Showing 60001 words to 63000 words out of 96677 words
Chapter 21 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt
daka sakani daka
maka tafarnuwa to a lokacin nahada da
kyankyason ta karasa maganar da tuntsirewa da
dariya.
Ai Aslam bai jira ta karasa magana ba y tashi da
kudi y fada kitchen y tsaya ajikin sink yahau
kwarara amai islam ganin haka ta kyalkyale da
wata shu'umar dariya ta mike ta fara kwasar
shoki tace yes anyi 1-1 da sauri tabi Aslam
kitchen ganin y takarkare yana xura hannu a baki
shine y sakata shekewa da dariya harda faduwa
da rike ciki,Aslam ganin ta tasa shi gaba tana
dariya,Shine y saka shi jin haushi a ranshi yace
wannan yarinya anyi bakar muguwa watako ita
komai akayi mata saita rama,kuskure bakinsa y
fice y barta a kitchen din,islam kuwa sai da tayi
dariyarta wali ishi sannan ta mike itama ta futa
xaune ta tarar da Aslam a palo y dafe
kansa,murmushi tayi ta wuceshi dinning area ta
wuce ta debo abinci memakon ta xauna taci
acan saita taho palo danneman magana.
Kallanta Aslam yakeyi da mamaki ganin yadda
take cika cokali tana danna loma harwani lumshe
idanu takeyi,tace kai yaya anya daka tafi aikin
soja bakuwa bangaren catering ka tafi ba,ta
karakai loma tace kai inaga kai dai Kirchner din
sojoji ne,murmushi yayi yace ba wannan nakeson
jiba.
Katse shi tayi ta hanyar cewa aff ai karya nakeyi
maka daxu,kawai ramu gayya nayi kasan ance
ramuwar gayya tafi ta gayya xafi,kawai
banbancin 1 ne mu daxu ta dole kasamu mukaci
abinci daga baya muka amayar,kai kuma cikin
farin ciki kakeci daga baya nasa ka ka amayar
tayi dariya tace kaga yanxu munyi 1-1 ko,Aslam
kuwa in banda mamakin islam babu abinda yake
yace anya yarinyar nan mutum ce kuwa,ranshi
yaji y baci ganin rainin wayon datayi masa,hannu
yakai y danko ta kara ta kwallah lokacin yayi
dai2 wayarsa tahau ringing.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 9:03 AM] +234 703 962 5239: *na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*91*
Hannu yakai y dauko phone dinnashi,har lokacin
islam tana rike a hannunsa tana raba idanuwa
tamkar bera a tarko,sunan general yusuf safana y
gani da sauri y hankada ta,kujera ta fada ta buga
kai kara ta saki saboda ta bugu sosai da sauri
yasa hannu y toshe mata baki yayi picking call
din,cikin girmamawa yace yallabai brk da dare
dftn kana lfy,dagacan bangaren general yace lfy
qlau ango y amarya,dan murmushi Aslam yayi y
kalli islam y harareta saboda kokarin cire
hannunsa datake a bakinta ta kasa,yace tananan
lfy,general yace masha Allah,dama wani training
ne akace anason sojoji masu matsayin captain
xa'a turasu singapore suyo wani training har
tsawon 2 years to bansani ba ko xaka iya xuwa
naga kanada sabon aure,cikin jin dadi Aslam
yace mai xai hana yallabai yaushe ne
tafiyar,general yace nan da 7 days Aslam yace
ngd Allah yabar girma insha Allah xanshigo nan
da 5 days,ameen general yusuf yace daganan
sukayi hiding call din,sai a lokacin Aslam yake
shirin budewa islam baki ganin haka da sauri
islam ta rike hannunsa ta gantsara masa cixo
mai xafi,har sai da Aslam yayi yar kara da sauri
ta sakar masa hannun ta kwasa a kuje sai da
tahau step sannan ta tsaya,ganin Aslam yana
yarfe hannu alamar cixon y shigeshi shine yasa
ka islam kyalkyalewa da dariya,dagacan inda
take tace hey hero karka manta nasha fada maka
islam bata yafiya duk laifin da akayi mata sai ta
rama gwargwadon yadda aka yi mata saboda
islam bata xalinci saita kara kyalkyalewa da
dariya,ganin Aslam ya mike shine yasa kata arta
a nakare,murmushi Aslam yayi ya koma y xauna
yace yarinya sai fitina ga kuma tsoro kamar farar
kura,islam kuwa sai data shiga daki tasa key
ajikin kofar ta tsaya tana mai da numfashi a haka
dai ta karasa kan bed dinta daganan bacci yayi
awon gaba da ita.
