Showing 18001 words to 21000 words out of 78990 words
k'ara fito da kyawun idanunta masu kama da madara , fitowa tayi palor tuni mutanen dake zaune cikin falor suka saki bakin kallon ta , Ammin Rauda tana duban ta tace " wow my Beautifull queen , murmushi Sanan tayi wanda siririyar wushiryar ta ta fito tare da dimple d'inta ya lotsa , ai take suka rud'e sai cewa suke " wow so beautifull nice , aikuwa Sanam tasamu abinda takeso wato a fasa mata kai ace tana da kyau , wani yauk'i tashiga yi har ta fito harabar gidan , lokacin Abokan Ango sunfara zuwa d'aukar su dan kaisu wajen Party , suna ganin Sanam kowanne ya kafeta da ido suna k'arewa k'ugunta kallo da k'irjin ta , wanina ciki yace " wannan Babyn ta had'u sosai dama zata yarda tabani dare d'aya dana mallaka mata duk abinda takeso , dukan su suka shiga yabon halittar Sanam wacce ta tsaya gefe d'aya tana danna waya da alamar kiran wani zatayi .......
Huneed tunda gari ya waye ya shirya ya shiga gari , sai wajen biyu da rabi yasamu kansa da son zuwa gidan da Sanam ta sauka , dai dai lokacin dayazo a dai dai lokacin Sanam ta fito da wannan shiga , bayan wata bishiya ya lab'e ya saka face mark d'in sa da glass yana lek'owa , ganin yadda maza ke kallon Sanam hakan ya kuma b'ata masa rai over , cikin ransa yace " wai wannan yarinyar anya mutum ce kuwa ? sai kace shaid'aniya zatayi irin wannan shigar , tamkar ma ba musulma ba dubi jikinta ko d'ankwali bata saka ba , Asuk' ne ya fito daga motar ya nufo wajen Sanam , tana zuwa yayi hugging d'in ta batare da ta kula dashi ba , tuni mutanen dake gurin suka fara yin tafi suna jinjina masa yadda yayi hakan , Huneed nadaga bayan bishiya jiyayi juwa na neman kamashi , wani abu yaji ya tokare masa a k'irjin sa tamkar numfashin sa zai tsaya haka yaji , Sanam jin yadda Asuk' ya rungume ta yasa ranta yayi mugun b'aci , k'arfin ta ta had'a guri guda ta hankad'ashi gefe , tana yin hakan tayi saurin komawa cikin gidan dan yagama b'ata mata rai over , Asuk' sosai yaji haushin abinda tayi masa dan har bige kansa yayi jikin motar , dan haka shima cikin gidan yabita.......
Huneed take ya yanke shawarar mutuk'ar Sanam tafito to sai ya d'auke ta , dan ya fuskan ci wannan guy d'in zai iya yimata komai yadda ya fusata , kuma shima bazai so ace ko d'an yatsan ta wani banza yasake rik'ewa ba , haka ya zauna zaman jiran fitowar ta , yana zaune motoci suka fara wucewa dan tafiya gurin Kamu , kwata kwata bai ga Sanam ta fito ba har ya tashi yafara nufar cikin gidan dan ganin me takeyi , lokacin kowa yatafi wajen party har Ammin su Rauda da k'awayen ta itama , ita kuwa Rauda dama tuni suna can ana shirya ta daga can za'a wuce sa ita , yana tsaye yana kai kawo a harabar cikin gidan sai ga Sanam da gudu ta fito tana kuka rigar ta duk ta yage ana ganin jikinta , bayan ta Asuk' ne daga shi sai gaje ran wando ya biyota da gudu shima , wajen Huneed ta nufo tana fad'in " dan Allah ka taimaka min wallahi d'an iska ne , wani mari Huneed ya tsinka mata sannan ya janyo hannun ta ya kawo ta wajen Asuk' dake tsaye yana kallon su yace " gatanan kayi mata duk abinda kakeso kayi , mamaki ne yaka ma Sanam tafara Nazarin a inah tasan wannan muryar ? Asuk' ya rik'e hannun ta tare da cewa " Huneed thank u Yana k'ok'arin janta ya shigar da ita cikin gidan , kwata kwata Sanam bata ceton kanta take ba so take ta tuna muryar waye wannan dan tabbas tasan muryar kuma taji ta ba sau d'aya ba , juyawa Huneed yayi yana dafe kansa yayin da Asuk' yake jan hannun Sanam zai shiga da ita cikin gidan , ita kuma tana wai wayen Huneed tana son sanin waye shi ? gab da zasu shiga k'ofar falor Huneed yace " Stop dawata murya wacce tasa dukan su suka firgita , tuni Asuk' yasaki Hannun Sanam yana duban Huneed wanda ya nufo su gadan gadan tamkar zaki , yana zuwa yashiga duka Asuk' yana fad'in " rungumar da kayi mata baiyi ba sai ka ai ga keta mata haddi , mara tarbiya kawai wawa jaki , sai dukan sa yake tamkar zautacce haka yakoma , tuni ya sumar da Asuk' sannan ya waiwayo kan Sanam wacce tagama tsurewa jikin ta sai rawa yake , yana zuwa yajanyo hannun ta batare dayayi magana ba har suka fita daga gidan suka nufi titi , tunda ya rik'e mata hannu ta tuno da ko waye , Huneed bai saki hannun Sanam ba har sai da suka isa Hotel d'in dayake suka shiga har cikin d'akin daya kama ...........
