Showing 54001 words to 57000 words out of 78990 words

Chapter 19 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3683

Huneed da Mummy suka san juna haka ? Duk tayaya tasan yayi tafiya harda k'arin girman da yasamu ? bamai amsa mata wanannan tambayoyin sai Huneed , wasan da Huneed yake da Twins d'in shiya dawo da ita daga tunanin datakeyi.........
[9/27, 10:06] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/












*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 36.




A hankali Sanam tacewa Hajiya Maimuna " Mummy ina yini , sosai Hajiya Maimuna taji abun kamar almara yau ita Sanam ta kira da sunan Mummy ? wani dad'i taji har cikin ranta tare da sakawa Huneed albarka dan tasan shine yabata wannan tarbiyar , amsawa tayi tare da cewa " lafiya k'alau muke dafatan kuma kuna nan lafiya keda Mummyn taki ? Sanam tace lafiya lau , Mummyn Twins kallon Huneed tayi tana me jinjina masa ta sigar lumshe idanuwa , murmushi Huneed yayi sannan yacewa Sanam " Aunty Sanam ga Twins suna mik'o gaisuwa , kunya ce ta kama Sanam ganin ko k'annan nata bata tab'a gani ba , da sauri ta matsa ta anshe macen wacce suke ce mata Amrah , tsayawa tayi tana kallon ta sai taga kamar su d'aya ita da Amrah , har dimple d'in da take dashi itama Amrah tana wangale mata baki taga ya lotsa , wata iriyar k'aunar 'Yar k'anwar ta ta taji ta kama ta , sumbatar ta tashiga yi tare da yi mata wasa , cike da so da K'auna Hajiya Maimuna ke duban Sanam d'in , cikin zuciyar ta tana fad'in " dama ace zasu dauwama a haka batare da Sanam tayi nisa dasu ba , ta shagala da kallon Sanam d'in wacce ta ware take ta wasa da Amrah har da mata wak'a , shima Huneed d'in kallon ta yake cike da jin dad'in yadda Sanam ta bashi had'in kai wajen faran ta ran Mummyn nata , wayar ta ta d'auko a jaka tashiga d'aukar Amrah video tana mata wasa , Hajiya Maimuna tana ganin haka ta tashi ta nufi sama dan ta d'an basu waje , bakin ta har kunne sai saka wa Huneed albarka takeyi ,...


Aikuwa tamkar jira Huneed yake ta tashi ya matso kusa da Sanam shima yafara d'aukar su a waya , Namijin shi kuma ana kiran sa da Ameeer , tuni Sanam ta ajiye Amrah tana fad'in " My Sojana bani Ameeer d'in shima , mik'a mata shi yayi tashiga kallon sa shima , sosai yafisu kyau ita da Amrah dan yaron ya had'u , bai kaisu haske ba amma kyansa abin kallo ne ya had'u , Sanam ta had'asu duka ta rumgume tana cewa yimana pic in d'ora a social media nima aga k'anne na , murmushi yayi yana duban ta sannan yace " ai baza a yadda k'annan ki bane , duban sa tayi da alamar tambaya ? ea mana ai sai dai ace 'Ya'yanki ne tunda ai kin isa haifar su , dariya tasa tana duban su Suma tamkar sunji me akace suka fara wangale mata baki , tuni Huneed ya shagala da kallon su yafara musu video , bayan kamar minty 20 Hajiya Maimuna tadawo hannun ta d'auke da tire , dambun naman kaji ne aciki tazo ta ajiye musu , ta kalli Sanam tace " in kuna buk'atar wani abun ki shiga kitchen ki dafa muku , ni yau tuwon semo nayi miyar yauk'i kuma nasan ba lallai kuci ba , Sanam tace " a k'oshe muke Mummy dambun naman ma ya isa , dama Mummy tasan Sanam din tana son damun nama , dan wani lokacin tanaji in suna waya da Daddyn ta zatace ya siyomata dambun nama , duk abinda Sanam ke so Hajiya Maimuna tagama sanin shi , tuni tafara cin dambun naman hannu baka hannu k'warya.....
Huneed duban ta yayi yana dariya yana fad'in " ci a hankali mana Madam , murmushi tayi sannan a hankali tace masa " bantab'a cin dambun nama me dad'in wannan ba shiyasa , sai wajen k'arfe goma suka bar gidan Mummyn Twins , Sanam cike da kewar Twins itama Hajiya Maimuna cike da kewar Sanam d'in .....




