Showing 45001 words to 48000 words out of 78990 words
tsaruwar datayi , cikin ransa sai kuma hamdala yake ga Allah da samun Sanam cikin Rayuwar sa , tana k'arasowa ta shigo cikin motar tana wani kashe masa ido , shima kashe matan yayi yana fad'in " kinyi kyau sosai My Wifey tamkar kar mufita kinsan banaso ana gane min ke , murmushi tayi cike da shagwab'a tace " to muko ma kawai mu zauna dama nima bason fitar nake ba , dariya yasa yana fad'in " ank'i wayon sai munje munga Twins d'in Daddy , tuni yatashi motar me gadi ya bud'e musu gate suka fice.......
Sai da suka biya wani kataferen store Huneed yayiwa jarirai siyayya , duk inda suka gilma sai ankallesu saboda had'uwar da sukayi , suna gama siyayyar suka fito Huneed ya mik'awa Sanam key d'in motar yace " ungo kiyi driving d'in mu nagaji dayawa , batare da musu ba Sanam ta karb'i mukullin tashiga b'angaren wajen driving , taja suka tafi.....
Tafiyar minty 10 ita takawosu Anguwar Asokoro , duk wanda ya kwana ya tashi a garin Abuja yasan Anguwar Asokoro unguwa ce ta masu dashi , unguwa ce data amsa sunan ta ta zallar masu kud'i da 'yan siyasa , gidaje ne had'add'u da suka tsaru tamkar a turai , Sanam ta shiga Hon. A k'ofar wani katafaren gida , dasauri aka wangale mata k'ofar gate d'in gidan me gadi yana musu sannu da zuwa , wajen parking space taje ta paka motar tana duban Huneed , murmushi yayi mata sannan yace " yayi kyau babbar direba , ashe haka kika iya motar sai kace wata enginer , dariya tayi har dimple dinta ya motsa sannan tace " ai kafini iyawa tunda kai kana jan motar yak'i , Huneed yayi murmushi yace " kema zan koya miki dai kishirya , ganin Sanam sai jan shi da hira take tak'i bari su fita daga motar yasa shi cewa " My Wifey yakama ta mu shiga daga ciki ko , batace masa komai ba ta bud'e murfin k'ofar motar ta fice abinta , shima fitowa yayi tare da saka me gadi ya d'ebo kayan cikin but d'in motar ya biyosu dashi ......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 31.
Jerawa Sukayi suka shiga cikin Palor gidan , kana ganin su tamkar miji da mata dan iya dacewa da juna sungama yi , Huneed tunda suka shigo cikin gidan ya raina kansa sosai , duk tsaruwar gidan su Sanam sai yaga ashe bakomai bane wannan shine k'arshen had'uwa , suna saka kansu cikin palor gidan wani k'amshi tare da wani dadda d'an k'amshi ya bugi hancin su , Sanam gawanar son k'amshi tuni ta lumshe ido tana kuma bud'e hanci tana shak'ar k'amshin turaren wutar , tunda takejin turaren wuta masu k'amshi bata tab'a karo da wannan me dad'in k'amshin haka ba..