*Comment plss*
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 14.
Sunfi kusan minty goma a haka sannan aka d'auke ruwa , da sauri Sanam ta mik'e daga jikinsa tana sunkuyar da kanta k'asa dan kunya ce ta kama ta , Huneed shima mik'ewa yayi tsaye yana dube dube tamkar wanda yake neman wani , motocin da suka hango sun nufo k'ofar gidan su Rauda ya tabbatar musu da Andawo daga wajen party , Huneed ya juyo ya kalli Sanam yace " zan iya tafiya yanzu tunda naga sundawo , inaso ki kula da kanki sai wani lokacin , bai jira amsar ta ba ya wuce yabar wajen......
Da kallo Sanam tabi bayan Huneed tana jin kamar ta tashi ta rungumosa, cikin ranta taji kamar ta kirashi tace yadawo su dauwa ma a haka, tana kallon bayan sa har ya k'ulewa ganin ta amman ta kasa d'auke idon ta akansa , tayi nisa cikin tunanin taji andafa mata kafad'a , da sauri tayi firgigit tadawo daga tunanin data keyi tana duban wanda ya dafa ta , Rauda tagani tasaha kwalliya cikin shigar amare ba k'aramin kyau tayi ba , Rauda tace " ina kikaje Sanam kwata kwata banganki a wajen Kamu ba , gashi in ankira wayar ki bakya d'agawa ina fatan dai lafiya ? murmushi Sanam tayi sannan tace " bansan wajen ba, kuma na hau taxi muka gama yawo bangane ba har aka fara ruwa , Rauda tace " amman Janifa ta gayamin cewa taga kin shirya cikin shigar da sukayi , kuma lokacin ankawo motoci amman baki shiga kowacce ba , Sanam ta mik'e tace " kawai Allah baiyi zanzo ba amman gobe insha Allah bazanyi missing d'in Lunch ba , tare suka jera suka shiga cikin gidan suna hira abinsu , koda suka shigo harabar gidan Sanam tashiga dube dube kozata ga Asuk amman bata gansa ba , haka suka shige cikin gidan wanda yake acike da mutane 'yan biki........
Sanam kwata kwata takasa rintsawa saboda tunanin Huneed , babu abinda ke mata yawo a ido sai hoton kwanciyar datayi a jikin Huneed , lumshe idon ta tayi tana wani murmushi tana k'ara rungume filon dake hannun ta , a hankali ta furta " wannan Guy d'in na musamman ne yana burgeni , a haka barci yayi gaba da Sanam cike da tarin mafarkan Huneed.......
A b'angaren Huneed tunda yabar wajen Sanam ya taho sukayi waya da ogan su , nan aka sheda masa kiran gaggawar da ake musu akan rikicin da 'yan ta'adda suke a garin sakkoto , Kwata kwata Huneed kiran bai masa dad'i ba kawai dai dan ba yadda zaiyi ne , amman kafin yatafi ko sau d'ayane sai yakoma yaga Sanam dan yarinyar ta tsaya masa arai , kawai halayen tane basuyi ba kwata kwata amman da sannu zai gyara ta .......
