Showing 24001 words to 27000 words out of 78990 words
wani lumshe ido yayi lokacin daya tuna yadda ta fad'o jikin sa da ana ruwan saman nan , tunda ga ranar ya tabbatar wa da kansa yana son Sanam d'in , dan haka dole da safe ya rarrashi Abarsa dan kar yaje wani yayi masa bugun baya abarshi da hamma , duk da yaga tarkon sa yakama kurciya bazai yi wasa da wannan damar tasa ba , amman dole sai ya jajurce akan tarbiyar Sanam , dan kwata kwata bata da tarbiya me kyau gashi uwa uba yadda ya fahimce ta bata da ilimin addini , a shirye yake ya tsaya tsayin daka ya gyara ta dan yasamu nagartattun 'Yaya............
*Tofa su Huneed har anfara tunanin Yara tun ba ashawo kan Sarauniyar Rigima ba*πΉπΉ
*Comment* plss
*'Yar Mutan Kanawa* _CeππΉ
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala Writer's Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Ina yiwa d'aukacin Masoyana barka da sallah , dafatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya karb'i ibadun mu , ππ»ππ»Allah ya mai mai ta mana Ameen_
*Mundawo hutu zamu d'ora Allah yabamu ikon rubuta dai dai ππ»ππ» wanda za'a amfana dashi*
Chapter 17.
Sanam kuka take sosai tamkar wacce akace Mahaifanta sun mutu , a haka bacci yayi gaba da ita mai cike da mafarki iri iri akan Huneed........
Hajiya Nafeesa ce rik'e da waya a hannu ta na neman number wata k'awar ta Hajiya Harira , bugu d'aya Hajiya Harira ta d'aga wayar tana fad'in " Manya manya maganin k'anana k'anana , murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " kune manya ai Hajiya Harira , kwata kwata ba'ajin ki agari tamkar laya kin b'ace , Hajiya Harira tace " Abubuwa sunyi yawa wlh shiyasa kikajini shuru , Hajiya Nafeesa tace " inason ganinki dan akwai wani aiki dana keso kimin , murmushi Hajiya Harira tayi sannan tace " shu'uma kice neman da kikemin badan Allah bane kenan ? dariya Hajiya Nafeesa tasa sannan tace " sai kinzo zamuyi magana kawai , nan sukayi sallama da juna kowacce ta katse wayar ta .......
Washe gari..
Sanam jitayi tanason tahowa gida , kwata kwata bata da sukuni saboda tunanin Huneed , babu kalmar dake mata yawo sai kalmar *Ina da Mata har da yara biyu,* wato mata garesa harda yara biyu ita kuma fa ? hawayen da ya cika idanunta tasa hannu ta goge , tabbas so baisan waje ba taya zai kaita inda bata da mahalli , dan ko zata mutu babu aure bazata auri namijin dake da mata ba , tayi nisa cikin tunani taji andafa kafad'ar ta , firgigit tayi takai duban ta ga gefen ta Mumyn su Rauda ce tsaye tana k'are mata kallo , wani murmushi Sanam ta k'ak'alo tana duban Mumyn , cikin harshen turanci Mumy ta tambayi Sanam meke damun ta haka take tunani , nan Sanam ta karkace tace babu abinda ke damunta kawai tana son tafiya gida ne , Mumyn Rauda ta zauna gefen Sanam tace mata " ko akwai abinda akayi mata takeson tafiya ? Sanam ta gyad'a kai alamun a'a , kawai tanason ta tafi ne saboda Babu Rauda zaman babu dad'i , Mumy Rauda tashiga lallab'ata akan tabari ta huta sosai sai ta koma k'asar Nageria d'in , badan Sanam ta so ba ta hak'ura akan zata k'ara sati sannan ta tafi.......
Huneed tuni yafara bincike akan gidan su Sanam , dan yanason sanin waye Mahaifinta da kuma asalin ta , cikin kwana biyu Huneed yasamu cikakken bayani akan wacece Sanam da kuma Mahaifinta har ma da sanin ai nahin wacce ta haifeta.....
