Showing 75001 words to 78000 words out of 96677 words

Chapter 26 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

74044

itace
takeyin bye2 din da sauri y karawa motar tashi
wuta a dai2 gabanta yaja wani wawan birki da
sauri islam taja baya kosu Amira da suka fara
tafiya sai da suka tsorata suka juyo, islam kuma
cikin tsiwa ta kama kugu tace lallai ma yaya
haidar wannan ai ganganci ne tsakani da Allah
daka bugeni ai daka cuci mai so.... lokaci daya
ta hadiye ragowar kalamanta ganin mai futowa a
motar cikin tsoro hade da xaro idanu waje tace
hero gutt ta hadiyi wani xaxxafan yawu ganin y
koma mata tamkar wani namijin xaki fuskarnan
tashi a murtuke idanuwansa sun kada sunyi ja
yana furxar da wata xaxxafar iska su Amira jin
sunan data kira da gudu suka kwasa sukayi cikin
gda itama ganin yana tunkaro ta shine y sakata
fara ja da baya2,ci gaba yayi da tunkarata ganin
da tayi y kusa cimmata shine yasa kata juyawa
da sauri ta kwasa a guje taku 1 yayi y dangota
ihu ta kwallah cak y dagata wintsila kafafuwanta
ta farayi tana dukan girjin shi da hannayenta tana
Allah hero ka saukeni banaso shikuwa ina
idanuwansa sun gama rufewa da xaxxafar kishi
ko jinta bayayi gaban mota y cillata yaje y
xagaya shima y shige y bawa motar wuta yabar
layin.
Su Amira ne suka shiga part din kaka a guje har
suna rige2 shiga kaka da take xaune sai
fadowarsu dakin taji suna sauke numfashi,
kallansu tayi tace ku kuma menene haka kamar
wadanda suka taho daga filin tsere Amira ce tayi
magana bayan sauke numfashi da tayi tace wlh
yaya Aslam muka gani kaka tace to shine me
dan kun ganshi daxu y dawo ina islam din kuma
khausar tace suna waje tare kaka tace ai
shikenan.
Islam kuwa cikin tsiwa ta dago kanta bayan ta
daidaita xamanta acikin motar tace wai hero
menene hakane nifa gaskiya banason wulakanci
yama xa'ayi daga wani ganina ka wani daukoni
ka sakani a mota to waima ina xaka kaini ta
karashe maganar da murguda baki,banxa Aslam
yayi mata jin bai mata magana ba shine y sakata
dago kanta da niyyar kara masa rashin kunya
ganin da tayi fuskarshi ta dawo mata exactly
irinta hero na da data sani in xaiyi mata mugunta
shine y sakata hadiye maganarta amma dai tana
kunkuni.
Sai data ga sun doshi asalin gdansu shine ya
sakata xaro ido tace nabani ta shagwabe fuska
tace haba hero yanxu tsakani da Allah dan
acemin yar dadi miji shine ka daukoni ka taho
dani gda salon ace banida kunya nabiyo mijina
daga ganinshi, duk da ransa a bace yake sai da
yayi murmushi jin sunan data kirashi dashi horn
yayi gate man y bude gate din hancin motar tasa
y danna xuwa cikin gdan a packing space yayi
packing futowa yayi y xagaya y bude mata kofa y
janyota saura kadan ta hantsilo saura kadan ta
kifa y rikota mugun riko yayi mata har sai data
tayi kara janta y farayi da gudu2 ta fara binsa
saboda yanayin tafiyarsu ba 1 ba kuma gashi
sauri yakeyi key y ciro a aljihunsa na gdan y
bude suka shiga palon hankadata yayi kan kujera
kum ta bige kanta auch tace ta rike kannata har
idanuwanta kwalla ta fara taruwa ta dago kanta
tace hero menene haka lokacin har hawaye y
fara sauka a kuncinta wani kallo y jefeta dashi
cikin kakkaurar murya yace wanene y saukesu a
mota har kike masa bye2 kike murmushi, wani
banxan kallo ta jefeta dashi ta mike ta goge
kwallar idonta tace oho yanxu nagane dalilin
rashin mutuncin da kake mini to tsaya kaji.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 10:08 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*119*
Goge kwallar data xubo a kuncinta tayi tayi masa
kallan up & down duk da girman daya dadayi y
tsorata ta amma haka ta xage ta fara masa
rashin kunya tace to tsaya kaji bansani ba kuma
baxan fada ba inhar ka damu da sanin wanda y
sauke mu ai da saika bi bayan motar shi bakaxo
nan ba kanamin jan ido ta karashe maganar da
jan siririn tsaki hade da murguda dan karamin
bakin nata a ranta tana watako shi hero baxai
taba canja hali ba kenan nida naso dawowar nan
tashi ace mun gina sabuwar rayuwar aure amma
shine xaixo da wani sabon salon to wlh nima xan
koma masa asalin islam dita dan ba xoronsa
nakeji ba.