Washe gari da misalin 11:00 o'clock islam ce
sanye cikin riga da wando rigar light pink wandon
kuma sky blue pencil powder ce kawai a puskarta
sai kwalli da lipstick amma tayi kyau after dress
tasaka mai flowers pink da stones pink
bakaramin kyau tayi mata ba veil ta nada pink
sai ta saka wani takalmi mai shegen tsini pink
mai igiya,Aslam ne yake knocking kofar dakinnata
yana wlh xan tafi ko an fada miki ni driver dinkine
xaki shanyani,murguda baki tayi kamar yana
kallanta tace da kai din menene in ba driver naba
turare ta fesa sannan ta futo tana tura baki.
Kallan ta yayi a ranshi yace lallai islam
bakaramar kyakykyawa bace,amma sabanin haka
a fili y tabe baki yace duk bata wa mutane lokaci
da kikayi ma ko kyau ba kiyi ba,banxa tayi dashi
domin a rayuwar islam taki jinin tayi kwalliya a ki
yaba mata,shiyasa take son sagir koya tayi
kwalliya y dinga xuxutata kenan yana daukarta
pics a haka har suka futa a gdan yasa key y rufe
suka karasa suka shiga mota get man y wangale
gate yana a sauka lfy yallabai.
Tafiya sukeyi ba wanda yacewa wani uffan,islam
dayake batasan gari ba sai kalle2 take (nikuwa
nace wayaga kifin rijiya ) dai2 shop rite Aslam
y tsaya yace bari naje nasiyo wa su kaka tsaraba
bakya je hannu na dukan cinya ba,kallan shi tayi
tace nima xanje yace toh futo muje futa sukayi y
rufe mortar suka karasa shiga mall din hannunsa
yasa y rikewa islam hannu.
Sai kallansu akeyi saboda sunyi kyau,Aslam
ganin mutane na kallansu sai yaji dama a mota
yabar islam saboda yadda yaga hankalin maxan y
karkata kanta,tsaki yayi ganin oganniyar ita ko a
jikin ta bakinshi yakai dai2 kunnanta yace wlh ki
nutsu kikamin rawar kai in muka koma gda saina
dakaki,banxa tayi dashi keken xuba kaya Aslam y
janyo suka fara xagayawa kurin turaruka suka
fara xuwa.
Kicibis Aslam yaji yayi karo da mutum a tare
suka dago fuskarsu,wani hadaddan guy ne baki
kyakykyawa (black beauty) yana da manyan
idanuwa farare tas yana da gira dai2 gwargwado
yana da dogon hanci bakinsa yana da dan girma
kadan inda kwantaccen sajensa y hadu da
xagayayyan gashin baki daya kawata fuskarsa
sumar kansa luf,bashi da jiki sam dan Aslam y
fishi girma sosai sai dai xasu iyayin tsayi 1 da
Aslam danko Aslam xai fishi tsayi to da kadanne,
wannan daga gani ko ba'a fada ba dan fillo ne.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 9:08 AM] +234 703 962 5239: a umma yahya musu*
*GOYON KAKA*
*93*
Aslam driving kawai yakeyi amma sam y rasa
nutsuwa,tunanin shi y tsaya tsam a guri
daya,yasara meyasa in yaga wani yana nuna
kulawa akan islam ko yace yana sonta yakejin
haushi,islam ce ta katse masa tunaninsa ta
hanyar cewa kai gaskiya hero abokinnaka yana
da kirki sosai a gaskiya inaji ma nafasa auran
sagir in ka sakeni gaskiya shixan aura ta karashe
maganar da mirmushi ta lumshe idanu.
