Showing 1 words to 3000 words out of 78990 words
[9/27, 09:36] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD* ✍🏻
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Dasunan Allah me rahama me jin k'ai , tsira da aminci su k'ara tabbata ga Shagaba Annabi Muhammad S.A.W ,_
_Wannan littafin nawa k'agaggene banyishi dan cin zarafin wata ko wani ba , duk wanda yayi dai dai da rayuwarsa to yazo ne a kasi , banyadda wani ko wata ya juyamin labarina ba batare da izinina ba , Yin hakan doka ce Akiyaye_🤝🏻🤝🏻
_Wannan littafin sadaukarwa ne gareki Masoyiya🥰 Hafsat Abdurrahman_ *Allah yabar k'auna* 🙏🏻🙏🏻🤝🏻
Chapter 1.
A garin Abuja yau antashi da ruwan sama kamar da bakin k'warya , hakan yasa garin yayi tsit kowa yana cikin gidan sa , wani katafaren gida nagani ana wangale k'ofar gate d'insa , wata motar ce ta danno kai da gudun tsiya tamkar zata tashi sama saboda gudu .....
baka hango wanda ke cikin motar saboda bak'in glass d'in dake jikinta , amman kasan duk wanda ke cikin motar basai anfad'a maka irin rashin jin shiba , saboda irin gudun dayake sharawa ga kuma wani kid'a na tashi tamkar dodon kunnen mutane zai tsage , a k'ofar wani katafaren gida motar ta tsaya ta danna hon. Da gudu megadi yazo ya bud'e dan yasan waye ko ba'afad'a masa ba , da gudu motar ta kuma shiga cikin wannan gidan kuma har a lokacin ba adaina ruwa ba , anfi minty biyar ba'a fito daga ciki ba sannan aka bud'e murfi aka fara zuro k'afa , wata had'addiyar Budurwace wacce tagaji da had'uwa ta fito daga cikin motar sanye da glass a idonta , ga wasu matsatstsun kaya datasa duk ilahirin jikinta a matse yake , takalmin dake k'afarta irin hill d'in nan ne , tana fitowa me gadi ya k'araso da gudunsa yana zubewa gabanta yana fad'in " sannunki da zuwa ranki shi dad'e Hajjaju mutan makka da madina , ko kallon arzik'i batayi masa ba ta wurga masa lemar data d'auko bayan motar ta , da sauri ya mik'e yana bud'e lemar tare da rik'e mata dai dai kanta gudun kar ruwa yatab'ata , shigewa tayi tana wani irin taku tamkar wahainiya har suka k'araso k'ofar wani had'add'en falor , shigewa tayi ciki shikuma me gadi ya tsaya a wajen saboda bin umarninta......
Tana shiga cikin falor tasamu 'Yan aikin gidan sai faman gyare gyare suke a falor , suna ganinta dukansu suka zube k'asa suna gaidata , kallo basu isheta ba bare ta amsa musu , step tafara hawa alamun sama zata hau , saida ta haye saman sannan dukan su suka mik'e suna girgiza kai kafin suci gaba da aikin gabansu......
Wani d'aki naga tashiga ko sallama batayi ba , wani Magidancin mutum ne a zaune yana danna cumputer lapton akan wani katafaren gado , sai kuma wata mata wacce ke had'a masa cofee a gefensa , kana ganinta kasan matar sace saboda yadda suke hirarsu cikin farin ciki da raha , jin anshigo yasa dukansu suka dubi k'ofah dan ganin waye ? koda suka ganta Mutum yafara fara'a yana fad'in oyoyo My luv , zonan naji waya tab'amin ke naga sai had'e rai kike ? Hajiya Maimuna tadubeshi tace " Alhaji nagama aikina zan'iya tafiya ? dubanta yayi tare da canza fuska yace " Haba Maimuna wai meyasa duk lokacin da *SANAM* zatazo sai kin bar wajen ? Hajiya Maimuna tace " kafi kowa sanin halin 'yarka batason kowa ya rab'eka mutuk'ar ba ita bace , dan haka duk lokacin data tafi zaka iya kirana inyi maka duk abinda kakeso , bata jira cewar saba tayi hanyar fita tafice abinta.......
