Showing 60001 words to 63000 words out of 78990 words

Chapter 21 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3687

tsaya kayi aikin da kaje insha Allah komai aka ƙullah to tabbas xai kwance , nan ta shiga kwantar masa da hankali tare da ƙarfa fa masa gwiuwa da kuma ƙara tunasar dashi akan yayi addu'a , sosai Huneed yaji kaso tara a cikin goma na daga cikin damuwar dayake yaragu , tabbas Mummyn Twins Uwa ce da kowanne Ɗa zaiyi Alfaharin samun ta , sallama sukayi ya kashe wayar ya koma bakin aiki........


Sanam kuka take sosai a haka bacci ya kuma a wan gaba da ita ,
. Washe gari tana farkawa ta tayi wanka wajen shaɗaya ta sauko da mukullin mota a hannu , lokacin Hajiya Nafeesa tana zaune ita da Maryam suna yin break fast , koda Sanam ta sauko Hajiya Nafeesa ta shiga yi mata murmushi tana faɗin " zonan my luv , Sanam taje Hajiya Nafeesa ta rungume ta tana faɗin ' kicire komai a ranki ki rabu dasu , kinga in kikasa damuwa a ranki to tabbas zaki wahalar da kanki a banza ne su kuma ba ruwan su , ni da zaki birgeni ma da kinfara kula Jaydeen kema dan ki nuna musu kema daman da wanda kikeso , nan Hajiya Nafeesa tashiga turawa Sanam Jaydeen ta ƙarfi da yaji wai dan ta ɗauki fansa , Sanam kwata kwata Jaydeen ba birgeta yake ba dan baya ɗaya daga irin mazan datake so , ganin inbata amincewa Mummyn nata ba zatai ta damun ta , dan haka tace tabata kwana biyu inta huta zata yanke yadda zatayi , tana cewa haka ta fice daga palor zuwa harabar gida, ....


Tana fita tahau motar ta ta nufi gidan su Diyana , tabbas zataje tayi mata rashin mutuncin da bazata manta da itaba a rayuwa........
[9/27, 14:26] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/








*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








_Alhamdulillah Allah yayi min dawo wa , ina mutuk'ar godiya gareku masoyana ta yadda kuka nunamin kauna tare da addu'oin ku gareni , naga yadda kukayi kewata sosai😊😊 nima nayi kewarku dayawa Allah yabarmu tare_ ❤️❤️🙏🏻🤝




Chapter 40.




Hajiya Nafeesa murmushin samun nassarar raba Sanam da mutane biyun data tsana,


Yanzu tasan komai zatace da Sanam zatayi tunda tarabata da masu zugata, burinta guda d'aya yarage a yanzu shine, taraba Sanam da Mahaifinta Alhaji Abba.....




Sanam na isa k'ofar gidan su Diyana tayi parking din motar ta tafito , tsayawa tayi tana kallon k'ofar gidan tare da tariyo video da tagani a idanuwanta, wani kishine yakuma taso Mata tamkar mahaukaciya haka ta nufi cikin gidan su Diyana....


Tana shiga tasamesu suna zaune suna hira su dukansu a cikin palor, Sanam ko sallama batayi musu ba ta tsaya a bakin k'ofa tanawa Diyana wani mugun kallo, Diyana d'auke da murmushi a fuskar ta tace " 'Yar halak yanzu nagama maganarki , Sanam cike da takaici tace "ai dole kiyi maganata maci amana wacce bata gaji arzik'i ba , duk mutanen da suke zaune a wajen suka shiga kallon Sanam tare da mamakin jin abinda ya fito daga bakinta , Diyana jikinta har rawa yake tana duban Sanam, a hankali ta furta " Sanam ni kike kira da maci amana wacce bangaji arzik'i ba? A fusace Sanam tace " nakiraki da hakan kiyi maganin abun , wallahi Diyana kinban mamaki ashe ked'in fuska biyu gareki , Kirasa Wanda zakiyi soyayya dashi sai Huneed, kuma kinfi kowa sanin matsayinsa a wajena , to anyi walk'iya naganku keda shi dan haka babu ni babu Ku munafukai kawai , tana cewa haka ta juya ta fita hawaye cike a idanuwan ta........
Tabbas Sanam ba iya maganar dataje zatayiwa Diyana kenan ba ,sotayi ta gasa mata maganganu Amman ganin idanun Umman Diyana yasa Sanam takasa, tana fitowa ta koma cikin motar ta zauna ta d'ora kanta kan sitiyarin tasaki kuka me cin rai , duk duniya bata da wata k'awa da suka shak'u kamar Diyana , sannan bata da wanda takeso take mafarkin rayuwa dashi kamar Huneed, Amman meyasa sukayi Mata haka ? ta dad'e tana kuka kafin taja motar ta tabar Unguwar su Diyana......