Hajiya Maimuna bayan ta dawo daga raka su Sanan jikin mota tad'au waya tashiga kiran Hajiyar ta , tana d'agawa tashiga bata labarin zuwan su Sanan d'in da komai da komai daya faru , Hajiya tashiga hamdala tare da cewa " lallai wannan yaron d'an Albarka ne , kuma shine wanda ya cancan ta yazama miji agare ta , nidama tun farkon ganina dashi naji ya kwantamin arai , ashe shine sanadin da zai dawo miki da farin cikin ki har gida , inaso kici gaba da addu'a tare da janyo yarinyar ki jikin ki a hankali , duk abinda kikasan tanason shi to ki dunga aika mata da shi da haka zaki jawota jikin ki , sosai Hajiya Maimuna tayi na'am da shawarwarin Hajiyar tata , nan sukayi sallama tana saka mata albarka.....




Sanam tun da suka taho baki yak'i rufuwa sai murmushi take , duban ta Huneed yayi sannan yace " Madam gaskiya indai mukayi aure kifara haifo mana Twins masu kama da su Amrah , Sanam tayi murmushi sannan tace " tamkar in dauwama ina tare dasu nakeji , gaskiya yaran sun shiga raina mutuk'a My Sojana , wlh da Mummy zata bani su tas zanyi mata rainon su , Murmushin dad'i Huneed yaji a zuciyar sa yace " anzo gurin , a fili kuma yace " taya Mummy zata baki su ko kin manta k'ananu ne basu isa abada su ba , in rainon su kikeso me zai hana bazaki dawo gidan Mummyn Twins d'in da zama ba , Sanam ta kalli Huneed sannan tayi shuru na wasu lokutan kafin tace " ai Mummy bazata bari nadawo ba , kasan ba shiri take da Mummyn Twins ba shiyasa , Huneed yace " in dai kinason rainon su kawai ki shirya ki koma gidan su , in kuma bazaki koma ba to kidunga zuwa kina musu kwana biyu biyu , ahaka zasu shak'u dake har sudunga ganeki inkinje , Nan Huneed yashiga yiwa Sanam dabara tare da cusa mata ra'ayin zuwa gidan Mahaifiyar ta ......


Tuni Sanam tasa pic d'in su ita da Twins ta rungumo su tana dariya , wasu tasa a status sai kuma ta zab'i guda d'aya wanda sukayi da Huneed da Twins d'in duka sunyi kyau ta d'ora a dp....
Hajiya Nafeesa tana chat da k'awayen ta manyan mata taga Sanam tayi status , mamakine ya kamata dan a iya sanin ta Sanam batayin Status , sannan pic d'in dake Dp ta yafi shekara uku tak'i canza shi , sai gashi yau taga tayi status tare da canza Dp , da sauri tashiga Status tafara dubawa k'irjin tane ya buga ganin Sanam rungume da k'annen ta a palor gidan su tana dariya , duk pic d'in data saka bawanda basuyi kyau ba ita da Twins d'in , tana duba dp nan ma sai da gaban ta ya fad'i , yaushe Sanam tafara son Mahaifiyar ta ? yaushe Sanam tafara zuwa inda Uwar ta take ? tasan ba wanda ya had'a wannan munafincin sai wannan shegen Huneed d'in , tabbas lokaci yayi dazatayi gaba da gaba dashi akan ya fita daga sabgar Sanam ,. Wani huci take tana kuma yin zoom d'in pic din tana gani , wato Hajiya Maimuna tana k'ok'arin yin nasara akan ta , to wallahi bazata sab'u ba dole takoma wajen bokan ta ayo musu farraqu me zafi........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/










*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 37.