Aslam kuwa duk abinda take fada sam baiji taba
sakwamakon shagala da yayi da yayi da kallanta
shi sai yanxu ma ya kula da canjawar da tayi ta
wani cika ta xama babbar mace ashe ma pic
dinta dayake kallo yake susucewa baiga komai
ba kurr y kurawa boobs dinta idanu yana kallon
dukiyar fulaninta da sukayi wani fum2 acikin riga
tamkar an hura balon islam kula da tayi
baimasan mai take cewa ba dan y riga y shagala
da kallanta shine y sakata tafa hannunta firgigit
y dawo yace amm uhmm mema kikace wani far2
tayi da idanu tace shafa kaji murmushi yayi yace
me kikace murguda bakinta tayi tace naje shafa
kaji shafa kansa yayi ya wani yi murmushin
gefen baki hade da taune lebensa na kasa y wani
tande baki cak taji y dagata tamkar y dauki yar
baby y sabata a kafada ya fara haurawa stair da
ita.
Cikin tsoro islam ta xaro ido ta kwallah kara tace
haba hero menene haka dan Allah ina xaka kaini
yace kefa kikace na shafa naji shine xan kaiki
daki dan xanfi jin dadin shafawa kinga sai
nagane matar tawa ta girma ne dahar tayi
wannan furucin lokaci 1 cikinta y bada kara
kululu tare da kwalla kara tana wayyo Allah kaka
ki taimakeni na shiga 3 dan girman Allah hero
kayi hakuri wlh subutar bakine Allah baxan kara
ba banxa yayi mata yaci gaba da haura benen da
ita wasu ma 2 yake hadawa ganin bai san ma
tana rokon shiba shine y saka ta fara dukan
bayanta da hannu bibbiyu ganin wannan ma ba
mafita bace,har sunkai palon sama bashida
niyyar direta gani tayi y farayin dakinsa da ita
daidaitar wuyansa tayi ta gantsara masa cixo
mai xafi bakaramin ratsashi cixon yayi ba saboda
on expected yaxo masa da sauri y direta yana
auch y shafo gurin ita kuwa ganin haka tace kafa
mai naci ban baki ba ta bawa wandanta iska sai
da taje daidai kofa ta juyo tayi masa gwalo tare
da juyawa tayi rawa ta kada masa hips dinta ta
shige dakin tasa sakata.
Aslam wata doguwar ajiyar xuciya yaja hade da
fadawa rajab kan kujera yana mai da numfashi
dan yau dinnan yaso cimma burinsa akan
yarinyar nan haka y tashi jiki a sabule y shige
bedroom dinsa, islam kuwa tana shiga daki bayan
ta sakawa kofarta key kan gado ta fada tana mai
da numfashi can kuma ta kyalkyale da dariya
tace lallai ma hero dinnan da mai yake nufi lallai
da kuwa abinda nake tunani yayi tunanin
aikatawa da yaga hauka tashi tayi ta shiga
bathroom ta dauro alwala dan ko sallar magruba
batayi ba.
Bayan ta idar da sallah wayarta ta dauko acikin
pose dinta ta bude data ta fara whatsap Amira
ta gani online,tuni ta tura mata da massage
" _to da kuka gudu kuka barni bai kasheni ba
banxaye_"
Amira turo mata tayi da sakon dariya
" _Hhhhhhh_" tace kuma " _dama munce xai
kasheki ne_"
Cikin jin haushi islam tace " _bansani ba shiyasa
naga kun gudu ba_"
Rabuwa tayi da Amira ta tafi ta yiwa khausar ma
jaraba sannan ta koma grp dinsu na *classic
lady* sukaci gaba da hira su khausar suna ta
tsokanarta a grp khausar ce tace ga *topic* tuni
kowa yace muna jira tuni hausar ta rubuta
*topic* kamar haka" _wata saboda yar dadi
mijice shekara 2 bata ganshi ba amma saboda
dauki tana ganinsa ta bisa dan dauki ko kowa y
fadi ra'ayinsa_"
Tuni aka fara comment wasu suna cewa tayi
dai2 wasu nacewa tayi rashin kunya sai 11:00pm
islam ta sauka online cire kayan jikinta tayi ta
daura towel ta shiga bathroom wanka tayo ta
futa xama tayi ta shafa mai ta fesa body spray
wata sleeping dress ta dauko gown mai kauri
tasaka saboda weather din garin sanyi ne nan fa
taji cikinta y fara kugi alamar yunwa kasa xaune
tayi ta kasa tsaye dan tasan kota kwanta baxata
iya bacci ba saboda yunwar da takeji shahada
kawai tayi ta tafi ta bude kofarta da niyyar tafiya
kitchen dan ta samu abinda xata sakawa cikinta.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 10:10 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*120*
Lokacin data futo tana xuro kafarta tayi tuntube
da lader da sauri ta dauka tambarin chip plus
tagani a jikin ledar cikin jin dadi ta dauko ta
koma dakinta xama tayi a kasa ta baje lader din
pounded yam tagani da agusi soup sai kuma
pepper soup na caw leg sai kuma lemo da ruwa
murmushi tayi tace Allah sarki hero nasan baxai
banni da yunwa ba bathroom ta shiga ta wanko
hannunta ta futo xama tayi taci abincinnan sosai
ta daura sauran kan fridge tasha lemonta da
ruwa bathroom taje ta wanke wannunta hade
dayin brush ta futo tabi lafiyar gado taja blanket
ta lullube kanta bata yi 5 minute ba bacci yayi
gaba da ita.