Wani mugun birki Aslam yaja wanda yasa islam
saida tayi gaba ta koma ta gwaru da kujerar
baya,xaro idanu tayi tana kalle2 ko xataga abinda
yasaka Aslam jan birki haka,Allah ne y kiyayesu
sun shiga irin titunan unguwa dan da a babban
titi suke babu abinda xai hanasu haddasa
hatsari,Aslam kuwa packing motar yayi a gefen
titi y dango islam idanuwansa yayi jajawur jikinsa
har bari yakeyi,lokaci daya jikin islam y fara rawa
idanuwa xaxxaro saboda tsabar tsorata,kallanta
yayi yace wlh this is the last warning about
wancan banxan yaron da kike kira xaki aureshi,ke
in banda baki da tunani ki rubuta ki ajiye auran
mu ba saki ba yaji,dan naga alamar bakida
hankali inajin kin manta xaman aure mukeyi ba
dadiro ba da harxaki na tunanin wadansu
maxan,naga alamar sam 2 bakisan menene aure
ba wlh3 kinji nayi rantsuwa 3 times ko in kika
kara maganar xan sakeki ki auri wani namijin
saina nuna miki real colour dina yayi murmushin
gefen baki yace naga ke haryanxu bakisan
wanene umar ba kawai kallona kikeyi,lokacin
daxan fara nuna miki halina y kama bakinta y
murde har sai da tayi kara ,yace wlh bakin tsiwar
nan sai y mutu y tankada ta,ta bugu da kofar
mota itadai islam ta tsorata ta kama bakinta ta
rike dan ba karamin maxa yaji ba jikinta kuwa har
rawa yakeyi dan ba karamin tsoro Aslam y bata
ba y canja mata gaba 1 tamkar namijin xaki
tunaninta y tsaya tsam takasa tabuka komai sai
kanta data sunkuyar tana kallan kasa,Aslam
kuwa sai daya dauki 10 minute yana xaune y
lumshe idanuwansa sai daya samu nutsuwa
sannan yaja motar suka tafi.
Aslam suna xuwa sukayi horn gate man y bude
musu suka shiga,tun kafin Aslam yayi packing
islam take kokarin budewa ta futa da sauri y
danna lock kofar motar ta ruke kallanta yayi
yace naga kanki yana rawa ki nutsu kiji abinda
xan fada miki kika sake iyayen mu suka gane irin
xaman da mukeyi in muka koma gda saina saka
bindiga na harbe miki kai,cikin tsananin tsoro ta
dago dara2 eyes dinta ta saukesu a kansa,yace
kalleni da kyau gwanda ki mutu konima na huta
da wannan aurannaki da baya amfana nida
komai,common girki baki iya ba balle akai ga
manyan ginshikan aure ina fatan kin fahinceni,da
sauri ta kada kanta dan sam takasa magana
saboda jin abinda Aslam yace naxai harbeta
sannan y bude motar yana ki jirani,sai daya bude
seat din baya y dauko tsarabar da suka siyo
sannan y xagaya y bude mata motar cikin sanyin
jiki ta xuro kafafuwanta hannunta y rike
cikinnasa fuskarsa dauke da murmushi part din
kaka suka nufa.
suna xura dai2 kofar shiga da sauri islam ta
kwace wannunta ta shiga da gudu tana kaka!
kaka!!kaka!!!,da sauri kaka ta futo daga daki har
xaninta na faduwa da gudu islam ta tafi ta
rungumeta tana farin cikin ganinta,kaka ma cikin
amarya Ashe yau kin tafe,xumbura baki Islam
tayi taja baya tace Allah fushi nakeyi dake baki
taba xuwa ba,haka ma su mommy ta saki kaka
ta juya tana komawa xanyi hawaye y xubo a
idanuwan ta,lokacin yayi dai2 da shigowar Aslam
da sauri y taho harda sakin kayan hannunsa
kamar gaske,yana kai waya tabamin my princess
dita y karaso y rungumota ganin hawaye nasauka
a fuskarta yace tab kaka dukarmin mata kikayi
yaja hannun islam suka xauna a kujera y daurata
a cinyarsa yana goge mata hawayen da
hannunsa.