Diyana tunda Sanam ta fita take tsaye tana maimaita kalmomin data kirata dasu, Umman su Diyana ta dubi Diyana wacce kowa ita yake kallo tace " Diyana me kikayiwa Sanam haka tabbas ba haka take ba dole akwai abinda kikayi Mata , kuma koma meye akan saurayine tunda gashi tafad'a , Hawayen da Diyana take ta Rik'ewa sune suka gangaro kan kuncinta, cikin muryar kuka Diyana tace "Umma wallahi kwata kwata bansan laifin da take tuhuma ta dashi ba , Umma kinfi kowa sanin halina bazan tab'a cin amanar Sanam., shuru Umman tayi dan tabbas tasan halin Diyana , bazata tab'a kula saurayin Sanam da sunan soyayya ba , inajin dai so ake arabasu Dan anga suna son junan su da gaskiya , Diyana d'aki tashige saboda kukan da ya kufce Mata ....


Sanam tana tafe cikin motar ta kiran Huneed sai shigowa yake amman ko kallon wayar taki yi , daga k'arshema kashe wayar tayi Dan ko kad'an batason ganinsa, jitayi batason komawa gida tasamu kanta da son zuwa gidan Mumyn Twins wato Hajiya Maimuna mahaifiyar ta....
Hanyar Estate d'in su ta nufa dan tanason inda zata samu Hutu nawani lokacin.....




A b'angaren Huneed kuwa hankalin sa tuni yagama tashi , Kwata kwata yakasa aikin da sukaje yi, Gashi kusan shine jigon tafiya Dan shine babba a gurin kowa umarninsa yake bi, jiyayi yana muradin ganin Sanam a yau basai gobe ba, tuni yafara shirin tahowa birnin tarayya wato Abuja.......




Sanam tana isowa tayi parking tafito tashiga cikin gidan nasu, tana bud'e k'ofar palor wani k'amshi ya bugi hancinta ,samun kanta tayi da lumshe idanunta tanajin nauyin da zuciyar ta tayi yana raguwa, sallama tayi duk da babu kowa a cikin palor, zama tayi a d'aya daga cikin kujerun da suka k'awata palor , banda k'arar ac babu abinda ke tashi acikin palor , tafi minty biyar a zaune saiga Hajiya Maimuna suna sakkowa daga step d'in benen cikin palor, ganin Sanam sukayi zaune tayi tagumi hannu bibbiyu tayi nisa cikin tunani , mamakine yakama Mumyn Twins. Yaushe Sanam tashigo cikin gidan har take zaune a haka ? Suna gama sakkowa ta mik'awa murja twins tace mata " kuje wajen motor ganinan , da yake fita zasuyi dubo Hajiyar ta batajin dad'i , har Murja tafice daga palor Sanam batasan anayi ba, dafa kafad'ar Sanam Hajiya Maimuna tayi , firgigit Sanam tadawo daga dogon tunanin da tatafi , murmushi ta k'ak'alo kan fuskar ta tana fad'in "Mumy ina wuni ya gida , cike da kulawa Mumy ta amsa tare da tambayar ta su Hajiya Nafeesa, Sanam tace lafiya lau suke , shuru sukayi nawani lokacin kafin Mumy Twins tace "meke damunki haka naga kinyi shuru kina tunani ko akwai wani Abun ne ? Sanam tayi k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannun ta , Mummy tana ganin haka tasan akwai damuwa a tare da Sanam kuma tana buk'atar a rarrasheta , kallon idanunta kawai tayi tagano irin Jan da sukayi saboda kuka, sosai Hajiya Maimuna taji tausayin 'yar ta yakamata , cikin sigar kwantar da hankali Mummy tace " ki hau sama kiyi wanka akwai abinci kid'iba kici sai ki kwanta ki huta , nima zani duba Hajiyar mu batajin dad'i , Amman bazan dad'e ba zandawo tunda ba a kwance take sosai ba , Sanam ta amsa da to tare da cewa tayiwa Hajiyar sannu..........
[9/27, 14:27] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️






*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/








*Bisimillahir Rahamanir Rahim*










Chapter 41.




