Showing 66001 words to 69000 words out of 78990 words
shagona ba ,. Huneed yayi murmushi yasa hannunsa cikin aljihi ya zato bandir d'in 'yan dubu dubu guda biyu dubu d'ari biyu kenan , da sauri Isma'il ya Kai dubansa kan kud'in Yana wani lashe harshe tamkar yaga abinci ,. Huneed Yana lura dashi sai yayi kamar baigansa ba yace " Bari natafi wajen wani tunda naga Kai baka buk'ata , dasauri Isma'il yace " Wallahi inaso Oga sai dai gaskiya inajin tsoron abinda zaije yadawo , Dan komai dayafaru a ranar da saka hannu na Amman bansan abinda akayi Mata ba , Huneed ya gyara zama Yana duban Isma'il yace " inaso kafad'amin gaskiyar komai da yafaru Babu abinda zaayi maka , Nan
Isma'il yabawa Huneed labarin yadda Maryam tazo tasamesa akan yasawa Diyana k'wayar bacci a lemo da kuma yadda yaga Maryam d'in tazo da wasu maza guda biyu , komai da Isma'il ke fad'i tuni Huneed ya nad'eshi a waya , daga Nan Huneed ya mik'e Masa sallama tare da ce Masa yabashi number Maryam d'in , Bayan yabashi Huneed ya gargad'i Isma'il akan karya kuskura ya shedawa Maryam zuwan sa , in kuma har yayi hakan to lallai zai hukuntashi , Isma'il yace " hakan ma bazata faruba Oga Nan yabashi kud'in da yayi masa alk'awari tare da barin gurin......
Sai wajen sha biyu sannan Sanam ta tashi tashiga wanka , Mummy nashiga d'akin taji alamar wanka take Nan ta bud'e wordrup ta d'auko mata d'aya daga cikin dogayen rigunan ta sababbi Wanda ko sawa Bata tab'ayi ba , ajiye Mata tayi akan gadon sannan ta had'a Mata da sabon Pant da breazia ta fita daga d'akin , Koda Sanam ta fito taga wannnan kayan abakin gado tasan Mummy ce ta ajiye Mata , Nan ta nufi kan mudubi Wanda ya cika da kayan shafa kala kala da kuma turaruka masu tsadar gaske ,. Nan tashafa Mai tasa kwalli sannan ta shafa kulacca da had'add'un Humra , rigar ta d'auko tasaka tamkar Dan ita aka siyo tayi Mata cif ajiki , gashi tayi Mata kyau sosai ta fesa turare sannan ta yafa d'ankwalin rigar ta fito daga cikin d'akin....
A falor k'asa tasamu Mummy da Twins sai wasan su suke , Tunda ta taho Mummy ta kafeta da ido lallai jininka jininka ne komai na Sanam irin natane lokacin data na budurwa ,. Sanam na k'arasowa tace " Mummy barka da Rana , Mummy Twins tace " sannu da fitowa , lallai kina Shan bacci da yawa. Haka kikeyi kenan a gidan naku bakya taya Auntyn naki aiki ? Sanam tayi Murmushi tana cewa " Mummy to mezanyi akwai 'yan aiki fa , Mummy tayi Murmushi itama sannan tace "duk da haka Yana da kyau kidunga shiga kitchen kina ganin yadda akeyin aikin girki , inkinje gidan ki ai dole kiyiwa Mijinki girki da kanki , Sanam tace " Mummy shi ma sai yaci na 'yan aikin kawai , Daddy ma girkin 'yan aiki yake ci Dan Mummy Bata shiga kitchen sosai ,.
Murmushi Hajiya Maimuna tayi cikin zuciyar ta tana tuno yadda Alhaji Abba keyi " duk ranar girkin Hajiya Nafeesa saiya ci ya k'oshi a gidan ta sannan yake tafiya , Dan akan hakan sunsha fad'a dashi tace Masa yatafi gidan sa yaje yaci abinci tunda ba girkin ta bane , yakance Mata shi bayajin dad'in girkin kowa indai bana taba , ko tafiya yayi yabar k'asar kullum saiya Mata k'orafin baya iya cin abinci sai su cheefs da coffe ,. Tabbas dole ta tashi tsaye wajen koyawa Sanam girke girke , mutuk'ar mace ta iya girki to ta hau mataki casa'in da tara a cikin matakan zama lafiya da miji ,
Kiran wayar ta da akayi yasa tadawo daga tunani data tafi , d'agawa tayi suka gaisa sa Huneed , Nan yake sanar Mata yasamu nasarar Fara gano Wanda suka musu wannan abun , gashinan Yana hanyar zuwa gidan yanzu haka , Mummy tace " to Alhamdulullah sai kazo , kashe wayar tayi sannan ta dubi Sanam tace " ga Huneed Nan yataho Yana hanya kishiga kitchen keda murja kuyi Masa jallof rice akwai komai a Frizer , Sanam tace " to sannan ta mik'e ta nufi cikin kitchen d'in.....
