Showing 69001 words to 72000 words out of 96677 words

Chapter 24 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

74067

ba,aunty amarya ce
ta kalli amir tace dauko mota mu bisu dauko
mota yayi suka futa suma da yake sunsan
asibitin da file din yan gdan yake can xa'akai
islam.
Abba kuwa lokacin dasu suka isa asibiti ko dai2
ta packing baiyi ba y futo a motar cikin sauri
shida daddy ne suka shiga cikin asibitin dayake
private hospital ne tuni nurse 2 suka taho da
gadon marasa lafiya suka saka islam akai suka
gangara da ita emergency.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 9:36 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*108*
Taimakon gaggawa nurse din suka fara
bata,amma har xuwa time din islam bata farfado
ba dalikin firgicin da tayi sunyi iya yinsu amma
ina Abu y gagara wata nurse ce ta futo a
emergency din da sauri kaka tasha gabanta tace
likita y jikin jikar tawa tana goge kwallah,lokacin
yayi dai2 da karasowar su aunty amarya,nurse
din tacewa kaka ki kwantar da hankalinki hajiya
munayin iya bakin kokarin mu yanxu haka ankira
dr din daxai karbi duty 8:00am yanxu saboda
yanayin ciwon nata kinga yanxu 6:45am ma kaka
ta share hawaye tana jan hanci tace kuma xaixo
kina gani nurse din tace eh hajiya gaskiya shi
bashida wulakanci irinna sauran doctors yana da
kirki sosai bata karasa magana ba sai gashinan
dr din y shigo sanye da jallabiyya brown colour
tayi masifar yi masa kyau saboda kyakykyawa ne
dr din ajin farko gashi fari tas yanayinsa dai
tamkar balarabe,da sauri yaxo yayiwa su daddy
sallama y shige dakin da islam take,nurse dinnan
tace yauwa kunga harya karaso ma bari nayi
sauri naje na dauko abin da nafito danshi na
koma ta wuce su kaka da suke jugum2 saboda
basusan halin da islam take cikiba.
Dr dinne cikin fada2 y fara yiwa nurses din
masifa yana y xakuna yin abu tamkar bakusan
kan aikin kuba,cikin tsoro sukace sorry sir(dr
samir yana da xafi musamman in y kula da yadda
nurses suke bada rashin kulawa akan pacient to
yanxu xai hausu da fada ba kakkautawa),kallansu
yayi yace treatment din daya kamata ku fara
bata shine ku samu ta farfado anma kun tsaya
kuna shirme yadanyi tsaki,cikin gaggawa da
kwarewa y fara aikinsa bai dauki 5 minutes ba
islam ta farfado,tana bude idanuwanta ta dorasu
akan dr sameer da sauri ta runtse idanuwanta
hade da dafe mararta tana wayyo Allah cikina
xan mutu gane menene yake damunta da sauri y
hada wata allura ta pain reliever y xugeta a sirinji
hade da anasizia y matsa kusa da islam yace ki
gyara nayi miki allurar da xata rage miki radadin
ciwon da kijeji.
Islam duk da tana cikin axaba hakan bai hanata
ware idanuwanta hade da xaxxaro su cikin kuka
hawaye na xuba a idanuwanta tsantsan firgici da
tsoro dr sameer y gano a idanuwan islam,cikin
shagwaba tace plz dr karkamin allura tsoronta
nakeyi ta karashe maganar da fashewa da
kuka,wani mugun tausayinta yaji saboda ko bata
fada ba shi y gano tsoron allura miraran akan
fuskar islam amma yayi murmushi yace kiyi
hakuri ki yadda nayi miki,su kuwa nurses da yake
ba sabon abu bane a gurinsu suka dr sameer
yana lallaba pacient dinsa balle wannan da
sukaga yarinya ce sam basu damuba,islam ganin
da gaske yake allurar xaiyi mata shine y sakata
fara kokarin saukowa daga gadon dukkuwa da
irin ciwon da marar tata takeyi mata dan islam ta
kwammace ta dawwama acikin ciwonta da ace
xa'ayi mata allura,kula da dr sameer yayi tana
kokarin sauka a gadon shine y sakashi cewa
nurses din yace su rike masa ita,rirrike ta sukayi
islam kuwa me takeyi inba kuka ba lokacin da dr
sameer yayi mata allurar wata gigitacciyar kara
ta saki harta firgita nurses din suna shirin cikata
y daka musu tsawa yace ku riketa mana saura 1
da sauri suka riketa y karayi mata a hankali bacci
y fara daukarta,canular y saka mata y jona mata
drip y kalli nurses din yace ku kaita daki shikuma
y futo.
