Showing 30001 words to 33000 words out of 78990 words
sai yimin fad'a tana yimin wa'azi , murmushi yayi sannan yace " haba Baby kinsan duk duniya bayan ni babu wanda zai soki tamkar ita , ko kin manta itace ta haifeki kinga dole zata soki fiye da saninki , Sanam tamkar wata yarinya tace " wallahi Mumyn nan gidan tafita sona sosai kuma kaima kasan hakan Daddy , shuru yayi yana nazari " tabbas yasan Hajiya Nafeesa nasan Sanam tamkar itace ta haifeta , sai dai yasan baza ta tab'a yi mata irin son da Mahaifiya kewa 'ya'yan taba , amman saboda kar yaja zancen yace " shikenan Baby abar zancen duk sanda kika samu lokaci kije sai ku gaisa da ita , turo baki tayi tana fad'in " to Daddy .......
Huneed tuni ya shirya cikin wani yadi me tsadar gaske , ga wani had'edd'en turare daya fesa sai tashin k'amshi yake , yana fito yashiga falor Hajiyar su d'auke da sallama a bakin sa , amsawa tayi cike da sakin fuska tare da nuna kulawa ga d'an nata , durk'usawa yayi a k'asan cafet yace Hajiya ta barka da wannan lokacin , cike da fara'a tace " Barka kadai My son , wannan wanka daga gani nasan wajen sirikata za'aje , sunkuyar da kai yayi yana dariya kafin yace " Hajiya ta inaso kiyimin addu'a yau zanje na sanar da wacce nakeso inason ta , murmushi tayi sannan tace " koda yaushe ina maka addu'a kai da d'an uwanka , Allah yazab'a muku mataye nagari masu k'aunar ku , Allah yayi muku Albarka tare da sauran 'Yayan musulmi baki d'aya , sannan inaso inkaje kagaida min da ita kace ina maraba da zuwan ta gidan gwarzon d'ana , murmushi Huneed yayi yana mejin dad'in maganganun Hajiyar tasa , mik'ewa yayi yana fad'in " zataji insha Allah Hajiya ta sai nadawo , yasa kai ya fice daga falor cike da farin ciki fal a zuciyar sa , ......
Hajiya Maimuna ce zaune ita da Mahaifiyar ta tana hawaye , share mata hawayen nata Mahaifiyar ta tayi tana fad'in " kici gaba da addu'a Maimunatu insha Allah komai zaizo k'arshe duk tsanani yana tare da sauk'i , wata rana zata gane muhimmancin ki kuma saitayi nadama sosai , yanzu kici gaba da mata addu'a dan addu'arki tafi komai tasiri a wajen ta , muma muna yi miki kuma duk daren dad'ewa komai zai zo k'arshe , da irin wannan dad'a d'an kalaman Hajiya Rabi take kwantar wa da 'yar ta ta hankali duk san da taje gida , yauma tun fitar Daddyn Sanam ta hau motar ta tayo gidan su dan kawo kukan ta da Mahaifiyar ta ta , Tabbas duk wanda yarasa *Uwa to yayi rashin Babban jigo a rayuwar sa wanda babu madadin ta* , *Allah yajik'an iyayen mu wad'an da suka rigamu hidan gaskiya* , _wad'an da suke a raye kuma Allah kabamu ikon yi musu biyayya_🙏🏻🙏🏻
Sosai Hajiya Maimuna ranta yayi mata dad'i da yadda mahaifiyar ta ta ta kwantar mata da hankali , nan tasaki jiki taci gaba da hira da Hajiyar ta ta har lokacin da tayi mata sallama ta koma gida .......
Hajiya Rabi sosai take tausayin 'Yar tata ganin yadda akayi mata fin k'arfi akan 'yar ta , ita kanta batace ga randa ta tab'a ganin Jikar tata Sanam tazo gidan nata ba , amman haka take kwantar mata da hankali har tasamu ta sauko......