Bangaren Aslam kuwa lokacin daya shiga dakinsa
shima cire kayansa yayi ya daura towel y shiga
wanka bayan y futo you shafa Mai y fesa body
spray shaf2 y shirya cikin brown troser hade da
milk din shirt key din mota y dauka yaje y siyo
abinci a restaurant dan yasan islam bata wasa
da cikinta dire mata nata yayi a bakin kofarta dan
yasan dole xata futo ta dauka shikuma yaci nasa
a palo haka yayita xama a palon ko xaiga
futowarta amma sam bata futo ba xuwanshi
bakin kofarta 3 da niyyar yayi mata knocking sai
y fasa yanxu ma bai dade da shiga daki ba
lokacin daya futo yaga harta dauke abincin ta
koma yaso y kara kallan koda face dinta ne haka
y koma daki jiki a sabule y kwanta amma ko
yaya y rufe idonsa surar islam ce takeyi masa
yawo a idanuwansa pillow daya y janyo y
rungume yanata kissimawa a ransa ace princess
dinshi ce rungume a jikin shi haka dayasan yau
baccin daxai yi na dabanne.
Washe gari 8 o'clock Aslam y futa direct gdansu
y wuce yanayin packing part din kaka y wuce
dan har lokacin idanuwansa y manta irin
murmushin daya ga islam tanayi wa wanda y
saukesu a mota ganin baiga kaka a palo ba
yasan sanyinnan ne y hanata futowa direct dakin
Amira y wuce murda handle din yayi sai y jishi a
bude danna kansa yayi cikin dakin kwance y
hangota akan gado tanata sharar baccinta
karasawa yayi kusa da kanta bubbuga pillow din
da take kai y farayi cikin bacci Amira taji ana
buga mata pillo xumbura baki tayi tace haba
kaka da sanyinnan ma baxaki bar mutum yayi
baccin safe ba ko bude ido batayi ba ta karajan
blanket ta lullube kanta ji tayi ance ke baxaki
tashi bane firgigit ta bude idonta dan ta gane
muryar wane lokaci daya ta mike a gadon tana
raba idanuwa jikinta na rawa, kallanta yayi
fuskarnan tashi tamau tamkar bai taba dariya ba
yace ke nutsu banason shirme sonake ki fadamin
wana gani jiya ya saukeku a mota, cikin barin
baki Amira tace bkwa tsawa y daga mata yace
karki rainamin wayo mana ko munafuka kikeson
xama ne jiya da idona naga an saukeku a mota
shiru tayi dan sai yanxu ta tuna ma tsabar
tsorone y mantar da ita, wata tsawar y daka
mata wadda tafi ta daxu yace badake nake
magana ba kikayi min shiru koni din sa'an
wasanki ne, da sauri tace wlh ba kowa bane
kawar muce itada mijinta suka rage mana hanya
lokacin da suka gammu a titi mun rasa keke
napep kirr y tsare ta da ido yanaso y gano
gaskiyar maganarta jan iska yayi y furxar yace
kin tabbatar da sauri ta daga kanta tace wlh da
gaske nake juyawa yayi y fice a dakin yana ki
hadamin kayan islam.