Sanam ta rakata da Hara sannan tayi tsaki taci gaba da taunar cingum d'in ta , Alhaji Abba yadubi tilon 'yartasa wacce yake mutuk'ar k'auna a duniya kuma akanta zai iya yin komai mutuk'ar za'atab'a masa ita yace " Sorry my luv k'yaleta kar ranki ya b'aci akanta , Sanam tayi wani k'wai da cingum d'inta har saida yatab'o hancinta tace " Daddy nazo ne akan maganar canzamin motar , kasan cikin account d'ina kwata kwata bakai adadin kud'in dana ke buk'ata ba , duk wannan maganar da Sanam takeyi a Shagwab'e takeyinta tamkar K'aramar yarinya , dubanta yayi yace " My luv ina ganin fa motar nan taki kwata kwata batafi kwana goma ba , kuma ace har ank'ara siyan wata , da bari kikayi wannan ta kwana biyu sai insa ayi miki order wata daga Jamus , had'e rai tayi sannan tace " Daddy yanzu kana so muyi anko motar da Zahra ne ? itama fa daga ganin wannan tawa tasa Daddyn ta yasiya mata irinta , nikuma gaskiya bazan dunga hawa motar iri d'aya da wata ba saboda banson Ajina ya zube , Murmushi yayi yana dubanta sannan yace " to shikenan nawa ne kud'in waccen motar d'in ? wani murmushi tayi wanda har sai da dimple d'inta ya lotsa tace " 50.Million ce kawai Daddyna , murmushi yayi yace " indai akwai ta sama da haka ni ita nakeso nasiya miki My luv , tashi tayi da sauri ta fad'a jikinsa ta rungumesa tana murna , ganin ta a farin ciki yafi masa komai a duniya , shima samun kansa yayi da farin ciki sannan ya sumbaci goshinta , Nan yatura mata 80.Million a accaunt d'inta yana fad'in " sai munzo celebrition my luv , ta shagwab'e fuska tare da manna masa kiss a kunci tace " thanks my special papa proud of U My Daddy , da sauri ta d'auki jakarta tajuya ta fice daga cikin d'akin ,..
Lokacin da ta sauko sukayi karo da Hajiya Maimuna , Sanam wani dogon tsaki taja tare da tsartar da miyau tana bin gefe harta fice daga falor , wannan Abun datayi wa Hajiya Maimuna ba k'aramin harzuk'ata yayi ba , taya yarinya k'arama zata dunga yi mata wannan abu ? tabbas wannan hali na Sanam yafara damunta zata iya ci gaba da zama da Alhaji Abba kuwa ? Sama ta nufa wajen sa ranta a mutuk'ar b'ace , tana shiga d'akin nasa ko sallama batayi ba tafara fad'in " a gaskiya Alhaji nagaji sosai da halin wannan 'Yar taka , a koda yaushe tazo gidan nan saita yimin abinda zuciyata zatayi min rashin dad'i , yau saboda iskancinta har miyau ta tsartamin dashi haba Alhaji , idan anyi magana sai kace ana takura mata ansa mata ido , a gaskiya indai zamu ci gaba da tafiya akan haka tabbas zanbar maka gidan ka dan hak'urina yafara kaiwa k'arshe , a fusace Alhaji Abba ya mik'e yana kallon Hajiya Maimuna yace " nasan dama dole sai kinzomin da wata sabuwar magana akan zuwan Sanam gidan nan , Maimuna ina d'aga miki k'afa sosai aka Sanam saboda wani Abu , amman duk randa kika isheni wallahi zaki gane waye ni , tsaki yaja tare da d'aukar mukullin motar sa yafito ......
Hajiya Maimuna tuni hawaye ya wanke mata idanuwa , fad'awa kan gado tayi tana kuka tare da fad'in " yaushe ne matsala ta zata kawo k'arshe a kan wannan yarinya ? yaushe ne zanyi zaman farin ciki a gidana koda yaushe indai zata kawo ziyara to tabbas sai tabar mata tabo , lallai hausawa sunyi gaskiya da suke cewa *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* Allah yabasu ikon cinye jarrabawar nan......
Koda Sanam ta fito har a lokacin megadi na tsaye ruwa yayi masa duka , ga lema a hannunsa amman yasan indai yasake yashiga cikinta to tabbas yagamu da jaraba , tana fitowa yayi saurin bud'e lemar yana rufa mata aka suka wuce har gun motar ta , tana shiga ya nad'e lemar yasa mata ita a bayan motar tare da kwasa da gudu yayi wajen gate. Bud'e wa yayi tazo ta fice da mahaukacin gudunta tamkar zata tashi sama , gudu take sosai titi ko wanne me motar matsawa yakeyi inyaganta , tana shiga estet d'in Airea 11 dai dai wani k'ofar gida wani matsahin saurayi ya fito a k'afa sanye da jallabiya jikinsa , kana ganinsa kasan sauri yake yasamu sallar Azzahar ta wanke sa da ruwan cab'i dukansa , kuma ta fiki motar ta tamkar batasan abinda tayi ba..............
