Showing 6001 words to 9000 words out of 78990 words
wayar tare dayin jifa da ita kan gado tana rik'e kai .......
Minty Goma na cika sai ga Diyana a gidan su Sanam tamkar Aljana , tana zuwa Sanam tafara bata labarin tun daga farkon Abinda Huneed yayi mata har izuwa yau d'in nan daya kafa mata wannan sharud'an , Diyana tace " inason sanin sunansa dakuma Number gidan su , Sanam tace " Sunansa Wai Huneed Abdallah number gidan su kuma wallahi bansan taba , sai dai inaganin in kika rik'e iya sunan ma yayi zaki samo min komai nasa , Diyana tace kibani 50 min. Zanfita induba miki cikin Estate d'in nan naku harda wajen sa , Sanam tace " hakan yayi dan sonake nayi shiri sosai akansa dan bazan k'yalesa ba tunda ya tab'oni , Diyana tuni ta mik'e dan fita nemo labari akan Huneed.......
Diyana na fitowa tafara duba cikin Estate d'in , duk k'ofar gidan dataga da megadi sai taje ta tambayesa ko yasan Wani Huneed Abdallah , sai da taje gidaje wajen guda hud'u kowanne yana baisan shiba , tana shirin buga gida na biyar sukayi karo da Hisham yafito daga k'ofar gate d'in gidansu , yana ganinta suka dubi juna Diyana tasakar masa wani shu'umin murmushi , k'arasowa tayi tana wani yauk'i sannan ta dubesa tace " dan Allah tambaya nakeyi ko Allah zaisa nadace ? Hisham yace " yi tambayarki ko Allah zaisa nasani , Diyana tace " ina neman wani Guy ne me suna Huneed Abdallah , dubanta Hisham yayi sosai sannan yace " Saurayin kine Kenan ? murmushi Diyana tayi sannan tace " ko d'aya wlh saurayin k'awatane shine ta aikoni gunsa kuma ni bansan gidan suba , nadai san a cikin Estate d'in yake shiyasa nake cigitashi ko Allah zaisa nagansa , Hisham yayi murmushi yace " ni ma bak'one a nan Unguwar sai dai kibari anjima zansamu me gadin gate d'in Estate d'in gaba d'aya na tambayesa ko zai san shi , Diyan cike dajin dad'i tace " yauwa nagode sosai kaga ka hutar dani , yanzu bari nabaka Number na inkasamu Labarin inda yake saika kirani , tuni Diyana tabawa Hisham number ta , dan ita kam tana ganinsa taji ya burgeta dan guy d'in yahad'u sosai , nan sukayi salama ta wuce tatafi Abinta , Hisham na tsaye har saida yaga b'acewar ta sannan ya juya yashiga gida.......
Diyana na dawowa tabawa Sanam labari duk yadda sukayi da Hisham , sai dai kwata kwata ta manata bata amshi number sa ba itace tabashi tata , gashi ko Sunan sa bata sani ba , dan haka suka zauna suna jiran kiran wayar Hisham ........
Koda Hisham ya shigo cikin gida tuni yakira Huneed , yana d'agawa ya sheda masa anzo nemansa kuma budurwa ce wai k'awar tace ta turota , Huneed yayi murmushi yace " kai me kake tunani akan haka ? Hisham yace " nidai bankawo komai ba nayi tunanin kodai ita wacce tazo nemanka d'in itace take sonka ? Murmushi Huneed yakumayi sannan yace " aikota akayi amman ba itace ba , kuma Bera ce ta saka ta tayi bincike akaina dan haka kabasu duk Abinda suke buk'ata indai basu wuce gona da iri ba , sai munsake waya kit yakashe wayar yabar Hisham rik'e da waya baki asake , yana bala'in mamakin Huneed da wannan halin nasa , tabbas zai iya cewa Huneed d'in d'an baiwane sosai acikin mutane.......
*Bana ganin Comment*π€
*Zantafi yajin aiki*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 5.
Har aka kira Magriba Sanam da Diyana basu ga kiran Hisham ba , k'arshe dai Diyana tayiwa Sanam sallama akan gobe zata dawo lallai sai ta nemo mata labarinsa......