Hajiya Nafeesa ta dubi Fahad sannan tace " nagaji da halinka na d'aukarmin Motar kufita yawo kaida wannan shegiyar mara galihu , duk inda kukabi indai mutanena sunga motar sai sunkira sunce yanzu na wuce , Fahad yace " Aunty Dan na d'auki motar ki na fita shine abin magana ? to kisa Mijinki ya canza Miki wata sai kibarmin wannan Kinga shikenan , Hajiya Nafeesa ta kalleshi da wani mugun kallo tace " lallai Fahad to ko canzamin motar Alhaji yayi kana ganin zanbar maka wannan ne ? Duk maganganun da sukeyi Maryam na lab'e tana jinsu tunda ga farko , k'ara kasa kunne tayi tanaji Fahad yace " ashe akwai abinda zaki iya hanani Aunty ? Hajiya Nafeesa cike da k'osawa da maganar Fahad tace " Dan Allah kafita Ina buk'atar hutu , tana cewa haka tashige can cikin d'akin ta tabar Fahad tsaye bashi da tacewa , ...
Shima fitowa yayi daga d'akin Yana meyin k'wafa , karo sukaci da Maryam ta kafeshi da idanuwa tana kallon sa , shima ita yake kallo da yimata alamar taji duk abinda suke cewa ? Nan Maryam tayi Murmushi mugunta sannan tace " naji komai kawai ka k'yaleta zamuyi maganinta kabari na haihu , Fahad yace " haba Merry har saikin haihu ma za'ayi maganin ta kawai ki nemo Mana mafita ,.
Maryam tace " kabani Nan da kwan biyu zan tsara Mana yadda zamuyi Mata .......
Huneed Yana zuwa bayan sun gaisa da Mummy ya kunna Mata Muryar Isma'il wacce yayi record a waya , komai sai da Mummy taji Nan tashiga salati tare da jinjina lamarin , tabbas mak'iyi abin gudune , kuma d'an Adam butulune yanzu ita Diyana da Wanda ta amincewa dashi aka had'a baki aka sa Mata k'waya a lemo tayi bacci , Sanam ce ta fito daga cikin kitchen tana turo baki , Huneed ya zuba Mata muyin idanun sa ko k'iftawa Babu , Mummy ta kalli Sanam d'in sannan tace "lafiya ke kuma kike turo baki haka ? Mummy Wallahi girki akwai wuya nidai kawai kicewa Murja ta k'arasa nagaji dayawa , Huneed ji yayi kamar yatashi ya rungumo ta yadunga juyata a cikin palorn , wani kyau yagani tayi na musamman lallai inyasamu Sanam yagama cika burinsa na duniya ,. Kwata kwata ya manta a inda yake ya kafeta da idanuwa sai kallo yake ita kuma tamkar wacce Bata gansa ba sai wani narkewa take tana zabga wa Mummy shagwab'a , sai da Mummy tayi gyara murya sannan Huneed yadawo sai dai Yana sosa k'eya , Mummy tace " wannan budurwar taka zaka sha fama sosai batason aiki ko kad'an yadda na Fahimceta , Murmushi Huneed yayi sannan yace " Mummy sai anemo Mana masu aiki Dan Nima bana so tasha wuya , Nan Sanam ta zauna kusa da Mummy suka shiga gaya Mata abinda yafaru , take Sanam taji jikinta ya kumayin sanyi akan abinda tayiwa Diyana , Nan suka shiga tattaunawa har number Maaryam da ya anso sai daya Gaya musu , take suka yanke cewar yasa sabon layi yakira number Dan asan yadda za'ayi su kamata , ....
