,cikin tsantsan tausayi yace wlh y futo xaije masallaci ya fadi shine yayi tsagewar gashi amma baba mai gadi y gyara masa cikin tashin hankali aunty amarya ta mike tace bari naje na dubo jikinnasa,Amir yace yayi bacci shiyasa na futo komawa aunty amarya tayi ta xauna jikinta duk a sabile.


Tashi tayi tace bari naje na fadawa mommy kai tashi kaje ka fadawa hajiya (kaka) saika wuce dakinnasa,yace toh a tare suka futa aunty amarya ta wuce part din mommy Amir kuma y wuce na kaka.


Aunty amarya ce ta shiga part din mommy xaune ta tarar da ita a palo khausar tana kan cinyarta xama aunty amarya tayi,mommy ta kalleta tace auntyn yara yana ganki wani sukuku kamar wani abinna damunki,aunty amarya ce tace wlh my son ne y fadi shine yayi tsagewar kashi a kafa,murmushi mommy tayi tace shine duk kika damu haka kin manta shi yanxu solder ne kilama karaje yayi irinnasu na sojoji y gabje kafar,aunty amarya tace ba haka bane,mommy tace toh Allah y sauwake anjima naje na dubashi,aunty amarya ce ta tashi tace dama nasan baxaki damu ba ni natafi duba my son dina kuma dana sani da banxo na fada miki ba ta kama hanya ta fice murmushi mommy tayi tace khausar tashi muje mu dubashi kinga aunty tayi fushi suka tashi.


Amir kuwa da yaje y fadawa kaka cikin kidima ta tashi tayo waje ta nufi part dinsu Aslam,Amira ta kalli islam tace yanxu 6ter kin kyauta abinda kikayi masa yanxu gashi kinja masa jinya,tashi Amira tayi ta daga kafada tace so what Ashe ba dadi mu yayi mana ai gwanda yaji a jikinsa kuma ko kifada kice nina saka masa ruwan karkashi ko karki fada ni da kaina xan fada masa ta shige daki,girgixa kai Amira tayi ta fice tabi bayan kaka islam kuwa daki ta shige ta fada gado tana tsalle (nikuwa nace islam ba tausayi 😏).


Wannan page dinnaku ne number *35* *&* *36* *Amira* *Aliyu* *&* *Aunty* *Zee* *ngd da nuna kaunar ku akan buk dinnan😊


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs* *hamisu* *taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:01 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (25/10/2016 3:00pm) *na* *umma* *yahya* *musa*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*37*
Dukkansu sunyi jugum2,Aslam kuwa baccinsa yakeyi cikin kwanciyar hankali,mommy ce ta kalli aunty amarya tace auntyn yara tunda bacci yakeyi ni bari natafi Allah y kara sauki,anjima inya farka nadawo na duba jikinnasa,ameen aunty amarya kawai tace ko kallan mommy batayi ba saboda fushi takeyi da mommy bata nuna kulawa akan my son dinta wai kunyar dan fari😏.


Aunty amarya ma tashi tayi tace bari naje nayi masa pepper soup kafin y farka nasan xaifi jin dadinsa ta futa,kaka ta kalli Amir tace wai garin yaya hakan ta farune,Amir yace nidai yacemin y futo xai tafi masallaci yayi sufa y fadi a bakin kofa kaka tace ikon Allah to ko ruwa aka xubar a gurin,Amir yace a'ah kawai tsautsayine.


Aslam kuwa bai farka ba sai 5:00 o'clock da salati ya tashi sannan yayi addu'ar tashi a bacci y bude idonsa karasowa sukayi dukkansu sunayi masa sannu da jiki,yace da sauki yatsina fuska yayi aunty amarya tace ya akayi,yace wlh jikina ke ciwo tace ai dole sannu yace yauwa.


