Showing 33001 words to 36000 words out of 78990 words
yadda sukayi da Huneed , yace " nifa yaron sosai ya burgeni dan har na aminta dashi , yanzu kawai sonke Inji ta bakin Shalele in ta amince dashi shikenan , Hajiya Nafeesa ta tab'e baki sannan tace " nikuma Alhaji sai nake ganin kamar kayi saurin yadda dashi , yana da kyau dai kayi bincike akansa sosai dan tabbatar da waye shi , sannan kana ganin Sanam ta dace da ta auri Soja ? gaskiya ni ba irin mijin da nakeso Sanam ta aura bane wannan , Murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " kufa mata akwai ku da san burga , amman fisabilillah ina aibun Soja ? kuma abin burgewa yaron yana kasuwanci sosai to meye laifinsa ? inaso ki sameta kuyi magana mutuk'ar yayi mata shikenan dan nima ya yimin , kuma gashi d'an gidan manyan mutane ko iya nan nasan Sanam tayi mijin da yadace , in kuma itama ra'ayin naki gareta to babu takura Allah yabata wanda zaiyi dai dai da ita , yana gama magana ya shiga toilet d'in dake cikin d'akin.....
Hajiya Nafeesa ta bi bayansa da harara tana fad'in " zaka canza ne dan wannan komawar da zanyi gun boka har da zancen shegen saurayin nata zanje , dan kwata kwata ni baiyimin ba ko kad'an kuma bazai tab'a yimin ba , take ta fice daga d'akin tana kiran number Hajiya Harira......
Sanam tana shiga d'aki tafad'a kan gado tana murmushi , ledar da aka kawo mata ta shiga bud'ewa , wasu manyan turaruka tagani masu tsadar gaske kala kala , sai wani Hankici me kyan gaske da hoton heart a jikin sa sai k'amshi yake , tana duba wata leda daban kuma taga su chocolate kala kala masu tsadar gaske , murmushi tayi tana fad'in tamkar kasan inason chocolate , sai wata Ambulance k'arama data gani ajikinta wata tak'arda an rubuta " _ina sonki da dukkan zuciyata Sanam_ tana bud'ewa taga bandir d'in dubu dari sannan ankuma rubuta " _Gashinan babu yawa ko sweet kinsha_ wani murmushi ta kuma yi tana jin dad'i , tunda take babu wani mahaluk'in daya tab'a bata kyautar kud'i , saboda yadda matsayin ta yake amman yau gashi Huneed yabata , duk da yasan matsayin ta da kuma irin dukiyar mahaifin ta amman baisa ya karaya ba yayi mata kyauta , tabbas wannan Huneed d'in nata nadaban ne , kuma taji dad'in yadda yayi mata hakan ko ba komai ya nuna mata irin k'aunar daya kemata , kwanciya tayi tana duba wannan takardar me rubutu tana ta maimaita kalmar " inasonki da dukkan Zuciyata Sanam.....
Huneed yana k'ara sawa gida ana sallar magariba , arwala yayi sannan ya wuce masallaci , tunda yashiga cikin masallaci bai fito ba sai bayan sallar isha'i , mutuk'ar Huneed yana gari to indai yashiga masallaci baya fitowa saiyayi tilawar k'ur'ani tare da azkar yake fitowa , gida yashiga kai tsaye ya nufi falor Hajiyar su , yana zuwa yasameta ita da Hisham suna hirar su gwanin sha'awa , dan Hajiyar su mace ce ita me janyo 'Ya'yan ta jikin ta , shiyasa sukuma suka maida ta abokiyar shawar su tare da fad'a mata duk wata damuwar su , yana shigowa ya k'araso gunta ya zauna yana fad'in " sannu da gida Hajiyata , murmushi tayi tana fad'in " sannu da dawowa Huneedullah dafatan kabaro sirikar tawa lafiya ? Murmushi yayi sannan yace " nabarota lafiya Hajiya har tace ingaidake kafin tazo , Hisham yafara murmushi yana fad'in " au kace zance kaje shiyasa naganka kayi guyu sosai tamkar sabon ango , dukan su suka sa dariya Huneed yana fad'in " Naje neman aure ne wacce zata zo ka runga ce mata Aunty , Hisham yasa dariya yace " zance mata Aunty indai zata dunga bani lafiyayyan Abinci , Hajiya tayi dariya tana fad'in " yauwa kaji acici ko baisan komai ba sai ci , nikam naga randa zaka rage wannnan cin Abincin naka Hisham, Hisham yace " aikuwa sai sai in k'ara Hajiya tunda gashi zamu samu kuku , kinsan 'Yan matan zamanin nan akwai iya girki kala kala , dariya suka kuma sakawa baki d'aya Hajiya na fad'in " kai tafican matan zamanin da duk basu iya girkin gargajiya ba sai nasu na iyayi , Huneed yace " ko bata iya ba Hajiya ai sai ki nuna mata kinga kema kin huta shiga kitchen , murmushi tayi sannan tace " baza ayi haka dani ba kuwa , yarinya daga zuwan ta ace tana aikin girki ai sai ta gaji baruwana , yanzu dai gayamin yadda kukayi da ita , nan Huneed yashiga bawa Hajiya da Hisham labarin yadda sukayi da Alhaji Abba da kuma ita kanta Sanam d'in .........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 24.
