Showing 69001 words to 72000 words out of 78990 words

Chapter 24 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3678

Wanda yake cikin motar , take hanjin cikinta ya hautsina wani zawo ya taho Mata babu shiri.......,.....









_Masoyana littafin_ *NI KO ITA* _haryanzu yana jiranku Kar ku Bari abaku labari , kuyi gaggauwar siyan naku akan farashi k'alilan_, 200


Duk meso yayi magana a wannan Number : 09137064556
[9/27, 14:28] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈπŸ€¦πŸ»β€β™€οΈ








*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*πŸ“š
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/








*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 45.



Da sauri tafara k'ok'arin bud'e motar ta fice , wata Uwar tsawa Huneed ya daka Mata tuni Maryam tasaki fitsarin dake matse jikinta , Huneed yaja motar da wani matsiyacin gudu yabar cikin unguwar , ...


Gidan da Huneed ya tab'a Kai Sanam farkon had'uwar su lokacin da take rashin jin ta Nan yakai Maryam, Yana zuwa ya kashe motar ya fito tare da zagayawa inda Maryam take ya bud'e murfin motar tare da fincikota , Maryam sai kuka take tana cewa " kayi hak'uri Dan Allah wallahi nadaina , Huneed ya bud'e gidan Yana rik'e da Hannun ta ko kallon ta yak'i yi saboda tsanar ta dayayi , Yana zuwa ya jefar da ita a k'asa sannan ya zare belt d'in jikinsa yafara dukanta , Maryam ihu take tana fad'in " kayi min Rai Dan Allah ka yafemin , Huneed ya tsaya da dukanta ya durk'uso wajen fuskar yace " inaso kifad'amin waye yasa ki shiga tsakanina da Sanam ? Maryam ganin irin dukan da tasha a Hannun Huneed gashi daga ganin sa har kisa zai iya yi , batare da ta wahalar da kanta ba tace " Hajiya Nafeesa itace tasani wallahi , Huneed ya tsaya Yana kallon Maryam sannan yace " ke meye had'in ki da Hajiya Nafeesar ? Shuru Maryam tayi batare da tace dashi uffan ba , aikuwa ya d'auko belt ya Fara Shirin zabga Mata dasauri tace " wallahi bani da had'i da ita kawai dai ni budurwar k'anin tane , Huneed ya mik'e yace " hakan yayi yanzu zanbarki anan dasafe zanzo dole ki fad'amin irin Shirin da kukeyi akan mu , Yana Gama fad'a Mata hakan ya fito tare da janyo k'ofar ya rufe , yanajin Maryam na kuka tana bashi hak'uri Amman ko waiwayen ta bai yiba ,


Yana fitowa ya shiga motar ya kunnah yabar unguwar , ring d'in waya yaji Yana tashi Nan ya kalli kujerar da Maryam ta zauna , jakarta yagani kuma ring d'in daga ciki yake fitowa , tsayawa yayi ya bud'e jakar ya d'auko wayar , lokacin wani Kiran ya kuma shigowa , number da aka kirata dashi ansa My Fahad , tuni Huneed yagane Fahad ne Dan haka yak'i d'agawa har ta katse, kashe wayar yayi baki d'aya yayi jifa da ita yahau titi ya nufi gida....


