Showing 15001 words to 18000 words out of 96677 words

Chapter 6 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt

02 Jan 2025

74037

kara futo da ainahin kyawunsa yace ai surprising dinku nayi,tace lallai kam kuma kaci hannunsa ta kama da daya hannun kuma y dauko jakarshi suka karasa shiga part din mommy a palo suka tarar da mommy tana kallon arewa 24 da sauri y saki hannun aunty amarya yaje y rungume mommy dariya mommy tayi tace auntyn yara gaskiya yaronnan naki baya girma kiga yadda yaxo y turmusheni,shagwabe fuska yayi yace kai my mom yanxu bakiyi missing dina ba (ni dariya y banima yadda yake shagwabe fuska 😂) aunty amarya tace a'ah mommy ai duk cikin kewarmu ne tashi Aslam yayi yace su daddy basu dawo ba mommy tace eh suna kasuwa yace OK banaje naga my granny da sassarfa y fice,mommy tace auntyn yara kiga yadda danki ya wani xama kato dariya aunty amarya tayi tace ai aikin soja ba wasa bane shiyasa nake alfahari da dana dariya mommy tayi tace gaskiya tashi aunty amarya tayi tace bari naje na hadawa my son abinda xaici tunda bai sanar damu ba girgixa kai mommy tayi itadai tana farin cikin irin yadda fateema takeson yayanta.


Da sallama y shiga part din kaka kaka ta tashi da hanxari tana wanake gani kamar mai gidana da sauri y karasa yahau juya kaka saida y wanata tamkar fanka sannan y rungumeta kaka kuwa sai maida numfashi takeyi 😂,yace wlh matar nayi kewarki sosai da sauri kaka ta kwace jikinta ta koma ta sauna ragwab akan kujera tana maida numfashi 1 da 1 tace lallai Aslam yauna tabbatar da sojoji bakuda imani ko tausayina bakaji ba kake wanani tamkar fanka,su ihsan da suke xaune a palo sukuwa me xasuyi inba dariya ba,Aslam ma murmushi yayi yace Allah y baki hakuri uwargidana wai irin yadda nayi kewarki na nuna miki doke hannunsa tayi da yake kan cinyarta tace naji dai murmushi yayi y tashi yana sosa keya kallansu ihsan yayi yace baku iya gaisuwa ba,suka gaisheshi y amsa sannan y fuce yana kaka ki damamin fura.


Yana futa yayi kicibis da Amir da sauri suka rungume juna,amir yace dawowata kenan daga skul aunty amarya take cemin ka dawo,Aslam yace eh shigowata kenan,Amir yace amma babu sanarwa Aslam yace eh surprising dinku nayi Amir yace gaskiya kam karasawa part dinsu sukayi bedroom dinshi Aslam y bude y shiga Amir na binshi kayan jikinshi y rage y xama daga short nikker sai vest yadau towel y shige bathroom,Amir kuwa dakin y fara kadewa y cire bedsheet y canja wani danma dakin ba wani datti yayiba kusan duk sati ana share dakin a gyara.


💘💘💘
*daga* *mrs* *hamisu* *taura*
💘💘💘




(17/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON* *KAKA*
*28*
Kafin Aslam y futo y gyara dakin yayi morphing ya dauko burner a dakinshi yasa turaren wuta tuni dakin yadauki kanshi (nikuwa nace lallai Amir matarka ta huta irin wannan gyara haka).


Da Aslam y futo mamakine y kamashi y kalli Amir yace ah my bros waye y gyara dakinnan murmushi Amir yayi yace waka gani a dakin,Aslam ne mamaki y kasa boyuwa a fuskarsa yace kana nufin kaika gyara lumshe idanunsa yayi y kwanta a gadon yace eh nina gyara Aslam yace lallai dan samari ka huta kai wlh ko aure kayi matarka ta huta murmushi Amir yayi yace kaima dole ka koya ai Aslam yace tab karasawa yayi gaban dressing mirrow ya shafa mai y taje sumarsa ya fesa body spray jallabiya y dauko acikin jakarsa y saka sannan y feshe jikinsa da turare kiran sallar magruba aka farayi bathroom Amir y shiga y dauro alwala,masallaci suka futa dayake a layinnasu.


