Showing 39001 words to 42000 words out of 96677 words
Chapter 14 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt
*61*
Lokacin dasu daddy suka koma gda,a tsaitsaye suka tarar dasu aunty amarya a sarraunding din gdan,da sauri suke tambayar shi y jikin Aslam din da sauki sukace baccima yakeyi lokacin da suka taho,sai lokacin hankakin su aunty amarya y kwanta.
Daddy ne yace aliyu jeka kirawo hajiya tunda part dinta akwai mutane saiku taho palo na xamuyi magana toh Abba yace y karasa part din kaka y kirata suka taho.
Xaxxaune suke,kowa yana jiran yaji mai daddy xaice y kirasu a darennan da xai kasa tsayawa har gari y waye,daddy yayi gyaran murya yace dangane da abinda ya samu Aslam ne ba komai yake damunshi ba illah matsanancin ciwon ciki,anan yayi musu bayani dai2 da yadda dr y fada masa,sannan da xabin daya basu.
Kowa hankalinsa y tashi,musamman da yaji har ana shirin yi masa aiki,kaka tace to mai xai hana ayiwa mai sunan malam din aure,Abba ne y tari numfashin ta yace to ai hajiya wai Ashe islam yakeso shiyasa yakiyin aure dan baxai iya hadata da wata mace ba a matsayin kishiya.
Kaka,aunty amarya da mommy ba karamin mamaki sukayi ba,saboda a iya saninsu ba wani shiri tsakanin islam da Aslam kwata2 basa xama a inuwa daya,kakace tace shi Aslam dinne y fada muku haka,daddy yace eh abokinsa y fadawa amma yace wai jira yakeyi ta gama makaranta.
Murmushi kaka tayi tace ai shikenan,yanxu menene shawara,daddy yace jira nakeyi yaji sauki kawai y nemo wata matar y aura,dan inya tsaya jiran islam ciwon xaifi haka tsamari tinda dududu nawa islam din take,in akwai rabo a tsakaninsu ko bayan ta gama makarantar sai suyi aure,aunty amarya tace gaskiya.
Kaka ce tayi tsaki,tace naji xancen banxa koku da kuke tsofai2 daku wane y ajiye mata 2,ta kalli aunty amarya tace ke kuma da kika biye masa fadamin wadda acikinku takeda kishiya,to wlh yadda dukkanku bakuda kishiya haka kuma baxa'a iya islam kishiya ba,na yanke hukunci nanda 2 weeks a shirya aurawa Aslam islam kuma kankanta da kuke cewa yanxu mu a kauye sa'ar islam ai tanada da,dan haka na yanke shawara in akwai mai magana sai yayi,mommy tace hajiya hakan yayi Allah y sanya alkhairi,kaka tace ameen,aunty amarya kuwa shiru tayi tana tunanin wannan kwamacalar.
Daddy ne yace hajiya munji shawararki kuma mun amince Allah y sakawa auran albarka,amma inaso dan Allah kar wanda y fadawa Aslam ko islam xancen aurannan saboda inaso nayiwa Aslam baxata,kaka ta washe baki tace ai wannan mai saukine Allah yayi muku albarka sukace ameen daganan taron y watse.
Aunty amaryace sai juyi takeyi akan gado,saboda tausayin yarda to nawa ma islam take da xa'ayi mata aure,meta sani a cikin rayuwar nan da har in akayi mata aure xata iya kula da mijinta,Abba ne yaga takasa bacci yace wai fateema meya hanaki vaccine,cikin sanyin murya tace wlh Abbn Amir ina tunanin aurannan da xa'a yiwa islam,nawa islam din take da xa'ace xa'ayi mata aure,dan allah kaje ka lallaba hajiya ta janye kudirinta akan aurannan,dan ina tausayawa rayuwar islam,tashi Abba yayi yace haba fateema yanxu kina nufin kinfi hajiya son islam karki manta hajiya ta xabi ran kowa y baci akan ran islam y baci,ni a ganina kawai muyiwa hajiya biyayya dan bahaushe yace abinda babba y hango yaro ko y hau bishiyar rimi baxai hangoba,addu'a xabin alkhairi ita y kamata kiyi ba damuwa ba,sai aunty amarya taji dadi a ranta saboda duk maganar da Abba y fada gaskiya ne tace toh Allah y xaba abinda yafi alkhairi,Abba yace ameen ko kefa.
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ.
