Showing 51001 words to 54000 words out of 78990 words

Chapter 18 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3688

itace take fita yawonta tasamo musu abinda zasuci ita da Maman ta da k'annen ta , Sanam jin Diyana tayi shuru yasa ta kalleta tace " ko kinfara bin diddigin ne tun yanzu ? murmushi tayi suka ci gaba da hirar su , sai dai Diyana ta k'udurta aranta tabbas sai tagano me Maryam tazo yi gidan su Sanam......




Bayan fitar su Sanam Maryam ta dubi Fahad tace " akwai matsala sosai fa , Fahad yace wacce irin matsala kenan ? wallahi wannan k'awar Sanam d'in da kagani unguwar mu d'aya da ita , tasanni farin sani gata da iya saka ido tamkar 'yar jarida , Fahad yace " karki damu bari muje muyi magana da Aunty intaka ma a hanata shigowa gidan nan sai a hanata , sai sannan Maryam tasaki ajiyar zuciya suka shige cikin gidan.......


Huneed tunda sukaje gidan Mumyn Twins wato Mahaifiyar Sanam , sai da ya koma sau biyu gidan gar number ta garesa , har waya suke da Mumyn yana kwantar mata da hankalin ta , anan ya kuma jin halin Hajiya Nafeesa da yadda ta lalata Sanam tuntana k'arama bata ganin Mutuncin kowa sai nata , kuma itace ta rok'eshi Alfarma akan tanason Sanam tasamu ilimin addini ko yaya ne , dan har da rashin ilimi yana d'awainiya da ita , haka Huneed ya shiga kyautatawa Mumyn Sanam duk da yasan babu abinda suka nema suka rasa , amman duk k'arfin mutum kuma duk kud'in sa yana mutuk'ar son yaga ana kyauta ta masa , kuma koda wasa bai tab'a gayawa Sanam ba bare ya nuna mata a fuska.......


Babban wajen Shopping Sanam sukaje ita da Diyana , sosai ta d'ibi kaya da turaruka manya tare da sabulai masu tsada , Diyana itama Sanam tace mata ta d'auki duk abinda takeso , haka ta zage ta d'ibi kayan kwalliya da turaruka itama , sai dogayen riguna had'add'u wanda ta d'aukar musu kala biyu ita da Sanam iri d'aya , suna cikin zagaye a wajen suka ci karo da Jaydeen yana tsaye yana duban su , wani tsaki Sanam tayi tare da k'ok'arin canza hanya , da sauri Jaydeen yasha gaban ta yana fad'in " plss ko Minty 5 kibani inason magana dake , Sanam ta galla masa harara tana fad'in " Malam dan Allah kabani waje ina da abubuwan yi , Jaydeen yayi murmushi yace mata " Sanam inasonki sosai araina kuma tunda nake ban tab'a son Abu ban samu ba , kamar yadda Mumyn ki tace mun in kwantar da hankalina tamkar nasameki ne , to kisani kafin Daddyn ki yabar k'asar nan sai da Daddyna yaje sukayi magana dashi , kuma shima Daddyn ki ya tabbatar wa da Daddyna cewar yana dawowa zai d'auramin aure dake , wani kallo Sanam tayi masa wanda yake nuni da baka da hankali , magana yaci gaba dayi yana fad'in " inaso inja kunnen ki akan wannan matsiyacin saurayin naki , daga yau sai yau karki k'ara binsa ko inah dan bazan jure ganin yanamin yawo da Mata a titi ba , wani takaicine ya kama Sanam takasa magana , tsaki tayi kawai ta wuce batare da ta kuma bi takan sa ba ,....




Suna k'arasawa gun biyan kud'i akace musu anbiya musu , Sanam cike da fad'a ta kalli wanda yace anbiya musun tace " to ce muku akayi bani da kud'in da zanbiya ne ? Malam inaso kubashi kud'in sa kufad'amin nawa zanbiya , wani daga ciki yace " haba Hajiya ai ba'a maida hannun kyauta baya , wata harara ta watsa masa sannan tace " to ni na maida sai ayimin hukunci , Diyana ce takamo hannun ta suka fito daga wajen dan inba haka ba yanzu zasuyi b'atacciya ,.......




Fahad shida Maryam tuni suka shedawa Hajiya Nafeesa maganar Diyana , Hajiya Nafeesa tashiga zage zage " nifah wallahi tuntuni na tsani yarinyar nan dama , kowanne aiki intayiwa Sanam ita take rusashi , lallai lokaci yayi da zatayi maganin ta dan wannan karon a shirye take da tayi komai dan burin ta ya cika , take ta shiga shirya yadda zata yi maganin Diyana ta shirin Had'ata fad'a da Sanam.....