Sosai Huneed yaji K'aunar Mahaifiyar Sanam na yadda ta sadaukar da 'Yar ta ga kishiyar ta , gashi yadda yasamu labari babu wanda ya b'ata Sanam face Daddyn ta da kuma kishiyar Mumynta , nan ya k'udirta aransa sai ya gyara ta tamkar yadda Mumyn ta take .....
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah ,
Sanam tuni an hallara a airpot d'in k'asar Turkey za'a taho gida , Mumyn Rauda da Rauda da mijinta sune sukayi mata rakiya zuwa Airpot , suna rungume da juna ita da Rauda sai hawaye suke har aka fara kiran sunayen fasinja , haka suka rabu suna kewar juna tare da d'agawa juna hannu har Sanam tashige cikin jirgi.......
*Gida Nageria*
jirgin su Sanam ya sauka a garin Abuja , tuni Fahad yaje d'auko a airpot , tana saukowa daga jirgi a hankali tamkar wacce batason saukowa , wani matashin saurayi shine ya matso daf da ita suka jero tamkar tare daman suke tafiyar......
[9/27, 09:49] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 18.
Dai dai da zasu sakko daga step din k'arshe na jirgin , Sanam ta zame tayi baya zata fad'i , da sauri wannan guy d'in ya rik'ota ta fad'a jikin sa tamkar a shirin film , duk wanda ya dubesu a lokacin sai yayi tunanin mata da miji ne suke tare , da sauri Sanam ta turesa tana janye jikin ta kafin tayi saurin saukowa daga jirgin , mutanen data gani ne yasa ta jin kunya tare da saurin nufar wajen ake parking din motoci.....
Tana k'ara sowa Fahad ya fito daga motar yana murmushi tare da nufota tamkar zai rungume yana fad'in " oyoyo My Angel , ganin yana neman rungume ta yasa tayi saurin dakatar dashi tana fad'in " thanks tayi saurin yi gefe tana bud'e bayan motar ta shige abin ta .....
Fahad sosai yaji babu dad'i akan abinda Sanam d'in tayi masa , murmushi yayi na mugunta a zuciyar sa yace " zakizo hannu zaki gane baki da wayo sai na cire miki wannan jin kan naki , nufar motar yayi zai shige a lokacin shikuma wannan saurayin ya k'araso , sallama yayiwa Fahad yabashi hannu sukayi musabiha , bayan sun gaisa saurayin nan ya dubi Fahad yace " dan Allah Yayan mu in babu damuwa zanyi magana da Babyn dake bayan motar , Fahad ya k'are masa kallo yayi d'an mutmushi yace " bisimillah ka yi mata magana , nan yayi masa godiya ya k'arasa jikin murfin motar inda Sanam din take , Fahad dariyar mugunta ya shiga yi masa dan yasan halin Sanam bata son jira mutukar tadawo daga tafiya , koda ya k'arasa jikin motar bubbuga glass yayi, Sanam tanajin sa kuma tana ganin sa amman ko motsi batayi ba bare ta bud'e , wayar ta tashiga dubawa tana jin wani haushi na tsayawar da Fahad d'in yayi bai shigo sun tafi ba , tsaki kawai tashiga yi dan batason b'ata lokaci ko kad'an , ganin Fahad bashi da niyyar tahowa su tafi kuma shima mutumin nan bashida niyar tafiya yasa ta sauke glass d'in motar , murmushi yayi yana duban ta kafin yace " kin kai kuma kin isa kiyi komai , kallo d'aya nayi miki nasan kin cika cikakkiyar mace wacce ta isa , ina neman Alfarma guda biyu zuwa uku a wajen ki dafatan zan samu ? Sanam tunda yafara magana tanajin sa amman ko kallon da batayi ba , cikin ranta tace " kaima ka isa a soka amman ko k'afar Huneed baka kama ba , nan take taji tanason ganin Huneed da kuma son jin muryar sa , cikin ranta take fad'in " nadamu da kai amman kwata kwata naga ko sau d'aya baka damu dani ba , Maganar