(14/11/2016 3:30pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*
*62*
Sai 11:00pm Aslam y farka,a hankali y fara bude idonsa ganin dakin dayake shine y sakashi fara kallon dakin a hankali,Amir da safwan y gani a xaxxaune kallansu yayi yace meya kawoni nan,da sauri Amir y futa kiran limits safwan kuwa matsawa yayi,yana cemasa sannu y jikin,Aslam yace kaini fa bangane ba lokacin Amir suka shigo shida dr.
Matsawa jikin gadon dr yayi yace captain A.U Abdul kadeer y jikin Aslam yace ba inda yakemin ciwo sai rashin kwarin jiki,dr yace ai dama hakan xai faru yanxu ga magungunan da xaka shanan in kaci abinci cikin sanyin jiki Aslam y girgixa kai dr y futa.
Amir ne y mike yace bari naje gda na dauko tea flask da abinci yanxu nadawo,safwan yace toh,bayan futar Amir,Aslam y kalli safwan yace meya kawoni asibiti,safwan yace muma mun dawo daga gurin walimar su islam mukaxo muka tarar dakai a kwance a kasa ko numfashi bakayi,sai lokacin Aslam y tuno da matsanancin ciwon cikin daya turnike shi,cikin fargaba yace to su waye suka kawoni asibiti,safwan yace nida Amir,wata doguwar ajiyar xuciya Aslam yayi yace tnx god,safwan yace amma su Abba sun biyomu daga baya,dan su dr ma yayiwa bayanin abinda ke damunka,xaro dara2 idanunshi yayi gaba cikin kidima yace shikenan na kade har ganyena yanxu bani da dalilin da xan fada musu su kyaleni banyi aure ba harna kai 30 years,dariyar shakiyanci safwan yayi yace gashi dr yace in anaso ka rayu ayi maka aure a kurkusa,cikin kufula Aslam yace dayake shine da rayuwar tawa,shiru kowa yayi yana tunani a ransa,Aslam kuwa tunani yakeyi shi yanxu in ance y futo da mata y xaiyi don haryanxu baiga mace irin choice dinshi ba,after 20 minute Amir y dawo dauke da tea flask da food flask,tea kawai Aslam yasha saboda a yanda yakejin ransa ba abincin da xai iyaci,yana gama shan tea yasha magani y kwanta bawai don baccin yakeji ba,sai don kawai yanaso y samu sassauci a ranshi.
Washe gari,daddy,Abba,kaka,mommy,aunty amarya sukaxo duba shi,sun masa y jiki yace da sauki,kaka cikin xaulaya tace nida harna tanadi geron gumba,sai kuma naji ka tashi,kowa dariya yayi a dakin,Aslam kuwa yake kawai yakeyi don yana tsoron hukuncin da daddy xai yanke masa,sai 12:00pm sannan su mommy suka tashi tafiya don su Abba sun dade da tafiya kasuwa,Amir ne y tafi mayar dasu.
Misalin 2:00pm Amira ce ta shigo tace sis ki taso xamuje asibiti kaiwa su yaya Aslam abinci daganan mu duba jikinshi,tsaki islam tayi ta gyara kwanciya tace wlh baxani ba,ke bari kiji indai har sainaje duba hero xai warke to wlh sai dai yayita fama da jinya,tsaki Amira tayi tace kada Allah yasa kijedin ta fice suka tafi dayake yaya haidar ne xai kaisu.
Yau kwanan Aslam 3 a asibiti,amma ko sau 1 islam bata tabayin tunanin xuwa ba,yauma xaune take tana game a t.v kaka ta futo xata tafi asibitin tace islam taso muje kema yau ki duba mai sunan malam,islam ta yatsine fuska tace ash kaka Allah kaina yake ciwo,kaka tace amma kike wannan latse2 islam ta tashi ta kashe game din tace kwanciya xanje nayi tai shigewarta daki,tana cewa Allah y kiyaye naje duba mugunnan.
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ
[11/16, 5:02 PM] π¬ππSalmaπ¬ππ: (16/11/2016 1:00pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*
*63*
Kaka suna futowa sukayi clashing dasu Aslam an sallamosu,kaka ce ta karasa tana washe baki tace gawa taki rami,tunda kace dai baxamuci gumbar nan ba dole na fitar da geron na bayar sadaka,tunda wanda na ajiye dominsa y mike,dariya safwan yayi yace kuma kaka wlh dama na dade banci gumba ba,wani mugun kallo Aslam y jefeshi dashi,Amir kuwa murmushi yayi saboda dama shi bamai yawan magana bane,part dinsu suka wuce kaka ma ta wuce nata.
Bayan sun shiga bedroom din Aslam,bandaki Aslam y shiga yayi wanka bayan y futo y shirya safwan ma y shiga abinci aka kawo musu bayan sun gamaci,aunty amarya da mommy sunxo sun dada duba jikin Aslam,haka yaran gdan sunata shigowa har tasleem amma ba islam ba alamarta.