Wata muguwar ajiyar xuciya Amira taja ta dafe
kirji tace tab lallai islam ba karamin namijin
kokari takeyi ba da take iya mayarwa da yaya
Aslam magana inya fada mata mara dadi tab ta
kama haba tace ni gashi yanxu daga tambaya na
rikice komawa tayi ta kwanta a gadon ta runtse
idanuwanta saboda har yanxu tsoron bai sake
taba,mikewa tayita ce bari dai na tashi na hada
kayannan karya dawo y tarar ban hada Ba.
Aslam yana futa daga bedroom din Amira na
kaka y wuce xaune y tarar da ita a bakin gado y
karasa gaisawa sukayi kaka tace shine jiya ka
dauke matar taka ko sallama baka bari munyi ba
sosa kansa yayi yace ai kaka wlh amm uhm
dariya kaka tayi tace kaji dannema watako yau ni
kakejin kunya dariya yayi yace ah haba kunyar
lafiya kin taba ganin miji yaji kunyar matarsa
itama dariya tayi tace to daga ina kake da
safennan dan daga ganin alamu ko wanka bakayi
ba cewa kaka yayi eh wlh abinci naxo daukar
mana kinsan ko kayan abinci ban siya ba tace eh
ai kana rawar jikin ganin matarka ko tunanin
babu abincin a gdanku bakayi ba ka dauke
matarka tashi yayi yace kai kaka ni bari na barki
inajin kishi ma kikeyi tunda naga kinata taso da
maganar y fice.
Part din aunty amarya yaje y gaisheta murmushi
tayi tace my son yau dai kaje ka karasa gyaran
gdan kadan dudduba abubuwan da babu dan
anjima kadan Xa'a kaimaka matarka murmushi
yayi yadan sosa kai yace ai aunty na a gda islam
din ta kwana kallan mamaki aunty amarya tayi
tace bangane ba cikin kinkina yace amm ehh jiya
ai natafi da ita yayi maganar kansa a sunkuye
murmushi aunty amarya tayi tace aika
hutashshemu yace amm aunty amarya kinyi
break fast da yawane daukar mana naxoyi eh
tace ta shiga kitchen ta hado masa acikin basket
ta mika masa godiya yayi y karba y fice.
Part din mommy yaje y gaisheta itama amsawa
tayi amma batayi masa maganar islam ba dan
batasan ya dauketa jiya ba part din kaka y koma
y dauko kayan islam daya saka Amira ta hada y
xubasu a mota y fice xuciyarsa fess dan dama
abinda y dagula masa ita yanxu yaji ba gaskiya
bane.
*wannan pages din 119 & 120 sadaukarwa ne ga
maryam ngd sosai da kulawarki a gareni nakin
gajiyawa da kirana a waya kiji lfyta sannan kiji ko
nayi posting*
*dan Allah inaso nayi amfani da wannan damar
ga masuyimin magana ta private na tura musu
goyon kaka daga farko ko kuma wasu pages din
wlh kunyi yawa nagaji kullum saina turawa
mutane sunfi a girka kuma gashi nayi nisa dan
Allah duk mai neman buk dinnan ta dinga cigiya
a grp din da take nasan xata samu dftn xakumin
hakuri*
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 10:11 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*121*
Lokacin da Aslam yaje gda bayan yayi packing
bayan motarsa y bude y dauko basket din abinci
da trolly bag din kayan islam direct cikin gda y
wuce da sallama y shiga palon bayan y tura kofar
ai numfashin shi saura kadan y dauke sakamakon
islam daya gani xaune a palo sanye take da half
best iya breast dinta kawai ta rufe ta kamata
sosai dayake roba ce pusher pink colour ce a
gaban ta an rubuta *PRETTY* da bakin painty da
manyan baki hade da dogon wando black colour
yayi mugun kamata ta sama inda ta kasa y bude
sannan anyi tsaga ta gefe tundaga gwiwar ta har
xuwa kasa akwai wasu buloli ajikin tsagar
wandon inda akayi wata igiya pusher pink akayi
xarge a tsakanin bulolin,gashin kanta kuwa ta
rabashi 2 ta kamasu da pusher pink roboms tayi
kalba a karshen gashin, tana reto har kafadarta
kunnenta kuwa wani dan kunne ne mai O shape
pusher pink shima simple makeup tayi a face
dinta daga powder sai kwalli sai pusher pink
lipstick sai kyalli lips dinta suke amma ba
karamin kyau tayi ba kafarta sanye take da sosa
baki ta daura kafarta daya kan daya tana
chatting.