Sosai Hajiya taji dad'in yadda Huneed ya sheda mata Baban Yarinyar ya amince masa , nan tayi masa addu'ar samun nassara tare da daidai tawa da Sanam d'in .......
Sanam na zaune a kan gadon ta rik'e da wannan takadda , sai murmushi take tare da d'aukar chocolate tana sakawa abakin ta , wayar tace tashiga ruri da sauri ta d'auka tana duba screen d'in wayar , number Diyana tagani da sauri ta d'aga tana fad'in " kina ina k'awata yau anzo har gida wajena zance , wai dama zanga wannan ranar ace ga wani yayi zarrar zuwa wajena da sunan yana sona ? Diyana tayi murmushi sannan tace " Besty ai kece kike tsare gida dayawa , amman kinsan ko a sch kina da tarin masoya 'Ya'yan Manya wanda suka amsa sunan su a Nageria , amman kallo ma basu isheki ba saboda halinki , lallai ko waye wannan ya cika me sa'a dakuma zarrah kuma lallai shid'in Sadaukine a cikin maza , Sanam tayi murmushin jin dad'in yadda Diyana ke kuranta Huneed , duk da itama ta yadda da lallai Huneed jarumine ko acikin mazan , a hankali ta furta " tabbas Jarumine sosai Diyana , kuma yayi Nasara a cikin zuciyata , dan tuni zuciya ta takamu da san shi tuntuni , Diyana ta k'yalk'yale da dariya tana fad'in " gaskiya da zangan sa a daren nan dana sheda masa cewa ya k'arawa malamin sa kud'i , dan wannan tsayuwar da yayi masa ta dare yayi amfani , dariya sosai Sanam take tana fad'in " wato dan kinji cikina shine zaki tsokaneni ko ? to ai ban sheda masa ina son nashi ba dan haka har yanzu zuciyar sa acikin zulumi take , Diyana tace " ai aikin gama ya ruga da yagama tunda har yayi nasarar shiga zuciyarki ai ya wuce gun , sosai suka sha hirar su wacce rabi duk labarin Huneed Sanam ke bawa Diyana , a k'arshe sukayi sallama akan zasu had'u gobe a garden wajen hutawa dan sake tattauna wa .........
Jaydeen sosai yasawa Mumyn sa rigimar sai an nemo masa gidan su Sanam , Hajiya Halima tace " to yanzu My son a wanne estete take da zan tafi nemo maka ? shuru yayi na wasu lokacin kafin yace " tana Estate d'in Area 11 kamar haka naji Direban daya zo d'aukar ta ya fad'a , Hajiya Halima tayi murmushi sannan tace " to ka kwantar da hankalin ka zuwa safiya sai mu shirya muje Area 11 d'in muduba cikin Estate d'in nasu , Jaydeen ba haka yaso ba so yayi ace a daren nan Mumyn nasa taje ta dubo masa gidan su Sanam , dan ko sunan ta ma bai rik'e ba sai dai zanen surar ta dayafi komai tafiya da hankalin sa har yatsaya masa aransa ,.......