Farin cikin dake d'auke a fuskar Sanam tamkar wacce aka yiwa tukuci da Aljannah , d'auke da murmushi a fuskar ta tadubi Huneed tace " My Hero bani da kalmar da zan furta maka wajen godiya , sai dai zanyi maka addu'ar Allah yabiya maka buk'atun ka na Alkairi , tabbas zuwana gidan mu yanzu yasa na fahimci lallai akwai Alaqa me k'arfi tsakanin ka da Mummy Twins , komai naka tasani hakan ya nuna min kazama d'an gida sosai da sosai , tunda na taso yaune karon farko da nafara ganin farin ciki d'auke a fuskar Mummy , Abinda yaban mamaki ko fad'an data saba yimin yau naga bayayi ba , lallai naji dad'in wannan yanayin kuma indai hakane daga yau zan dunga kawo mata ziyara kodan inga K'annena , Huneed cike da jin dad'i yace " ai dama Mummy Twins bata da laifin komai Bby , kece bakya zuwa ki gaida ta shiyasa takejin rashin dad'i , suna tafe suna hira wacce duk akan maganar zuwa gidan Hajiya Maimuna ce har suka k'araso gida......


Suna shigowa harabar gidan basu dad'e ba Huneed yayi mata sallama yatafi......
Sanam sai da taga fitar sa daga cikin gidan sannan ta juya ta nufi ciki , tana shigowa cikin palor tasamu Fahad da Maryam suna ta wasan banza , had'e fuskar ta tayi dan ta tsani wannan k'azamar rayuwar da sukeyi , zata wuce kenan Maryam ta mik'e da gudu tana kakarin Amai a karo na biyu , aikuwa Sanam ranta ya kuma b'aci dama d'azu da zata fita tayi mata haka wato shine yanzu ma zata kuma yi mata , to wallahi ko waye uban ta yau saita bar musu gida , a fusace Sanam tabi bayan Maryam har wajen k'ofar toilet , Maryam na fitowa tayi karo da Sanam ba wata wata Sanam ta shak'i wuyan Maryam d'in , cikin tsananin b'acin rai Sanam tace " meye a jikina da kike rainawa kan ki hankali in kika ganni ? d'azu da zan fita kinyi min haka yanzu ma kuma da nadawo sai ki kuma yimin , Maryam sosai taji shak'ar da tayi mata dan ko magana ta kasayi , gashi turaren sai kuma dukan hancin nata yake wani Aman na sake taso mata , Fahad ne ya k'araso da gudu dan ya kwaci Maryam , sai dai koda yazo Sanam bata cika ta ba sai marin fuskar ta take tana fad'in " wallahi sai kin fad'amin abinda kikewa Amai a jikina , Fahad yacewa Sanam " dallah cikata dan kinga tazo gidan ku shine kikeson tozar ta ta , Sanam da wani mugun kallo ta bishi sannan taci gaba da tambayar Maryam akan lallai sai tafad'a mata me tagani ajikin ta da take amai , hayaniya tayi yawa har Hajiya Nafeesa taji ta sauko , koda tazo da k'yar ta kwaci Maryam daga hannun Sanam , Maryam ana kwatar ta takuma shiga toilet da gudu tana shara amai , Hajiya Nafeesa ta kalli Fahad tace " meye ya had'asu haka ? Sanam ta ja tsaki tare da barin gurin dan bata da abin fad'awa Mummy ........
Fahad yabita da harara tare da kallon Hajiya Nafeesa yace " a gaskiya wannan yarinyar bata da mutunci , kawai dan Marry ta nufi toilet tana amai shine ta nufo ta tahau duka wai da ita take , Hajiya Nafeesa ta dubesa tace " tabbas akwai abinda Sanam take shirin yi , dan nima yanzu tagama bani mamaki wai itace yau harda zuwa gidan Uwar ta , yanzu nake shirin sakkowa na fad'a maka har status tayi ita da Twins d'in su , Fahad yace " tabb lallai kina Ruwa Aunty kina nufin kicemin Yanzu Sanam tafara son Mahaifiyarta kenan ? Hajiya Nafeesa tace " ga alama nafara gani kuwa , ba wanda yake had'a wannan muna funcin kamar shegen yaron nan , Fahad yace" kawai kibamu aiki akan sa wallahi zamu rabasu nida Maryam , fitowar Maryam daga Toilet yasa dukan su suka fara duban ta , Hajiya Nafeesa tace mata " sannu kinji kiyi hak'uri da abinda tayi miki , Maryam tace " babu komai Hajiya koni ce abinda zanyi kenan , kuma wallahi turaren data sane bayamin dad'i , inajin sa sai naji Amai yatahomin shiyasa , Hajiya Nafeesa tace " cikin jikin kine bayaso tunda kinga masu ciki sunajin irin hakan , abinda nakeso dake kawai kidaina zama a palor gudun irin haka , kuma indai kina yin haka to lallai shirin mu zai lalace , dan Sanam tana da hankali dole zata gano akwai wani abu a k'asa , Maryam tace " zankiya ye dama ba sosai muke had'uwa da ita ba , Dawowa cikin palor suka zauna sannan Hajiya Nafeesa ta dubesu tace " Maryam inaso kiyimin wani aiki , Maryam ta dube ta sannan tace " fad'i ko wanne irin aiki kikeso zanyi miki , Hajiya Nafeesa tace " tunda kinsan wannan k'awar Sanam d'in inaso kiyi min aiki akansu , zan samo number Huneed da ita Diyana a wayar Sanam zaki had'amun su , Maryam ta dubi Hajiya Nafeesa tace " ki fahimtar dani ban gane me kike nufi ba ? Hajiya Nafeesa tace " inaso Kisan yadda za'ayi Huneed yaje k'ofar gidan su Diyana , sannan itama Diyana ta fito wajen sa ayi musu hotuna a turawa Sanam yadda zamu saka mata tsanar su , nasan wace ce Sanam akan kishi mutuk'ar taga wannan pic d'in zata d'auka gaske ne , Maryam tayi wani shu'umin Murmushi tace " ki kwantar da hankalin ki wannan aikin ai me sauk'ine kisa aranki kamar anyi angama , murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " yau Jarumata shiyasa nake yinki saboda kaifin basirar ki , Fahad yace " shiyasa kika ga na zab'o ta akan tayi mana wannan aiki dan ita kad'ai ce zata iya , nan wayar Hajiya Nafeesa tashiga k'ara ta mik'e tana barin gurin dan tayi waya da Alhaji Abba , .......