Washe gari.....
Tunda Sanam ta tashi taji tana k'aunar ta sake ganin Huneed , bayan ta karya tayi wanka tashirya cikin wata doguwar riga me kyau daga cikin wad'an da ya siya mata , samun kanta tayi da saka d'aya daga cikin Hijab d'in mahadin rigunan , ba k'aramin kyau tayi ba ita kanta sai sai k'ara duba mirror take , tana fitowa su Rauda suna zaune suna shirya abubuwan da zasu yi amfani dasu anjima , suna ganin ta suka tsaya suna kallon ta kowanne sai yaba kyan datayi suke , Rauda tace " Sanam kowanne kaya kikasa sai kinyi kyau inama ace nice haka , murmushi tayi sannan tace " kema haka ai kike My R kowanne dresing kikayi sai yayi miki kyau , Rauda tayi murmushi tace " ai nasan kinfini nesa ba kusa ba , wai ina ma zakije haka muna shirye shirye kina ficewa ke kuma ? Sanam tace " sorry my R yanzu zandawo ba dad'ewa zanyi ba , da sauri ta fice dan batason Ammi taji zata fita ta tsaida ta ma , tana fitowa harabar gidan suka kuma karo da Asuk , tana ganinsa ta had'e ranta tana yin gefe da fuskar ta , shima dayake yanajin haushin ta ko kallon ta bai kuma ba ya shige abinsa tamkar bai ganta ba .....
Taxi ta tsaida tagaya masa inda zai kaita , sai da ta shiga ta zauna sannan tafara zancen zuci " to yanzu innaje mezan ce masa nazo yi ? wata zuciyar tace " kawai kice kin yarda abinki ne shine kika dawo d'auka , tana wannan tunane tunanen nata har suka zo dai dai k'ofar Hotel d'in , fitowa tayi sannan tabiya me taxi kud'in sa yayi gaba , ta dad'e a k'ofar wajen tana kaiwa da komowa , da shawarar da zuciyar ta ta yanke nacewa wani abun ta yardar tashiga ciki......
Tunda gari ya waye Huneed ya had'a kayan sa cikin jakar sa , wajen goma na safe a can k'asar ya fita yashiga gari zaiyiwa Hajiyar sa siyayya , daga can ya biya airpot yagama komai jirgin su zai tashi k'arfe uku na rana , yana gama komai ya nufi gidan su Rauda ya tsaya daga wajen daya saba tsayawa yana lek'en harabar gidan ko Allah zai sa Sanam ta fito , yafi minty 30 amman baiga kowa ba sai yara suna ta wasan su abinsu , ganin yana k'ara b'ata lokaci yasa ya juya zai tafi , wata zuciyar tace " to inta fito mai zai ce mata ? kawai ya juya ya hau taxi yakoma Hotel d'in , a lokacin Sanam na zaune a reception dan sun sheda mata me number da ta tambaya ya fita , tana xaune ta had'a kai da gwiwa taji wani k'amshi ya doki hancin ta , tana d'agowa taga wucewar Huneed batare da ya kula da ita ba , sai da tabari ya jima da wucewa sanna ta nufi d'akin nasa......
Tana zuwa ta k'wank'wasa k'ofa daga ciki yace " yes coming , tura k'ofar tayi tashiga cikin d'akin lokacin dagashi sai tawul zai shiga wanka , tana ganin da haka ta juya da baya zata koma waje , da sauri yace " karki fita bati nashiga toilet wanka zanyi , da sauri ya fad'a cikin toilet d'in yanajin wani farin ciki da ganinta dayayi , Sanam kuwa yadda tagansa ba k'aramin tsoro taji ba , tunda take bata tab'a ganin jikin namiji haka ba sai yau , samun waje tayi ta zauna tana tunanin meyake shirin faruwa da itane.......
*Comment* plss
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[9/27, 09:45] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 14.