Take Huneed yasa sabon layi a wayar sa ya dannan Number Maryam , sai data kashe ya kuma Kira sannan ta d'aga , Babu sallama Babu komai tace " waye ne yake neman damuna da tsakar ranar Nan haka ? Huneed a hands free yasa wayar Nan ya dubi Sanam da Mummy suka Masa alama da yayi magana ,. A hankali ya furta aminci agareki barka da hutawa sarauniyar Mata ,. Kallon Sanam yayi wacce ta runtse idanu tana kauda kanta gefe , tabbas shima ba haka yaso ba Dan dai kawai Mummy tace yaje Mata da sigar soyayya wannan ne kawai zaiyi nasarar sanin inda take ,. Maryam tace " yauwa barka kadai sai dai bangane waye ba , Huneed cike da jin tsanar ta aransa yace " Masoyine Wanda yake mafarkinki a Koda yaushe , inafata Zaki amshi tayina dan ba wasa nazo ba , Maryam tace " haba Oga banganka ba bansan ya kake ba kawai sai na karb'i tayinka , kabari muga juna sai muyi ciniki inka siya da tsada saina sallama maka , Huneed cike da k'osawa da maganar Maryam yace " ok to a inah zamu had'u Ni a shirye nake ? Maryam tace " kazo ka d'aukeni a Area 11 Estate d'in gidan Makama gida me No. 13 anjima bayan sallar Magriba , tuni Sanam ta zabura tana mik'ewa ta dubi Huneed da Mummy tace " gidan mu fa kenan , anya kuwa wannan tasan me take fad'i kodai mistake address tafad'a ? Mummy shuru tayi tana mamaki to wannan wace yarinya ce haka take neman Yarinyar ta da sharri , tabbas wannan address d'in gidan Hajiya Nafeesa ne to wacece wannan d'in ? Huneed ne yayi magana da cewa " ku kwantar da hankalinku koma wacece yau shirinta yazo k'arshe Dan tabbas saina kamata kuma zata gayawa aya zak'in ta ,. Ai abun yazo da sauk'i tunda har tayi saurin amincewa Dani komai yazo k'arshe ,. Nan suka shiga zantawa tare da yin al'ajabi akan wannan abin.....
Maryam tana kwance kan katifa tana Danna wayar ta. Cikin zuciyar ta tana tunani tagaji da rashin kud'in Nan da take fama dashi , ta fuskanci Hajiya Nafeesa ba ta Bari aci kud'inta , dole tadunga fita tana barikinta Dan tasaba da rik'e kud'ad'e a hannun ta , Fahad d'in ma bawani kud'i yake samu ba Dan ko sigari in zaisha itace ke siya Masa wani lokacin , haka za'a ajiyeta ba'a Bata manyan kud'ad'e tabbas baza ta sab'u ba Dole ta fita ta nema , addu'a tashiga akan Allah yasa wannan da sukayi wayar me kud'ine sosai yadda zai jik'ata da nera , tasowa tayi tafito palor Dan tasamu abinda zataci , tana fitowa tasamu Hajiya Nafeesa da wata k'awar ta suna maganar ta , Hajiya Nafeesa tace " Wallahi Hajiya Harira tana haihuwa zansa a kasheta. , tabbas indai har nabarta a raye to tabbas barazana ce ga rayuwata ,
[9/27, 14:27] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 44.
Maryam dake lab'e tana jinsu take jikinta yashiga rawa , lallai rashin Imanin Hajiya Nafeesa yayi yawa , tsayawa tayi taci gaba dajin su ...
Hajiya Harira ta nisa sannan tace " hakan kawai zakiyi domin wannan yarinyar mutuk'ar kika barta to sai ta tona Miki asiri , Hajiya Nafeesa tace " ai shiyasa na fad'a miki barin ta tamkar tonuwar asirina ne , Nan suka shiga tattaunawa akan yadda zasuyi da Maryam inta haihu ,...
Maryam tana gama ji ta koma cikin d'akin tana Kai kawo , wato tana haihuwa tagama musu amfani kashe ta zasuyi , to kafin akai ga hakan itama zata tona asirin Hajiya Nafeesa , me take k'aruwa dashi a wajen su Daman kawai kwana cikin ac da kuma cin abincin lafiyayya Wanda tana gidan suma shi takeci ,. Tana da samari kuma suna Mata duk abinda takeso Dan haka me zai dameta , gobe zataje a zubar Mata da cikin jikinta Amman kafin lokacin dole sai tasamo number Alhaji Abba Dan ta Gaya Masa duk irin makircin da Matar sa keyi ,.......
Huneed ya d'auko Sanam ya kawota gida , sai dai bai shiga ciki ba saboda Kar Shirin su ya b'aci ,. Ajiye ta yayi ta shiga Dan tanason d'ebo kayan sawar ta ta dawo gidan Mummy , a yanzu haka hankalinta kwata kwata yafita daga gidan Mummy Nafeesa tafison gidan Mummyn ta , tana shiga masu aikin gidan suka shiga gaidata ta amsa ba yabo ba fallasa .....