Sallama sukayi su dukan su dan Huneed k'in yarda yayi ya tsaya a harabar gidan , shi burun sa bai wuce yaga Twins da suka kasance k'annen Bbyn tasa , palor cike yake da 'Yan uwan Hajiya Maimuna suna ta hira abinsu hankali kwance , sallamar da Su Sanam sukayi itace duk ta dakatar dasu daga hirar da sukeyi , tuni kallo ya dawo gun Sanam da Huneed wanda suka tsaya daga bakin k'ofa sukayi turus , Hajiya Maimuna idanu ta zubawa Sanam tana mamakin zuwan ta , dan rabon data ga Sanam a gidan nan har ta manta ma , d'aya daga cikin 'Yan uwan Hajiya Maimuna ce tace musu " sannun ku da zuwa bisimillah ku shigo , Sanam tamkar wacce batason tafiya haka ta taka ta zauna a d'aya daga cikin kujerun palor , Huneed ya durk'usa har k'asa yana gaidasu su duka , amsa masa sukayi cike da sakin fuska sannan ya mik'e shima ya zauna , Mamaki ne ya kama zuciyar Huneed ganin duk matan dasuke cikin palor kusan kamar su d'aya da Sanam , Wacce ya ke kallo kuma yaji ajikin sa itace me jegon tafi kowacce kama da Sanam , dan wallahi badan tana da shekaru ba kuma gata da jiki wallahi si yace Sanam ce , dan kamar tasu ta b'aci sosai . cikin zuciyar sa yake tunanin tabbas akwai abinda Sanam ke b'oye masa , amman wannan kana Ganin ta basai anfad'a maka ba kasan itace wacce ta haifi Sanam , wata ce daga cikin Matan tace " Sanam baki gan mu bane kikayi shuru batare da kin gaida mu ba ? sai sannan Huneed ya tuna da abinda Sanam tayi wato rashin gaida mutanen da tagani , shuru tayi tamkar wacce batasan ana magana ba , Huneed ya dube ta itama shi take kallo yashiga yi mata alama da ido akan ta gaidasu mana , d'auke kai tayi tana turo baki kafin tace " ina yinin ku , amsawa sukayi da lafiya sannan kowacce ta mik'e tana barin palor , Hajiya Maimuna ya rage a ciki itama kuma mik'ewar tayi zata bar palor , da sauri Huneed yace " Mumy ina Twins d'in suke plss , cak ta tsaya tana juyowa ta kallesa tabbas wannan ko waye yana da matsayi me girma a wajen Sanam , kuma ita kanta tunda suka shigo tare ta yaba da nutsuwar sa da kuma kwarjinin sa , a hankali Hajiya Maimun ta furta zan turo akawo maka su yanzu , sai dai dan Allah inaso kar kabawa wannan yarinyar ta kusa da kai yarana , dan shi mak'iyi duk lokacin da zai kusan ce ka to dole akwai mugun abu acikin ransa , tana gama magana ta juya ta bar palor abin ta itama...
sosai maganar Hajiya Maimuna ta ratsa zuciyar Sanam , mik'ewa tayi da sauri tayi hanyar barin palor idanun ta cike da hawaye , da sauri Huneed ya sha gaban ta yana fad'in " ina zakije Sanam ? inaso kidawo ki zauna dan akwai abinda nakeso ki sanar dani game da Mumyn Twins , meye ya had'a da ita kuke irin wannan rayuwar haka ? sannan jikina yabani Mumyn Twins itace wacce ta haifeki Sanam duba da yadda kuke kama sosai , dan Allah ki taimaka ki cireni acikin duhu wallahi kaina yafara d'aukar zafi , daga Bayana su yaji ana cewa " tabbas Maimuna itace Mahaifiyar Sanam , Itace wacce ta ta raineta tuntana ciki har Allah ya fito da ita duniya , ta shayar da ita na tsawon shekara biyu bata re da ta k'osa ko gajiyawa ba , da sauri Huneed ya jiyo da ganin wacece take magana wata dattijuwa ce fara sol tamkar ita tayi kanta saboda kyau , kamar su d'aya da Sanam har tafi kama da Sanam d'in akan Mumyn Twins , Hannun ta rik'e da kyawawan jariran wad'an da suka sha kayan sanyi ajikin su , Sanam k'urawa Hajiya Babba idanuwa tayi dan tunda take bata tab'a ganin taba , gashi komai nasu iri d'aya dan har tafi kama da ita fiye da Mumyn nata , tabbas wannan ko tantama babu itace ta haifi Mumyn ta , take taji soyayyar dattijuwar me cike da kwarjini da kamala ya kama ta , ido ta zuba mata ko k'iftawa babu tana kallon ta , Hajiya Babba taci gaba da magana " tunda ga randa aka yaye Sanam bata k'ara zama tare da Maimuna ba , Mahaifinta ya d'auke ta yayi wa Matar sa kyautar ta wacce itace sanadiyyar raba Uwa da 'Yar ta , Sanam jin ance Hajiya Nafeesa itace sanadin rabata da Mumyn ta yasa taji haushin Hajiya Babbar ya kamata , take ta bud'e k'ofar palor ta fice abinta rai a b'ace , dan duk duniya batason atab'a Mumyn ta Hajiya Nafeesa wacce takejin ta duk duniya bata da kamar ta , ....