Sanam sosai takeson sake ganin Huneed , dan ita komai nasa ya tsaya mata aranta , tabbas bata tab'a ganin mutum da bashi da tsoro ko kad'an ba irinsa , dan haka tanaso ko sau d'ayane ta bashi tsoro ta kuma nuna masa wacece ita......
Duk wani motsi na Sanam tuni Huneed yasa asaka masa ido akanta , dan haka ma yasan shirin su akan sanin waye shi ita da Diyana..
Washe gari Hisham ya kira wayar Diyana yace mata inta shirya a inah zasu had'u yabata labarin Huneed d'in , aikuwa tamkar anyi mata albishir da gidan Aljannah haka takira Sanam ta sheda mata , Sanam tace " kawai ki kawosa gidan mu cikin Garden sai muzauna anan yagaya mana , da wannan shawarar Diyana ta kira Hisham ta fad'a masa inda takeso su had'u , nan suka tsaida lokaci sannan sukayi sallama.......
Tuni Diyana ta iso gidan su Sanam dan bataso yazo bai sameta ba , suna zaune suna hira saiga kiran wayar Hisham akan ya k'araso , sawa sukayi aka shigo dashi tare da kai masa kayan motsa baki , yafi minty 10 dazama sannan yagansu sunjero sun taho suna hira abinsu , suna zuwa suka gaisa da Diyana , ita kuwa gogar sai wani shan k'amshi take ita ala dole tanajin kanta , Hisham ya dubeta yace " barka da hutawa Hajjaju dafatan kina lafiya , ata k'aice ta amsa masa da cewa lafiya , daga haka taja kujera ta zauna tare d fara danna wayar ta tamkar batasan damutane a wajen ba , murmushi Hisham yayi cikin zuciyar sa yana fad'in " tabbas wannan yarinyar bamai saita ki sai Yaya Huneed shine zai iya saita ki , a fili kuwa yace " to Malama Diyana nasamo miki labarin Wannan guy d'in da kika sani , Diyana tace " ina godiya sosai dan haka ina sauraren ka ......
Da farko dai Sunan sa Huneed Abdallah Ma'aji , Haifaffen garin Borno state ne acan yayi karatunsa tunda ga matakin primary har yakai ga kammala Digree d'insa , Mahaifinsa ya kasance Babban Soja a Barrack d'in Borno , su biyu iyayensu suka haifa dagashi sai d'an uwansa , Mahaifinsa Canal Abdallah Ma'aji yarasu a wajen wani yak'i da akayi lokacin a garin Barno , tunda nan Huneed yayi shirin maye gurbin Mahaifinsa , tashi farko dayatafi training yadawo da babban resure akan and'aukesa aikin soja , kuma yafito da babban matsayi yanzu haka Shima babban Canal ne , aiki ne yadawo dasu Abuja shiyasa yataho da Mahaifiyar sa dakuma d'an uwan sa , Huneed mutum ne me rik'o da Addini gashi da son zumumci , sai dai Akwai abubuwan da baya shiri dasu sune baya shiri da mutum me girman kai , baya shiri da mutum me wulak'anta Al'uma , sannan bayason mutumin da girmama na gaba dashi , miskili ne sosai inkinga dariyar sa to yana cikin 'yan uwansa ko kuma yana tare da mahaifiyar sa , bayason yawan tambaya ko kuma a dunga yi masa dariya , hakan na harzuk'asa sosai kuma yana son wasa da k'ananan yara , a b'angaren cima kuma mutum ne me son tuwon biski miyar taushe , yana son saka kaya k'ananu sannan duk Juma'a yana saka jallabiya , yanason k'amshi sosai yana shiri da dukkan mutum me tsafta da kuma k'amshi , wannan shine cikakken labarin Huneed Abdallah Ma'aji , sai dai kuma abinda ba'a rasa ba wanda bansani ba .....
Ajiyar Zuciya Diyana tayi tare da cewa " mungode sosai Hisham , Sanam tuni ta mik'e tabar wajen tamkar batasan da wasu mutane ba abinta , binta Hisham yayi da kallo yana fad'in tabbas akwai babban aiki atare da Yaya Huneed , Diyana ta dubesa tace " magana kakeyine ? yayi sauri ya mik'e yace " ni zan zo na wuce dan nasan lokacin da Hajiyar mu zata sha magani yayi , nan sukayi sallama da Diyana ya wuce yatafi abinsa ........
