Showing 78001 words to 78990 words out of 78990 words

Chapter 27 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3681

,. Haka sukasha Dinner kala kala da Reception , nera tayi kuka Dan tsayawa fad'in irin kud'in da aka kashe da kuma kyan Ango da Amarya sukai b'ata baki ne , ....


An d'aura auren aranar lahadi a masallaci dake cikin unguwar Asokoro Abuja , daga Nan Sojoji suka shiryawa Ango da Amarya Babban Reception , anci ansha sannan Sojoji sukayi wasa da bindiga tare da gwangwajewa , ....


Diyana ma a Nan gidan su Sanam akayi komai nata kuma komai tare suke , yamma nayi aka kawo motocin d'aukar Amare , Nan Aka Kai Sanam da Diyana wajen Alhaji Abba yashiga yi musu nasiha me ratsa zuciya , Mummy itama shigowa tayi Nan itama tayi musu nata fad'an tare dayi musu fatan Zaman lafiya da mazajen su , Alhaji Abba ya d'auki mukullayen mota kowacce yabata kyauta , Nan aka fito dasu kowacce aka nufi gidan ta da ita.......




Gidan Sanam dake Unguwar Maitama yagaji da had'uwa , ga Uwar dukiya da ka narka Mata tamkar basa son kud'in ,


Bayan kowa ya watse sai Sanam a bakin gado tana kukan rabuwa da gida , Ango Huneed ne ya shigo cikin d'akin d'auke da Manyan ledoji a hannun sa , Yana zuwa ya bud'e fuskar Sanam Yana fad'in "My wifey wannan kukan ya isa haka Kar ki janyomin ciwon Kai , shagwab'e Masa tayi sannan tace " My Sojana nifah gaskiya komawa gida zanyi dan Ina missing d'in Twins , rungumota yayi jikinsa Yana fad'in " indai Twins ne Nima Ina missing d'insu Amman Wanda Zaki haifomin a wannan cikin naki , shafo cikin yayi Yana Murmushi Sanam ta ture hannunsa tana mejin kunya......


Wanka Huneed ya shiga bayan ya fito itama tashiga tare da d'auro arwala , Bayan sunyi sallah ya gabatar Mata da tambayoyi akan karatun addini tabashi amsar abinda tasani , ledojin da yashigo dasu ya bud'e musu suka Fara cin kajin da yashigo dasu , da k'yar Sanam taci Dan kawai iya su Madarorin kwali ta dunga Sha , suna kammalawa ya d'ebe sauran ya nufi cikin frize da su ....


Brush Sanam tayo sannan tasa wata rigar bacci tare da feshe jiki da turaruka masu k'amshi tabi lafiyar gado , Huneed shima dashi sai boxer da singlet ya nufo gadon ya kwanta , Nan zance ya canza salo Dan tuni Su Ango Huneed aka Lula duniyar da ba'atab'a zuwanta ba , sosai Huneed yayi mamakin samun Sanam a virgin d'inta , Dan ganin irin yadda ta taso idanuwa a bud'e ga tsantsar wayewa da rashin ji sayake tuni ta bayar da jikinta , sai yasamu sab'anin hakan , Dan haka ya shiga Samata albarka tamkar ya had'iyeta ......



*Bayan shekara d'aya*


Tuni su Sanam anzama Manyan Mata , wata irin soyayya suke itada mijin ta Huneed tamkar Laila da Majnun , kullum suna tare ko dama tuni yadaina zuwa ko Ina saboda yanzu yaxam Babba , Koda yaushe Yana tare da Matar sa musamman yanzu da take laulayin ciki .....


A can b'angaren Hajiya Nafeesa kuwa ansako su duk ta rame ta lalace saboda bak'ar wuyar da suka Sha , tun a cikin virson suka rabu da Hajiya Harira baram baram , Dan haka suna fitowa kowacce ta kama gabanta , Hajiya Nafeesa da k'yar tasamu kud'in motar da ta koma can garinsu meduguri , Koda ta koma tuni sun samu labarin komai akanta a wajen Fahad Wanda ya dad'e da komowa gida ,.


Tunda ta koma take fama da cutar tari , daga k'arshe aka gane ta kamu da tarin tv Dan haka 'yan uwa kowa ya gujeta , dama data na gidan Alhaji Abba bawani zumunci take ba ko ganin su ba zuwa takeyi ba bare ta tallafa ,shiyasa kowa ya gujeta da k'yar take samun abinci so d'aya a Rana ,........




Cikin Sanam Yana isa haihuwa ta haifi Santalelen yaron ta me kama da Babansa , ranar suna yaci sunanan Mahaifin Huneed suke Kiran da da Abeeh , sosai aka Sha hidima lokacin itama Diyana ta haifi yarinyar ta data saka Mata sunan Besty ta Sanam , suke ce Mata Uktee , Hajiya Maimuna tuni suka koma can k'asar Paris ita da Alhaji Abba da Twins , lokacin tana mak'ale da cikin ta k'arami Wanda keta tsokanar ta da cewa " 'Ya na haihuwa uwa nayi , ....


Zaman lafiya da kwanciyar Hankali tsakanin Sanam da Mijin ta Huneed sai abinda ya k'aru , Koda yaushe in suna zaune sai Huneed ya tsokani Sanam farkon Had'uwar su shida ita data fesa Masa ruwan tab'o , Nan zasuyi dariya yace " aini ruwan tab'o Yayimin Rana tunda ya mallakamin wacce ba kowanne namiji ne zai sameta ba sai me sa'a , Nan Sanam tayi Murmushi tace " Nima Ina godiya da samun gwarzon Namiji jajurtacce Wanda ko wacce mace take burun samu , Alhamdulillah Allah ya kuma tsaremin Kai mijina Abin k'auna ta Uban 'Yayana kuma My Sojana,.......






*Alhamdulillah*


*Anan nakawo k'arshen wannan littafin ina rok'on Allah kuskuren danayi a cikin sa ya yafeminπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ» Allah yasa ya amfani al'umma baki d'aya*




_Nagode sosai Masoyana da yadda kuka dunga bibiyataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° har nakawo k'arshen wannan labari_




✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 *Kubiyoni a sabon Book Dina me suna*
_Bazawara CE_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login