Huneed duban Hajiya Babba yayi cike da girma mawa ya gaida ta , amsawa tayi cike da sakin fuska dan tayaba sosai da hankalin sa , kuma tanaji ajikin ta shine zai kawo wa jikar tata Alkairi a cikin Rayuwar ta , ansar yaran yayi tare dayi musu addu'a ya d'auko wayar sa yayi musu pic , tabbas Daddy yayi gaskiya daya cewa Sanam sunfita kyau sosai gaskiya yaran sun gaji da had'uwa , k'aunar suce tashiga ratsa shi ta ko 'ina yana kallon su , tunowa da Sanam yasa yabawa Hajiya Babba su tare da mik'ewa yana fad'in zai tafi , Hajiya Babba ta dubesa tace " Yaro mungode sosai Allah yayi maka albarka , nasan wannan zuwan da kukayi kai ne ka saka Sanam tazo , hakan ya nuna mana tana sonka kuma kaima kana sonta , dan Allah inaso kayi amfani da soyayar ka da ita ka dai daita tsakanin ta da Mahaifiyar ta , ka kuma dunga nuna mata muhimman cin Mahaifiyar ta dan duk duniya bata da kamar ta , duk da munsan komai datakeyi yasamu nasaba ne daga irin hannun data taso , ilimin addinima ba lallai tana dashi ba dan Maimuna tasha gayamin ita kanta marik'iyar ta ta bata damu da ibada ba , dan Allah yaro ka taimaka ka ceto rayuwar ta daga cikin duhu ka dawo da ita haske , dan ajikina nakejin had'uwar ku da ita alkairine kuma tunda naganka naji kashiga raina , Huneed yace " insha Allah zanyi iya k'ok'arina naga Sanam ta canza halayen ta marasa kyau , kuma kiyiwa Mumy Albishir insha Allah ni Huneed nayi mata Alk'awari Sanam sai tadawo gare ta cike da so da k'auna , wani dad'i Hajiya Babba taji nan danan tashiga saka masa albarka yayi mata sallama yatafi.....
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Inayiwa d'aukacin Masoyana Barka Da Sallah , Dafatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya maimaita manaππ»_
*Masu k'orafin bana typing dayawa da masu cewa sai na dad'e nake Typing , ina mai baku hak'uri akan hakan duk zangyara amman kudunga yin uziri , sannan duk wani marubuci yanaso yaga ana yi masa Comment duk lokacin da ya turo da book d'in sa , Amman dayawa a cikin ku basayin Comment , dan Allah munaso inkuji dad'in Book kudunga fitowa kuna yabawa Marubutan dan suma suji dad'i ,*
*Nagode Sosai Masoyana* _nima ina k'aunar ku tamkar inzo in sace ku mu rayu tare_πΉπ₯°π₯°π€π»ππΉ
Chapter 32.
Koda Huneed ya fito daga cikin gidan su Sanam neman ta yayi yarasa , da sauri ya shiga motar ya fice daga cikin gidan....
Hanya ya dunga dubawa ko zai ganta amman harya fita daga estete d'in Anguwar bai ganta ba , haka ya dunga ware ido yana kallon titi ko zai ci karo da ita , can ya hangota a tsaye tana kallon titi ranta duk a b'ace , dayake Unguwar babu masu Napep sosai sai dai in Allah yasa sun shigo da wani , wannan yasa Sanam bata samu abin hawa ba har wannan lokacin , yana k'arasowa ya kashe motar tare da fitowa daga ciki , Sanam ganin sa da tayi yasa ta kauda Fuskar ta gefe tamkar bata gansa ba ,...