Sanam tana hawa sama toilet ta fad'a tayi wanka sannan b'acin ran nata yaragu , amman cikin ranta ta shirya ciwa Maryam mutuncin da har sai tabar musu gida , kayan baccin ta tasa ta haye gado tana me d'aukar wayar ta ,......


Hajiya Nafeesa tana d'aga waya tafara yiwa Alhaji Abba shagwab'a , tuni ya rud'e yana fad'in " kodai nadawo muyi rainon cikin tare ? murmushi tayi cike da kissa sannan tace " basai kadawo ba yallabai na , nafiso kadawo kaga bby boy kawai an haifosa , Alhaji Abba yace " haba Mummyn Sanam ayimin afuwa dai nadawo naganki da ciki , dan inaso naga yadda ciki zaiyi a jikin ki nasan zakiyi kyau sosai , Hajiya Nafeesa tuni tsoro ya cika mata ciki , cikin zuciyat ta tashiga fad'in "ina zanso kadawo ai asirina ne zai tonu mutuk'ar kadawo , maganar sace ta katse mata tunanin datakeyi " yanaji kinyi shuru ko da matsala ne ? da sauri tace " babu matsalar komai Dear kayi zaman ka indai cikine zanyi maka video sa da kuma hotuna in turo maka , murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " shikenan ai daman cikin bayaso nagansa tunda saida ya koreni sannan yazo , haka suka ci gaba da hirar su kafin daga k'arshe suyi sallama.......






*Bayan kwana biyu*
Maryam bata k'ara yadda sun had'u da Sanam ba , itama kuma Sanam d'in bata bin takan su saboda karatun dayasha mata kai , kuma a wannan lokacin Hajiya Nafeesa tayi nasarar samo number Huneed da ta Diyana a wayar Sanam , tana samowa tasamu Maryam ta tura mata tare da ce mata tana jiran ta da kyakkywan result , ....
Maryam tuni ta shiya yadda zatayi aikin batare da tasamu matsala , unguwar su ta nufa sanye da nik'af tana zuwa tasamu wani me shago dake kallon gidan su Diyana , tana zuwa ta d'age nikaf d'in tana duban sa , Deeni yana ganin ta ya washe baki yana fad'in " Hajjaju Maryam ashe kina nan kwana biyu bakya lek'omu , murmushi Maryam tayi sannan tace " Ina nan Malam Deeni yagari ya yan gari inason muyi wata magana in badamuwa , Deeni ya washe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login