Sanam d'aki guda Mummy ta ware Mata Nan ta zuba kayanta a wordrup d'in d'akin , tana kwance tana tunanin yadda zata je tabawa Diyana hak'uri sai ga Kiran Huneed , da sauri ta d'aga tana fad'in " My Sojana barka da wannan lokacin , Huneed ya lumshe idanu tare da cewa " barka kadai My Wifey ya Daren ya su Mummy da Twins d'ina ?Sanam tace " lafiyar su k'alau sai dai muna kewar ka nida su Twins ,
Huneed yace " badan dare yayi ba Dana dawo Nima Dan nakuma tozali da kyawawan 'Ya'yan Mummy , Murmushi Sanam tayi sannan tace " ya kukayi da shegiyar yarinyar Nan ? Huneed yace " da safe ki shirya zanzo na tafi dake wajen da na ajiye ta , a yadda na Fahimta ba iya wannan ne shirinsu ba akwai wani abun a k'asa.
Sanam tace " kamar me kenan ? Huneed yace " a yanzu bazan ce Miki ga Shirin su ba sai dai a gobe inaso inyi Mata abinda komai sai ta fad'a Mana , Amman ta sheda min cewa ita ba 'yar Uwar su Hajiya Nafeesa bace , Ni a yadda na Fahimta ma a unguwar su Diyana k'awarki take , take Sanam ta tuno da ranar da zasu fita ita da Diyana sunfito sukayi karo da Maryam , Nan Diyana tashiga tambayar Sanam meye had'in su da Maryam , Ashe Ashe maganar da Diyana tafara Gaya Mata akan Maryam d'in gaskiyane , Huneed ya katse Mata shurun ta da cewa " Ya kikayi shuru ne ko akwai abinda kike tunani ? Sanam tace " ea akwai Nan tashiga sheda Masa farkon had'uwar su da Maryam ita da Diyana , Huneed yace " gud dole gobe mutaho da Diyana Dan itama inason tambayar ta wasu abubuwan , Sanam tace " kana ganin Diyana zata zo kuwa ? Huneed yace " zatazo Amman sai kinje gareta kin Bata hak'uri sannan , Sanam tace " inhar zan Bata hak'uri ta hak'ura me zai Hana zanje kuma itama dole tamin uzuri , nayi Mata komai ne bisa rashin sani kuma ko itace a irin matakin Dana samu kaina zatayi irin hakan,. Huneed yace " gaskiyane Matar Soja Ashe dai ana kishin Sojan Nan haka , dariya Sanam tasa sukayi sallama akan anjima zai Kira inya yi Shirin bacci , Nan sukayi musayar kalaman soyayya sannan kowanne yakashe waya cike da begen junan su .....






*Washe gari*


Wajen k'arfe goma na safe Huneed ya dira a gidan Mummy twins , tare dashi suka yi break fast suna hira , anan Huneed ya shedawa Mummy duk yadda sukayi da Maryam , Nan Mummy ta jinjina lamarin Hajiya Nafeesa , sai dai batayi mamaki abinda Hajiya Nafeesa tayi ba Dan tafi gaban hakan , Bayan sun kammala Break fast Sanam ta mik'e Dan ta d'auko mayafinta , tana fitowa suka yiwa Mummy sallama suka fita......


Unguwar su Diyana suka nufa Sanam duk kunya ta kamata, sai tunanin yadda zata shiga gidan su Diyana ta had'a idanu da Umman Diyana , suna tsayawa a k'ofar gidan Diyana na fitowa zata tafi sch , Nan Sanam ta tuna itama tana da lucture Amman sai Sha biyu , kwata kwata Diyana Bata lura da Motar Huneed ba , da sauri Huneed ya fito Yana fad'in " barka da safiya Diyana , tsayawa tayi cak tana kallon sa cikin zuciyar ta tana tunanin me yakawo shi wajen ta , ko shima yazo ya ci Mata mutuncin ne kamar yadda budurwar sa tayi Mata , Bata gama tunani ba sai ga Sanam ta fito itama daga cikin motar , Diyana d'auke kanta tayi tana k'ok'arin ci gaba da tafiya , da sauri Sanam tasha gaban ta tana me rik'e jakar dake hannun Diyana .........




*Plss kumin afuwa*


*Wlh yau Ina fama da ciwon kai*😒😒😒😒
[9/27, 14:28] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈπŸ€¦πŸ»β€β™€οΈ






*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*πŸ“š
( Domin Marubuta Mata )
✨ ( W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/








*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 46.