Bowl Amir y dauko da brush da ruwa a buta Aslam y wanke bakinshi saboda baxai iya tashi ba shiwo a idon sahu sai anyi taka tsan2 dashi bayan y wanke bakinshi aunty amarya ta hada masa tea mai kauri da pepper soup din kayan ciki da yasha kayan kanshi da tafarnuwa sai kamshi yakeyi,bayan y gamaci y daura alwala y tada sallah danko axahar baiyi ba.


Su kaka kuwa da sukaga jikinnasa da sauki sai suka tashi suka futa,side dinsu suka wuce daki Amira ta wuce ganin bata ga islam a palo ba,kwance ta ganota tayi dai2 akan gado tanata sharar baccinta,Amira ce tayi tsaki ta matsa gaban gadon ta daidaici cinyar islam ta daka mata duka firgigit islam ta mike tana mitsitstika ido ganin wanda taimata wannan danyan aikin shiya ta dakawa Amira wata muguwar harara cikin hayayyakowa ta fara mata masifa wannan wanne irin wulakancine xaki tasheni ina cikin baccina mai daki,Amira ma harararta tayi tace natasa din ai dole kiyi bacci tunda kin aikata mugun kudirinki kin tashi hankalin kowa shine ke harkin samu damar bacci tayi tsaki ta shige bandaki.


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs* *hamisu* *taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:01 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (25/10/2016 3:30pm) *na* *umma* *yahya* *musa*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*38*
Tsaki islam tayi tayi sabon juyi ganin Amira ta futo ta shimfida sallaya shiya sa tagane anyi la'asar itama ta shiga bathroom din ta dauro alwala ta futo ta tada sallah.


Yau kwanan Aslam 2 a kwance in xai shiga toilet sai y daddafa haidar da Amir,amma islam koda wasa bata taba xuwa dubashi ba,haka Amira ma ta daina kulata da islam tanayi mata magana taga Amira din tana shareta shine ta futa harkarta.


Su islam ne suketa shiri yau xasu tafi gwarxo hutu itada kaka,Amira harda khausar xasu tafi da sauri islam ta tafi side dinsu Aslam saboda yau ta gudiri niyyar fadawa Aslam itace tasa masa karkashi y taka y subale yaji ciwo,kamar gaske ta shiga dakinnasa a kwance ta ganshi kuma shi kadai wani farin ciki taji y ratsata karasawa tayi ta xauna kusa a kujera daya ta dora kafarta daya kan daya tana wani yatsina fuska.


Kallanta yayi y hade rai kamar yaga wani abokin gaba yace ubanme kikaxo yimin a daki yau kwana 2 dajin ciwona bakixo dubani ba sai yau dan munafirci,wani murmushi tayi da ita tasan ma'anarsa ta tashi tsaye tace calm down dan gurgu a xabure y kalleta y maimaita dan gurgu,kashe ido daya tayi tace yes πŸ˜‰,yanxu ma ba sannu naxoyi maka ba xuwa nayi na fada maka wata magana mai matukar muhimmaci kaga ciwonnan na kafarka ta nuna kanta tace nicenan silarshi saboda nina saka maka ruwan karkashi ka taga ka subale tayi wata dariya tace a gabana komai y faru,ta tsareshi da idanunta irinna masu jin bacci tace kasan dalilin dayasa,sororo y tsaya kallanta tace dalilin shine ka sakamu kamun kunne alhalin bamuyi maka komai ba shiyasa nadan gwada maka nima kadan daga cikin irin axabobin dana tanadarwa mugu irinka ta wani kalleshi shekeke tayi tsaki ta tofar da yawu ta fice,tana shirin fita amir y shigo yace kefa suke jira tace toh dama yaya naxo naduba ta juya tace yaya muntafi saimun dawo.


Shikuwa Aslam mamaki yake a ranshi yana lallai ko wacce mace da makircinta aka haifeta tuni idonshi yayi ja jijiyoyin kanshi duk suka tashi gashin jikinshi y miki ya fara tattauna lebensa,(nikuwa nace ran maxa y baci bari nagudu karnaje allurarsa ce ta motsa y gwabgwabjeni nafice a 360 πŸƒπŸΌ).