Cikin xaulaya safwan yace abokina nifa banga jerry dinka taxo dibiya ba dukkuwa da safa da marwan da yaran gdannan sukeyi,Aslam ne y daga gira daya yace so what,dama banaso taxo dannasan in taxo ba alkhairi ne xai kawota ba,shiru safwan yayi yana jadda irin taurin xuciya irinna islam,ace gata yar karamar yarinya amma kwata2 batasan yafiya ba,Aslam ne y katse masa tunaninsa ta hanyar magana yace wlh ni babban abinda nake tsoro bai wuce irin hukuncin dasu daddy xasu yankemin ba,dan tunda kaji sunyi shiru to Allah ne kadai yasan abinda suke kullawa,murmushi safwan yayi yace karka damu abookina insha Allah duk hukuncin da xasu yanke baxai maka tsauri ba,Aslam yace Allah yasa,safwan yace ameen daganan sukaci gaba da hira.
Bayan sallar isha'i su Aslam suna xaxxaune suna hira wayarsa ta fara ringing,ganin wanda yake kiranshi shine y haddasa masa faduwar gaba cikin sanyin murya y daga,dagacan bangaren daddy yace kaxo yanxu ka sameni a palo na,Aslam yace to y katse kiran,kallan safwan yayi yace ta faru ta kare,safwan yace anwa mai dami 1 sata meya faru,Aslam yace daddy ke nemana yanxu,safwan yace toh Allah yasa kajiyo alkhairi,tsaki Aslam yayi yace y wuce yamin xancen aure ni wlh tunanin yarinyar daxan aura nakeyi dan duk kano banga tsarata ba (nikuwa nace karyane π) gashi bankai 30 year dinba,safwan yace toh nan da kakai 30 year ai in Allah y nufa munada baby kenan ko y tuntsire da dariya,harararsa Aslam yayi yace dadina dakai kai banxane wlh yayi tsaki y fice,dariya safwan yayi yace naji.
Aslam ne xaune a gaban daddy,Abba,kaka,aunty amarya,mommy,daddy yace ba sainayi dogon bayani akan rashin lfyrka ba saboda kasan mai yake damunka,haka muma munsani dukkuwa da tsawon lokaci daka dauka kana boyemana,to yanxu muda iyayenka mun yanke hukuncin aurar dakai,kuma basai kayi tunanin nemo matar aureba,nariga nayi shawara da wani dan'uwana aminina kuma abokina xamu hadaku aure da yarsa,lokaci guda komai na Aslam y tsaya cak nayan mintuna wani gumi neya fara karyo masa,dukkuwa da sanyin a.c da yake dakin,daddy ganin yanayin da Aslam y shiga shine y sakashi murmushi don duk a tunaninsa y shiga wannan halinne saboda xa'a rabashi da islam.
Aslam kuwa a ranshi cewa yakeyi yanxu da girmana xa'amin auran dole,bama wannan ba dama anawa namiji auran dolene,tuni kanshi y wani sara masa,idanuwanshi suka yi jajawur gashin jikin shi duk y tashi,daddy ne yace kuma dududu yanxu aurannaku saura 9 day,cikin raxana Aslam y dago rinannun idanuwansa y saukesu akan daddy,daddy yace yarinyar bata kasarnan tana calfonia tana karatu,ranar da xata dawo shiyayi dai2 da ranar daurin auranku,cikin sanyin murya Aslam yace toh dan baxai iya ja da hukuncin da daddyn sa y yanke a kansa ba,daddy yace ko kanada magana girgixa kai Aslam yayi dan yadda xuciyarsa take masa tukuki da xafi baxai iya magana ba,daddy yace toh Allah y yima albarka dukka dakin sukace ameen.
Aunty amarya kuwa wani mugun tausayin Aslam taji saboda ganin irin yanayin daya shiga,da tana da dama babu abinda xaisa ta hana afkuwar aurannan to itama anfi karfinta ne,dady y kalli su Abba yace akwai mai magana sukace a'ah,kaka ce ta washe baki tace Abu yayi kyau Allah yayi albarka y sanya alkhairi,kowa yace ameen,daddy yacewa Aslam xaka iya tafiya,tashi yayi wani mugun jiri yaji yana kwasarshi ahaka dai y futa yana hada hanya ikon Allah ne kawai y kaishi dakinsa,saboda yadda idanunsa yake ganin dishi2.