Ana idar da sallah suka dawo daddy da Abba suka je suka gaisar da suke part din mommy abincin da aunty amarya ta hada masa part din mommy ta kawo masa daukar warmers din yayi Amir y dauki jug din coconut drinks din da akayi masa suka wuce part din kaka.


Acan suka tarar da yaran gdan sun saka kaka a gaba sunata mata shakiyanci,xama Aslam yayi y karewa yan dakin kallo yace wai kaka ina yan matanki ne,kaka tace suntafi gidansu kawarsu kausar wan kawar tata ya hada musu party,kasan sun gama karamar makaranta cikin bacin rai yace what saida muryarshi ta karade dakin tuni sauran yaran suka nutsu yace yanxu Ashe haryanxu basuyi hankali ba to tunma karfe nawa suka tafi haidar ne yace wlh tun 4:00pm na kaisu,idanunshine sukayi jajawur jijiyiyin kanshi suka futo baro2 (nikuwa nace ran maxa y baci)yace wanene y basu damar tafiya kaka tayi xaraf tace nice koban isaba tashi yayi y tsallake abincin daya faraci yace xomuje karakani gdan haidar,da sauri haidar y tashi Amir kuwa part dinsu y koma damashi bashi da magana sosai shiyasa yaran basu fiya tsoronsa ba.


Su Aslam sunje gdan a gate din y futa yayi knocking mai gadi y futo ta karamar kofa Aslam yace sannu baba,baba mai gadi yace yauwa sannu dannan Aslam yace dan Allah kashiga cikin gidannan ka kirawomin Islam da Amira baba mai gadi yace yanxu suka futa da sagir a mota godiya Aslam yayiwa baba y juya yashiga mota suka koma gida xuciyarsa in banda suya da radadi ba abinda take a haka harsuka karasa gda lokacin ana kiran sallar isha'i tura haidar yayi yace jeka ganomin in sun dawo kace suxo nan su sameni haidar yace toh Aslam ya shige part dinsu domin yayi alwala a kofa suka hadu da Haidar y dawo yace naje basu dawo ba Aslam yace OK y futa xuwa masallaci Haidar ma shiga yayi yayo alwala y futa masallaci.


💘💘💘
*daga* *mrs* *hamisu* *taura*
💘💘💘




[11/12, 8:59 PM] ‪+234 703 443 5155‬: (19/10/2016 2:00pm)na umma yahya musa


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON* *KAKA*
*29*
Har suka dawo a masallaci suna dawowa gda Aslam direct part din kaka y nufa yagani ko su islam sun dawo,amma dayaje basanan lokacin dayaje yake tambayar kaka wai hanyanxu yarannan basu dawo ba,budar bakinta sai cewa tayi eh basu dawo ba to waima kai mene naka na damuwa daga dawowarka xaka dagawa mutane hankali,ni nasan su islam vaxasu bata ba acikin kano kuma komai dare yaronnan xai dawo dasu,tsaki Aslam yayi y fice daga part din kaka can kofar gda y futa sai xagaye yakeyi,a ranshi yana wannan wacce irin rayuwa ce yara kanana su futa a gda sukai har wannan lokacin amma ba wanda y damu tsaki yayi y hurar da wata xaxxafar iska daga bakinsa yace dole nadauki mataki nagyara wa yarannan xama dagasu har kakan da take kin bari a tsawatar musu.


Kusan 30 minute y dauka sannan yaga wata mota tashigo layin parking tayi a kofar gidansu da hucinsa y tafi wajan motar bangaren driver y tafi y fara nocking,a hankali sagir y fara xuge glass din windon ya kalli Aslam yace malam lfy,Aslam ganin islam ce a gaba tana shan ice cream shiya dada bata masa rai da sauri y bude gambun motar y shako wuyan sagir yace gidan ubanwa kakai yarannan a darennan,sagir yaji matsa sai raba idanuwa yakeyi,su islam sukayi sauri suka futo jikin Amira da khausar sai rawa yakeyi Islam kuwa ko a jikinta saima xumbura baki tayi tace haba yaya Aslam dan Allah ka sake shi ice cream fa da shawarma y kaimu y siya mana ta juya tana kallon su Amira,itadai Amira shiru tayi,Aslam kuwa mamakine y kamashi da sauri y cillah sagir gefe saura kadan y kifa ya kalleshi da idanunsa da sukayi ja yace this is the first & last warning wlh duk randa nakara ganin ka da kannena yayi wani murmushin gefen baki ya gyada kai da sauri sagir y shige mota khausar ma ta shiga a 360 yabar layin.