Washe gari sai wajen Sha d'aya Sanam ta tashi daga bacci , dama batayi baccin gajiya ba shiyasa bata tashi da wuri ba , abinka da wacce ibada bata dama ba , tana mik'ewa tashiga toilet tayo wanka abinta tare dayin brush , tana fitowa ta zauna gaban Mirror tana shafa mayukan ta masu tsadar gaske , sannan ta d'auko Humra masu k'amshi tabi jikin nata dasu , take tafara wani lafiyayen k'amshi tamkar amarya , Kwata kwata kwalliya ba damun Sanam tayi ba , kwalli kawai tasa a idon ta sannan ta shafa lips stick a abakin ta , take tayi wani kyau na daban tamkar kasace ta , tabbas duk Namijin da yayi tozali da Sanam dole zuciyar sa ta harba , wani kyau gareta me d'aukar hankali , ribom ta d'auko tashiga tattaro gashin kanta me uban yawa wanda baya kitsuwa , tana saka ribom d'in ya zubo gadon bayan ta tamkar a indian film , bud'e wajen kayan ta tayi ta d'auko wasu riga da wando sababbi masu kyan gaske , rufewa tayi sannan ta d'auko turarukan da Huneed ya kawo mata tashiga fesawa a cikin kayan , tana saka kayan tasake yin wani kyau tamkar kasace ta , rigar ta tsaya mata iya cinya me k'aramin hannu , shikuma wandon tamkar fela haka k'asan sa ya bud'e tare da wasu duwatsuna masu kyan gaske , mayafin kayan ta yafa d'an k'arami ta rufe kanta sannan tasa filet d'in takalmi tafito daga d'akin tayo k'asa.......
Jaydeen tuni ya shirya yasa Mumyn sa a gaba sun nufo Area 11 , dayake unguwa ce ta masu dashi kuma bawani yawa gidajen ciki suke dashi ba tuni me gadin cikin Estate d'in yagane wacce yake nufi , take ya sheda musu number gidan , wasu mahaukatan kud'i Jaydeen ya d'iba yabawa me gadin tare da yi masa godiya , har k'asa ya durkusa ya ansa yana musu godiya suka wuce ciki .....
Sanam na saukowa ta nufi dinning don karyawa , tana zuwa me aikin su tayi saurin had'a mata tea tana rissinawa tana fad'in " ranki ya dad'e barka da fitowa tafatan antashi lafiya , Sanam batare da ta dube ta ba tace " lafiya taci gaba da danna wayar ta , sak'on Huneed ne ya shigo wayar ai take tafara murmushi , Uwani ta rissina tana fad'in " ranki ya dad'e me zan had'a miki a cikin kayan karin ? Sanam tace " jeki kawai zan had'a da kaina ta fara duba sak'on , kowanne sak'o na soyayya ne masu dad'in karantawa , nan Sanam ta shagalce wajen karan ta sak'on Huneed tare da maimai tasu , .......
Tunda ga k'ofar gate Hajiya Halima tasan lallai ba k'aramin me kud'i bane me gidan , hon sukayi me gadi ya lek'o dan ganin waye , ganin bai dan motar ba yasa ya fito ya k'arasa wajen su , gaisawa sukayi sannan suka sheda masa su bak'ine sunzo gun matar gidan , megadi yace " to Hajiyar tasan da zuwanku ? Hajiya Halima ta yi murmusjo sannan tace " batasan da zuwan mu ba amman kaje ka sheda mata matar Ambasador ce tazo gunta , da sauri Mehadin yace to bari naje nadawo , komawa tayi ciki dan shedawa Hajiya Nafeesa zuwan su , koda yashiga yasamu Sanam sai wayar ta take sha abinta hankali kwance , sallamar ma batasan yanayi ba , har Hajiya Nafeesa ta sauko daga sama ta amsa masa ya sheda mata bak'in datayi , izini ta bashi akan yabarsu su shigo....
Hajiya Halima suna shigowa ciki ta k'ara tabbatar da irin gidan da take so d'an ta ya nemo aure , murmushi tayi tana kallon Jaydeen wanda shima ita yake kallo yana murmushin , K'ofar palor suka tura dai dai lokacin Sanam ta mik'e zata koma sama dan wayar tasu da Huneed ta yawaita , taga kuma kamar Hajiya bak'i tayi ita kuma batason duk abinda zai shigar musu rayuwa , karo taci da Jaydeen tatafi zata fad'i k'asa yayi saurin taro ta jikin sa , a hankali ta bud'e ido suka had'a idanuwa da Jaydeen , wata fad'uwar gaba ce ta ziyarci Sanam cikin ranta ta furta wannan lokacin ma , to meya shigo dashi gidan mu har muka kuma karo haka ? suntafi tunani su dukan su sun manta a inah ma suke sukaji gyaran muryar Hajiya Halima , Da sauri Sanam ta turesa tana mejin kunya , sannan tayi saurin hayewa sama abinta...........