Islam kuwa tana xuwa tashiga mota kaka ta kalleta tace munafircin banxa dakin damu da Aslam din tunda yaji ciwon bakije kin dubashi ba sai yau xumbura baki islam tayi tace toh laifine lokacin baba mai gadi y wangale musu gate suka fice.


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs* *hamisu* *taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:01 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (27/10/2016 1:00pm) *na* *umma* *yahya* *musa*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*39*
Aslam kuwa ranshine yake xafi yace lallaima yarinyar nan wlh yau bada ban ina xaune ba da inna fara babballaki sai kinyi dana sanin abinda kika aikatamin duk a ranshi yayi wannan maganar.


Wata kara ya saki yahau yayyamutsa gashin kansa da sauri Amir y ajiye laptop din kan cinyarsa y matsa kusa dashi yana menene Aslam meyake damunka,banxa Aslam yayi masa idanuwansa sunyi jajahur saboda tsabar bacin rai duk da Amir baisan abinda y batawa dan'uwannasa rai ba haka y dinga lallashinsa yana fada masa maganganu masu dadi yace kadinga fadar *innalillahi* *wa* *inna* *ilaihirraji'un* insha allahu duk wata damuwar da kake ciki xata yaye,a hankali y fara fada sai yaji xuciyarsa tanayi masa sanyi haryaji kashi 70% daga cikin 100% na damuwarsa y ragu a hankali y koma y sulale y kwanta akan pillow bacci yakeson yi amma sam y kasayi.


Su islam sun isa gwarxo cikin farin ciki da ko xama basuyi ba ta kwashi su khausar suxo suje gidansu hanne kallan garin takeyi saboda yan canje2 da aka samu.


Da sallamarsu suka shiga gdan hanne ce xaune mahaifiyarta tanayi mata magana akan taje ta debo mata ruwa a rafi amma idan ta kwaso wani uban tsalle ta dire sai tace yasin baxata ba,kara uwarta dauko xata buga mata tasaka ihu kenan xata futa tajiyo sallamar kawarta wadda baxata taba mantawa da muryarta ba da gudu ta tafi ta rungume islam suka hau ihun murna.


Su Amira ne suka karasa suka gaida mmn hanne,ta amsa cikin farin ciki,hanne kuwa dakyar ta saki islam suka karasa itama ta gaida innar (inna kuwa farin ciki takeyi tana ganin kamar islam ta shiryu a ranta tana nima Allah ka shiryamin tawa diyar) innar hanne tace baxakixo kije ki dibomin ruwan ba na daura sanwa da sauri hanne taje ta dauki tulun saboda farin cikin tagasu islam,islam ta kalli su Amira tace kuxo muje rafi sukace toh suka tashi suka futa innar hanne tana maimakon ku tsayata ta dawo aiko saurararta basuyi ba suka fice.


A kofar gda sukayi kicibis dasu yusufa akace musu su islam sunxo shine suka biyota tare suka rankaya suka tafi rafin.


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs* *hamisu* *taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:02 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (27/10/2016 1:30pm) *na* *umma* *yahya* *musa*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*40*
Sai da suka share awa 2 churr a rafi sannan suka kawowa inna ruwanta a lokacin inna harta gaji ta aika almajiri y debo mata,lokacin inna tana daki hanne ta kwala mata kira tace inna ga ruwannan suka koma da gudu.


Islam ce tace kuxo muje gonar malam tanimu hanne tace kai aini rabona da gonarsa tun lokacin da mai gari yayi mana iyaka da ita murmushi islam tayi tace yanxu ma ba sato masa xamuyi ba da kanshi xai bamu,hanne ta kama haba tace malam tanimun tab Ashe kin mance matsiyaciyar rowarsa a haka har suka karasa.