Kaka kuwa sakin baki tayi tana kallan ikon a
ranta tace ikon Allah dama yarannan xasuyi shiri
a rayuwa,cikin jin dadi kaka tace haba mai gdan
nikuwa mai xanyiwa islam dita,Aslam yace to
amma in ba abinda kikayi mata mai xaisa tayi
kuka,kaka tace kawai fa shagwaba ce dan banxo
gdan kuba,Aslam ne y fara bubbuga mata
baya,yana kiyi shiru kinji mai princess islam kuwa
tayi luf a kirjin Aslam tana futar da numfashi a
hankali.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 9:13 AM] +234 703 962 5239: na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*94*
Kaka ce tace to yar dadi miji baxaki sakko daga
cinyar tashi ba kika wani dane cinyar miji ko
kunya ta bakyaji,Aslam ne yace naji tsohuwar
nan da iyayi to ina ruwanki koma metayi mini
kema fa mijinta kikace ba wani ba ke wama
yasan irin tabarar da kika yiwa naki mijin dan
inaga kinada 9 years akayi miki aure,islam ce ta
kyalkyale da dariya tace Allah my prince kaka
tana 9 years akayi mata aure,wani dadi Aslam
yaji a ransa jin irin sunan da islam ta kirashi
dashi,yace eh mana islam tace tab wayaga
gwida yara,a tare suka kyalkyale da dariya Aslam
da islam,kaka ma dariya tayi tace naji ja'iran yara
kun tasani gaba kunamin shakiyanci sai a lokacin
islam ta sakko daga cinyar Aslam tace eyya kaka
ta ba wani shakiyanci abinne da ban dariya kina
fa 9 years kaka ce tace oho muku dai,sai lokacin
suka gaidata ta amsa mika mata ledar dinta da
sukayo mata shopping atamfa 1,turare1 sai
sabulu cikin jin dadi ta karba tayi godiya tana
saka musu albarka Aslam ne y tashi yace my
princess xomuje part din su mommy tace toh ta
mike hannunsu sakale cikin na juna suka
fuce,kaka kuwa tsantsan farin cikin datake ciki
yaki boyuwa tace ai dama nafada ana auradda
yarannan xasu shirya gashi kuwa nagani da kaina
ta tashi tahau rawar murna.
Su Aslam kuwa suna futa,Aslam yace yayi kyau
aljanar kaka kinaso wasanna mu yayi
kyau,murguda masa baki kawai tayi yace kin
manta matsar da nayiwa bakinki daxu ko,da sauri
tasa dayan hannunta ta tamke bakin,dariya
yadanyi mai sauti a haka suka karasa part din
mommy suka gaidata itada daddy dayake yau
sonday basu futa kasuwa da wuri ba,suma sun
basu tsarabarsu sunji dadi sun saka musu
albarka daddy ne y kalli islam yace my daughter
dftn dai xaman naku babu wata
matsala,murmushi tayi sai data kalli Aslam taga
shima ita yake kallo tace,dammm kirjin Aslam y
buga,lfy qlau dady,wata ajiyar xuciya Aslam yayi
har sai da daddy y kalleshi,da sauri y sunkuyar
da kansa,daddy yace da gaske kike daughter
bayayi miki komai tace eh daddy kanta a
kasa,yace to Allah yayi muku albarka sukace
ameen suka tashi,part din aunty amarya suka
shiga suma sunji dadin ganinsu bayan sun gaisa
Abba yace son dftn dai bata baka matsala a
xamannaku,Aslam ne y sunkuyar da kansa yace
eh daddy muna xaune lfy tanamin abinda
nakeso,murmushi Abba yayi yace to Allah yayi
muku albarka y baku yaya da xasuyi muku
biyayya,cikin jin kunya Aslam yace ameen nan
ma suka ajiye musu tsaraba suka koma part din
kaka.