Su Abba sunyi cirko2 a bakin dakin saboda
lokacin da islam tayi kara suma sunjita dr sameer
y futo,daddy ne cikin sauri yace dr meya faru
munji tayi ihu,murmushi dr sameer yayi wanda y
kara masa kyau yace bkmai allura xanyi mata
shine tayi karannan amma karku damu jan
numfashi daddy yayi,dr sameer y duba agogonsa
yaga 7:30am yace dan Allah kuyi hakuri naje gda
nayo wanka nadawo sai nayi muku bayanin
abinda ke damunta godiya sukayi mishi y wuce y
shiga mota,lokacin aka gangaro da islam akan
gado tana bacci xuwa daki.
Sai 8:00am islam ta farka sai taji ciwon marar
tata yayi sauki sosai lokacin data bude
idanuwantab iyayenta duk ta gani a gaban
gadon,kokarin tashi tayi mommy ce da sauri ta
karasa ta tasheta sannu suketa jera mata tana
amsawa,mommy ce ta kula islam duk tayi
staining din xanin gadon jan hannun amir tayi
suka futa tace kaje gda ka daukowa islam
kaya,kuma ka suyomin paf,amir yace toh amma
kuda Amira xakuje ta kalli amira tace ki dauko
mata panties dinta toh Amira tace suka tafi.
Dawowa dakin mommy tayi ta kalli su daddy
dasu aunty amarya tace kudan bamu guri xanyi
magana da yata futa sukayi mommy ta shiga
bathroom ta hada wa islam ruwan wanka sannan
ta futo ta kama hannun islam ta sakko da ita
daga gadon tace maxa jekiyi wanka saurin cire
bedsheet din tayi ta canja wani,islam kuwa data
shiga bathroom wanka kayanta ta cire lokacin
data cire pant taga duk jini a jiki durkushewa tayi
tace wayyo mommy na mutu.
*Dan Allah kuyi hakuri da rashin ganin posting
dina kwana 2 hakan y farune dalilin wani uxiri
daya tasomi amma insha Allah yanxu xakuna
ganin posting dina kullum na yauma xaku ganshi
kadan kuyi hakuri*
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 9:37 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*109*
Da gudu mommy ta karasa cikin bathroom din
islam ta gani a durkushe tana sheshshekar
kuka,mommy ce ta dagata ta bata towel ta daura
sannan tace haba my daughter wlh kinyi mugun
tsoratani natsata wani abinne y sameki,cikin
gunjin kuka ta fara magana har numfashinta
nayin up & down tace mommy tun a gda nake ta
bleeding bayannayi mafarki wai hero uhm uhm
sai kuma ta kasa magana,tace mommy ina
tsoron ko ciki na samu saita dada barkewa da
kuka,murmushi mommy tayi saboda ta gane mai
islam take nufi tace kiyi shiru ki daina kuka,islam
tace mommy y xakice na daina kuka bayan jinina
yana ta xubewa xai kare,mommy tace kiyi wanka
ki futo xanyi miki bayani to fice islam kuma ta
cire towel ta fara wanka amma sai kuka takeyi
saboda ganin tana fitsarin jini (nikuwa nace
watako islam batasan girma ne y kamata ba ).