Diyana tasakar Mata jakar tana k'ok'arin wuceta tabar gun , Sanam tayi saurin k'ara Shan gaban Diyana tana cewa " plss My bestyna kitsaya ki saurareni , Nan Diyana ta tsaya cak tana duban Sanam , Sanam batace komai ba kawai videon dake wayar ta ta kunnawa Diyana tana cewa " Dan Allah ki kalli wannan video sai ki fahimcine , Diyana ta rik'e wayar tana kallon video take idanun ta sukayo waje , a hankali tashiga furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un , da sauri ta kalli wajen da Huneed yake tsaye sannan ta kalli Sanam tace " wallahi bansan sanda wannan Abun yafaru ba besty , Nan Huneed yadubi Diyana yashiga bata labarin duk abinda yafaru , Diyana a mugun fusace ta nufi wajen Isma'il me kanti , Huneed ya dakatar da ita yace " ki k'yalesa Nan da kwana biyu zansa azo akamasa , yanzu in kika Masa maganar zai iya guduwa Dan Kar muka Masa , Diyana sosai ranta ya b'aci da irin abinda Isma'il yayi Mata , wato mutum dai ba abin yarda bane , duk yadda take mutunci da Isma'il Ashe za a iya had'a baki da shi Dan acutar da ita , Nan Sanam ta dafa kafad'ar ta tace " Besty Kinga abinda nagani idanuwana suka rufe har nakasa jurewa sai Dana zo gareki nayi Miki wannan Abun , inaso kiyimin afuwa da abinda nayi Miki Dan nasan ko kece kika ga irin hakan matakin da Zaki d'auka kenan , Diyana ta juyo tana kallon Sanam cike da so da k'auna irin na K'awayen asali , take ta rungumeta tana saka kuka tare da cewa " wallahi ko d'aya banrik'e kiba kawai dama nasan had'amu akeson ayi , Sosai suka burge Huneed dan kana ganin su kasan suna k'aunar junan su da gaskiya , ....


Dukansu suka shiga motar suka nufi gidan da Huneed ya ajiye Maryam ,..


Tunda Huneed ya kaita gidan na yabaro ta Bata sake jin motsin kowa ba , ga uban sauro dake cizonta sai kuka take tana yiwa Huneed Allah ya isa , tunda take bata tab'a kwana a k'ask'ancen cen waje ba sai yau , tana zaune tana kuka tare da tarin tsoro da ya mamaye Mata zuciyar ta har bacci yayi gaba da ita , ....




Acan b'angaren Hajiya Nafeesa kuwa tun jiya suke Kiran wayar Maryam Amman akashe , Fahad yadubi Hajiya Nafeesa yace " Wai bata fad'amiki inda zataje bane ? Hajiya Nafeesa tace " Ina tafad'amin kuwa ni bansan ma bata gidan ba inbanda kagayamin ,. Fahad yace " to kodai gidan su ta tafi ? Kuma indai Maryam zataje gida ai tana sanar min , Hajiya Nafeesa ta tab'e baki sannan tace " wayasani ko zuwa tayi ta kwana da wani gardin , kasan halin ta dan wallahi wannan yarinyar kwata kwata batayi ba , kana ganin ta kasan tana da mugun son abin duniya , Fahad ya dubi Hajiya Nafeesa sannan ya tab'e baki yace " kema ai kina da son kud'i Aunty , tunda yarinyar nan tazo gidan nan baki tab'a Bata kud'in kashewa sai dai inzata Miki wani aikin , Kinga kuwa Dan taje ta kula maza a waje ai ba laifi tayi ba , Hajiya Nafeesa ta gallawa Fahad harara sannan tace " to angaya maka banki ce ni da zan dunga bata kud'i , duk irin hutawar datakeyi a gidan Nan bai yi Mata ba , taci abinci me kyau tasha lemuka masu tsada ta kwanta a waje me kyau to metake buk'ata sama da hakan ? Fahad ya kalleta shima cike da takaici yace " duk wannan abubuwan da kika lissafo ai kud'i Yana gaba dasu , Hajiya Nafeesa a fusace tacewa Fahad "bazan Bata kud'in ba kuyi yadda zakuyi dani , ta haye sama tana sababi tamkar zata kifa ....
Fahad haushine ya kamasa ya furta " kiyi kigama wallahi duk kud'in da kika tara saina k'wacesu ko ta halin k'ak'a , mace bata da aiki sai mugunta tana da kud'i Amman bazata Bari aciba , tsaki yaja yafice daga cikin gidan baki d'aya......