Tana shigowa palor tasamu Hajiya Nafeesa ita da Hajiya Harira suna hira ,.Hajiya Nafeesa tana ganin Sanam cike da kissa tafara cewa " oyoyo my luvly Dauther nayi missing d'inki , Sanam tayi Murmushi tana k'arasowa kusa da Hajiya Nafeesa tace " Some 2 U my Mummy , Nan ta dubi Hajiya Harira tahad'e ranta , batason ganin Matar Nan a gidan su duk wani Abu itace ke koyawa Hajiya Nafeesa ,. Hajiya Harira ta yak'e baki tana fad'in " Hajiya Sanam 'Yan Mata ya kike ya karatu ? Sanam batare da ta dube ta ba tace " lafiya sannan ta nufi Sama tana cewa " Mummy Bari na fito Bata jira abinda Hajiya Nafeesa zata ce Mata ba ta haye sama abinta...
Tana hayewa sama Hajiya Harira ta dubi Hajiya Nafeesa tace " wannan yarinyar taki kwata kwata bata da mutunci , kidubi kiga wani banzan kallo data keyimin , Hajiya Nafeesa tayi Murmushi sannan tace " a haka ma Wai kura tayi lafiya tunda wannan shegen yaron ya d'an canza ta , da dane wallahi ko kallo baki ishi Sanam ba ke kinsani , Hajiya Harira tace " hakane kam to Allah ya kyauta , Nan suka canza hira wacce duka akan yadda zasuyi da Maryam ne..,...
Sanam rik'e da Trolly d'inta tafara sakkowa daga kan step a hankali tana yin waya , k'arasowa tayi tana cewa Hajiya Nafeesa " Mummy inaso zankoma Gidan Mummyn Twins inyi kwana biyu ,. Hajiya Nafeesa ta kalli Sanam cike da kissa tace " wanne laifin nayi Miki haka kikeson ki gujeni ? Sanam tayi Murmushi sannan tace " Mummy bakimin komai ba kawai dai inason zuwa , Hajiya Nafeesa tace " shikenan My luv duk yadda kikeso hakan za'ayi , ki gaidamin da Mummyn Twins d'in ki kuma ce musu nayi fushi , Sanam ta mik'e tana fad'in " zasuji Mummy sai munyi waya , Nan ta fice abinta suka ci gaba da waya da Huneed har ta k'arasa wajen da motar sa take.....
Sanam na fita Hajiya Nafeesa ta d'auki waya tashiga Kiran Alhaji Abba, kukan kissa ta sa Masa akan Wai Sanam ta had'a kayanta tabar gidan , a halin yanzu ma batasan Ina zataje ba Dan a buge taganta tashigo , Alhaji Abba hankalinsa tuni yayi mummunan tashi , Me Sanam takeson ta koma ? Angaya Mata gata wasane da zata zama haka , bai ga laifin taba tunfarko shine ya sakar Mata da yawa shiyasa take hakan , kashe wayar yayi yafara tunanin wa zai Kira , indai ya Kira Mummyn Sanam d'in yasan tabbas saita nuna Masa kuskuren sa akan tunfarko shine me laifi , .
Hajiya Nafeesa tayi Murmushi tana duban Hajiya Harira, itama murmushin tayi tana fad'in " gaskiya kin iya tuggu Hajiyata , Kinga kuwa wannan had'in da kikayi Mata a wajen uban nata zaisa ya tsaneta , Hajiya Nafeesa tayi wata dariya sannnan tace " Kinga yanzu baruwana da fargabar Kar Sanam taganni cikina baya girma , kuma yanzu zamuyi yadda mukeso tunda tayi gaba , ....
Bayan Sanam da Huneed suntafi ya biya da ita ta shopping , sai da ta zab'i abuwan da zatayi amfani dasu sannan ya dawo da ita gida.......
Bayan Magriba Huneed ya shirya cikin shigarsa ta babban Captain ya nufi k'ofar gidan su Sanam , Kiran wayar Maryam ya shiga bugu d'aya tamkar jira take ta d'aga , sallama tayi cike da kashe murya tace " Alhajina kardai kace min har ka k'araso ? Huneed yace " Kinga laifina ai ba'a sanya da zuwa wajen irinku , Maryam tayi Murmushi sannan tace " gani Nan fitowa kabani minty 2 kacal ,. Kashe wayar tayi sannan ta d'auki mayafinta ta fesa turare ta fito , aikuwa tayi sa'a palor Babu kowa tasa Kai ta fita daga cikin gidan baki d'aya , nesa kad'an ta hango motar Huneed tana ganin motar tasan tayi kamun Babban Alhaji tuni ta canza tafiya harta k'arasa ta buga murfin motar , bud'e Mata yayi tashiga tamaida murfi ta rufe tana fad'in " Alhajina gani naso gareka..... Cak bakinta ya tsaya ganin