Mommy bayan ta futo a bathroom din knocking
din dakin akayi taje ta bude Amira tagani rike da
leda karba tayi ta koma dakin ciro pad 1 tayi
tasaka ajikin pant ta ajiye,after 10 minutes islam
ta futo tana tafiya a hankali tanata harhade kafa
tamkar wadda kwai y fashewa aciki idanuwanta
kuwa sai tsiyayar da kwalla yakeyi mommy ce
tamika mata pant tace ungo maxa ki saka karba
tayi tana kallan wandan tace mommy a haka
xansa,hararar wasa mommy tayi mata tace Allah
islam kin fiya shirme kisa mana,hawayen daya
xubo mata ta goge tasa pant din,bakin gado ta
xauna ta shafa mai doguwar riga ta atamfa ta
saka lemon green da kwalliyar pink ba karamin
kyau tayi mata ba dukkuwa da yar ramar da
fuskarta tayi mommy ce ta kira sunanta tace
islam.
Cikin nutsuwa islam ta amsa tace na'am mommy
kanta mamakin islam takeyi saboda yadda taga
duk ta nutsu,tace inaso ki bani hankalinki sosai
kinga wannan jinin da kike gani ba jinin jiinki
bane har kike tunani wai xaki mutu,islam
rinannun idanuwanta ta dago ta daurasu akan
mommy da alamar tambaya a fuskarta mommy
tace eh wannan jini shi ake kira da jinin
haila,wata muguwar kunya islam taji ta rufeta
hannunta ta saka ta rufe fuskarta dariya mommy
tayi tace naji ja'irar kaya yanxu kuna kunyata
akeji bayan an gamamin kuka,dariya islam ta
kyalkyale da ita tace Allah mommy naxata
mutuwa xanyi,dariya mommy itama tayi tace a'ah
nasan basaina yi miki bayani akan jinin haila ba
saboda kunyi a makaranta ko akwai abinda baki
gane ba a kansa,girgixa kai islam tayi tace duk
na gane mommy kuma dama inayin wankan
tsarki duk ranar friday mommy tace toh shikenan
Allah yayi miki albarka,islam tace ameen.
Su daddy ne suka shigo Amir da Amira kuma
dauke da basket a hannusu,islam kuwa sai wani
sussunkuyar dakai takeyi wai ita kunya,bayan su
daddy sunyi mata y jiki ta amsa a kunyace har
xasu futa saiga dr sameer y shigo bayanshi nurse
ce dauke da try da magunguna aciki.
Bayan sun gaisa dasu Abba y kalli islam da
takecin chips yace ah Ashe pacient din tawa ta
warware shiru islam tayi ta sunkuyar da
kanta,murmushi yayi yace nagama jikinnata da
sauki xuwa an jima xa'a iya sallamarta yanxu dai
ga magungunanta,sai lokacin islam ta dago kanta
ta kalli dr cikin muryar shagwabba kamar
mesonyin kuka tace dr bayan allura har magani
xansha,eh yace mata y ballo magungunan y mika
mata,karba tayi hade da xumbura bakinta gaba
tana kunkuni ita batasan magani baxata
shaba,murmushi yayi yace toh ai shikenan y kalli
nurse yace jeki debo injections tunda batason
magani,da sauri ta kurbi ruwa ta watsa
magungunan a baki ta dada korasu da
ruwa,dariya duka yan dakin sukayi,ita kuwa islam
runtse idanuwanta tayi hade da tabe baki alamar
daci.
Dr ne y kalli su daddy yace ku biyoni office y
futa su daddy ma mara masa baya sukayi.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 9:39 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*110*
Xaune dr sameer yake akan kujera su Abba kuma
suna xaune a wadda aka tanada domin masu
ganin dr,sai da y daidaita farin gilashin da yake
fuskarsa yadanyi rubutu a file din da yake
gabanshi sannan y fara magana,alhj ba komai ne
yake damun yarinyar kuba illah menses data fara
to dama mata halitt2 ne wadansu in lokacin
menses dinsu yayi xakuga suna bala'in yin ciwon
mara wannan ba komai bane illah wadansu
kwayoyin halitta da suke a marar mata to in
lokacin al'adarsu yayi sai kwayoyin halittarnan
suna dan cixonsu to shine yake haifar da ciwon
mara,suman da tayi kuma bkmai bane illah firgici
data shiga a lokacin da taganta a cikn bakon
yanayi wannan shine bayanin kawai.