*Comment* *d'inku* *shine* *zai tabbatar min da karb'uwar da littafin zaiyi*
*Dafatan wannan salon shima zai k'ayatar daku*
Kardai kumanta Alk'alimin *'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ ✍🏻😍🌹
[9/27, 09:36] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 2.
Bin motar yayi da kallo har ta k'ure sannan yadubi jikinsa , duk jikinsa a b'ace da cab'i , wani takaici yaji ya kamashi sosai tabbas duk wanda yake cikin wannan motar ba k'aramin mara mutunci bane , amman tabbas saiya gano ko waye a cikin motar tunda acikin Estet d'insu yake , juyawa yayi ya nufi cikin gidan su ransa a b'ace ga takaicin rasa jam'i dazaiyi....
Wani mahaukacin Hon Sanam ke dannawa a k'ofar gate , lokacin megadin su yatada sallah , babu shiri ya sallame daga sallar saboda sanin hali , da gudu ya bud'e k'ofar gate d'in yana fad'in "sannu da zuwa hajjaju , dawani mugun gudu ta shigo tamkar zata bi takansa , da sauri ya buga wani tsalle yana jan baya tare da dafe k'irji saboda razanar dayayi , tafi minty goma kafin tafito daga cikin motar ta dubesa a wulak'ance tace " mekakeyi da har yafi hon d'in motar ta muhimmanci ? da sauri ya zube yana fad'in " tuba nake ranki shi dad'e wallahi sallah na tayar shiyasa , wani tsaki tayi sannan tajuya ta nufi cikin gida......
Hajiya Nafeesa tana cikin kitchen tana ta k'ok'arin had'a Abincin dare taji shigowar Sanam , k'wala mata kira taji tanayi tamkar k'aramar yarinya , da sauri tafita daga kitchen d'in ta nufi Falor , Sanam naganinta ta taho da gudu tana fad'in " Mumy Kitayani murna Daddy yabani kud'in yace in canza motar , Hajiya Nafeesa tace " shiyasa nafad'a miki kije kisamesa kinsan komai kikeso yana faranta miki , Sanam tayi murmushi sannan tace " Mumy nasan Daddyna yana sona fiye da komai a duniya , Hajiya Nafeesa wani abu taji ya tokare mata a k'irji na takaici amman saboda bariki irin tata sai cewa tayi " in bai soki ba Baby wazaiso ? ke kad'ai Allah ya mallaka mana a duniya kinga kuwa dole musu farin cikin ki , k'ara shiga jikinta Sanam tayi tamkar wata k'aramar yarinya tana jin dad'i , Hajiya Nafeesa cikin ranta take fad'in " duk yadda zanyi na raba wannan soyayyar taki da Mahaifinki sainayi , a koda yaushe na bud'e ido naga yadda yake sonki yake kulawa dake wani takaici ne yake min yawa , a fili kuma tace " bari nakoma kitchen dan kinsan yau girkin da kikeso shinake miki , Sanam ta d'ago tana fad'in " shiyasa nake sonki Mumyna kina sakani farin ciki sosai , ba kamar waccen matar Daddyn ba yauma danaje saida ta b'atamin rai , da sauri Hajiya Nafeesa ta dubi Sanam tace " me Hajiya Maimunar tamiki haka ? Nan Sanam tafad'a mata yadda sukayi da Hajiya Maimuna , wata dariya suka saka tare da tafawa Hajiya Nafeesa tace " kin kyautamin walllahi dakika tofah mata miyau , nan Sanam ta haye sama d'akinta tana fad'in " ai ko gobe naje gidan nan saina kuma mata kalar wani rashin mutunci mutuk'ar zata shiga gonata .....
Hajiya Nafeesa kitchen ta nufa tana fad'in " banza wawiya wacce bata san ciwon kanta ba , Wai har dad'i takeji dan tayiwa Uwar ta rashin kunya , yarinya zakiyi bayani ne sannan gaba , duk wannan soyayyar danake nuna miki badan Allah bane kawai saboda dukiyar Ubanki nake lallab'aki , dasannu zaki gane cewa duk inda kishiyar uwa take to tabbas kishiyar ce , tun zuwanki duniya nakeshan wuyarki kawai ina dannewa ne saboda lokacin baki wuya baiyiba , saina sa kinsan cewa rik'on danake miki shine wanda hausawa suke cewa *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* zanci gaba da hak'uri dake tare da nuna muku tawa kalar siyasar......