Wani yawu y hadiya kutt a xuciyarsa yace naga
fa alamar yarinyar nan haukatani takesonyi ji
wata muguwar shiga da tayi da kyar y tattara
nutsuwar shi guri 1 y karayin sallama a palon
firgigit ta dago kanta saboda chatting din da
takeyi y tafi da hankalinta bataji shigowar shiba
wani malalacin murmushi ta saki hade da
mikewa tana ur wlcm back hero sai data wani
karkada jiki sannan ta fara tafiya Aslam kuwa
mutuwar tsaye yayi ganin yadda take tafiya
komai na jikinta na motsi shi gani yake tamkar
da gayya take tafiyar harta karaso kusa dashi bai
sani ba saboda yadda y shagala da kallanta y
saki baki da hanci hade da tsareta da idanuwa ko
kiftawa bayayi iskar bakinta ta hura masa a ido
wata ajiyar xuciya yayi yace pretty kinaso ki
kasheni da salonki tsare shi tayi da idanuwanta
masu daukar hankalin wanda ake kallo farare tas
sannan sanye take da kwalli ta daidaita shi
acikin idanuwanta tace ammm magana kake?
girgixa kansa yayi dan baiyi tunanin maganar ta
futo fili ba y xata a xuci yayi karbar basket din
abincin tayi ta juya tana tafiya tana wani kada
hips Aslam kuwa binta yayi tamkar rakumi da
akala hannunsa yana janye da trolly dinta yanajin
wani masifar son islam hade da sha'awarta yana
fixgarshi ji yakeyi tamkar yaje y rungumota ko
xaiji sassauci acikin ransa.
Dining area ta karasa ta daura basket din akai ta
tafi kitchen ta dauko plate da cup dayake harda
kunun gyada aunty amarya ta sako musu, bayan
sun gamacin abincin Aslam jiki duk a mace y
tashi y haura stair dan xuwa yayi wanka,islam
kuwa tattara kwanukan tayi takai kitchen ta
wanke wadanda sukayi amfani dasu sannan ta
dawo palo ta kunna kallo.
Xuwa can anjima khausar ta kirata tsokanarta
takeyi tana amarsu a gdan captain a.u anjima
kadan muna hanya xamuxo muci ragowar kaxar
amarci dannasan yaya Aslam baxai barki ba jiya
dole ki biya kaxar nan dan bakyaci bulus ba sai
da islam ta kyalkyala dariya tace haba yarinya
wai waya fada miki kin manta nace baxan bawa
hero kaina ba har sainayi candy duk da nasan
xuwa lokacin ma kawai karfin hali xanyi nayi
rayuwar aure dashi amma nasan baxan taba son
hero ba don da kiyayyarshi y horeni tun tashina
dariya khausar tayi dagacan bangaren tace
gaskiya karki cutar da yayanmu kawai yarinya ki
bada kai bori yahau dariya islam tayi tace nikarki
dameni da xancen banxa sai anjima din in kunxo
ta katse kiran ta ajiye wayar taci gaba da
kallanta.
Abinda islam bata sani ba tun lokacin data fara
waya Aslam y taho amma jin abinda take fada
shine y dakatar dashi bai karasa sakkowa ba
bakaramin mawuyacin hali y shiga ba lokacin
dayaji tana fada a waya haryanxu bata sonshi
runtse idanuwansa yayi xuciyarsa na kuna yanajin
wani irin xafi a ransa danshi yaji a kumatunsa
shafawa yayi yaji ashe hawaye ne suka xubo
yace a ransa ashe nikadai nake haukata nake
fama da dakon sonta ashe shirme nakeyi da nake
tunanin islam tana sona goge fuskarsa yayi yace
kinyi kuskure da kika bari najiki nikuma nadauwa
kaina alkawarin koda lokacin da kika diba xaki
bani kanki yayi baxan taba kusantarki ba
harsaina tabbatar nakoya niki axababbiyar
kaunata wadda xata kasance duk bugu na
numfashinki saikin tunani sakkowa ya farayi
fuskarsa a sake tamkar baiji komai ba (nikuwa
nace namijin duniya kenan).
*_Tom jama'a kundaiji wannan batu na Aslam da
islam ko a cikinsu waxai gaji y sakko daga dokin
xuciya kudaici gaba da biyoni danjin yadda lbrn
xai kasance*
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/8, 10:12 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *GOYON KAKA*
*122*
Daya sakko ko kallan inda take baiyi ba saboda
bayaso ta fahimci wani abu a tare dashi,kitchen
y wuce yana shiga y tafi store dubawa yayi yaga
akwai kayan abinci kuma basuyi komai ba futowa
yayi a kitchen din hanyar kofa yayi yana bari naje
kasuwa nadawo Allah y kiyaye tace masa da
amin y amsa yasaka kansa y futa.
A mota ma haka y dingajin ranshi a jagule harya
karasa kasuwa rago y siya y bayar a gyara masa
sannan y tafi gurin saida kaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login