Showing 54001 words to 57000 words out of 96677 words
Chapter 19 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt
sukabar gdan dayake akwai driver
dayake jiransu.
Aslam ne kwance a dakinsa safwan y shigo yana
haba ango tun daxu an kaimaka amaryar ka y
kamata ka shirya muje mu rakaka daganan musai
bakin amarya,wani mugun kallo y jefi safwan
dashi y doka wani uban tsaki y shige bathroom
dariya safwan yayi y samu guri y xauna,20
minute Aslam y dauka y futo daure da towel yana
tsane jikin shi da wani xama yayi a gaban
dressing mirrow y shirya tsaf y taje kanshi da
kwantaccen sajenshi bayan y saka singlet da
boxwr y dauko wata arniyar shadda galila ash
colour y dauka y saka y feshe jikinshi da turaruka
masu dadin kanshi hula dara baka yasa sai
takalmi mai danyatsa shima baki ba karamin
kyau yayi ba dukkuwa da yanda fuskarsa take a
tamke,wayoyinsa y dauka akan dressing mirrow
da key din mota y kama hanya xai fice ko kallan
safwan da amir baiyi ba,safwan ne yace ah haba
ango tun daxu fa kai muke jira muyi maka rakiya
amma naga kana shirin wucemu wani yatsina
fuska Aslam yayi yace bana bukata ko ana dole
yasa kai y fice.
Sallama yaje y yiwa iyayanshi sannan y kama
hanya y tafi driving yakeyi amma ranshi duk a
jagule,tsintar kanshi yayi da tsayawa gurin mai
saida kaxa kulli 2 yasaka akayi masa y cillasu
bayan mota y wuce,horn yakeyi a bakin gate din
gdannashi cikin sauri gateman y bude yana sara
masa yana ur wlcm sir dayake soja ne,direct
packing space yaje yayi packing din motar.
Islam kuwa bayan ta futo a wanka gani tayi
bataga su Amira ba,harta shagwabe fuska xatayi
kuka xatayi kuka sai kuma ta tuna kila suna palo
xama tayi gaban dressing mirrow ta shafa mai
sai powder tadan xixara kwalli,tasaka lip stick ta
mulke jikinta da humra mai mugun kanshi ta
dada da body spray sannan ta saka sleeping
dress din ta kama gashinta da ribon ganin irin
kyawun da tayi da ai sai tahau tsalle da sauri ta
saka wani takalmi sosa ta kwasa da gudu ta futo
a dakin ganin bataga su khausar a palon ba tayi
kasa wayam tagani basu khausar ba alamarsu
tahau kwala musu kira khausar!Amira!mommy!
Jin shiru ai saita hau kuka da gudu ta haura
sama saboda tsoron da taji y kamata direct
dakinta ta wuce ta fada kan gado tahau
shashshekar kuka tana kiran sunansu.
Futowa yayi a motar bayan y dauko ledojin kajin
daya siyo,cikin tafiyarsa ta xaratan maxa yake
takunsa cikin kasaita harya karasa shiga
palon,siririn tsaki yayi ganin yadda palon y
kawata amma sai dai kash ba matar da xaiji
dadin rayuwar auransa bace a gdan,bismillah yayi
y sakawa kofar key y haura stair tun daga palo
yakejin shashshekar kukanta cikin jin haushi da
xafin xuciya yayi hanyar dakinnata tura kofar yayi
da karfi a xafafe yace kukan uban me kike yiwa
mutane sai kace gdan makoki,cikin raxana islam
ta dago kanta ganin wanda yake tsaye shine y
sakata yin tsaki,a ranta tana Allah y isa tsoron
daya bata,ta komar da kanta kan pillow taci gaba
da kiransu mommy tana kuka tsaki shima yayi a
ransa yana xan gyara miki xamane,cilla mata
kunshin kaxa 1 yayi yace gashinan in kinga dama
kici yaja mata kofa.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:37 AM] +234 703 962 5239: *GOYON KAKA*
*81*
Direct dakinshi y wuce xuciyarshi nayi masa
tukukin ciwo,bude kofar yayi wow gaskiya shima
dakinnashi y hadu exartly kayan gadon irinna
dakin islam ne colour ne kawai y banbanta,cire
hularshi yayi da ogogo da wayoyinsa y daurasu
kan bedsite cabinet sannan y cire rigarshi y bude
wardrop y sakaleta ajikin hanger y xamana
dagashi sai singlate bakin gado y xauna tsaki
yaja y dafe kanshi saboda baraxanar tarwatsewa
da yakeyi saboda tsabar damuwa a ranshi yace
gaskiya an cuceni y kamata a yanxu ace inacan
inajin dadi irinna ko wanne ango ranar da amarya
ta tare amma nisam abin ba haka yake ba saima
dan karen damuwa da tamin yawa (nikuwa nace
kai kaso ) tsaki y karayi y kwanta kafafunshi na
kasa fuskarshi na facing din p.o.p din dakin y
tallafe kanshi da hannuwanshi biyu tunani y
xurfafa sosai.