Su islam ne suka juya xasu shiga gda kallansu yayi yace kuje ku ajiye kayan kwalamar taku tunda kunxama mayu kwadayayyu kuxo dakina ina jiranku islam ce ta murguda baki tace wlh mu ba mayu bane inma mayune mu to kaima mayene taja hannun Amira da jikinta yaketa rawa suka shige gda.


Xaune suka tarar da kaka da sauri islam ta tafi dare cinyarta tace wash kaka mundawo wlh I'm very tied saboda munyi rawa sosai kaka tace to sannunku tun daxu wancan mai bakar xuciyar yake xiryar nemanku kamar wanda akace xa'a saidaku,dariya islam tayi tace ai yaya Aslam mugune kinga yadda y shake wuyan yaya sagir kuwa kaka tace lallai bai kyauta ba,kaka ce ta kalli Amira da take tsaye tace ke kuma fa kin tsaya kikam kina muxurai tamkar wadda tayiwa sarki karya,Amira tace yaya Aslam ne yace muje dakinsa mu sameshi kaka tace toh babu inda xakuje Islam tayi maxa ta tashi tace kaka karkiyi mana bakin ciki kila tsarabarmu xai bamu kaka tayi tsaki tace ku karbo uwar tsaraba ma (nikuwa nace lallai kam islam xaku karbo tsaraba).


💘💘💘
*daga* *mrs* *hamisu* *taura*
💘💘💘
[11/12, 8:59 PM] ‪+234 703 443 5155‬: (19/10/2016 2:30pm)na umma yahya musa


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON* *KAKA*
*30*
Aslam kuwa xagaye yakeyi a dakinsa hannunsa sakale a bayansa yace lallai yarinyar nan ni xata mayarwa da magana har tacemin wai in su mayune nima mayene lallai yau xan tabbatar mata da soja ba wasa bane xan gwada mata kadan daga cikin irin horon da aka bamu.


Islam da Amira ne a kofar dakin Aslam,Amira ce ta tsaya tace nifa islam wlh tsoro nakeji karmuje y dakemu kinsan ance sojoji basu da imani tsaki islam tayi tace toh in dukannamu xaiyi ke tsayawa xakiyi mene amfanin kofofin da Allah yayi miki ba saimu bawa wandonmu iska ba ta karashe maganar da bude dakin Aslam,suna shiga islam tace gamu tana murguda baki murmushi yayi irinna daki ganene yace toh ku xauna ina xuwa da sauri islam ta tafi bakin gadonsa ta dare Amira kuwa a kujerar da aka ajiye guda 2 ta xauna a daya duk a darare,Aslam futa yayi y duba dakin Amir yaga baya ciki yace dakyau saboda bayaso in y fara axabtar dasu Islam a samu mai kwatarsu yaje y duba dakin su haidar da yusuf suma basa ciki murmushi yayi yaje yasakawa part din key y juya y koma dakinsa yana shiga y tura kofar y rufe da key yasa key din a aljihu tuni y murtuke fuskarsa tamkar bai taba dariya ba cikin Islam ne yayi kara kuuuu saboda yadda y bata tsoro tamkar xaki karasawa tayi kusa da ita y daura kafarsa ajikin gado daidai inda islam tace yace ni kikacewa mace koh duk data tsorata da irin kallan da yakeyi mata hakan bai hanata murguda baki ba (nikuwa nace mai hali ai baya fasa nuna halinsa)nace to kaine fa kace mana mayu kuma naga duk abu dayane yayi m.....bata karasa ba y dauketa da wani lafiyayyan mari kara ta kallah tana ihu kamar wadda ake xarewa rai tuni Amira tahau kuka dantasan itama nata dukan yananan yana jiranta da hannu yayi mata alamar tayi masa shiru xubura baki tayi hawaye nabin fuskarta yace watako harkunyi girman da xaku tafi wani kato y hada muku fati sannan bayan y gama y daukeku y kaiku yawan shakatawa ko da sauri Islam tace ba yawan shakatawa y kaimu ba ice cream da shawarma kawai mukaje y siyo man...da sauri yakai hannu xai doke bakinnata itama cikin xafin rai tayi kasa da kanta y bugi iska yace watako bakinki baxai mutu bako maxa ku tashi kuyimin kamin kunne,kamin kunnen sukeyi y ciro belt din wandonshi na kayan sojoji yace koda wasa duk wanda y dago sai dai yaji saukar belt dinnan a gadon bayanshi,tashi sukayi suka farayin kamun kunnen,shi kuwa komawa yayi y xauna a kujera daya daga cikin kujerun dakin y daura kafa daya kan daya yana shan lemon gwangwani shani sun dauka abinna wasane sukaga saiyi sukeyi yaki yace su dago kuka suka fara wiwi2 ga yawu ga majina amma y tashe kunnensa da ear pies din waya yanajin waka,kusan 30 minute suka dauka duk sun hada kumi amir ne yaxo xai shiga part din yaji a kulle,kiran layin Aslam y fara yana dagawa,yace maxaje wai ina kashiga ne naxo naji kofar a rufe,Aslam yace bari naxo nabude maka tashi yayi y kalli su islam yace ku tashi tasowa sukayi amma sukaji bayansu y ruke islam ce ta bare baki tace wayyo bayana ta koma ta xauna lokacin Amira harta fice kallanta yayi yace oh baki gajiba kenan to kici gaba da sauri ta tashi tana wlh nagaji murmushi yayi,kofar suka karasa y bude musu da sauri suka fice islam ce ta juyo tace Allah y isanmu mugu axxalumi Allah kuma saiya saka mana ta falfala a guje Amira ma kuwa tabawa wandanta iska tamara mata baya.