Maryam tana kwance kan tayes duk ta takure saboda sanyin da takeji , jitayi an bud'e k'ofar gidan alamar za'ashigo , dasauri ta mik'e tana kallon hanya aikuwa ido biyu tayi da Diyana da Sanam ,. Jitayi tamkar ta nutse dan shikenan tasan asirin ta ya tonu itakam , Diyana ta tab'e baki tace " banyi mamakin irin abinda kikayi ba dan komai akace zakiyi nasan Zaki aikata , Amman ba laifin kiba ne laifina ne Dana d'auki yadda nabawa Isma'il shikuma yasamu damar cin amanata , Sanam tana k'arasowa ta dubi Maryama kuma a dai dai lokacin Huneed yashigo , durk'usowa yayi Yana cewa Malama Maryam ga abin Kari nakawo Miki kici ki k'oshi sai kibamu bayani akan shirye shiryen da kukeyi keda uwar d'akin naki , take away ya ajiye Mata indomi'e ce aciki tare da ruwan shayi a leda , Maryam tabbas tana jin yunwa Dan da badan haka ba bazata iya cin komai ba a halin datake , Amman itama zataso tafad'awa Huneed duk shirin da Hajiya Nafeesa keyi akan Mahaifin Sanam , tunda itama Hajiya Nafeesar ai ba Amana gareta ba , Nan ta janyo take away tafara cin Abinci hannu baka hannu k'warya , ...


Tana kammalawa tasha ruwan tea sannan ta ajiye sauran data rage , Huneed ya dubeta yace " muna sauraranki kuma mutuk'ar kika b'oyemin gaskiya to tabbas zaki ji ajikin ki , Maryam cike da rawar Murya tace " Dan Allah in nafad'a muku gaskiya Dan Allah kasakeni intafi gida , Huneed yace " in har hakan zai yuwu mazai Hana muna jinki , Nan Maryam ta fara bawa su Sanam labari tundaga farkon had'uwar ta da Fahad har ya zo garin Abuja tare da kuma Kiran ta akan aikin da zatayiwa Hajiya Nafeesa , Maryam duk wani Shirin na Hajiya Nafeesa akan Sanam da Mahaifin ta sai data Gaya musu , sannan ta kuma Gaya musu k'udirin Hajiya Nafeesa nasan raba Sanam da Mahaifin ta har maganar da Marayam taji Hajiya Nafeesa nayi ita da k'awar ta akan kashe ita Maryam d'in sai data Gaya musu , Sanam tuni taji wata iriyar zufa na tsatstsafowa ta jikinta baki d'aya , dukan su bawanda bai girgiza dajin irin Shirin Hajiya Nafeesa ba , .......









πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *NI KO ITA* _littafine daya Sha bambam da sauran. Kudai kuyi saurin mallakar naku dan kashe k'wark'watar idanuwan ku ,. Anan zakuji yadda Uwa take tarayya da 'Danta na cikinta tamkar Miji da Mata , kudai Kar kubari yabarku kuyi saurin Mallakar naku akan Farashi 200 kacal_✍🏻
*Domin mallakar naku ku tuntub'i Marubuciyar akan wannan Number : 09137064556 sai najiku*🀝🀝😘




_Taku a ko yaushe_
*Zeee MD*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈπŸ€¦πŸ»β€β™€οΈ




*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*πŸ“š
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/










*Bisimillahir Rahamanir Rahim*







Chapter 47.




Sanam Hawaye ne yashiga zubowa a kuncin ta , Ashe duk irin yadda Mummy Nafeesa ke nuna Mata k'auna ba gaskiya bane ? Duk tana yin hakane Dan kawai ta shiga tsakanin ta da Daddyn ta , shiyasa kwana biyun Nan in takira Daddy a waya baya d'agawa , yanzu inta kirashi ma akashe ake cemata , kuma tanajin yauma da safe ya Kira Mummy twins , Diyana ce ta dafa kafad'ar Sanam tana cewa " Sorry Bestyna nasan da ciwo ace wacce ka d'auka a matsayin uwa itace zata maka hakan , Amman ki godewa Allah da yasa asirin ta ya tonu tunkafin ta kammala Shirin ta , Sanam cikin muryar kuka tace " me nayi Mata haka takeson shiga tsakanina da Mahaifina ? Duk wata soyayya na nuna wa Mummy Nafeesa , zan iya cewa nafison Mummy Nafeesa akan Mummyna data Haifeni , Daddy ba gatan da baya nuna Mata , kafin yayiwa Mummyn Twins Abu sau d'aya yayiwa Mummyn Nafeesa sau goma , Amman kiduba kiji irin abinda takeson aikata Masa , ta d'auki d'an shege a matsayin d'an da zata ce shine jininsa , lallai duniyar Nan abin tsoro ce , Huneed ya mik'e tare da cewa " ki share hawayen ki duk abinda ta shuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login