Can wata xuciyar tace masa haba Aslam
alkawarin da kayiwa iyayenka kenan xaka rike
islam amana,wannan itace amanar ace kaxo ka
tarar yarinya na kuka koka lallameta alhalin
kasan kuruciya na dibanta kuma tunda take
yauce rana ta farko da xata kwana ita kadai a
daki ka duba girman alkawari fa,daya xuciyar ce
tace to ai na tsaneta banason ganinta sam,daya
xuciyar tace dole ka sassauta kiyayyarta a
xuciyarka saboda yanxu ita wani nauyi ce da
Allah y daura maka,kuma tabbas xa'a tambayeka
ranar lahira yaya katafi da hakkokinta na
duniya,xuruf naga y mike kamar wanda aka
tsikara y fice a dakinnasa dakin islam y tafi a
hankali take tafiyar tamkar wadda wani Abu yake
masa ciwo a ciki tura kofar yayi har lokacin tana
kife akan pillow tana kuka a hankali y tura kofar
dakinnata y dade tsaye a kanta,sannan y bude
bakinsa yace ke kamar wanda bakin yakewa
ciwo.
Rinannun idanuwanta ta dago ta kalleshi ta daka
masa wata uwar harara ta murguda baki ta
mayar da kanta kan pillow taci gaba da kukanta
tana kiransu mommy,jikin shine yayi sanyi lokaci
daya tausayinta y dirar masa abinda bai taba jiba
a iya tsayin rayuwarsa duk da islam ta wuce 2
years,a hankali y buda baki y kira sunanta islam!
wani dam islam taji girjinta saboda yadda taji
Aslam y fadi sunanta ita bada ban kartayi karya
ba da tace duk duniya yafi kowa iya fadin
sunanta saboda yadda yake fitar da kowanne
harafi (nikuwa nace to fa) sai kuma tayi tsaki ta
karkatar da baki tace kila dan ban saba jin y kira
sunanta bane daga yace *ke* sai *aljanar
yarinyarnan* ko *banxar yarinyarnan*,shine y
katse mata tunanin nata yace kukan me kikeyi,da
kamar baxatayi magana ba saboda haushinsa da
takeji tunda shine dalilin daya saka yau aka
rabata da yan'uwanta,sai kuma can ta budi baki
tace mommy ce ta tafi dasu Amira ni ka mayar
dani gda ta karashe maganar da kuka,tsaki yayi
yace ke a ina kika tabajin a ranar da akakai
yarinya gdan miji a daren an mayar da
ita,kallanshi tayi shekeke tace to ka sakeni
bashikenan ba,kallanta yayi da mamaki yace
watako hartasan saki shine abinda xai
rabasu,murmushin yake yayi wanda yafi kuka
ciwo,yace baki fini son mu rabuba amma hakan
baxai yiwu ba saboda su daddy ne suka hada
auran kinga su suke da alhakin rabashi,idan har
kina ganin xaki iya xuwa kisaka suce na sakeki
fine y daga kafada yace hanya a bude take,shiru
tayi dan tasan baxasu taba yadda yaya Aslam y
saketa ba domin da xasu yadda da tun ranar da
akace an daura musu auran yadda ta tubure tace
batason shi da an rabasu,tsaki tayi ta tashi daga
kan gadon tana wlh komai daren dadewa sai
mutum y sakeni na auri wanda nakeso,jikin jin
haushi da gajiya da bakaken maganganunsa yayi
kanta y daukota yace da uban wane yace shi
yana sonki,kuma inna karajin kinyi xancen wani
kina gdannan to wlh ranki sai yayi mugun baci y
hankadata gadon y fice a dakin yaja kofar da
karfi,tashi tayi tace aikin banxa ba wanda y isa y
hanani hirar masoyi na kuma farin cikin
rayuwata,karasawa tayi ta dauko kaxarta xama
tayi ta cita sosai,dan rabon data nitsu taci abinci
tun randa aka sanar mata itace matar Aslam
bayan ta gamaci ta nade ragowar ta daura kan
dan karamin fridge din dayake dakin,ta bude ta
dauko fresh milk tasha bathroom taje ta wanko
bakin ta da hannunta,ta kwanta kan gadonta taja
blanket bata dade ba,bacci mai dadi y kwashe ta