Mumyn Twins na fita Sanam ta mik'e ta haye sama , tana shiga cikin d'akin taji wani k'amshi ya daki hancin ta me saka nutsuwa , komai a gyare tsaf tamkar ba mai shiga cikin d'akin , toilet ta shiga wanda yake agyare tsaf sai k'amshi yake fitarwa , had'a ruwan wanka tayi tashiga tafarayi tana lumshe idanu ,


Acikin kashi d'ari na damuwar yanzu babu arba'in , tabbas ta yadda Uwa Uwa ce ita kad'ai tana samarwa da 'Ya'yanta nutsuwa, kawai yanzu abinda ke damunta shine tunanin Huneed wanda yakasa barin zuciyar ta ta huta , tabbas ko mafarki tayi akace mata Huneed zaici amanar ta to tabbas zata k'arya ta wannan mafarkin , amman sai gashi a gaske abin yafaru wai Huneed d'inta wanda take burin rayuwa dashi shine yake bin k'awarta harda rungumo ta jikinsa, runtse idanu tayi tamkar yanzu take ganin hoton abun.....


Ta dad'e acikin ruwan wanka sannan tayi wankan tafito , kitchen d'in cikin d'akin tashiga dan ta had'a ko ruwan lipton ne tasha, don batajin zata iya cin abinci acikin nan nata , tana dubawa taga akwai ruwan tea a flast da kuma Samosa a jiye itama, d'aukowa tayi tafito ta dawo d'akin ta zauna tafara ci......






Tuni Huneed ya sauka a garin Abuja ko gidan su bai nufa ba ya nufi gidan su Sanam, yana zuwa me gadi ya sheda masa Sanam tafice bata gida, juyowa yayi gidan su Hajiyar sa na Palor suna hira da me musu aiki Huneed yayi sallama, kallo d'aya Hajiya tayi masa tasan ba lafiya ba , gaishe ta yayi sannan suka gaisa da meyi masu aiki, d'akinsa ya nufa batare daya kuma magana ba ,


Hajiya mik'ewa tayi tabi bayansa dan tasan lallai ba lafiya bace tadawo da Huneed , aikuwa tana shiga tasamesa ko takalmin k'afarsa bai cira ba 'ya kwanta akan gado yayi rubda ciki....


Hajiya tasamu waje gefen gadon ta zauna tayi gyaran murya kad'an , cikin nuna kulawa irin ta mahaifiya tace " lokacin dawowar ka baiyiba kuma naga damuwa akan fuskar ka inason insan meye yake damun Babban Soja , Huneed ya mik'e a Hankali ya zauna yana duban Hajiyar tasa , tabbas bashida wanda yafita a duk duniya , kuma komai zaiyi saiya nemi shawarar ta kuma kome yake damunsa itace tafarko a duniya dayake gayawa , nan take ya sheda mata duk abinda yake faruwa tsakanin sa da Sanam tundaga kiran wayar k'awarta har izuwa yanzu ,
Tamkar zaiyi kuka yace "Hajiyar mu yanzu haka Sanam bata d'agamin waya , wani lokacin ma inna kira wayar kashewa take , shuru Hajiya tayi nawani lokacin sannan ta d'ago da kanta tana duban Huneed , akwana biyu duk yarame ya canza tamkar bashi ba , tabbas tasan Huneed yanason Sanam sosai , dan haka itama take k'aunar Yarinyar duk da bata tab'a ganin ta azahiri ba sai a hoto , dafa kafad'ar shi tayi sannan tace " Tabbas wannan shiri ne aka shirya muku kaida ita , duk wannan abun anyini dan arabaku kuma gashi wad'an da sukayi suna neman yin nasara akan ku , abinda nakeso dakai a yanzu shine kabi komai a hankali zaka kamo bakin zaren , kuma ka zama ja jurtacce kar kabawa mak'iyanku k'ofah da zasu samu nasarar rabaku , yanzu katashi kayi wanka kazo palor kaci abinci sai kakoma gidan nasu ko tadawo yanzu , Huneed ya ya mutsa fuska yana cewa " bazan iya cin komai ba Hajiyar mu mutuk'ar ba Sanam nagani ba , Murmushi Hajiya tayi sannan ta mik'e tana fad'in " lallai Sanam zankamata da laifin horon mu da Yarona datayi , Soja guda yana neman zama sullutu , maza kayi wanka kasameni a Palor inyaso ko zancen nema sai naraka ka , sosai Huneed yasamu saukin damuwarsa , dama duk wata damuwa yana zuwa da ita gaban Hajiyarsu take masa maganin ta , tabbas shima ya yadda wannann shirine aka shirya musu shida Sanam dan A rabasu , amman tabbas zaibi duddugi harya gano wanda yayi musu wannan shirin Sai ya d'an d'ana kud'arsa.....