Sanam hirar su suke akan komawar ta sch dazatayi , Hajiya Nafeesa ce ta fito daga b'angaren ta tamkar babu abinda yake damunta , tana zuwa tasamu guri ta zauna hirar suka ci gaba dayi har ita , cikin ranta tana fad'in " kuyi duk abinda zakuyi nan da kwana hudu zan raba ku da farin cikin dake fuskokin ku , sallamar da megadi yayi ita ta katsesu , cike da girma mawa yace " ranki yad'ad'e ana sallama dake a waje , Sanam tasan da ita yake amman ko kallon sa batayi ba , sai Hajiya Nafeesa ce tace " waye yakeson ganin nata ? risinawa yakumayi yace " wani mutum ne a waje ban waye shi ba , Hajiya Nafeesa tace " kaje kace " yashigo ka kaishi d'akin saukar bak'i gatana zuwa , Sanam da sauri ta kalli Hajiya Nafeesa tana fad'in " Mumy taya zakimin haka ? murmushi tayi cike da kissa tace " haba my Luv kinsan dai yakamat ace kinfara sauraren samari dan kin isa kuma kin kai , nan tashiga lallab'a ta har tasamu ta amince zataje , Alhaji Abba yana jinsu ko tari baiyiba yada saka aransa zai fita dan ganin waye yazo gun 'yar tasa , dan yanson ace kowaye yazo to yaasance d'an mutunci ne wanda yasan mutucin ta , wanda zai iya rik'e masa yar sa batare da ta nemi komai ta rasa ba , mik'ewa Sanam tayi ta fita ahaka dan tace babu abinda zata canza ko kuma ta gyara , .....
tana zuwa K'ofar d'akin saukar bak'i taji wani k'amshi yana fitowa , lumshe idanun ta tayi tana son tuna inda tasan k'amshin turaren , ta dad'e a tsaye tana tunanin sannan ta tura k'ofar a hankali tare da yin sallama , Huneed na zaune yana dannan waya yanajin shigowar ta ya d'ago yana amsa sallamar tare da duban ta , Sanam naganin Huneed k'irjinta ya buga take taji wani abu ya tsaya mata a k'irji wanda tarasa ko na farin cikine ko akasin hakan , kafesa tayi da ido tamkar taje tafad'a jikin sa wani kyau dataga yayi mata , tayi nisa a tunani taji yana hure mata ido yana fad'in " irin wannan kallo sai kace baki tab'a ganina ba , da sauri ta rufe fuska tana murmushi tare dajin kunya , shima murmushin yayi yace " barka da fitowa shugabar 'yan rigima , rigimar ki tana da yawa kinsa na rud'e har naga bazan iya jira ba sai nazo , Sanam wata kunya takumaji tamkar ta nitse cikin ranta tace " kardai ace ya fahimci ina kishinsa ? kuma mutuk'ar ya fahimta to tabbas yasan tana sonsa kenan ? a hankali ta furta " wayyo shikenan na rusa ajina a idon sa , Huneed kamar yasan abinda take tunani yace " Sanam dan mace taso Namiji ba laifi tayi ba fa , hasalima hakan yayi duk da baki furta min kina sona ba , amman iya hakan ya bayyana min cewa yadda nakamu da sonki nima haka kike sona , sai dai a zahirin gaskiya nafi sonki dan tunda ga randa nafara ganinki nakamu da sonki sosai , duk wannan takurar da nayi miki da kuma yadda na dunga bibiyar ki wallahi sonki ne yasa hakan , durk'usawa yayi da gwuiwar sa k'asa yace " Sanam yau ga Huneed a gabanki ina me rok'on soyayyarki , inason kizama uwa awajen 'Yayana sannan ki zama wacce zata zame min bangon jingina duk lokacin da nazo gareki ......
Sanam tamkar zata saka ihu saboda murna , wani dad'i takeji har ranta sai dai kuma ai yace mata yana da mata , to taya zata rayu da wanda yake da mata , dan ita fa ko a sittira batason kishiya balle a rayuwar gidan mijin ta , dan ta tsara rayuwar da zatayi da mijinta mutuk'ar tayi aure , to taya zataso wata takasance tare da mijin nata , ganin shurun da tayi yasa Huneed karaya yana mik'ewa yana duban ta , idanun sune suka had'u waje guda take kowa yaji wani abu tunda ga tsakiyar kansu har ilahirin gangar jikinsu............
[9/27, 09:55] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 23.
Sunfi Minty biyar ahaka kafin Sanam tayi k'arfin halin janye nata idon , Ajiyar zuciya suka saki lokaci d'aya kafin kuma shuru yasa ke biyo baya , k'wan k'wasa k'ofar d'akin ce ta katsesu su dukan su suka dubi hanyar shigowar , Me gadin gidan ne ya shigo d'auke da sallama a bakin sa sannan yace " ranki ya dad'e Alhaji yace kuje keda bak'on naki ku samesa a palor sa , Sanam ta d'aga masa kai alamar to batare da ta furta komai ba , Bayan fitar megadi da kamar minty biyar Sanam tadubi Huneed tace " Bisimillah katashi muje gun Daddy yana kiran mu , Huneed batare da fad'uwar gaba ba ya mik'e suka jera suka nufi cikin gidan ....