saboda kukan dataci a hankali take sauke ajiyar
xuciya.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:43 AM] +234 703 962 5239: *GOYON KAKA*
*82*
*washe gari*
Aslam y futo xai tafi masallaci har xai shige
dakin Aslam kawai yaji a ransa y kamata yaje y
tasheta tunda yanxu hadda hakkin kula da
addininta ne a kansa kofar y tura kawai saiya jita
a bude,can y ganota kudindine acikin blanket
tana ta sharar baccinta hankalinta kwance
tashinta y farayi yana ke,ke,ke a hankali ta fara
bude idonta tarr ta saukesu akan Aslam xumbura
baki tayi ta mayar da kanta gefe tace
menene,harararta yayi yace dallacan tashi kiyi
sallah kin saki baki da hanci kina bacci kin
cikawa mutane gda da munshari,murmuda baki
tayi tace wlh ni bana munshari,harararta y
kumayi yace nayi karya kenan,ta yatsina fuska
tace eh kusan hakanne,xaro ido yayi yana
kallonta ita kuwa ta diro daga gado tayi mika
hade da salati ta tattara gashinta daya barbaje
garin bacci tashige bathroom ta barshi baki
sake,tsaki yayi y juya y fice,islam tana futowa
wardrop ta bude ta dauko hijab kato har kasa da
sallaya ta shimfida sai da tayi raka'atanul fijri
sannan tayi sallar asuba,axkar tayi takaranta
qur'ani kusan ixu 2 sannan tayi hasbunallahu
wani'imal wakil kafa 450 taci gaba da istigfari sai
6:30am ta tashi ta karayin nafila raka'a 2 sannan
ta koma kan gado bata dade ba bacci mai dadi
yayi gaba da ita.
9 o'clock ta farka a hankali tayi salati ga annabi
sannan tayi addu'ar tashi a bacci kamar haka
*bismikallahumma amutu wa ahya*
*alhmdllhillaxi ahayana ba'ada ma a matana wa
ilaihinnushur* sannan tayi mika dirowa tayi daga
kan gado ta karkadeshi duk da ba datti yayi ba ta
gyarashi tsaf (nace kai Ashe islam din kakan ta
iya gyara ) tana gamawa ta fada bathroom ta
sakarwa kanta shower 10 minute ta dauka ta
futo tana tsana jikinta da towel xama tayi gaban
dressing mirow mai kawai ta shafa sai powder
sai ta saka lipstick jikinta ta mulke da humrah
sai ta fesa body spray sai ta shafa roll on,abinda
nayi noticing da islam ita sam bata kwalliya ko
iyawa ne kuma batayi ba oho ,wani three quarter
wando baki ta saka sai body hug datasa purple
colour mai gajeren hannu ta taje gashinta ta fesa
hair spray na olive ta tufke gashinnata da purple
ribom jelarshi ta sauko har gadon bayanta tana
reto (nikiwa nave amaryar xamani watako bata
tunanin baki tasaka englis wears) wani daddadan
turare ta dauko ta dunga feshe jikinta tana gama
kintsawa ta tsaya gaban mudubi ta karewa kanta
kallo sai kuma tayi murmushi jin cikinta yana
mata kugi shine y sakata shagwabe fuska tace
wash yunwa nakeji y xanyi kawai sai tayi nasai2
da ido tana shirin yin kuka sai kuma naga ta xura
takalmi ta fita karewa palon kallo tayi tace wow
gaskiya palonnan yayi kyau a hankali ta tafi
sadaf Sadat ta tura kofar dakin dayake opposite
nata aikuwa a bude yake turawa tayi wani
daddadan kanshine y dakar mata hanci har sai
data lumshe ido a hankali ta karewa dakin kallo
komai need kayan furniture din ma irinna
dakintane kome ta tuna kuma sai ta tabe baki
taja kofar ta rufe,kofar kusa da dakinta taje ta
tura sai tajita a ride,tsaki tayi kome ta tuna kuma
sainaga ta koma dakinta da sauri gwangwanin air
freshiner ta bude ta fesawa dakinnata kusan kala
3,tana eh nima mutum baxai nunamin tsafta ba
ta karashe maganar da murguda baki sannan ta
futo tajanyo kofar ta sauka kasa.