[9/27, 09:59] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir* *Rahim*
Chapter 25.
Jaydeen yayi murmushi tare da binta da kallo har ta haye saman , juyowa yayi ya kalli Mumyn sa sukayi murmushi tare , dai dai lokacin Hajiya Nafeesa ta sauko daga sama cikin shiga ta Alfarma sai zabga k'amshi take , tana ganin Hajiya Halima tasaki murmushi tana fad'in " lale marhabun da manya manya , Hajiya Halima itama tagane Hajiya Nafeesa dan sun tab'a had'uwa so biyu , d'aya a wajen Wankin kai d'aya kuma a Dinner bikin 'yar gidan Hajiya Turai , dan har sunyi musayar contac kafin asace phone din Hajiya Halimar , nan suka gaisa cike da sakin fuska tare da tambayar bayan saduwa , nan danan Hajiya Nafeesa tasa aka kawo musu abin motsa baki , hira suka shigayi sosai shikuwa Jaydeen duk hankalin sa na wajen Sanam , Allah Allah yake yaga takuma fitowa dan yanason yasake ganin ta da wannan shigar , Hajiya Halima ta dubi Hajiya Nafeesa tace " to mufa da magana mukazo akan yaron naki , murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " to meke tafe daku dan tunda kuka shigo naga yakasa sakin jiki , Hajiya Halima tace " dama yarinyar wajen ki yagani sunhad'u a jirgi tun daga Turkey , tunda yadawo bashi da zance sai nata yau dai nasashi a gaba muka fito neman ta , to Allah yasa muka samu gidan ashe ma yar wajen kice , Hajiya Nafeesa tayi murmushi sannan tace " tabbas Sanam ce dan itace taje Turkey , lallai abu yayi kyau to Allah ya tabbatar mana da Alkairi , cike da fara'a Hajiya Halima ta amsa da Ameen , sannan tace " amman ina fatan ba'ayi mata mijiba dan karmuyi nema cikin nema , dariya Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " bakuyi ba dan bata kula kowa saboda karatu takeyi , wani dad'i Jaydeen yaji aransa jin ance bata kula kowa nan ya k'udurta aransa zaiyi yadda zaiyi ganin tazama tashi shi kad'ai , sakkowar Sanam daga sama yasa Jaydeen katse tunanin sa yq zuba mata sex eyes d'in sa , wasu kayan yakuma gganin ta dasu wanda sukaci uwar na d'azu kyau da tsaruwa , gashi sun kama mata jikin ta komai nata ya baiyana , jiyayi tamkar yatashi yatafi da gudu ya d'auketa cak yadunga zagayawa da ita , ko kallon inda suke Sanam batayi ba tanufi hanyar fita daga falor , da sauri Hajiya Nafeesa tace " My luv zo mana , Sanam ta tsaya cak tamkar baza ta zo ba sai kuma ta jiyo ta tako a hankali , tana k'arasowa ta tsaya tana turo baki tare da cewa " Gani Mumy sauri nake zamu fita nida Diyana , Hajiya Nafeesa tace " baki ga munyi bak'i bane zaki fita ko gaisawa bakuyi ba , Sanam ta d'an turo baki tare da kallon b'angaren da Hajiya Halima suke tace " sannu n ku anyini lafiya , Hajiya Halima cike da sakin fuska tace " lafiya lau My Dauther , Sanam bata sake bi takan su ba tayi sauri juyawa ta fice Abinta , Jaydeen tuni yatashi yabi bayan ta dan yana son suyi magana.....
Hajiya Halima da Hajiya Nafeesa sukayi murmushi ganin yabita , Hajiya Halima taja ajiyar zuciya tace " Allah ya dai dai tasu dai , Hajiya Nafeesa ta amsa da Ameen , suka ci gaba da hirar su irin tasu ta manyan mata......
Sanam na fitowa tuni dama tasa an wanke mata motar , tana fitowa ta nufi wajen motar zata shiga , da sauri Jaydeen yasha gaban ta yana