💘💘💘
*mrs* *hamisu* *taura*
💘💘💘
[11/12, 9:00 PM] ‪+234 703 443 5155‬: (20/10/2016 3:00pm)na umma yahya musa


🍒🍒🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒
🍒
*GOYON* *KAKA*
*31*
Aslam ne yayi murmushi y girgixa kai yace yarinyarnan baxaki taba gyaruwa ba Allah y shiryeki,Amir kuwa kallan Aslam yayi yace mai kayi musu ne daga kafada yayi yace kawai punishing dinsu nayi saboda fitar da sukayi suka kai dare murmushi Amir yayi yace Allah y kyauta Aslam yace ameen suka shiga part dinnasu.


Islam kuwa kan kaceme hartakai part din kaka a kuje dama wajan gudu islam tamkar yar barewa ta fada kan kaka da take kwance a firgice kaka ta tashi dan har bacci y fara daukarta,tace ke lfy xaki fadomin kai koso kikeyi ki karyani,baki islam ta xumburo tace to ba yaya Aslam bane y sakamu kamun kunn....bata karasa ba Amira ta shigo itama faduwa tayi tana maida numfashi islam tana ganinta yadda take maida numfashi yasata dariya tahau kyalkyala dariya ba kakkautawa Amira kuwa ranta duk y baci saboda tana ganin rashin kunyar da islam tayiwa Aslam ne yasa yasakasu kamun kunne,ganin islam taki daina kukan yasa Amira fara kuka kawai ta tashi ta shige daki,da sauri islam ta tashi tabita tana haba sis menene na fishin dan Allah kiyi hakuri ta tashi tabita dakyar saboda yadda kafafunta sukeyi mata ciwo.


A kwance ta tarar da Amira tana kuka wiwi da sauri islam ta karasa ta dagota ta rungumeta tana haba 6ter dan Allah kiyi hakuri indai ni nabata miki rai kuma wlh naci alwashin saina daukar mana fansar abinda yayi mana kamar yadda yasaka mu a wahala muma saimun rama ko baikai yadda mukasha ba da sauri Amira ta tashi tace me xakiyi masa sis islam tayi wani shegen murmushi tace kawo kunnenki,Amira ta mika mata kunne ta rada mata magana.


Da sauri Amira ta xabura ta matsa daga kusa da Islam tace gaskiya sis inajin tsoro,harararta islam tayi tace kefa banxace kinfiya tsoro wlh kina nufin wahalar daya bamu yaci bulus kenan islam ta girgixa kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login