Har suka baro wajen Shopping Sanam na ruwan jaraba , babu abinda yafi tsaya mata arai sama da maganar da yace Daddyn ta da nasa sunyi , yaushe wannan abun yafaru batasani ba ? dama taga take taken Mumy bason Huneed take ba , tasan tunda Jaydeen ya kasance d'an gidan k'awar ta dole zata bi duk yadda za'ayi ta cusa mata shi , itakuma wallahi ko ba'abata Huneed ba babu abinda zatayi da Jaydeen , ko maza sun k'are a duniya da ta xauna dashi wanda ta mutu babu aure , Diyana dai babu bakin magana , dan tamkar Sanam zatayi aljanu haka tashiga yi tana zage zage , addu'a Diyana tashiga yi akan Allah yakaisu gida lafiya dan yadda take tuk'in motar ma tashin hankaline , a haka Allah yakawosu gida lafiya tashiga dannan Hon. me rikitar wa , me gadi tamkar zai kifa haka yayi sauri ya nufi gate d'in yana bud'ewa , yana gama bud'ewa motar tana danno kai da mugun gudu cikin gidan , wani uban tsalle me gadi yayi dan karta take masa k'afa , bin motar yayi da kallo ya tabbatar da lallai yau antab'o 'Yar gwal , tana fita daga motar ta nufi cikin gida kai tsaye tana k'walawa Hajiya Nafeesa kira " Mumy Mumy kina ina inason magana dake , da Hajiya Nafeesa da Fahad da Maryam duk mik'ewa sukayi jikin su na rawa jin irin kiran da Sanam kewa Hajiya Nafeesar , tuni suka shiga jin tsoron kodai Diyana ta je ta nemo labarin abinda yakawo Maryam cikin gidan ? In kuwa hakane to tabbas sai tayi magani Diyana a yau basai gobe ba , Sanam tana shigowa palor tabi su da kallo sannan tace " Mumy inaso kijawa wannan 'Dan gidan k'awartaki kunne wallahi yafita daga sabga ta tunkafin insa ayimin maganin sa , wata ajiyar zuciya Hajiya Nafeesa tasaki tare da hamdala a zuci , Cike da kissa da nuna kulawa tace " wanne d'an k'awar tawa kenan ? Sanam tace " wannan kalar 'Yan daudun dan banason sa ko kad'an ya fita daga sabga ta , tana gama fad'ar haka ta haye sama tabarsu baki bud'e , Hajiya Nafeesa taja tsaki sannan tace" aikin banza kalar d'an daudun kuma shine mijin ki , dan duk yadda zanyi yazama mijinki sainayi banza wawiya , Fahad yasa murmushi yana kallon Hajiya Nafeesar sannan yace "Aunty ai batasan kinayiba dama binta kikayi kika fad'a mata , wata harara ta galla masa sannan sukasa dariya su dukan su , dai dai lokacin Diyana tashigo cikin palor idanun ta akan su , aikuwa su duka suka canza fuska tamkar basu suke wannan dariyar ba , Diyana ta kalli Mumy ta rissina tana fad'in " barka da yamma Mumy , Hajiya Nafeesa tayi tsaki sannan tace " barka shugabar munafukai , Diyana tamkar bataji ba tashige abinta batare da tabi takansu ba , ....


Hajiya Nafeesa tace " inaso asan yadda za'ayi a had'a Sanam fad'a da wannan shegiyar yarinyar , Maryam tace " wannan shirin kibarmin shi a hannuna dan nafi kowa son naga sunyi fad'an da baza ta kuma takowa gidan nan ba , kawai inason inga saurayin da Sanam tafi so dan ta dalilinsa zamu saka su yin fad'a , nan suka saka wata shewar murna dan shima shegen dama so suke yadaina zuwa , dan tun sanda yakawo mata malamin dazai dunga koya mata karatun Hajiya Nafeesa takuma tsanar sa , kuma sosai taga canji yanzu a tare da Sanam , komai inzatayi yanzu tadaina gaya mata sab'anin da , tabbas zataso ace sun rabu dan komai zai fi mata sauk'i........








*Kumin Afuwa Zazzab'i nadamunaπŸ˜”πŸ˜•*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈπŸ€¦πŸ»β€β™€οΈ




*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*πŸ“š
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/










*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 35.