Taku har kullum *sisin mama*
πππ
*mrs hamisu taura*
πππ
[11/16, 5:02 PM] π¬ππSalmaπ¬ππ: (16/11/2016 2:00pm) *na umma yahya musa*
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON KAKA*
*64*
Yana shiga bedroom din ko sallama baiyi ba y fada kan gado y dafe kansa,saboda yadda yake baraxanar tarwatsewa,safwanne ganin yanayin da abokinnasa y shigo dashi,y sashi yin magana yace y dai aboki wai meya farune.
Sai da Aslam ya dauki 3 minute sannan yace su daddy ne suka yanke hukuncin yimin auran dole,cikin raxana safwan y xaro idanunsa waje yana auran dole y nuna irin baisan komai dinnan ba,a ranshi kuwa yana addu'a Allah yasa da islam xa'a hada abokinnasa dan sunyi bala'in matching halinsu nedai da banbanci,Aslam y dago rinannun idanuwan shi y saukesu akan safwan yace eh,cikin jimami safwan yace toh wace yarinyar da aka hadaka da ita,Aslam yace nima ban santa ba amma yar gdan abokin Abba ce a colfonia wai take karatu,cikin mutuwar jiki safwan yaji bada islam xa'ayi auran ba yace toya sunanta daga kafada Aslam yayi yace nima bansani ba dan yadda hankalina y tashi ko tambayar sunanta banyi ba,safwan yace kayi hakuri kayi musu biyayya insha Allah baxaka tabeba xakayi alfahari da aurannan gaba,tsaki Aslam yayi yace to xancen yaushe ma bikinfa wai saura 9 day,dariya safwan yayi yace ah kace mun kusa angwancewa lallai ranar xamu kwashi shokii,harararsa Aslam yayi yace uban wane xaiyi wani bidiri a bikin,safwan yace wlh baka isaba dole muyi bikin da xa'a gani a kara gani,kai y kamata ma tun yanxu mu fara rubuta preparation din da xamu gudanar,wani malolon bakin cikine y turnike Aslam ganin safwan ma murna yake da aurannan,yace da ubanwa xakayi preparation din safwan cikin jin dadi yace to duk duniyar nan akwai wanda y kamata ayi shirye2 bikinsa dashi daya wuce ango,a xabure Aslam y mike jin safwan y kirashi da ango don saiyaji tamkar y burma masa wukane,wani naushi y kaiwa safwan da sauri safwan y goce yana dariya y fice a dakin da gudu yace bari naje nayiwa Amir albishir din bikin babban yaya,y fice a dakin,Aslam kuwa gini y nausa y koma y fada kan gado shi kadai yasan irin wulakanci da rashin mutuncin daya tanadarwa yarinyar nan tunda tayi gigin yarda ta bata masa dukkan plan dinsa,wani murmushine y subuce masa tunawa da ixayar daxaiwa wannan amaryar mara rabo.
Washe gari mommy da kanta takirawo mai gyaran jiki a waya tanaso xatayiwa yarta gyaran jiki na 8 day sukayi xata xata bata 50k har kunshi mommy tace toh yau takeso a farayiwa amaryar amma bataso ta nunawa amaryar saboda aure xa'a yimata gyaran jikin,mai gyaran jikin tace toh.
2:00pm mai gyaran jiki taxo mommy da kanta taje dakin kaka ta tahoda islam tun a hanya mommy tace yata saboda kokarin da kikayi a makaranta nasaka mai gyaran jiki taxo tayi miki saboda inaso ki dadayin kyau,baki islam ta washe tace kai ammafa mommy naji dadi ngd ni kadai xa'a yiwa ba Amira mommy tace eh sai an gamayi miki na 8 day sannan xa'a yiwa Amira cikin jin dadi islam tace toh suka karasa part din mommy,wani empty room mommy ta basu anan aka fara gyaran jiki sai da suka dauki 3 hour sannan suka gama tuni islam ta dauki wani kyalli da sheki banda fitinannen kanshin da takeyi sakamokon hadadden turaren jiki na amare da mai gyaran jikin ta turara mata,islam kuwa sai dariya takeyi saboda yadda skin dinta ta kara kyau da sheki,ita kanta mai gyaran jikin masha Allah kawai take cewa saboda ganin yadda ayi daya islam tayi mugun kyau,kunun hulba ta dama mata islam sarkin kwadayi taji madara da suga aciki kamar xasuyi magana da wuri ta shanye aka xuba mata xumima shima shanye shi tayi tana tande baki π,mai gyaran jikin ta kalli islam tace toh yata daga yanxu ta futo da wani sabulu tace da wannan xakina wanka sannan ta dauko humrah 2 tace wannan