*Kuyi maneji*
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ πΉπ
[9/27, 09:37] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}* β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 6.
Diyana na shiga cikin gida tasamu Sanam a falor tana zagaye , tana ganin Diyana tace " tabbas dole asameshi da wannan halin ashe soja ne , to tabbas saina janyo masa ansallameshi daga wajen aikin dayake tak'ama dashi , tunda harya shigo rayuwata sai yagane bashi da wayo , nagode Diyana nasa miki dubu d'ari biyar a account d'inki kasha ice cream , tana gama fad'ar haka ta haye sama abinta , Diyana cike da murna ta fice abinta tana murnar samun kud'i........
Tundaga nan Sanam tayi sercing d'in Huneed a Social media , duk wani posting d'in dayayi sai data bi ta duba , tab'e baki tayi cikin Zuciyar ta tana yaba kyan halittar Huneed , samun kanta tayi da kafe shi da ido tana kallo saita ke ganin tamkar murmushi yakeyi mata , Wurgi tayi da wayar sannan a hankali ta furta Huneed zakasan nice nashiga rayuwar ka bakaine kashiga tawa ba....
Washe gari tuni motar Sanam data canza ta iso , nan tasha wanka tashiga tafara zagaya gari , ranar gudun datakeyi ya wuce ko wanne irin gudu datake , duk inda tayi saikaga kowa na neman hanyar tsira da ransa , a haka ta k'araso gidan su Diyana dan nuna mata motar ta , tana shigowa lokacin Diyana na fitowa daga cikin gidan su , sakin baki Diyana tayi tana kallon had'uwar motar da Sanam ke ciki , cikin ranta tace " arzik'i yayi arayuwa , Allah yabamu rabon mu mu inba dan muna shiri da Sanam ba banga dalilin da zai hanani auran Daddyn taba , dai dai lokacin Sanam ta fito cikin wasu d'amammun riga da wando tana sanye da glass a idonta , mukullin motar ta na hannunta sai karka d'ashi take tana taunar cingum , da gudu Diyana ta k'araso tana fad'in " wow congrat my k'awa kice motar ta iso , Sanam tayi murmushi tana duban Diyana tace " Zahra meyin gasa dani to wlh wannan motar ko Babanta baitab'a hawan irinta ba , Diyana tace " wace ita taja da me *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* ai duk kud'in Baban ta bai isa ya siyamata irin wannan ba , Sanam tace "kinshirya hawan ta ko ba yau ba ? da Sauri Diyana ta zagaya tana fad'in " wanne ba yauba yanzu ma haka dama ice cream zani sha , nan Sanam ta shiga taja motar dawani mugun gudu.......
Alhaji Abba yana zaune a falor sa yana cike wasu takaddu , Hajiya Maimuna ta sakko daga sama tana zabga k'amshi tamkar sabuwar Amarya , tana k'arasowa tace " sannu da aiki My Husbee , murmushi Alhaji Abba yayi yana duban Hajiya Maimuna yace " yauwa tauraruwar mata , samun waje tayi ta zauna tana duban sa sannan tace " inason magana dakai amman ina fatan kayimin kyakkyawar fahimta , Alhaji Abba yace " ina sauraranki ki fad'i duk abinda kikeson fad'a , Hajiya Maimuna tace " inaso dan Allah ka nemawa Sanam makarantar islamiyya kasata a ciki , yadda take tafiyar da rayuwar ta yakamata ace tana da ilimin addini ko Allah zaisa ta rage wasu abubuwan , Alhaji Abba yayi shuru yana nazarin maganganun Hajiya Maimuna , can ya nisa yace " kinsan a yanzu My Baby ta girmi zuwa makarantar islamiya , sai dai zanyi magana da ita muji yadda zatace , inta amince sai asamar mata akaita , dan kinsan tunda tadawo daga k'asar turkey tace hutu take buk'ata , amman zanyi mata magana duk yadda tace haka za'ayi , dubansa Hajiya Maimuna tayi sannan tace " Haba Husbee taya zakace sai yadda tace haka zakayi wai kaine ka haifi Sanam ko kuma itace ta haifeka ? Murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " bazaki gane irin son danakeyi wa Sanam ba , karki manta itace kad'ai 'Yar danake da ita a duk duniya sai kuma abinda yake cikinki , kinga kuwa wanda yake ciki bani da tabbacin samunsa ita kuwa tana doron duniya dole insota fiye da komai , Hajiya Maimuna tace " ban hanaka kaso Sanam ba amman inaso kasani yakamata kasan cewa ita fa mace ce kuma gidan wani zataje , mutuk'ar tana tafiyar da halayyar ta yadda takeso to tabbas bazata iya zaman aure ba , da sauri Alhaji Abba yadubi Hajiya Maimuna yace " dole saitayi auren ? inaso kisani mutuk'ar mijin da Sanam zata aura bazai k'yaleta tayi yadda takeso ba to wallahi sai dai ta zauna haka dan bana son ace antakurawa Rayuwa ta , wallahi Maimuna badan kece kika tsugunna kika haifi Sanam ba to wallahi zance kinq kishi da ita , kuma da yanzu kindad'e da barmin gida , wani tsaki yaja tare da d'ebe takardunsa dukansu ya nufi sama......