Murmushi Huneed yayi sannan ya k'araso wajen da take , duban ta yayi yaga idanun ta sunyi ja tamkar ma kuka tayi , da sauri yace " Baby me yafaru dake haka naga idonki yayi ja ? Sanam jitayi tamkar yazo mata da rainin hankali , komai daya faru ai shine ya janyo mata , inda bai takura mata tazo ba taya zasu ganta bare su gaya mata magana , cike da jin zafin sa tace " dama sai da nace maka bazan zoba amman ka takura min nazo , ko kad'an basa k'auna sannan sun tsani Mumyna to meye amfanin inje inda suke , Huneed yayi murmushi sannan ya rik'o hannun ta yace " sud'in sunfi kowa sonki da k'aunar ki , kintab'a ganin uwar da zata durk'usa ta haifi d'a a cikin ta sannan tace bata k'aunar shi ? tamkar k'aramar yarinya haka Sanam ta gyad'a kai alamar a'a , Huneed yaci gaba da magana " To kidaina cewa basa sonki dan dukan su nagano tsantsar soyayyarki a idanun su , kece dai bakya son su tunda naga hakan atare dake , Sanam ta d'an dubesa kad'an sannan ta kauda fuskar ta , har wannan lokacin Huneed na rik'e da hannun Sanam d'in , k'asa yayi da murya sannan yace " inaso Babyna tadaina fushi da Mumyn ta kuma Mahaifiyar ta wacce takawo ta duniya , nasan zaki d'auka cewa Mumy Amarya tafi sonki fiye da Mumyn ki , to ba gaskiya bane dan duk duniya bayan Allah daya halicceki ba wanda ke sonki sai Mumyn Twins , karki manta itace tayi rainon cikin watakila ma bata iya cin komai , a haka har tayi nak'udar ki ta haifeki ta shayar dake har kika kawo wannan matakin , kinga kuwa duk wanda zai nuna miki soyayya bayan ta yake , tunda Huneed yafara magana jikin Sanam yayi sanyi sosai , ganin hakan yasa Huneed yaci gaba da yi mata nasiha tare da nuna mata girman iyaye musamman girman uwa , har suka shiga motar suka tafi yana kuma yi mata nasihar wanda yake da tabbacin tana ratsa Sanam har sassan jikinta.......
Hajiya Nafeesa tunda ta fita gidan Hajiya Harira suke shirya makircin su , har maganar Maryam da yadda suka shirya ita da Fahad sai data gaya mata , Hajiya Harira kuwa taci gaba da ingiza Hajiya Nafeesar akan hakan da sukayi yayi dai dai , sannan ta d'ora da cewa " kinga inkika samu ta haihu ta baki d'an shikenan dama kafin lokacin kin raba Sanam da Alhaji kinsa masa tsanar ta , Hajiya Nafeesa ta tab'e baki sannan tace " ai yanzu ko Alhaji ya daina son Sanam ba muci riba ba , tunda gashi yanzu ta kuma haifo masa wasu , yanzu haka maganar dana ke miki baki ga yadda yake rawar k'afa ba tamkar akansu aka fara masa haihuwa , Hajiya Harira tace " suma dole atashi tsaye akan su dan sonake dukan su ya tsanesu har ita uwar tasu , Hajiya Nafeesa tace " kin manta wannan shegiyar matar batajin asiri , wanne irin boka ne ba muje gunsa ba akan araba ta da gidan amman kina kallo kamar dasa ta ma akeyi , Hajiya Harira tace " kibani lokaci zan samo mafitar yadda za'ayi masu dukan su , haka suka yini suna k'ullah yadda zasu tarwatsa Sanam da Hajiya Maimuna.......
Huneed yaso su biya ta gidan su Sanam ta gaisa da Hajiyar sa , amman ganin duk Sanam d'in bawani walwala take ba yasa ya wuce da ita gida , suna shigowa Harabar gidan suka ci karo Jaydeen a tsaye jikin motar sa yana danna waya , Huneed na kallon sa yaji wani kishi ya kamashi dan ko ba'afada masa ba yasan wajen Sanam yazo , Sanam ta kalli Huneed lokaci d'aya taga ya canza fuska yana kallon wajen da Huneed yake , tamkar tasa dariya haka taji ganin yadda ya had'e girar sama da k'asa tamkar bashine ke lallab'ata ba , a zuciyar ta tace bari nayi tsokana yanzu , kallon sa tayi tace " My dear ni zan shiga gida sai munyi waya ko , Huneed yadubeta sannan yace " zaki shiga gida ko kuma zakije wajen bak'on ki , to in kingaji da ganina ni bangaji da ganin ki ba kuma bayanzu nakeso ki tafi ba , wani murmushi Sanam tayi najin dad'in yadda Huneed ke san ta , dan tasan so ne kesawa a dunga jin kishin mutum , ta karyar dakai tana duban sa cike da shagwab'a tace " haba My dear daga ganin mutum sai kace bak'o na ne ? kasani ko bak'on Mumy ne ni bani dawani wanda mukayi dashi zai zo , Huneed yace " to koma waye dai bazaki fita ya kallemin