Koda Diyana ta hau sama ta samu Sanam cike da nutsuwa tace " dan Allah Besty kirage saurin zuciya , wannan halayyar bata dace dake ba , Sai sannan Sanam ta sai ta kanta tafara magana "Diyana inason Huneed fiye da tunanin ki banason duk abinda zai zame mana barazana a cikin soyayyar mu , kinajin abinda Guy d'in nan yafad'a wai Daddyna danasa sunyi magana , duk da nasan Daddyna bazai tab'amin auren dole ba , amman naga kamar Mummy tafison wannan Jaydeen d'in akan Huneed , Diyana ta mik'e ta k'arasa kusa da Sanam sosai tace " ki kwantar da Hankalin ki Besty tunda har kinsan Daddyn ki bazai aura miki wanda bakyaso ba , kawai dai shawarar da zan baki shine kiyi magana da Huneed akan yasami Daddyn ki da maganar auren ki , Sosai Sanam taji dad'in abinda Diyana tace mata , dama Huneed tuntuni yake damun ta da Maganar yanaso yaturo , itace take ce masa yabari tayi nisa a karatu sai ya turo ayi magana , amman tunda abun yana neman zame mata tashin hankali dole tayi masa magana, da haka suka shiga hirar su wacce duk rabi akan soyayyar ta da Huneed ne......


*Washe gari*
Tunda Sanam ta tashi take shirin tarar Huneed , bawani girki ta iya ba bare tace zata shiga kitchen da kanta tayi masa , sai dai kawai tasa angyara d'akin saukar bak'i sannan aka turaresa da turaruka masu dad'in k'amshi , shiga kitchen tayi tasamu me yi musu aiki tace tana so tayi mata girki na musamman tana da bak'o , Alawiya cike da girmamawa tace " ranki ya dad'e me da me kike so a dafa masa ? Sanam tayi shuru na wasu Mintyna tana nazarin me Huneed yafiso , can ta tuna wani lokaci suna hira yake tambayar ta wai ta iya Dambun Shinkafa yaji gyada da zogale , a lokacin tayi wani murmushi tace masa ta iya indai so yake , nan ta kalli Alawiyya tace inaso kimin Dambun shinkafa yaji zogale da gyad'a , sannan sai kiyi min farfesun Kayan ciki , ki d'ebi naman kaji ki soya sai ki yi masa kunun Aya , Alawiya cike da girma mawa tace " angama ranki ya dad'e Sanam ta fita daga kitchen ta nufi d'akin ta.....




Tunda Huneed ya sauka a Abuja yakejin sa cikin wani farin ciki , Hisham ne ya d'aukosa a mota sai hira suke abin su , suna k'arasowa gida Hajiyar su ta taresa cike da farin ciki da so da k'auna , 'Dakin sa ya nufa dan yarage kayan jikin sa yayi wanka , yana fitowa kiran wayar Sanam na shigowa wayar sa , Murmushi yayi sannn ya d'aga yana fad'in " My Wifey sai yanzu kika tuna da mijin naki ? Murmushi Sanam tayi sannan tace " dama koda yaushe ina tunanin sa araina , ina fatan My Husbee na ya dawo lafiya ? Huneed yace " waye yafad'a miki nadawo ? Murmushi tayi sannan tace " a jikina naji cewar Masoyina yana kusa dani , sannan in nasaita Nunfashina tasaitin gidan ku inajin bugun zuciya ta yana k'ara yin yawa , hakan ya tabbatar mun da cewa Sojana yana cikin garin Abuja , Wani dad'ine yakama Huneed yayi murmushi yana lumshe idanu sannan cikin wata kasalalliyar Murya yace " tabbas Matata batayi k'arya ba , yanzu haka ina cikin gidan mu a d'akin ina shirin tahowa inga Matata , Sanam tamkar tayi tsalle saboda murna kawai murmushi take baki yak'i rufuwa , ahaka wayar ta katse tuni tafad'a toilet danyin wanka.....




K'arfe biyar dai dai Huneed ya iso gidan su Sanam , tunda yashigo masu aikin gidan suke girmama shi , indai Huneed yazo to suma ranar sai sunsamu rabon su , dan hannuwan sa a bud'e yake akwai shi da kyauta , dan haka kowa keson zuwan sa kuma suke girma mashi ......
Sanam tuni ta shirya cikin wani Material me tsadar gaske , d'in riga da siket sun zauna a jikinta das , sabon takalmi kalar jikin adon less d'in tasa tasa kuma mayafi kalar takalmin , fad'in irin kyan da Sanam tayi b'ata lokacine , inbanda K'amshi babu abinda ke tashi ajikinta , tuni Huneed ya sheda mata zuwan sa , nan tace masa ya shiga d'akin saukar bak'i gatanan zuwa.......