Mik'ewa yayi yashiga toilet dan shima yanaso yaji sanyi ko yayane ajikinsa,.....




Sanam tana gama shan tea da samosa bacci yayi awon gaba sa ita,..


Mumyn Twins tunda taga jikin Hajiyar ta da sauki sosai take shirye shiryen tahowa gida , Hajiyar ta ta kalleta tace " wai Maimunatu naga sai sauri kike ki koma gida ko Alhaji Abba yau zai dawo ne ? Mumyn Twins jitayi tanajin nauyin cewa Hajiyar ta Sanam ce tazo gidan takeso takoma , Murja me kula dasu Twins ce tace " Auntyn su Twins ce tazo muka barota agidan shiyasa , Hajiya ta yi murmushi tace "Sanam ce kenan tazo gidan naku shine kuma kota biyoku taga jikinan nawa , Murmushi Mumyn Twins tayi sannan tace " da'alama ba zuwan dad'i tayi ba , dan yanayinta yanuna akwai abinda ke damunta , Hajiya ta nisa sannan tace " to maza kutashi kutafi dan kije kiji meyake damunta , tunda har kikaga tataho gidan ki to tabbas tana buk'atar kulawarki , Hajiya takuma nunawa 'Yar ta yadda zata janyo yarinyar ta jikinta har tadunga nuna mata dai dai, hala sukayi wa Hajiya sallama suka kama hanyar dawowa gida....




Sai Bayan sallar Magriba sannan Huneed yakama hanyar zuwa gida su Sanam , kafin 'ya fito sosai Hajiyar sa tayi masa nasiha tare da kuma k'arfa fa masa gwuiwa akan lallai 'ya jajirce kar asamu nasarar rabasu , dan haka da k'arfin gwuiwar sa ya nufi gidan su Sanam,


Koda yaje megadi yakuma sheda masa har wannan lokacin bata dawo ba , sosai Huneed yashiga mamakin inda Sanam taje haka har wannan lokacin ace bata dawo ba , yasan dai yau babu sch bare ace lacca taje kuma ko shopping taje yaci ace tadawo yanzu , tsayawa yayi jikin motar sa yana danna wayar sa , yafi minty 5 a tsaye ya hangi Fahad da Maryam sun nufo gidan hannu cikin hannu suna wasan banza ,
Huneed kafesu yayi da idanuwan sa yana nazarin su tamkar yanaso yagano wani Abu atare dasu , suna hangoshi suma sai da gabansu ya fad'i , dan yadda yake kallon su tamkar yagane sune suka had'a musu wannan shirin ,
Take suka tsaya suna Diri dirin juyawa su koma , Maryam dabara ta fad'o mata tace " kar mujuya yin hakan zai sa ayar tambaya akan mu , juyowa sukayi suka kama hanyar shiga gidan , da sauri Huneed ya dakatar dasu dacewa " dan Allah kutsaya zanyi magana daku , jikin su har rawa yake suka tsaya cak suna kallon sa , yana k'arasowa yabawa Fahad hannu suka gaisa sannan yace " dan Allah Sanam ina taje ance bata nan ? Wata ajiyar zuciya suka saki atare sannan Fahad yace " gaskiya bansan ina taje ba , sai dai koke Maryam kinsan inda taje ne ? Maryam tace " tun wajen sha biyu tafice na rana kuma bansan ona taje ba , nan Huneed yayi musu sallama yashige yahau motar sa yatafi.....




tunda Huneed yabaro k'ofar gidan su Sanam yasamu kansa da son zuwa gidan Mumyn Twins , yanaso suyi magana itama da ita ko zai samu sassauci a zuciyar sa , hanyar gidan ya nufa duk jikin sa a mace tare da tunanin inda Sanam take , gashi kwata kwata wayar ta bata shiga inyakira ce masa akeyi akashe take , har test ya tura mata amman bashi da tabbacin ma yaje tunda wayar akashe take......




Sanam bayan ta tashi daga bacci ta sauko k'asa tazauna tana kallo , bata dad'e da zama ba su Mumyn Twins suka shigo cikin gidan , sosai Mumyn taji dad'in ganin damuwar fuska Sanam ta ragu sosai , amsa musu sallamar tasu tayi tana musu sannu da zuwa , zama Mumy tayi kusa da Sanam tana cewa " ya gidan dafatan kinci abinci , Sanam tana ansar Twins a hannun Murja tana cewa Mummyn " naci amman yajikin Hajiyar dafatan dai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login