Jan numfashi Abba yayi yace toh dr kana iya
ganin xata iya daina wannan ciwon,dr yace eh to
alal hakika gaskiya yanxu dai magunguna xatana
amfani dasu wadanda duk lokacin da menses
dinnata yaxo innatayi amfani dashi to xai lafa
mata,amma hanyar waraka 1 ce shine in Allah
yasa tayi aure da xarar namiji y kusance ta to
xata iya dainawa,numfashi Abba yaja yace to
mungode dr ammafa yarinyar nan tanada aure
yanxu haka watanta 2 da sati 2 da aure kenan da
tsantsan mamaki dr sameer y kalli su Abba harda
cire glass din idonshi y mai2ta aure kuma,Abba
yace eh mijinnata ma y tafi wani course ne xaiyi
2 years kafin y dawo,sai da dr sameer yaja
numfashi,Abba yace amma yanxu muna ganin
kawai xamu tura masa ita tunda lalurar tasu duk
iri 1 ce,anan Abba yayiwa dr sameer bayanin
cutar Aslam a lokacin dr fu'ad ne y dubashi,shiru
dr sameer yayi a ranshi yana tunani tabbas aka
tura yarinyar nan gurin mijinta to ba karamin
cutuwa xatayi ba dan da dukkan alamu mijinta
xaiyi jaraba,daddy ne yace dr kayi shiru,firgigit dr
sameer y dawo daga tunaninshi yace a gaskiya
shawaran da xan iya baku shine kubar islam
saboda tayi yarinta da yawa baxata iya daukar
lalurar mijinta ba xata iya cutuwa amma shawara
ta ku kyaleta taci gaba da karbar magani duk
lokacin menses dinta har mijinnata y dawo toh
suka cewa dr sukayi godiya suka futa.
Da misalin 4:00pm aka sallami islam suka koma
gda ranar dai haka ta wuni sukuku jinta takeyi
tamkar sabuwar halitt.
7 days islam ta dauka tana menses sannan tayi
wanka nanfa rashin ji y dawo,duk wanda yayi
mata Abu a lokacin da take menses sai data
rama ranar kuwa kaka wuni tayi tana raba fada.
*A GURGUJE*
Yau su islam suka koma makaranta,lokacin da
xasu tafi sai da kaka tayi mata nasiha sosai akan
ta kula banda kula maxa domin ita matar aurece
bayan haka yanxu kuma ta girma koya ta bari
namiji y taba jikinta tofa xata iya daukan ciki
islam ta xorata sosai da maganganun kaka haka
suka tafi makaranta a hanya islam sai da tayiwa
su Amira warning akan duk wanda y sake y
fadawa yan ajinsu anyi mata aure wlh in sun
dawo gida mai rabata dasu sai Allah ta kalli
khausar tace musamman ke nasan kinfi rawar
kai,khausar cikin masifa tace saina fada din,wani
kallo islam ta jefeta dashi tace Allah y baki iko
(islam abinda bata sani ba Abba y riga da yaje
makarantar y sanar musu),haka islam ta dinga
dari2 a makaranta wai dan kartayi ciki ,su
khausar kuwa bawanda yayi gigin fada dan
sunsan halin islam batada m.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya wani lokacin
dadi wani lokacin rashin haka to hakance ta faru
da Aslam ganin har yayi 9 months da tafiya
amma bai taba waya da princess dinshi ba duk y
damu,safwan ganin damuwar da Aslam yake ciki
tanason shafar aikinsa dan in yana tunani in
xa'ayi tayi masa magana to baji xaiyi ba harsai
an tabashi shine kawai y bawa Aslam shawara
yasa amir y siyawa islam waya ko chatting ne su
dingayi,cikin jin dadin shawarar da safwan y
bashi a take y turawa amir text massage yanaso
asiyowa islam waya,lokacin da Amir y tashi da
asuba yaga sakon Aslam reply yayi masa da to.