Sunfi kusan minty goma a haka sannan aka d'auke ruwa , da sauri Sanam ta mik'e daga jikinsa tana sunkuyar da kanta k'asa dan kunya ce ta kama ta , Huneed shima mik'ewa yayi tsaye yana dube dube tamkar wanda yake neman wani , motocin da suka hango sun nufo k'ofar gidan su Rauda ya tabbatar musu da Andawo daga wajen party , Huneed ya juyo ya kalli Sanam yace " zan iya tafiya yanzu tunda naga sundawo , inaso ki kula da kanki sai wani lokacin , bai jira amsar ta ba ya wuce yabar wajen......
Da kallo Sanam tabi bayan Huneed tana jin kamar ta tashi ta rungumosa, cikin ranta taji kamar ta kirashi tace yadawo su dauwa ma a haka, tana kallon bayan sa har ya k'ulewa ganin ta amman ta kasa d'auke idon ta akansa , tayi nisa cikin tunanin taji andafa mata kafad'a , da sauri tayi firgigit tadawo daga tunanin data keyi tana duban wanda ya dafa ta , Rauda tagani tasaha kwalliya cikin shigar amare ba k'aramin kyau tayi ba , Rauda tace " ina kikaje Sanam kwata kwata banganki a wajen Kamu ba , gashi in ankira wayar ki bakya d'agawa ina fatan dai lafiya ? murmushi Sanam tayi sannan tace " bansan wajen ba, kuma na hau taxi muka gama yawo bangane ba har aka fara ruwa , Rauda tace " amman Janifa ta gayamin cewa taga kin shirya cikin shigar da sukayi , kuma lokacin ankawo motoci amman baki shiga kowacce ba , Sanam ta mik'e tace " kawai Allah baiyi zanzo ba amman gobe insha Allah bazanyi missing d'in Lunch ba , tare suka jera suka shiga cikin gidan suna hira abinsu , koda suka shigo harabar gidan Sanam tashiga dube dube kozata ga Asuk amman bata gansa ba , haka suka shige cikin gidan wanda yake acike da mutane 'yan biki........
Sanam kwata kwata takasa rintsawa saboda tunanin Huneed , babu abinda ke mata yawo a ido sai hoton kwanciyar datayi a jikin Huneed , lumshe idon ta tayi tana wani murmushi tana k'ara rungume filon dake hannun ta , a hankali ta furta " wannan Guy d'in na musamman ne yana burgeni , a haka barci yayi gaba da Sanam cike da tarin mafarkan Huneed.......
A b'angaren Huneed tunda yabar wajen Sanam ya taho sukayi waya da ogan su , nan aka sheda masa kiran gaggawar da ake musu akan rikicin da 'yan ta'adda suke a garin sakkoto , Kwata kwata Huneed kiran bai masa dad'i ba kawai dai dan ba yadda zaiyi ne , amman kafin yatafi ko sau d'ayane sai yakoma yaga Sanam dan yarinyar ta tsaya masa arai , kawai halayen tane basuyi ba kwata kwata amman da sannu zai gyara ta .......
Washe gari.....
Tunda Sanam ta tashi taji tana k'aunar ta sake ganin Huneed , bayan ta karya tayi wanka tashirya cikin wata doguwar riga me kyau daga cikin wad'an da ya siya mata , samun kanta tayi da saka d'aya daga cikin Hijab d'in mahadin rigunan , ba k'aramin kyau tayi ba ita kanta sai sai k'ara duba mirror take , tana fitowa su Rauda suna zaune suna shirya abubuwan da zasu yi amfani dasu anjima , suna ganin ta suka tsaya suna kallon ta kowanne sai yaba kyan datayi suke , Rauda tace " Sanam kowanne kaya kikasa sai kinyi kyau inama ace nice haka , murmushi tayi sannan tace " kema haka ai kike My R kowanne dresing kikayi sai yayi miki kyau , Rauda tayi murmushi tace " ai nasan kinfini nesa ba kusa ba , wai ina ma zakije haka muna shirye shirye kina ficewa ke kuma ? Sanam tace " sorry my R yanzu zandawo ba dad'ewa zanyi ba , da sauri ta fice dan batason Ammi taji zata fita ta tsaida ta ma , tana fitowa harabar gidan suka kuma karo da Asuk , tana ganinsa ta had'e ranta tana yin gefe da fuskar ta , shima dayake yanajin haushin ta ko kallon ta bai kuma ba