Tunda Jaydeen ya isa gida ya ke maganar Sanam , Mumyn sa ta dube sa tace " My Son. Kodai gamo kayi a hanya ne ? tunda ka dawo kake zancen yarinyar nan , ko abinci kaki tsayawa ka nutsu kaci , murmushi Jaydeen yayi sannan yace " Mumy dan dai baki ganta ba ne shiyasa zaki ce haka , Yarinyar ta had'u sosai Mumy ga ta irin macen da nakeso ce , Hajiya Halima tayi murmushi sannan tace " wacce irin mace ce kake so My son . ? kafad'i ko wacce irin mace ce a duniyar nan , mutuk'ar kud'i zai iya siyo maka soyayyar ta to tabbas kasame ta ka gama , yanzu abinda nakeso dakai shine " ka tsaya kaci abinci kayi wanka sai ka nutsu ka fad'amin yar gidan waye a garin nan na Abuja , Murmushi Jaydeen yayi najin dad'in abinda Mumyn nasa tace , fara cin Abincin yayi yana fad'in " nasan komai nakeso a duniyar nan kuna samar min shi Mumy , dan haka inaso a wannan lokacin a nemomin auren wannan yarinyar dan shine kawai cikar burina a yanzu , nan yaci gaba da bata labarin irin had'uwar da Sanam d'in tayi , har kwatan ta mata yadda take magana yake cike da sauk'i , Jaydeen kenan 'Da d'aya tilo a gurin Ambasador da kuma Hajiya Halima......
Sallama su Sanam sukayi a palor cikin gidan inda Daddyn nata yake zaune shi da Hajiya Nafeesa , amsawa Hajiya Nafeesa tayi d'auke da murmushi a bakin ta , sai dai tana had'a ido da Huneed taji k'irjin ta ya buga , kwata kwata taji tana tsoron sake kallon sa batare da tasan me hakan ke nufi ba , A b'angaren Alhaji Abba kuwa yana kallon Huneed yaji ya masa kwarjini gashi ingarman Namiji wanda kowacce mace zatayi burin kasan cewa tare dashi , take ya fara fara'a tare da cewa " sannu da zuwa sirikina , kunya ce ta kama Huneed ya durk'usa yana gaida Alhaji Abban , da sauri Alhaji Abba yace " mik'e ka zauna a kujera kaji kasaki jikin ka tamkar ba yau kafara zuwa cikin gidan nan ba , Huneed ya mik'e ya zauna a kujera yana murmushin jin dad'in karamcin da Alhajin yayi masa , Sanam zama tayi kusa da Daddyn nata tana murmushi najin dad'in yadda taga mahaifin nata ya karb'i Huneed , gaisawa sukayi cike da mutuntawa sannan Huneed ya juya yana gaida Hajiya Nafeesa , amsawa tayi tana k'ak'alo murmushin dole tare da yi masa sannu da zuwa , mik'ewa tayi sannan ta dubi Sanam tace " My Angel zo muje ki kawo masa kayan motsa baki , haka ake tarar bak'o maza muje kinji , Sanam ta mik'e tana turo bakin shagwab'a tana fad'in " kai Mumy nifa kinsan bansan yadda akeyi ba , da ido Huneed yabi Sanam da kallo a zuciyar sa yana fad'in " ashe a cikin gidan ma haka kike Sanam manya kenan , Alhaji Abba na lura da yadda Huneed d'in ke kallon 'yar tasa wani murmushi yayi irin nasu na manya......
Nan Alhaji Abba ya shiga yiwa Huneed tambayoyi game da asalin sa , Huneed ya gyara zama yafad'awa Alhaji Abba asalin sa da kuma aikin da yakeyi , Alhaji Abba yanajin Huneed yace shi d'an gidan Canal Abdallah marigayi ne yasan Huneed , dan bawani Mahaluk'in da baisan Canal Abdallah ba , yayi aiki tuk'uru a k'asar nan kafin Allah ya amshi ransa , kuma har gobe ana labarin yadda yayi gumurzu da mugayen mutane , Nan take Alhaji Abba ya jinjinawa Huneed da yadda yake k'ok'ari shima , dan da alama shine zai maye gurbin Mahaifin sa , sosai Alhaji Abba yaji ya yarda da Huneed kuma ya amince masa a matsayin wanda zai zama miji ga shalelen 'Yar tasa , gyaran murya yayi sannan yace " naji duk bayaninka kuma na gamsu , dan haka nabaka izinin kaci gaba da zuwa wajen Sanam har Allah ya dai daita hankulan ku , Allah yayi muku Albarka yasa Alkairi a cikin tarayyar ku , Huneed ya amsa da Ameen tare da rissinawa yana fad'in " nagode sosai Daddy Allah yaja da rai , da Ameen Alhaji Abba ya amsa tare da mik'ewa ya haye sama ....