Islam ce tace kaka ina Amira ne,kaka ce ta
karkata baki tace kinsan kasace ita tana daki
tana bacci mikewa Islam tayi ta cire after dress
din jikinta,tace bari naje na tasota,kaka kuwa
ruke baki tayi tace yanxu islam xaku futo ma
baxaki iya saka kaya na mutunci ba,islam ce
tana tafiya tace to kaka menene aibun
kayannan,kallan Aslam tayi tace ai laifin kane da
kana gani tasaka kayan baka hanata
ba,murmushi yayi yace kaka ai sam2 banason
bacin ran islam dan haka abinda takeso takeyi y
kwantar da kanshi a kujera y lumshe ido kaka ce
tayi tsaki tace Allah y kyauta.
Islam kuwa tana shiga dakin kan gado ta haye ta
janye blanket ta dakawa Amira duka firgigit
Amira ta farka a baccin da take,ganin islam ce ta
tashe ta da sauri ta rungume ta,tana oyoyo 6
yaushe kikaxo,islam tace ban sani ba kedai ba
kinanan kina bacci ba,Amira tace haba 6 bama
haka dake fa,islam tadan yatsina fuska tace daxu
ta tashi tana ki sameni a palo ta futa Amira
kuma ta shiga bathroom.
Haka su islam suka wuni a gda Aslam sai nan2
yakeyi da ita kamar gaske itama tasaki jikin ta,da
akaxo cin abinci firr Aslam y dage shida islam
xasuci domin a gda tare sukeci a cewarshi,haka
sukaci abincinnan yana bata a baki tana basa ko
kunyar su mommy basaji har suka koshi.
Da kyar Aslam y yadda Islam taje gdansu
khausar,hakan ma sai da Amira tace ai yaya
sagir din y tafi Jordan karatu,mammy taji dadin
ganin islam da xasu tafi mammy ta bata xumar
mata tace tadinga sha kullum da daddare islam
sarkin kwadayi ta dandana taji xaki tace toh ta
gode suka futo ita da Amira,da khausar.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 9:16 AM] +234 703 962 5239: Na Umma Yahya Musa*
*GOYON KAKA*
*95*
Sai da akayi sallar isha'i bayan Aslam y dawo a
masallaci sunyi dinner y kalli islam yace to my
princess ki tashi mu tafi,cikin shagwaba ta fara
magana harda diddira kafa haba my prince nifa
naxata ka dawo dani gda kenan,cikin mamaki su
mommy suke kallanta,daddy ne yayi murmushi
yace haba mamana ina kika taba ganin an aurar
da ya ta kuma dawo gdansu da xama,a lokacin
harta fara hawaye da sauri Aslam yaje y kama
hannunta yasa nashi hannun yana goge mata
hawaye yace haba princess harda kuka kuma,ki
bari nayi miki alkawari next week xan dada
kawoki kinji,cikin jin dadi ta washe hakora tace
Allah my prince kansa kawai y gyada yana
murmushi kallansu daddy tayi dayake hardasu
Abba a palon tace mun tafi saina dawo,dariya
Abba yayi yace ja'ira y kalli Aslam yace kai kuma
ka takarkare kana wani lallashinta harda goge
mata hawaye ko kunyar mu bakaji,lokaci daya
dukkansu suka dau dariya,banda islam data tura
baki gaba,Aslam kuwa keya y sosa,mommy ce ta
mike tace xonan my daughter taja hannunta suka
shige daki,ta kalli islam tace daughter kina tsarki
da ruwan dumin danace miki murmushi islam tayi
tace eh ai kwata2 ma bana tsarki da ruwan sanyi
cikin jin dadi mommy tace yauwa white misk ta
dauko a wata babbar kwalba tace ungo duk dare
ki dinga inserting dashi kanji,cikin mamaki islam
tace mommy ban game a,anan mommy tayi mata
bayani,dariya islam tayi tace to maganin
mene,murmushi mommy tayi tace maganin
sanyine sannan xakina kanshi kinji karfa ki dinga
mantawa,gyada kai islam tayi tace ai baxan
mantaba mommy tace yauwa daughter na tashi
muje Allah yayi miki albarka,islam tace ameen
suka futa,xaune suka tarar dasu daddy 5k daddy
da Abba suka bawa islam karba tayi tana godiya
suka futa part din kaka sukaje sukayi mata
sallama sannan Amira da sauran yaran gdan
suka rakosu mota suka tafi.