Hajiya Maimuna binsa tayi da kallo tana mamakin irin halin Alhajin , kwata kwata indai akan Sanam ne bashi da mutunci , zai iya rabuwa da kowa akanta ita kanta tasheda , saboda Sanam yarabu da ' Yan uwansa da dama a hankali ta furta Allah kasa sugane shi da 'yar tasa.......
Sanam da Diyana sunshiga gari sai faman wasa suke da motar , duk inda suka wuce sai anyi Allah wadai dasu , gidan su Zahra suka nufo dan nuna mata motar , lokacin Zahra na zance da saurayin ta Najeeb , ji sukayi anayin wani shegen hon. Me gigita mutane , da gudu megadi ya bud'e gate d'in aikuwa Sanam ta figo motar a guje tashigo cikin gidan , Zahra da Najeeb tuni suka mik'e tsaye ganin yadda aka shigo da motar da gudu tamkar za'a yo kansu , bin motar Zahra tayi da kallo dan tasan bata tab'a ganinta ba , kuma sannan Daddyn ta yana gida bare tace shine yayi sabuwar motar , kid'an dataji yana tashi tamkar anje club yasa tagane Sanam ce aciki , tuni taji ranta yayi mugun b'aci , bata gama tunani ba taga anbud'e murfin motar Sanam ce ta fito tana taunar cingum tamkar wata karuwa , d'aya gefe kuma Diyana nace tafito itama , dukansu bawacce tayi shigar mutunci ko wacce surar ta a bayyane take , wani kishine ya ziyarci Zahra dan tasan halin Najeeb sarai da son mata , musamman had'add'un mata irin su Sanam , Diyana ce tace " barka da hutawa Zahra dafatan munsameku lafiya , daman zuwa mukai mu nuna miki sabuwar motar da Sanam tayi , itama idan kinga zakisa Daddyn ki yasai miki to mukuma zamu kuma canza wata , dan kinsan *'Yar kishiya* anriga da antara mata ba Albashi suke d'auka ba , Zahra sosai taji zafin maganganun Diyana amman sai ta dake tace " *'Yar* *Kishiya* ina tayaki murna Allah yasanya Alkairi , ke kuma Diyana ai wanda ni ansan muna dashi kefa dakike binta kike maula , murmushi Diyana tayi sannan tace " dad'in abin nice nake maular ba Ubana ba , kuma inayin maular ne a inda nasan akwai abin bayarwa , Zahra zatayi magana Najeeb yace " sorry Baby ba girmanki bane , kishare kawai karki biyewa 'yar yaga riga , wani mugun kallo Sanam tayi masa sannan tace " waye 'Yar yaga rigar ? Najeeb yace " wacce take take miki baya mana , Sanam tace " ka gyara lafazinka tunkafin mu kunyata ka a gaban budurwar taka , tana gama fad'ar haka tashige cikin motar suka bata wuta sannan suka fice daga cikin gidan.......
*Zantafi yajin aiki tunda ba'ayin Commentπ*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Nagode sosai Mutanena da tarin addu'oinku , Allah yabar k'auna_
Chapter 7.