saurayin dayake tsaye a kanta itace tadawo da ita daga duniyar tunanin Huneed datakeyi , murmushi tasamu kanta dayi sannan ta dubesa tace " bawan Allah kayi hak'uri sauri nake kazo kasameni a gida muyi magana , Murmushin jin dad'i yayi sanna ya dubeta yace " nagode sosai kuma zaki ganni in sha Allah , sunana Jaydeen A Ambasodor nasan kinsan Mahaifina a cikin garin nan na Abuja ? sarai Sanam tasan waye Jaydeen kuma tasan waye mahaifinsa da irin kud'in da yake dashi , amman sai cewa tayi " nifah bansan wani me irin wanna sunan ba ma , sosai Jaydeen yaji rashin dad'in maganar da Sanam tayi , amman saboda yarinyar lokaci d'aya ta tafi dashi , dan duk yawan duniyar da yayi bai tab'a karo da mace me k'irar Sanam ba , ga kyau ga diri tamakar itace ta shirya kanta , maganar tace ta katseshi tace " dan Allah yiwa direban can magana yazo mutafi , mamaki ne ya kama Jaydeen ganin yadda Fahad ya had'u amman take ce masa direba , shi duk a tunanin sa ma Yayan tane , zuge glass tayi batare da tak'ara magana ba , shima shigewa yayi yasanar da Fahad tare da tambayar sa inane gidan su , nan Fahad yabashi address sukayi sallama kowa yashige ya tafi.......
Hajiya Nafeesa tuni sunje wajen wani boka ita da k'awar ta Hajiya Harira , duk ta sanar dashi yadda takeso araba tsakanin Sanam da Abban ta , nan yabata magun guna kala kala wanda zatayi amfani dashi ......
Tana dawowa tashiga kitchen da kanta tayi girki kala kala , tana murna yau Sanam zata dawo taci wannan maganin shikenan Daddyn ta ya tsaneta , dan duk duniya bata da wacce ta tsana a yanzu tamkar Sanam ......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 19.
Tunda ga farko gate masu gadin gidan Alhaji Abba suka san 'yar lele tadawo , dan yanayin yadda akeyin hon. Kad'ai zai tabbatar maka da isowar Sanam gida ......
Tunda tafito daga motar suke zubewa suna mata sannu da zuwa amman ba wanda ta amsawa , hanyar k'ofar falon su tabi tana danna wayar ta , Tura k'ofar tayi wani k'amshi ya daki hancin ta , lumshe ido tayi dan tana mutuk'ar k'aunar k'amshin turaren wutar , cikin ranta take fad'in " Mumy akwai san k'amshi da tsafta shiyasa ko da yaushe intayi tafiya take missing d'in komai na Mumyn nata , bata gama zancen zucin ta ba taji muryar Mumyn tana fad'in " oyoyo My luvly dauther your welcome , da sauri Sanam ta fad'a jikin Hajiya Nafeesa tana fad'in " Miss u my mumyna , ina dawowa naji k'amshin turarenki me dad'i , murmushi Hajiya Nafeesa tayi tana wani rausayar da kai tace " wannan k'amshin ai na musamman ne , dan ke nasa *Zee MD* ta had'amin turaren ta me k'amshi da kama gida da jiki da kuma kaya , nasan kina son had'in turaren ta shiyasa na shirya takanas naje gidan ta harda na wanka da Humra na anso miki , murmushi Sanam tayi sannan tace " nagode Mumyna bari nashiga ciki nayi wanka sai na fito , da sauri ta nufi sama inda d'akin ta yake ......
Hancin motar Huneed ce ta shigo gate d'in gida su , saukar sa kenan daga taraba sunje wani aiki , yana fitowa daga motar sukayi karo da Hisham yana k'ok'arin fita , yana ganin d'an uwan nasa yafara fara'a yana fad'in " Soja mazan fama saukar yaushe ? Huneed yayi murmushi yace " saukar yanzu dan ko cikin barrack bashiga ba nataho gida , Hisham yace " sannu da zuwa ya anshi jakar hannun nasa ya juya suka shiga cikin gidan tare.......