Sai da akayi kusan minty 5 sannan Sanam ta sakko cikin takunta na isa , tana gama sakkowa tasamu bakowa a palor sai Maryam , Maryam tana ganin Sanam ta zuba mata idanu , turaren da Sanam ta fesa Maryam na shak'ar sa taji Amai ya taso mata , da gudu ta nufi toilet d'in dake cikin palor tana kakarin Amai , Sanam tuni ranta yayi mugun b'aci me wannan 'Yar iskar take nufi da har zata hau Amai dan taganta ? kamar ta je gurin Maryam amman sai tafasa ta fita daga cikin palor , sai dai tabbas indai Huneed yatafi dole zata sameta taji dalilin ta nayi mata hakan , duk b'acin da ranta yayi tana tozali da Huneed taji duk yatafi , murmushi yakar mata itama ta maida masa da nata Murmushin , Huneed ji yayi kamar yatashi ya rungumeta amman yasan hakan bazai yuwu yanzu ba , zama tayi kusa dashi tana fad'in " sannu da zuwa My Sojana, Huneed ya rik'o Hannun ta yana fad'in " Matar Soja itama Sojan ce My Wifey irin wannan kyau haka ? tamkar an canzamin ke komai naki yakuma k'arayin kyau , nan yashiga yabon kyan datayi da fad'in dole yasiyi wannan kwalliya , wayar sa ya d'auko yashiga d'aukar ta pic , duk yadda ta motsa sai yayi mata kuma ko wanne yayi sai tayi kyau , sai da yagama yi mata sannan ya matso kusa da ita yayi musu tare batare da ta kulaba , tana gani tayi saurin rufe fuska tana murmushi , nan suka shiga hirar su wacce rabin ta akan yadda sukayi Missing d'in juna , anan Huneed yashiga shedawa Sanam anyi masa k'arin girma nan da kwana biyu za'ayi bikin karramashi , Murna Sanam tashiga yi tana godiya ga Allah , tuni ta bud'e masa Abincin datasa akayi masa tafara seving d'insa.....


Bayan Sallar Magriba Huneed yace ta tashi suje wata Unguwa su dawo , batare da musu ba ko tambayar inda zasu Sanam ta mik'e suka jera har jikin Motar , suna zuwa suka shiga sannan suka fice daga cikin gidan.....




Sun shagaltu da hira shiyasa Sanam bata fahimci inda suka nufa ba , sai da suka shiga cikin Estate d'in sannan tagane Gidan Mummyn Twins zasuje , kallon Huneed tayi yasakar mata murmushi sannan yace " Mummy tanason ganin kyakkyawar 'Yar ta , Sanam ta turo baki tana fad'in "Haka tace maka kenan kawai dai kanaso kadatsemin farin cikin danakeyi yau , tsayawa yayi dai dai k'ofar gate d'in gidan yana hon. Sannan yace mata " kintab'a ganin Uwar dazata datsewa 'Yar ta farin ciki ? Sanam ta yi shuru bata bashi amsa ba , kuma dai dai lokacin Megadin gidan ya bud'e musu gate , Huneed yace "to kidaina cewa haka dan duk wata Uwa da kike gani tafison Farin cikin 'Yayan ta fiye ma danata farin cikin , haka suka fito daga cikin Motar ya rik'o mata hannu suka nufi cikin Palor gidan .....


Koda shigar su wani k'amshin turaren wuta ne yadaki Hancin su , Sai kuma sukayi ido biyu da Hajiya Maimuna tana zaune tana bawa Twins d'in ta nono , sallama sukayi mata a tare Sanam tamkar wacce k'wai yafashewa a cikin ciki take tafiya har ta isa kan kujera ta zauna , shima Huneed xama yayi sannan yashiga gaida Mummyn cikin girmamawa , ga Mamakin Sanam sai taga Mummyn nata ta amsa masa cike da sakin fuska dakuma nuna so da k'auna , harji tayi tana tambayar sa ya Hajiyar sa da kuma Hisham , bayan ya amsa mata da duk lafiya suke sannan takumaji tace masa " ya hanya dafatan kadawo lafiya , ina tayaka murnar samun k'arin girman dakayi , Allah yatsareka yakuma kareka a duk inda kake , Sanam tamkar mutum mutumi tazama agun , dan abun yabata mamaki sosai cikin ranta tashiga tambayar " Yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login