Sanam ce ta fito ta wata kusurwa rik'e da tire a hannun ta , tana k'arasowa ta ajiye a gaban Hubeed tana fad'in " bisimillah ga abin tab'awa , Huneed ya kalleta yana murmushi tare da kashe mata ido yace " ai bazan iya tab'a komai anan ba sai naji daga bakin gimbiya ta in ta amince dani , Sanam tayi wani wal da ido sannan tace " ni bazan iya soyayya da me mata ba , da ace baka da mata to tabbas zan iya ansar tayinka kodan na rama abinda kamin a baya , da sauri Huneed ya dubeta yace " waye yace miki ina da aure kuma ? Sanam ta kallesa tana hararar sa tare da turo baki tace " waye kuwa ya gayamin in ba kai ba , ko kamanta randa muka fara waya kace na tasoka kan tare da iyalinka , sannan sauran wayoyin ma da muke kullum sai kamin zancen matar ka , wata irin dariya Huneed ya fashe da ita yana duban Sanam , sai dayayi me isar sa sannan yace " ni fa bani da wata mata tsokanar ki nakeyi for sale ne inkin shirya , duban sa tayi ya kashe mata ido ta kauda kai sannan tace " sainayi shawara naga a wajen da yakama ta insaka , Huneed ya taso ya dawo kuda da ita numfashin su na dukan juna yace " abar maganar wasa Babyna wallahi da gaske nake k'aunar ki kuma aure nakeso muyi , yanzu maganar da nake miki Daddy ya amince min akan inzo neman auren ki ya bani ke , da sauri Sanam ta dube sa ya d'aga mata kai alamar da gaske , k'asa tayi da kanta dan tabbas ba wasa a cikin idon sa , ci gaba yayi da magana yace " ina fatan zaki iya zama da Soja ? Sanam bata d'ago ta dube sa ba kuma batace komai ba , Huneed jikin sa yayi sanyi kodai Bata son sa ? wata zuciyar tace " inbata sonka yazatayi kishinka , jin shurun da yayi yasa Sanam d'agowa tana duban sa kafin tace " dama kai Soja ne ? Huneed cike da Comfidence yace " Soja ne ni Sanam ina fatan jin hakan bazai sa ki canza ra'ayi akaina ba , yadda ya marairaice yayi kalar tausayi yasa tace " inaso kabani lokaci zanyi tunani , sannan ta mik'e tafara tsiyaya masa lemo a cup , kallon ta yashiga yi yana zancen zuci " Allah yasa ki amince min dan in har kika k'i to tabbas nasan zan shiga wani halin Sanam , mik'o masa lemon tayi tare da janyo filet d'in su donut da samosa tane fad'in " maza kaci kar muyi fad'a , murmushi yayi yana curb'ar lemon yana fad'in " ai bazan so yin fad'a da Gimbiya taba , sai dai lallashi da tausasawa wanda kayi ada ma angode , Sanam tace " nikuma kasan ban gode ba , dan saina rama duk abinda kamin d'aya bayan d'aya , dariya yasa yana gutsirar Donut d'in yace " haba gimbiya ta kiyi hak'uri dan karkimin horon da zan kasa rik'e kaina , hira sukeyi sosai me dad'i har yayi mata sallama yatafi.......
Bayan fitar sa da kamar minty biyar saiga megadin su ya shigo , har lokacin Sanam na zaune tana murmushi ita kad'ai tare da jin wani nishad'i , zuwa yayi ya rissina a gabanta yana mik'a mata wata leda yace " ranki ya dad'e gashi inji bak'on ki daya fita yanzu , hannu tasa ta ansa sannan ta sallamesa yafita , tashi tayi da ledar a hannu ta nufi sama cikin d'akin ta ....
Alhaji Abba yana hawa sama d'akin Hajiya Nafeesa ya shiga , nan ya zauna yana fad'a mata