Xaune ta ganshi yana kallon lbrai shima yayi
wanka yana sanye da shadda light purple kanshi
ba hula amma gashin shi sai kyalli yakeyi sajensa
kuma y kwanta luf,hannun shi daure da agogon
gucci na fata light purple,kafarshi sanye da
slippers milk colour na fata sai xuba kanshi yake
saikuma ta tabe baki lokacin data gama
kallansa,hararta yayi yace menene kika xubamin
wannan manyan idonnaki kamar na mayu kina
kallona,murguda baki tayi tace kai da wanne idon
kasan ina kallanka,kuma in manyan idone ai ka
fini kaga saika tantance idon waye yafi kamada
na mayu ta karashe maganar tana harararsa,cikin
jin xafin maganganunta y tashi da niyyar kwade
ta dan baxai iya cika alkawarin daya daukarwa
aunty amarya ba,ita kuwa ganin abinda yake
niyyar yi y sakata tashi da sauri shirin runtumar
na kare takeyi taku daya yayi y dankota kwallah
kara tayi tana wayyo Allah nashiga 3 xai kasheni
daga hannu yayi da niyyar buge mata bakin sai
yaji an danna bell.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:44 AM] +234 703 962 5239: *na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*83*
Daga hannu yayi da niyyar bige mata baki,ita
kuwa ta tattara hannuwanta ta rufe fuskarta
saukar mari kawai take jira sai sukaji karar
bell,hankada ta yayi ta fada kan kujera,hararar
bayanshi tayi tace Allah y isa.
Xuwa yayi yana waye muryoyin su Amira yaji
suna mune yaya tsaki yayi y bude y coge ba
bakin kofar,cikin rawar jiki sukace yaya ina
kwana,sai daya gama shan kanshinsa sannan y
amsa da lfy,y yatsine fuska yace uban me
kukaxo min gda da sassafennan cikin rawar
murya sukace break fast muka kawo
muku,kallansu yayi yace waya kawo ku sukace
isya driver amma y koma sai lokacin y matsa
musu hanya suka wuce,islam da take xaune kan
kujera tana tacin magani saboda lokacin da
Aslam y hankada ta kan kujera ta buge kanta
ganin wadanda suka shigo gdan da gudu ta tashi
tana murna hade da tsalle taje ta
rungumesu,suma cikin jin dadi suka tungumeta
suna ta murna,Aslam kuwa ganin shirmen da
sukeyi y saka shi tabe baki yayi tsaki basket din
da sukaxo dashi y dauka yakai dinning kitchen y
shiga y dauko cup da plate da tea spoon da pock
y futo y wuce dinning area domin yaci abinci.