Fahad yanemi parking space ya ajiye motar sannan ya shigo cikin gidan , karo sukayi da Hajiya Nafeesa lokacin Sanam ta hau sama sai ita kad'ai a zaune , Kusa da ita Fahad ya zauna yana fad'in " ina 'yar mulkin take ? Hajiya Nafeesa tayi masa nuni da baki alamar tana sama , tab'e baki yayi sannan yace " wallahi wannan yarinyar bata da mutunci ko kad'an , wai ni zata kallah ta kirani da direban ta , Hajiya Nafeesa ta dube sa tace " Sanam d'in ce tace maka direba ? Fahad cike dajin haushi yashiga bawa Hajiya Nafeesa labarin duk yadda sukayi a airpot , sannan yace " wanda yaje gun nata da zumar yana sonta shi ta turo wai ya kira mata direban ta , murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " k'yale ta kawai iya yaune duk rashin mutuncin nata , dan mahaifin ta tana juya mata baya zata dawo k'ark'ashin ikon mu , a lokacin zaka shigar da manufarka nasan auren ta kaga babu ta yadda za'ayi tak'i ka saboda bata da majin gina , dama kuma kaga bata damu da wannan saunar uwar tata ba , hasalima sai da nasan yadda nayi ta tsani mahaifiyar tata , kaga bata da inda zata nufa dole sai wajen mu dai , wani dad'i sosai Fahad yaji har da murmusawa tare da jinjinawa yayar tasa , dan yana mugun jin sha'awar Sanam , tunda yake mu'amala da mata bai tab'a cin karo da mace me k'irar jikin Sanam ba , komai na jikin ta ya had'u sosai , hatta da faratan hannun ta da k'afa abin kallah ne , nan yafara hango shi yana jikinta yana sarrafa ta yadda yakeso......
Sanam na shiga d'akin ta taci karo da wani k'amshin na musamman , lumshe ido tayi tana bud'e hanci tana shak'ar k'amshin , toilet ta fad'a danyin wanka , nan ma karo tayi da turaren wanka me k'amshi ta tsiyaya a cikin abin wankan ta , cikin ranta ta furta " gaskiya matar nan ta iya turaruka masu k'amshi , ga k'amshin me sanyi da kuma dad'i da sanyaya zuciyar me shak'a , tana shiga cikin ruwan wankan tafara lumshe ido tana wani sirtaccen murmushi.......
Koda Sanam tagama wanka tafito , shieyawa tayi cikin wasu riga da wando masu kyan gaske , gasu da rashin nauyi sosai sunyi kyau , wayar ta ta d'auka ta fito daga cikin d'akin ta sauko k'asa abinta.......
Tana sakkowa idon Fahad k'ur akanta yana kallonta , wani yawu yake had'iya jikake k'utt.
duk kallon dayake mata kwata kwata bata kula dashi ba , dan ta tattara hankalinta akan wayar ta tana nemo lambar Daddyn ta , tana k'arasowa taja kujera ta zauna tafara magana " Mumy me kika dafa min dan nayi missing din girkin ki , Murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan cikin kissa tace " abincin da kika fiso my Shalele , dan nasan dama dole zakiyi missing din girkin nawa , Sanam zatayi magana kenan sai Alhaji Abba ya d'aga wayar yana fad'in " welcome my queen dafatan kindawo lafiya ? Sanam tace " lafiya lau my Daddy , nayi Missing d'inka inason inganka , nan tashiga zabga masa shagwab'a tamkar wata yar k'aramar yarinya , da k'yar ya lallab'ata sannan ya sheda mata gashinan yanzu zai taho , murna tashiga yi sosai tana niyyar kashe wayar ya dakatar da ita , cike da lallab'awa yace " kin manta baki tambayi Mumyn taki ta biyu ba , Sanam tamkar tana gaban su ta tab'e baki sannan tace " nifa Daddy banda wata Mumy bayan tanan gidan kuma ai ita gata muna tare , Hajiya Maimuna dayake wayar Hands free take tana jin abinda