Wani had'ad'd'en d'aki Sanam tashiga sai k'amshine ke tashi , komai na cikin d'akin kalar pinky ne har fentin d'akin , toilet d'in dake manne jikin bed d'inta tashige , bayan minty 15 tafito daga toilet d'in d'aure da tawul iya guwa sai k'amshin turaren wanka take , zama tayi gaban mirror tana goge jikin nata tare da janyi mansha fawa tafara shafawa , Sanam nada kyau sosai kana ganinta kaga zallar shuwa arab , tana da kyau na nunawa sa'a ga dirin jiki tamkar itace tazab'i ayita hakan , farace sol fatar jikinta har shek'i takeyi saboda hutu da gyara , wayar tace tashiga ruru amman ko kallo wayar bata isheta ba har kiran ya katse....
Shiryawa tayi cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando , duk wata sura ta jikinta sai data baiyana , ta d'auki wani tsadadden turare ta fesa ajikinta , tuni k'amshi ya gauraye ko inah na jikinta abinka da 'yar gayu , wani filet d'in shoe d'inta ta d'auka tasaka tarae da d'aukar jakarta swuga tarik'e tafice daga d'akin....
Lokacin data sauko k'asa dai dai lokacin Hajiya Nafeesa take jera abinci a daining , k'arasowa tayi taja kujera ta zauna tana fad'in " Mumy yunwa nakeji plss kiyi seving d'ina , Hajiya Nafeesa tace " to my Babyna bari nagama d'akko sauran Kayan sai na zuba miki , turo baki tayi sannan tashiga dannan wayarta , sai a lokacin taga me kiran nata k'awarta ce Diyana , da sauri ta dannah calling d'in number , bugu d'aya aka d'aga ana cewa " Baby Sanam wai ina kika shigane yau kwata kwata bakizo an had'u ba ? kinsan fa yau Zahra take celebrition d'in siyamata sabuwar motar da Daddyn ta yayi , kuma kinsan da gayya takeyin hakan saboda ke , tab'e baki Sanam tayi sannan tace " k'yaleta kawai Diyana banda lokacinta amman ko saboda kar ace ina mata bak'in ciki anjima zanshigo , katse wayar tayi batare da tajira me Diyana zatace mata ba , lokacin Hajiya Nafeesa ta k'araso tana ajiye kayan hannunta sannan tafara zubawa Sanam Abincin , Faten doya ne wanda yaji Naman kaji sai k'amshine ke tashi , Sanam tuni tafara zubawa cikinta tana wani danna waya , Saida takusa cinyewa sannan ta ture wai ta k'oshi , lemo ta tsiya tasha sannan ta mik'e tana duban Hajiya Nafeesa tace " Mumy nidai zanfita kibani mukullin motar ki da ita zanfita , Hajiya Nafeesa tace " yana kan dirowar mirror d'ina kije ki d'auko , sannan karki dad'e dan kinsan anjima Kad'an Daddyn ki zaizo , Sanam tace " to Mumy kikulamin da kanki bye bye , Hajiya Nafeesa ta raka ta da harara tana fad'in " shegiyar yarinya tamkar Aljana dan kyau..
Sanam tana fitowa tashiga motar Hajiya Nafeesa , da sauri megadi yaje ya bud'e mata gate yana fad'in adawo lafiya Hajjaju , ko kallonsa batayiba tasaka kai ta wuce abinta.....
tunda Huneed ya shiga gida canza kaya yake cika yana batsewa , dubansa Hisham yayi yace " wai mutumina ya akayi naganka haka naga jallabiyar ka ta b'aci da cakwali saikace k'aramin yaro , gashi kuma naga sai faman had'e rai kakeyi ? Huneed yace " wallahi nafita sallar Azzahar d'azu kawai wani wawa yazo wucewa a motar ya feshe ni da cakwali , murmushi Hisham yayi sannan yace " duk cikin Estete d'in nan bawanda yake irin wannan gudu sai wata yarinya me suna Sanam , itace take gudu da motar tamkar zata tashi sama , kowa yasanta kaima dan dai baka dad'e da dawowa ba shiyasa bakasanta ba , Huneed ya dubi Hisham yace " wai kana nufin kace wannan gudun da akeyi da motar mace ce haka ? murmushi Hisham yakumayi yana cewa " Allah ya taimakeka ma daba ta taka kaba , dan kusan duk Estate d'in wallahi kowa yasan wannan mugun halin nata , shiyasa