Su islam kuwa bayan sun gama tsalle2 nasu ta
matsa gefe ta rike kugu ta karkace baki tace
meyasa jiya kuka gudu kuka barni,shikuwa Aslam
dayake dining area murmushi yayi yace wannan
yarinyar bata da hakuri watako duk murnar
ganinsu da takeyi amma sai tayi mita,Amira ce
tace wlh mommy ce tace mu tashi mu tafi
gda,islam tace toh amma yau Allah sai kun
kwana khausar tace a'ah mommy tace anayin
magruba mu koma,tsaki islam tayi ta kufa
banxayene ku tashi muje muyi break,Amira ce ta
xauna a kujera tace nidai nakoshi bansan kausar
ba,itama tace ta koshi islam ta juya tace nikam
yunwa nakeji dama tun daxu kamar naci babu ta
wuce.
Karasawa tayi taja kujera 1 ta xauna ta kalli
Aslam tace ina plate dinnawa kuma,wani banxan
kallo y jefeta dashi yace yaje koyan
gaisuwa,murmushi tayi har dimple dinta y lotsa
tadan sosa kai tace au ina kwana,tsaki yayi yace
daban kwana ba xaki ganni itama tsakin tayi tace
naji mutum yace na gaisheshi,na gaisheshi kuma
yana min iyayi,kallan mamaki yake mata yama
kasa magana saboda y fahinci rainin hankalin
islam yayi yawa ko yaushe da kalar wanda take
kirkiro dashi,katse masa tunaninsa tayi ta hanyar
cewa yaya nifa yunwa nakeji,harararta yayi
yadanyi tsaki yace wlh in baki daina min rainin
hankalinnan ba yanxu jikin ki xai fada miki in
banda kin rainani ma ni kikeso natashi na dauko
miki plate da cup din,kuma da kike cemin yunwa
kikeji gaba abinci ba koni kikeso naxama abincin
ciki,bude bakinta tayi tana kallansa da mamaki
sai kuma tayi yar dariya tace tab to ai kai yaya
ko abinci kaxama wlh babu mai cinka saboda
sam baxakayi armashi ba ta karashe maganar da
kyalkyalewa da dariya,shikuwa Aslam ji yayi wani
tukukin bakin ciki y turnike shi ga wani Abu
dayaji y tokare masa xuciya tunani y tafi wai
meyasa yarinyar nan ta iya fadar bakaken
maganganu masu ciwo ne can wata xuciyar tace
ai kai kadai take fadawa maganganu son
ranta,dafe kanshi yayi yace to meyasa ta rainani
ne a iya sanina ko matasa sa'anni na shakkata
sukeyi kallan kansa yayi yaga irin kirar da Allah
yayi masa ta karfafan maxa kwafa kawai yayi y
mike lokacin islam ta dawo rikeda plate da cup
ganin y tashi tace yaya harka koshi,yace bansani
ba y wuce daga kafadarta tayi ta murguda baki
tace kada Allah yasa ka Sani din.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:45 AM] +234 703 962 5239: *GOYON KAKA*
*84*
Palo y karasa y dauki key din mota da wayoyinsa
y fuce su Amira sunayi masa a dawo lfy ko amsa
musu baiyi ba shiga motar shi yayi y fice direct
gda yayi.
Islam kuwa xama tayi ta cika cikinta daganan ta
koma palo selection suka saka na india suka
kure home theater har bakin gate anajin karar
suka har dirkar rawa baji ba gani,islam kuwa sai
wani karye2 takeyi tamkar karina kapoor lol
,saboda islam ba baya bace dama wajen rawa.
Islam kuwa yana xuwa direct part din mommy
yace suka gaisa ta tambaye shi y islam,kanshi y
sosa yace tananan lfy jiya tanata kuka wai kun
tafi kun barta dakyar na lallameta tayi
shiru,murmushi mommy tayi tace islam rigima
dan Allah son ka rike islam amana nasan sai kayi
hakuri saboda yanxu kuruciya na dibanta amma a
hankali komai xai dai2 ta domin irin abinda ka
horar dashi to dashi xata tashi dan haka ka koya
mata dabi'u masu kyau jikinsa ne duk yayi
sanyi,sannan dan Allah karka dinga takura mata
kasan dai yarinya ce batasan komai akan rayuwar
aure ba,cikin jin kunya yace toh mommy tace
Allah yayi muku albarka yace ameen,tambayarta
yayi yace daddy fa tace sun tafi kasuwa yace
Allah y dawo dasu lfy,mommy tace ameen y
tashi yace bari nakarasa gurin aunty na
murmushi mommy tayi shikuma y tashi y futa.