Da sallama su islam suka karasa kaban malam tanimu suka gaisheshi a daddakile y amsa saboda tsaf y ganesu,islam ce tayi gyaran murya tace dama babana ne y bani kaya da yawa yace innaxo nan kauye na rabar to saina ga kai kadai y dace nabawa saboda irin barnan da mukayi maka shine danakai kayan gidanka akace kana lambunka shine naxo na gaisheka kuma nafada maka.


Tuni malam tanimu y washe jajayen hakoransa yace nagode sosai yar albarka kamar kuwa kinsan bikine dani gobe ainasan duk kauyennan ba wanda xai kaini hadewa saboda kayan yan birni daban suke dana yan kauye murmushi islam tayi tace toni natafi da sauri yace tsaya2 y koma cikin lambunsa y ciwo mata katuwar leda dasu mangwaro kashu goba kai harda fasa dabur sannan y ciro dari 2 y bata yace ki gaida kakar taki sainaxo godiya toh islam tace tayi godiya ta tafi dakyar take daga ledar saboda yawan kayan.


Can gurinda su hanne suka buya ta karasa da mamaki suke kallanta,dariya tayi tace kun kasa magana sai kallo to ku tsaya kuji ta yadda y bani kayannan anan ta labarta musu yadda sukayi da tanimu,dariya su hanne suka kwashe da ita su kace lallai malam tanimu garane da har xaki iyayi mai wayo,islam tace kunga har 200 y bani kuxo muje muci kifin sale mai kifi suka tafi yusufa y dauki ledar,su Amira kuwa duk mamaki y ishesu da abinda islam tayi.


Bayan sun sayi kifin sunci islam tabawa su hanne komai bibbiyu ba yadda suka iya haka suka karba dan sunsan bala'in Islam.


Suna xuwa gda kaka tahau fada akan sun tafi yawo islam ta xumbura baki tace to waike kakannan mutum baxaije yaga gariba,kaka tace saiku karata ai ganinsu da katuwar leda cike da fruit shiya bawa kaka mamaki tace yanxu islam daga xuwanmu har xaki fara debo mana magana,islam tace kai kuji kakannan batasan y akayi ba amma xata faramin sharri,kaka tace uwar sharri da uban sharri xan miki nidai nasan ko karan haukane y ciji tanimu baxai baki kayannan ba,islam tace toh kuma sai aka samu akasi tunaninki baiyi daidaiba shiya bani,sallamar tanimu suka jiyo a kofa kaka ta dauki mayafi sukuwa suka bushe da dariya.


πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*mrs* *hamisu* *taura*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
[11/12, 9:02 PM] β€ͺ+234 703 443 5155‬: (31/10/2016 1:00pm) *na* *umma* *yahya* *musa*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’
*GOYON* *KAKA*
*41*
Kaka tayi tsaki tace ku kuka sani ta fice malam tanimu ta gani a xauren yana ganinta cikin girmamawa y durkusa yana hajiya brk da yamma bakinnan nashi a washe tamkar gonar auduga,cikin mamaki kaka tare brkn mudai,yace dftn kin wuni lfy,tace lfy qlau,yace y kuka baro su alhjn dftn kunxo lfy,cikin xakuwa kaka tace lfy dan duk ta damu taji dalilin daya saka tanimu yake jero mata gaisuwarnan,yadanyi gyaran murya yace dama ina xaune bakin gdan gonata ne islam tace ta sameni ta fadamin abin arxiki shine nace toh baxanyi kasa a gwiwa ba sai naxo nayi godiya,kaka ta kalli tanimu tace wai wanne abune y faru,ya danyi murmushi yace kaya da mahaifinta y bata ta kawowa yan kauye aini ta kaiwa,dariya ce taso kufcewa kaka tace toh ikon Allah gaskiya ni bansan da wannan xancen ba amma kaje gdan ka gani,malam tanimu y tashi jiki duk a sanyaye yace ikon Allah to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login