Tafiya sukeyi a cikin mota ba wanda yayi
magana,islam ce ta kalli Aslam ta marairaice
murya tace hero ice cream da shawarma
nakeso,harara y dallah mata yace to mai cikin
xani naga yanxu kika gamacin abinci,itama
harararsa tayi ta murguda baki tace naji mutum
da cikinsa ba'a hanashi cin abinci ba wasu ma
yanxu suna gadon asibiti so akeyi suci amma
babu hali,murmushi yayi a ransa yace yarinya
tausayin ki nakeyi amma hmmm,parking ya futa
y siyo mata shawarma da ice cream y mika
mata,dariya tayi tace ngd yaya,kallanta yayi yace
da akayi me?ta yatsina fuska tace
kawai,murmushi yayi a ransa yana yarinyar nan
ta daban ce watako ita bata barin takwana.
Tun a mota islam ta fara cin shawarmar ta kafin
suje gda harta cinye 1 tasha ice cream rabin
roba,gate man y wangale musu gate Aslam y
danna hancin motarsa yayi parking suka
futo,islam mika tayi tace wash Allah nagaji hero
kallanta yayi yace me kike nufi,kashe masa ido 1
tayi tace wai daka goyani duka yakai mata
takwasa a guje sai data je dai2 kofar shiga gdan
ta tsaya saboda key din yana hannun
Aslam,girgixa kai Aslam yayi yace narasa wanne
hukunci xanwa yarinyar nan ta dinga shakkata,sai
daya dauko ledar shopping din da bilal yayiwa
islam a wani dofane yana yatsina fuska tamkar y
dauko kashi,sannan y dauko ta shawarma da ice
cream y rufe kofar motar y karasa mikawa islam
ledar kayan yace dallah can rike kin barni da rike
kaya kamar wani danki,murmushi tayi tace to
naga daxu ma kaika dauka acan gda,banxa yayi
mata bai magana ba suka karasa shiga gdan.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 9:20 AM] +234 703 962 5239: *Na Umma Yahya Musa*
*GOYON KAKA*
*96*
Washe gari islam sai 10 o'clock ta tashi kamar
yadda ta saba bayan tayi sallar asuba ta
koma,bayan tayi mika tayi salati ta daura da
addu'ar tashi daga bacci bathroom ta shiga tayi
brush ta wanke fuska futowa tayi saboda kugin
da cikinta yakeyi mata sai data leka dakin Aslam
ta tarar dashi fes tabe baki tayi tace oho dai
baka fini tsafta ba nima dan inajin yunwa ne
shiyasa ban gyara bedroom din ba down stair ta
fara sauka tun tana kan step takeji wani
hadaddan kanshi y doki hancinta dada hura
hancin tayi ta shaka sai kuma ta lumshe ido tace
kai hero ba baya bane wajen iya girki karasa
sauka tayi ta leka dinning area taga
bayagun,kitchen ta tafi ganinshi tayi tsaye a
gaban gas cooker yana daure da eprome da hula
murmushi tayi tace gud morning hero,juyowa yayi
ganin ko wanka batayi ba murmushi yayi dan
yasan may be yunwa ce ta korota,yace morning
how are u,yatsina fuska tayi tace I'm not fine
because I'm feeling hungry murmushi yayi,yace
to acici meyasa baki futo tun daxu kin dafa ba
xakixo ki dameni da yunwa kikeji,hakora ta
washe a ranta tace baxan mayar maka ba dan
bakasan yunwar da nakeji bane, tadan sosa kai
tace kasan kafini iya abincine shiyasa,dai2
lokacin y gama soya kwai yace to naji xoki dauki
try dinnan kikai dinning dauka tayi takai shima y
futo dauke da wani try din.
Yau lfyr Allah sukaci abincinsu,chips da kwai sai
pepper soup na kayan ciki da tea daya saka su
citta da kanin fari,bayan sun gama islam ta mike
tace toh alhmdllh bayan ci xama tsegumi tana
shirin barin gurin,rikota Aslam yayi yace kina
nufin anan xaki bar kayan murmushi tayi tace
namanta kwashe kayan suka yi suka kai kitchen
futa islam take shirin yi da sauri Aslam yace ai
baki isaba