Da sallama y shiga part din aunty amarya ta
amsa masa sallama cikin farin ciki fuskarta
dauke da murmushi da sauri y karasa y xauna a
kusa da aunty y daura kanshi a kafadarta yace
aunty ne barka da safiya cikin jin dadi ta shafa
kanshi tace barkan mudai y gda,y angwanci
dariya yayi yace aunty angwanci kuma (saboda
tun tashin Aslam baya taba iya boyewa aunty
amarya damuwarsa saboda itace abokiyar
shawararsa) tace eh mana ko xubawa islam din
ido kayi dariya yayi yadan shafi kansa yace haba
aunty nawa islam din take nikam saina raineta
ma nifa ina tunanin islam bama tasan menene
aure ba,dan xungurinsa tayi tace au haka kake
tunani ashema auran bashi da wani amfani tunda
baxai yi maganin cutar taka ba tashi yayi yana
dariya yace nifa aunty na gaskiya kunya nakeji
banaso ta rainani y mike dariya itama aunty
amarya tayi tace kujini da ja'irin yaro to kasata a
gaba kana kallo tamkar t.v ficewa yayi a part din
yana dariya part din kaka y wuce.
Xaune y tarar da ita tana kallan t.v da Sauri y
karasa yayi hugging dinta yace uwar gda ran gda
uwar gda sarautar mata,dariya kaka tayi tace ni
cikani ja'iri,hade rai yayi yace Allah xan sakeki
kika kara kirana da wannan sunan kinsan yanxu
inada mata kuma in kika bari nayi xuciya to saina
shekara 1 baki kara ganina ba,harararsa tayi tace
toda yanxu wane y kiraka inka tashi tafiya kafi
ruwa gudu kuma ma ai da tsohuwar xuma ake
magani,yanxu naxata kasan kana da amaryar
amma ka taho gurina,dariya yayi yace yar
tsohuwar nan da kishi kike to maida wukar
kinsan dai amaryata special 1 ce tsaki kaka tayi
tace kaikasan abinda kake nufi,tashi yayi yana
naga yau xuciyar ki a kusa take bari natafi kafin
fadannaki yakai ga duka y fice.
Part din samarin gdan y wuce direct tsohon
dakinsa y nufa saboda yasan safwan yana can a
kwance y tarar da safwan yana bacci tashinshi y
farayi,a hankali safwan yake bude idanuwanshi
tarr y tsaidasu kan Aslam mikewa yayi y shiga
bathroom yayo brush y futo.
Taku har kullum *sisin mama*
*mrs hamisu taura*
[3/7, 8:46 AM] +234 703 962 5239: *na umma yahya musa*
*GOYON KAKA*
*85*
Safwan yana futowa daga bathroom y fara ango
ango kasha kanshi kaga yadda kake kyallin
angwanci kuwa,lallai daga ganinka jiya ka kashe
arna irin wannan kyau haka y karashe maganar
da dariyar shakiyanci,Aslam ne yayi tsaki yace
dadina dakai wlh banxa ne wataran in xakayi
magana sam baka taunata kawai fadar ta
kake,dariya safwan yayi yace to menene acikin
magana ta laifi,cikin kufula Aslam yace
bkmai,safwan yace nifa yau xan koma dan
harnaje na yanki ticket by 5 o'clock flight din xai
tashi,Aslam yace OK nima next week xan
dawo,cikin mamaki safwan yake kallanshi yace
ammh amma da islam din xaka taho ko,wani
kallan tara saura kwata Aslam yayiwa safwan
yace eh tunda naxama na mamajo ba,dariya
safwan yayi yace xaka iya xama hakan ma amma
y xame maka dole ka taho da matarka tunda 1
month aka baka hutu,wani kallan banxa Aslam
yayiwa safwan yace toh sannu daddy tunda har
umarni kake bani,dariya safwan yayi yace ba
haka nake nufi ba kasan dai