Su Islam ne xaune a palon kaka,mamakin
girmansu nakeyi musamman islam ta taxatama
budurwa kirorin budurci sosai suka futo a jikinta
dan in ba fada maka akayi shekarunta 15 ba
saika xata yar 17 years ce saboda yadda kirjinta
yake a cike tamkar xai fasa riga,ga wani irin hips
mai daukar hankalin mai kallo.
Amir ne y shigo palon da sallama yace little 6
mijinki y bani Sako gurinki hannunshi dauke da
leda,cuna baki islam tayi tace Allah ni ba little
bace y Amir ni big ce hararar wasa yayi mata
yace to gyanbo sarkin son girma baki tambayeni
sakon mijinnaki ba sai korafi kanta ta juyar gefe
tana nifa y Amir bani da miji ehe ta murguda
baki tsaki yayi yace ke kika sani ledar hannunsa
y xaxxage wayoyi ne 3 suka fado dukkansu
iphone 6+ akwai pink,white,sai yellow yace xaki
dauki 1 da sauri ta juya washe hakora tayi
lokacin da tayi toxali da wayoyin pink din ta
dauka ya kalli Amira yace kema xaki dauka
yellow din ita ta dauka,yace to wannañ kuma ku
bawa kausar duk akwai sim card a ciki Amira y
jefa da wani kallo yace saura ki bawa samari
number dinki duk randa naji kona gani seizing din
wayar xanyi murmushi tayi ta sunkuyar dakai
shikuma y fice.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 9:40 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*111*
Bayan Amir y futa murna su islam suka fara
harda rawarsu da sauri suka tafi suka sassaka
chargy,islam ce ta kalli Amira tace anya 6 ba
sonki kuwa yaya Amir yakeyi ba kuwa,Amira tace
ki jiki da fassara me kika gani,sai da islam ta
kada idanuwanta sannan tace alamu sun nuna
yaya sanki yakeyi dan gane da irin kallan daya
jefeki dashi sannan bakiji yace saura yaga
numbobin samari a wayar taki ba indai ba sonki
yakeyi ba ina ruwansa da samarin da xakiyi,Amira
hmmm kawai tace,islam ce tace yauwa dan Allah
yi maxa ki tashi muje gdansu khausar mukai
mata tata kan kakannan ta futo tace baxan futa
ba,Amira tace ki bari mana sai anjima islam tace
wlh baki isa ba ta tashi tasa hijaba bakisan
yadda kafata take kaikayi ba rabona da futa waje
fa tun ranar friday da mukaje makaranta kuma
kinga munyi hutu yanxu wa yaga ranar kara futa
ta tayi waje Amira ma hijabi tasaka ta dauki
ledar tasa wayar khausar din tabi bayan islam.
Amira tace to uwar axarbabi da kika bar wayar
da in kinje me xakice wa khausar din dariya
islam tayi tace ai mantawa nayi a nutse suke
tafiyarsu har sun kai bakin kofa islam ce tajiyo
miryar aunty amarya tana ku islam ina xakuje cak
islam ta tsaya ta kalli Amira tace nabanu yanxu
aunty amarya xata hanani futa,aunty amarya ce
ta fara takowa wajensu islam ganin haka da gudu
ta kwasa ta fuce waje dan a yadda takejin
kafarta na mata kaikayi wlh ko daddy ne y
hanata futar nan saita fita,aunty amarya ta
karaso tace Amira ina xakuje ne,Amira tace
gdansu khausar, aunty amarya tace me xakuyi
acan da tsakar ranar nan,Amira tace waya xamu
kai mata,aunty amarya ta maimaita waya!,Amira
tace eh yaya Amir ne y siyo mana aunty amarya
tace y kyauta to meya saka islam guduwa
kuma,Amira tace wai tsoro takeji karki hanata
futa dan kafarta kaikayi takeyi,dariya aunty
amarya tayi tace Allah y shirya islam watako
saboda tsabar yawo kafarta har kaikayi
take,itama Amira dariya tayi aunty amarya tace
to saikun dawo,Amira tace toh ta fice.
Xaune Amira ta tarar da islam akan wani sock
away da yake gaban gidansu kadan,Amira tace
to tashi mu tafi,islam tace toh wlh dadin iskar
waje ma daban take data cikin gda ta wani
lumshe ido,murmushi Amira tayi tace gaskiya
islam ban taba ganin mace mai shegen son yawo
irinki ba watako iskar cikin gda data waje har
banbanci ne da ita,yatsina fuska islam tayi tace
eh ni wlh ma wannan hutun dole a gwarxo xan
yishi,dariya Amira tayi tace harda dole kamar kin
manta bake kikeyin iko da kanki ba,tsaki islam
tayi tace Allah sai naje saboda mugunta irinta
hero y barni da igiyoyin auransa a kaina suna
hanani rawar gaban hantsi ta karashe maganar
da murguda baki,dariya Amira ta karayi tace
watako 6 xanso naga ranarda bakinki xai
mutu,wani birki islam taja tace tab yasin ba ranar
da bakina xai mutu sai dai in mutuwa nayi gaba
1,dariya Amira ta karayi tace bama saikin mutu
ba yaya Aslam xai kasheshi cikin masifa islam
tace Allah y kiyaye lokacin yayi dai2 da
karasawarsu gdansu khausar shiga sukayi suka
gaida baba mai gadi suka wuce.
A xaune suka tarar da mammy da sagir suna hira
gaishesu sukayi mammy ce kawai ta amsa sagir
kuwa mikewa yayi,islam sai taji duk ba dadi dan
rabonta dashi tunda y tafi cairo karatu sai yau ta
ganshi gani tayi y kara girma sosai,islam tace
mammy ina khausar fa mammy tace tana daki
tashi sukayi suka shiga dakin kwance suka tarar
da khausar tana bacci daka mata duka islam tayi
tace toh kasa sarkin bacci saiki tashi firgigit
khausar ta mike tana sosa cinyarta hararar islam
tayi tace wannan wanne irin iskancine,islam tace
naji mai da wukar naga yaya sagir yaushe y
dawo,khausar tace tun ranar friday islam tace
shine bakixo kin fadamin ba,khausar tace
amfanin me fadar xaiyi miki shiru kuma islam
tayi Amira ce ta daura mata ledar a cinya
budewa khausar tayi ganin waya aciki kuma
wadda ake yayi iphone 6+ shine sakata waro ido
waje tace wayar waye.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 9:41 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*112*
Amira ce tace takice,khausar ce tace banason
wasa dan Allah ki fadamin gaskiya,islam tace
abinda yafi bakyason wasa to wa kike tunanin
xaiyi miki karya,khausar tace to masifaffiya bake
nake tambaya ba,Amira sai da tayi dariya tace
Allah takice yaya amir ne y siyo mana guda 3
kowa 1 cikin murna khausar ta fuce a palon da
gudu taje ta nunawa mammy ta tayata murna
dftn alkhairi da gudu ta fice ta tafi part din sagir.
Kwance ta tarar dashi kan 3 seater yana tunanin
islam tafiyarshi harya manta da ita amma yanxu
ganinta dayayi y taso masa da kikin xaxxafar
soyayyar da yayi mata,wata xuciyar ce ta
kwabeshi tace haba sagir y xakana aikata
haramun karka manta matar wanice istigfari y
farayi khausar ce ta shigo tana my bro kaga
wayata ta mika masa karba yayi tare da yin
murmushi yace to my 6 waya siyo miki,dariya
tayi tace yaya amir ne y siyamin nida su islam
murmushi yayi yace y kuwa kyauta nima an jima
xan futo muku da tsarabobin da nayo muku cikin
murna ta runguneshi ta bashi peck a kumatu ta
fuce murmushi yayi y tashi y shiga dakinsa
katuwar trolley y janyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login